Chapter 3
by @ummubasheer
*_MAHASEEM_*
{ ```Heart``` ```Touching``` ```Story``` }
_NA_
*_UMMU_ _BASHEER_*
```HASKE``` ```WRITER'S``` ```ASSOCIATION``` ...💡
*Page 03*
```Mahaseem```Ce zaune kayan kwaliyya ne a gaban ta, Ta shafa wannan ta goga wannan, Ta dauki kwali ta damb'ara shi kan girar ta mai cika sai ya wani dankare, aka diga kwali a goshi da hanci, sai kumatu da kasan bakin ta duk tayi d'ige d'ige, ta dauki jambaki ja ta shafa a lips din shima yaji sosai gashi dama ta shafa powder yayi ranbad'au, madubi ta kalla tana murmushi tace"Ho ni, Ho ni aradu na hadu, nayi shegen kyau fah"
Inna Jummai dake lazimi ta kalle ta tace"Wai lafiyar ki qalau kuwa kike kwaliya da daren nan?"
Ajiye madubin tayi tace"Dandali zanje fah, kin manta dazu n fad'a miki"
"Dandali kuma Mahaseem, kinsan cewa na hana ki zuwa , kina y'a mace ace zaki fita da daddare, ke ko tsoron duhu da aljanu ba kya yi"
Turo baki tayi ta b'ata rai"kai Inna yanzu fah akayi isha'i, kuma ni banjin tsoro"
"Aiko ba inda zaki, kinyi kwaliya sai kace Aljana"
Kamar za tayi kuka tace"Nidai ba Aljana bace, kuma duk yan matan kauyen nan na fisu kyau"
Banza da ita Inna Jummai tayi can Mahaseem ta mik'e wai zata je bayi,tana fita kuwa tayi murmushi ta fara sand'a zata fita, tana kallon bayan ta, tazo gurin k'ofa taji taci karo da mutum arazane ta dago kai, wa zata gani, kawun tane a tsaye shigowar shi kenan sukayi karo, Tsawa ya daka mata"gidan Uban was zaki kike sand'a?"
Sosa keya ta fara"ehm...da..wai..zan..rufe kofa ne fah kawu"
Tsaki yaja Dan yasan karya take ai ko ya fatatake ta, ta wuce d'aki ta shiga tana ta guna guni, Inna Jummai tace"Ke Kuma lafiya, kika shigo kina magana ke kad'ai?",
Fashewa tayi da kuka tsabar takaici domin tayi zasu had'u da Indo a dandali, Inna Jummai tayi magana juyin duniyar nan taki kula ta a haka bacci ya dauke ta.
Washegari da safe bayan tayi sallar asubah ne Inna ladi ta tasa ta a gaba wai sai ta jawo mata ruwa a rijiya haushi duk ya ishe ta, ta tsani Jan ruwa da sanyin safiya, haka tana Jan ruwan tana guna guni, Sai data cika wata robar, tana gani Bibalo ta fito d'aki tana hamma ita sai lokacin ma ta tashi, kwafa Mahaseem tayi tace"yarinya zaki ci na jaki, a kanki zan rama, wato ke da ake so ba kya aiki koh"
Bibalo bata ji ta ba saboda suna da Dan nisa tsakani, bayan ta gama tayi wanka ta shirya cikin kayan makaranta dark blue wando sai farar riga da hijab fari iyakar gwiwa ta dauki jakan makarantar zata fita dakin Inna Jummai tace"ah ina zaki baki karya ba"
Tsaki tayi tana sa sandal tace"Kawai da sasafe a ishi mutum da massifa ga aikin tsiya sai kace wata jaka"
Inna Jummai tasan akan mai take mawa nan tace"hakuri za kiyi komi na rayuwar nan lokaci ne wata rana sai labari, ki bar ma Allah komi"
Mikewa tayi tace"Inna ki bari kawai nasan mai zanyi...yanzu bani kudin break"
Mika mata naira hamsin tayi tana mata addu'ar a dawo lafiya, har ta fita k'ofa ta dawo tace"Inna y'ar Akuya ta Dan Allah ki kular min da ita kinji"
Murmushi tayi tace"Mahaseem mai akuya karki damu maza yi sauri kar ki makara"
Wucewa tayi daidai zata fita taga kokon da Inna ladi ta dama shi kenan yana gaban murhu taje dauko sugar, kawai Mahaseem tasa k'afa ta kifar dashi ta fita da sauri tana dariya ai ko banza dai ta rama.
Bayan sun fito break ne Mahaseem ta kalli Indo da wata yar ajin su Lami tace "kai kuzo muje gidan headmaster mu samo gwaiba"
Da sauri Lami tace"Kutt aradun Allah ban zuwa, headmaster idan ya kama mu buga zamu sha"
Dungure mata kai Mahaseem tayi"Banza matsoraciya kawai, Indo zo muje kuma saura idan kin gani kice zaki sha , nasan ki da shegen kwad'ayi"ta kare tana jan hannun Indo, ita kanta Indo tsoro take amma tasan halin k'awarta yanzu sai ta daina kula ta akan hakan.
