MAHASEEM

Chapter 5

by @ummubasheer

*_MAHASEEM_*

       

{ ```Heart``` ```Touching``` ```Story``` }



_NA_

*_UMMU_ _BASHEER_*


```HASKE``` ```WRITER'S``` ```ASSOCIATION``` ...💡

{ _Home of Expert and Perfect Writers}_ 





 *Page 05*





 _Zaune_ yake gaban Abbi suna tataunawa akan hospital din SY can Daddy ya kalle shi cikin nutsuwa yace"Nibras shekara d'aya kenan dana b'ude wani hospital a wani k'auye, ban sanar da kowa bane kawai, akwai wani aboki na Doctor yasan kauyen sosai, wani kauye ne dake Kaduna State basu da hospital sai irin chemist da clinic haka, suna shan wahala sosai ga k'arancin doctors, wannan dalilin ne yasa muka je kauyen naga yanda yake, wani karamin Clinic muka je, naga anyi ma wata mata CS ta mutu ita da babyn hakan ya b'ata min rai sosai, shine mukayi magana da Abokin nawa aka bud'e hospital din, na d'auki kwararon likitoci, kuma ana kai duk wani abu na bukata can, sau biyu kawai na tab'a zuwa naga yanda abubuwa ke gudana, yanzu ma ina son zuwa domin ganin ya abubuwan ke tafiya"ya numfasa tare da kallon Nibras.


Nibras cikin jin dadin taimakon da Abbi yayi yace"Naji dadin hakan Abbi ubanghiji Allah ya taimake ka, ya kare ka"


 "Ameen"yace cikin murmushi, can kuma ya sake magana" Naso in d'aura ka akan shugabanci ka kula da wancan hospital din bayan dawowar ka daga Australia, sai kuma naga kafi son hospital din nan"


D'ago kai yayi da sauri"Aa Abbi nafi son nan gaskiya"


Dariya yayi ganin yanda d'an nashi ya rude, lalai baya son kauye, haka suka cigaba da hira cikin nishad'i, Ummi data shirya cikin doguwar riga kayan bacci ita ma tazo ta zauna aka danyi hirar da ita, Nibras ganin har 11pm kawai ya tashi yayi musu sai da safe ya nufa side din shi.




Washegari da safe yana zaune a office sai ga Sahal ya shigo yana waya, aikin shi ya cigaba, Sahal ya dad'e yana waya sai zuba soyaya yake, da kyar yayi sallama da Nusy dinshi ya kalli Nibras"My Man ya dai"


Tsaki Nibras yayi yace"Idan ba iskanci ba, kawai sai ka bar office dinka kazo ka ishe ni da hayaniyya"


"Ahyee soyayar tawa ce hayaniyya, lalai baka San whats it to fall in love ba, koda yake how will you know after all you're still single"


Nibras mik'ewa yayi tsaye tare da d'aukar cup ya zuba Coffee bayan ya danna d'an wani karamin abu kamar water Despenser, yayi sipping yace"Meye abin dad'i a soyaya idan ba shirme ba"


"Kutt lalai kana ruwa wallahi idan har soyayya ne shirme, ga Naila na sonka amma kana mata yanga"


Tsaki yayi rai b'ace ya ajiye cup din"Idan maganar ta za kayi min ga door nan you can go, don't even dare to call her name again"


Sahal mamaki yake wannan wani irin hali ne Friend din nashi keda shi, shidai baiga aibun Naila ba, canza hirar yayi kawai.






Taci Uban kwalliya tasa riga da skirt wanda yayi fitting dinta, Dan karamin veil ta d'aura a gefen kaf'adar ta, ta dauki karamin jaka bayan tasa hill shoe colour din jakar, chewing gum tasa a baki tana taunawa ji kuke kasss kasss, downstairs ta sauko cikin shagwab'a ta karasa gurin Mom dake kan kujera ita da Hibban, shagwabe fuska tayi"Mom zan tafi gurin birthday party nan kowa sai kirana ake ni kawai ake jira a fara"


Murmushi mom tayi ta zaro rafar yan 1k ta mik'a mata tace"Kiyi sauri ki tafi tohm"


Hibban kallon wall clock yayi ganin 9pm da sauri yace"Aunty Naila where are u going at this time"


Hararar shi tayi"Inda ka aike ni d'an sa ido, u better mind ur business "tayi tsaki ta fita.


Hibban yace"Mom bai kamata ki barta ta fita at this time ba...."


Kafin ya gama magana cikin massifa tace"What concern u, Hibban ka fita harkar ta kaji na fad'a ma"


Mik'ewa yayi kamar zaiyi kuka ya nufa Bedroom dinshi, gaba daya Mom dinsu bata son gaskiya.




Naila kuwa tana zuwa parking lot zata shiga motar ta sai ga motar Nibras ya shigo yau bai dawo aiki da wuri ba, Kallo d'aya yayi mata ya kawar da fuska, yana fitowa ta karasa gurin shi tana juyi"My Nibras nayi kyau"


Kamar ya shak'e ta Dan haushi, ya daure fuska yace"bani hanya in wuce Kafin nayi ball dake"


Maimakon taji haushi sai ma murmushi tayi"ya Nibras wai Dan Allah meye laifina Dan kawai ina kaunar ka, meye bani da shi wacce namiji zai buk'ata gurin y'a mace kalle ni da kyau"


Tsaki yayi tare da rab'awa ta gefen ta ya wuce yana cewa"Tarbiyya kika rasa"


Aiko ya caka mata magana, taji zafi Sosa, wasu hawaye ne suka zubo mata har ga Allah tana mutuwar son Nibras kuma tana bala'in kishin shi, amma zata jure duk wulak'ancin shi matukar zai aure ta, da tunane tunane iri iri ta bar gidan.


Nibras ko mamaki yake ina za taje cikin Daren nan, ya wuce side dinshi yayi wanka, abinci ya gani kan dining da alama Ummi tasa aka shirya mai, tunda tana da key din side dinshi, bayan ya gama Dinner ya shiga gurin Ummi.





