Chapter 4
by @ummubasheer
*_MAHASEEM_*
{ ```Heart``` ```Touching``` ```Story``` }
_NA_
*_UMMU_ _BASHEER_*
```HASKE``` ```WRITER'S``` ```ASSOCIATION``` ...💡
*Page 04*
Inna Jummai ce tasa Mahaseem a gaba tana mata nasiha akan ta daina tsokana da neman rigima, ta dinga yin abinda Inna larai tasa ta, Jinta kawai Mahaseem take amma ko kad'an bata d'auki maganar ta ba domin washegari ta fito za taje aiken da Inna Jumai tayi mata, tana tafe taga mai suyar awara kawai ta k'arasa gurin"mai awara zuba min na d'ari kisa yaji sosai"
Tana kwashewa ta zuba a laida har Mahaseem na cewa ta k'ara mata yajin, tana mik'a mata ta karb'a zata juya mai awara tace"baki bani kud'in ba"
Rik'e k'ugu tayi"k'arfi yaci, Idan kin isa ki k'wata" ta juya yayin da mai awara ke mata Allah ya isa.
Washegari da safe
Sauri take yi domin ta tafi makaranta yau ta makara kuma aikin Inna Ladi ce ya tsayar da ita, ta fito zata tafi Inna Ladi ta tsayar da ita cikin jin haushi ta turo baki"ungo nan ki siyo min kosai"
Murgud'a baki tayi"Nifa makaranta zanje nayi latti"
Rik'e baki tayi"iyeeeh uwar ki kika murgud'a ma baki, kuma dole kije, malam malam...."
Jin malam zai fito yasa Mahaseem ta karb'a kud'in da sauri domin tasan zai iya dukan ta ita kam ta tsani duka da sasafe, haka ta fita tana hawaye, sam bata jin dadin abinda ake mata,amma za tayi maganin ta tunda tasa ta makara, ai ko tana siyo kosan ta d'eba kasa ta zuba ta kakabe tana dariya ba dai za suci k'osai ba ai sai suci din, tana zuwa gida ta mik'a mata da sauri ta juya tana k'unshe dariya, tana fita Inna Ladi ta bude sai ganin kamar k'asa tayi tasa d'aya a baki domin tabatarwa kawai taji k'asss da sauri ta tofar tana zagin Mahaseem domin tasan da gangar tayi dama idan ba tayi niyyar abu ba toh sai tayi mugunta, haka tayi ta massifa ita kad'ai.
_Sultan Yero(SY) Hospital_
Nibras ne zaune kan Kujerar shi yana operating system sanye yake da Suit maroon colour kunsan yanda maroon suit zaiyi ma farin mutum kyau dai, yasa medical glass, wani Doctor ne ya shigo da salama, Nibras bai d'ago kai ba domin yasan aminin shine Sahal, Jan kujera Sahal yayi tare da zama yana cewa"Dr Nibras Congratulation matar da kayi ma CS ta rayu bayan duk an cire rai da ita, ba karamin wahala tash ba gaskiya"
D'ago kai yayi tare da zare glass din ya ajiye kan table"Thanks be to Allah" shine abinda yace.
Dr Sahal ya bud'e fridge ya dauki Coke mai sanyi ya bud'e yana sha tare da cewa"Wai yaushe zaka raka ni gidan su Nusy ne, tunda naga yarinyar nan hankali na ya kasa kwanciya, ya kamata kara ni in gabatar da kaina"
D'an karamin tsaki yaja cikin gajiya da surutun Sahal yace"idan ka gama surutun ka, pls u can go, as you can see I'm working now"
Zaro ido yayi"bana son wulak'anci waye toh baya aikin, gidan su Nusy kawai zaka raka ni anjima"
B'ata rai yayi"ka ga bani da lokacin ka"
Dariya Sahal yayi domin yasan halin abokin nashi cikin sanyin murya yace"zanzo gida anjima fah ka shirya cikin manyan kaya kasan gidan surikai za muje"
Murmushi yayi yace"naji jeka pls"
Yana fita ya sauke Nibras ya cigaba da aikin shi.
A gajiye sosai ya fito daga motar shi ya nufa side dinshi yana zuwa yayi wanka yasa riga white mai long sleeve da Black jeans ya feshe jikin shi da turare, ya d'auki glass yasa, masha Allah yayi kyau sosai, straight ya nufa side din Ummi yana shiga yaga Hibban da Nawwal suna duba littafan School dinsu, gaishe shi sukayi, bai amsa ba yace"where is Ummi"
"She's in her room Broh" Cewar Nawwal
Baiyi magana ba ya hau upstairs yana zuwa ya samu Ummi a bedroom, waya takeyi yana zuwa ya zauna kusa da ita shafa kanshi tayi tana sallama a wayar ta ajiye tace"Habibi ka dawo, ya patients dinka?"