Sad'af sad'af haka suka shiga gidan da yake gidan cikin makaranta ne,Mahaseem ta kalli Indo"Ke Indo maza haye ki tsinko"
Zaro ido tayi"Tsoron hawa bishiya nake Allah kuwan"
B'ata fuska tayi"dallah can ki hau ki tsinko ko sai yazo ya ganmu ne"
Jiki na rawa Indo ta fara k'okarin hawa kwatsam sai ga Headmaster"Dama kune masu zuwa satar gwaiba koh?Allah ya kama Ku yau"
Indo da sauri ta tsaya tana rawar sanyi tsabar tsoro domin ta tsani duka, Mahaseem ma ta tsorata amma cikin tsiwa tace"Headmaster kaji tsoron Allah yaushe muke zuwa, yau nefa, kuma ma ai cikin makaranta ne nan duk cikin PTA dinmu za'a cire Idan ma munsha"
Takaici ne kama shi aiko ya tasa su a gaba har makarantar baiyi magana ba, Suna zuwa ya sasu Kneel down, ya samu bulala yayi musu biyar biyar masu kyau, Indo sai kuka take Mahaseem ko idon nan yayi Ja amma ko hawaye, aranta ko tunanin ya za'ayi ta rama take, haka suka koma aji ko karatun ma bata nutsu taji ba.
Bayan an tashi tana hanyar zuwa gida ita da Indo ta hango Bibalo rik'e da bokitin nik'a, dariya tayi tana zuwa daidai Bibalo ta kifar mata da nik'ar gaba daya kayan miyan ya zube a jikin Bibalo, ta fashe da kuka ta zauna a gurin.
Mahaseem ko jan Indo tayi suka bar gurin, Tana zuwa ta shiga gida da d'an wak'en ta, Inna Jummai dake tuk'a tuwo a tsakar gida tace"Mahaseem ke dai ba zaki dinga jin magana ba koh, sallamar fah"
Lokaci daya annurin fuskar ta ya dauke ganin tuwo"kai Inna meye haka kuma ya nake ganin Tuwo, gaskiya ba'ayi min adalci ba idan na zama shugaban k'asa zan hana yin tuwo a Nigeria "
Dariya Inna tayi"Allah dai ya shirye ki, idan ba kici ai sai ki siyo wannan taliyar yaran kici"
Da murna tace"yauwa innata shiyasa nake sonki, amma fah ba taliyar yara bace Indomie ake cewa"
"Oho dai tunda kin gane"
Bibalo ce ta shigo gidan da kuka wuff Mahaseem ta shige d'aki ta kulle, da sauri Inna Ladi ta fito jin kukan shalelen ta, nan Bibalo ta fad'a mata abinda ya faru rai a b'ace ta nufi bakin kofar tana cewa"Shegiyar yarinya, irin jaraba, yanzu ni kin raina ni a gidan nan koh, wato ana goya miki baya, fitinaniya"
Mahaseem ta window ta lek'o tayi gwalo tace"Ga fitinaniya nan Bibalo, mai kan kwakwa"
Habawa ai nan ranta ya kara b'aci tayi window harda daukar mucciya, da sauri Inna Jummai ta tare ta tana bata hakuri cewa karta biye ma kuruciyar Mahaseem ita ko massifa take tana cewa ai Inna Jummai ce take koya mata iskanci iri iri a gidan, ita dai aiki ta koma tana yi, tunda taga mahaseem tayi shiru, ita koh Uniform take cirewa tana dariya domin ta maida Inna ladi mahaukaciya.
Suna hanyar dawowa daga Islamiyya ita da Indo sunzo wucewa ta wani lungu suka hango Headmaster ya duk'una yana bayan gida, Da sauri Mahaseem ta rad'a ma Indo Wani abu a kunne Indo zaro ido tayi tana girgiza kai, Mahaseem ta harare ta, waigawa tayi taga wani katon kadangare, ai ko tayi lamo ta cafko shi Dan bata tsoron kadangare, a hankali ta isa bayan headmaster ai ko ta wurga mai kadangaren, da sauri taja hannun Indo suka ruga a guje, jin kamar wani abu ya fad'o mai yasa ya mik'e sai baiga komi ba, ya cigaba da abinda yake kawai sai jin waiwayi yayi a wuya yana tab'awa yaji kadangare, ai wani ihu yasa saboda a rayuwar shi baya son kadangare bare wannan kutu mai jan kai ne,Headmaster a guje ya ruga ko wandon bai gama sawa ba, yana rike da ita a hannu.............
Sannu a hankali yake tafiya zuwa Side din granny, sanye yake cikin white shaddah, kanshi ba hula gashin shi ya kwanta luf luf gwanin sha'awa irin na larabawa, Nibras kenan, tafe yake cike da kasaita yana danna wayar shi, Wani kyakyawan saurayi na hango fari amma ba sosai ba, yana sanye da sky blue Yadi, kanshi hula ne colour kayan, Fawwaz kenan fuskar shi dauke da murmushi ya mik'a ma Nibras hannu suka gaisa, a tare suka nufa side din granny, Wanda Fawwaz ne ke Dan jan Nibras da hira shidai Uhm ko hmm yake cewa, Fawwaz bayan gama karatun shine Abbie ya samar mishi aiki a Abuja shine yake zaune dasu.
Around 4pm ne kowa ya hallara a parlour granny domin duk Friday suna haduwa dukan su, ayi hira har zuwa magrib,Granny ce ta kawo shawaran hakan domin kara kusanta da juna, Dan tasan Mom da Ummi ba shiri suke ba, bata son su raba mata kan y'aya da jikoki, Shigowar su a tare yasa kowa ya kalle su, Kawu Ne yayi saurin cewa"Ku kuma sai yanzu ne zaku shigo biyar saura"
Nibras ko kallon shi baiyi ba ya nufa gurin Granny, Fawwaz ne yayi murmushi yana cewa"Kawu ayi hakuri Dan Allah, sannun Ku da gida"
Kawu yaji haushin yanda Nibras yayi mai, ciki ciki ya amsa ma Fawwaz, nan suka gaida kowa, dai ana ta hira cikin anashuwa idan aka cire Mom da Ummi wacce basu wani sa baki a maganar, Salman ko ganin Nibras ya shigo bakin ciki ya kama shi kawai sai ya tashi ya bar gurin, Nibras ko wayar shi kawai ya cigaba da dannawa, Naila wacce taci uban ado saboda shi ta dawo kusa da jujerar da yake tana magana k'asa k'asa"Ya Nibras kayi kyau, gaskiya ina kishin ka Allah yasa ba wacce ta ganka da shigar nan"
Banza yayi da ita, haka tayi ta zuba ba tare data damu ya kulata ba, Mom dake kallon ta sai signal take mata da ido akan ta bar kusa dashi, ita koh yar duniya ko a jikinta, Ummi tana lura dasu amma bata damu ba Dan tasan d'an nata mata basa gaban shi bare kuma Naila tasan ba sonta yake ba. Haka akayi ta hira ana wasa tsakanin Granny da jikokinta,
Sai gurin magrib aka watse aka bar granny, tana jin d'adin yanda take kasancewa tare da familyn nata, damuwar ta daya Lawal baya nan, amma kuma ai ga Fawwaz da sauki.
Mom tana suna shiga side dinsu taja hannun Naila zuwa bedroom"ashe ke wawuya ce, bance ki fita harkar miskilin yaron can ba?"
Turo baki Naila tayi ta d'aga hannu"Abeg pls mom ki barni da wanda nake so, nidai ina son shi kuma aure za muyi"
Cike da takaici Mom tace"Dan Ubanki ba sai ki auren shi in gani ba, kullum ina fahimtar dake gaskiya amma kink'i ganewa....."
"Brain dinta na kifi ne, ai , Stupid Mara zuciya, meye amafanin son wanda baya sonka baya son iyayen ka?" Salman ne ya katse maganar Mom lokacin da yake shigowa dakin.
Naila cikin rashin kunya tace"No Ya Salman kar fa ka takura min, kowa fah abinda yake so yakeyi a gidan nan, kai waye ya takura ma" wani irin duka yazo kai mata ta zille ta fita brdroom din a guje, zai bita Mom ta jawo hannun shi"wai kai meye hakane, yanxu sai ka bita kuna tsere shiyasa ta raina ka ai, Respect ur self pls"
Yana huci ya zauna kan bed yana cewa"da kin barni nayi maganin rashin kunyar ta ai"
Zama tayi tana mai nuna mai bak'in cikin ta akan Ummi da yaran ta, shi kanshi bakin ciki kishi da hassada ya rufe mai ido.
~Kauye~
"Kam bala'i, yau sai kinci Ubanki yarinyar nan" Inna Ladi ta fad'a lokacin da Mahaseem tayi mata wurgi da bokiti wai ba zata sha ruwan ba.
Ganin tayo kanta rai b'ace tana bala'i yasa ta fasa k'ara tace"Wayyo Inna zata kashe ni,zo ki ceci rai"
Kafin Inna Jummai ta fito Inna ladi ta cafke Mahaseem dake shirin guduwa, wani ice ta jawo ta shiga dukan Mahaseem dashi, Inna Jummai ce ta k'wace ta da k'yar amma bakin Mahaseem yak'i mutuwa cewa take"Wayyo Allah zata kashe marainiya, jama'a za'ayi kisan kai, wayyo Allah ya isana"
Inna Jummai ne ta jata gurin dakin ta yayin da Inna ladi me cewa"Massifafiyar yarinya duk kin ishe mu agidan nan toh bari malam ya dawo, dole asan abinyi, shegiya irin mayu mai kama da Aljanu"
Mahaseem na kuka tace"Ban yafe ba wuta balbal, kuma sai na rama gurin Bibalo"
Za tayo kanta ta shige d'aki tasa sakata.
```Nidai nace Mahaseem ga tsoro ga tsiwa```
_TAKU CE UMMU BASHEER_