A hankali yace"Alhamdulilah Mom, ya jikin ki?"
Shafa goshin ta tayi"Headache ne kawai yanzu"
Tab'an goshin nata yayi"your Temperature is normal, mom pls ki dinga shan Drugs dinki bana Son BP ki yana hawa"
Murmushi tayi cike da k'aunar d'anta nata"Don't worry Son"
Mik'ewa yayi yana duba wristwatch dinshi ganin to six yasa yayi mata sallama ya nufa Side din Granny yana tana zaune kan kujera tana rik'e da katon carbi, Murmushi yayi ya gaishe ta, amsawa tayi tana tambayar shi gurin aiki"Tasbihi yau kike yi ba kallon"
Hararan shi tayi"Allah ka kiyaye ni Nibrasu"
B'ata fuska yayi jin ta b'ata mai suna, wayar shi ne yayi ringing sai da ya kusa katsewa sannan ya d'auka daga can akace"Friend gani na shigo cikin gida ka fito pls muje time is going "
Tsaki yayi yace"gab da magrib ne zamuje gidan mutane, kazo ina gurin Granny"ya kashe wayar bai jira abinda zai ce ba,in few minutes sai gashi ya shigo yana zuwa ya gaishe da granny ya fara ma Nibras Mita wai su tafi shi koh yace ba inda zaije sai anyi isha'i, haka nan Sahal ya hakura badan yaso ba, domin ya k'osa yaje yaga Nusy dinshi.
Granny tasa mai aikinta ta kawo ma Sahal abinci,sai ko da akayi Isha'i Nibras ya raka shi gidan budurwan nashi acan ma danne danne wayar shi kawai yake bai wani bi takan su ba, da ya gaji ya fara damun Sahal akan su tafi ganin yak'i tashi kawai yayi musu sallama ya fita haka nan shima Sahal ya bishi bayan ya fad'a ma Nusaiba irin son da yake mata ta kuma amince, a mota sai complain yake wai Nibras ya katse mai soyayyar shi, tsaki yayi domin har ya gaji da surutun Sahal.
~K'auye~
Mahaseem ne a class a gaban allo ta tsaya tana kallon yan ajin,Home Economic ta rubuta, ta juya tare da toshe hanci d'aya ta face d'ayan hancin tace"dooo... u... andastan....?"ta fad'i cikin in ina.
Aka kwashe da dariya, harda tafa hannu, domin kuwa ta iya kwaikwayon malamin Home Economics dinsu, ganin wata malama zata shigo yasa tayi sauri ta koma kujerar ta,Bayan sun tashi makaranta ne suna hanyar zuwa gida ne tana tafe ita da Indo wani saurayi ya tsayar dasu,
K'are mai kallo Mahaseem tayi jin yace yana sonta, bak'i ne shi yana da tsawo da jiki, leb'en shi bak'ikirin da alamu yana shan taba,idanun shi kuwa jajazur ga wani uban gashi daya tara akai ya daura comb shi a dole Dan gayu, hak'oran shi kuwa yellow ne da yayi magana sai wari, toshe hancin ta tayi tace"Kai Garzali watan ka nawa ba kayi wanka da wanke Baki ba?"
D'aure fuska yayi"Ke karki rainan hankali man eh yane wannan ai yawa ne,dube ni da kyau ni gaye ne, sonki nake kuma auren ki zanyi"
Kwashewa tayi da dariya Indo ko tsoro take ji domin tasan Garzali a kauyen nan bashi da mutum shi ga shaye shaye da yin ma k'ana nan yara fyad'e, iyayen shi suna goya mai baya.
Mahaseem tace"kai bara kaji ni ban isa aure ba, kaje can ka nema daidai da kai domin ni Mahaseem nafi k'arfin ka"
Zaiyi magana ta juya ta bar gurin.
Tun daga wannan ranar shikenan fah Garzali ya hana Mahaseem sak'at domin kullum sai yazo gidan su ya aika a kirata, tak'i fita,idan ko zata islamiyya ko ta dawo school haka yake tare ta a hanya yana mata hirar soyayya, tsaf take wanke shi ta fad'a mai bak'aken maganganu amma da yake yana sonta bai damu ba, Kwana biyun nan har bata son fita saboda yanda ya takura mata gashi ta tsane shi, bata son ganin shi, tsoron shi take ji saboda jin mugayen halayen shi, tana tsoron yayi mata wani abu domin Inna Jummai tana mata nasiha tace kar ta bari wani namiji ya tab'a ko hannun tane hakan haramun ne,kuma kar ta keb'e da wani namiji, shiyasa bata son fita.
_TAKU CE UMMU BASHEER_