 ```Kauye```



Mahaseem ce durk'ushe tana kuka kamar ranta zai fita yayin da Kawu yake ta fad'a taje ta jawo rigima shine yayi mat shegen duka, duk yaji mata ciwo, Inna Jummai ce tazo tana bada hakuri ita ma ya rufe ta da bala'i ya kara da cewa"duk Iskancin da yarinyar nan ke yi laifin kine...."


Ganin za'a daura ma Innar ta laifi tayi saurin Cewa"Wallahi ba ruwan ta...."


"Rufe min baki munafuka, aure ma zanyi miki kowa ya huta da fitinar ki" ya fad'a a zafafe.


Wani ihu Mahaseem tasa"wayyo na shiga uku Dan Allah Kawu na tuba kar kayi min aure"


Kakab'e rigar shi yayi ya shige daki, Inna Ladi dake gefe tabi bayan shi cikin murna, Inna Jummai ta d'ago ta tana rarashin ta yayin da take ihu tana cewa ba ta son aure, a haka ta kaita daki tana bata hakuri, ta dabo ruwan dumi ta Gaza mata jiki saboda raunin da taji, da kyar Mahaseem ta daina kuka, haka ranar ta yini cikin bakin ciki wai ita za'ayi ma aure amma koh da an cuce ta.



Kawu na shiga daki Inna Ladi ta same shi da maganar da yayi akan auren Mahaseem, yace ba dagaske yake ba kawai so yake ya tsorata ta ko ta daina jan musu rigima, Inna Ladi cikin makirci tace"Malam a ganina mu aurar da yarinyar nan mu huta mu saki jiki muci arzik'i, gadon ta muyi Kane Kane dashi"


Murmushi shima yayi"kuma fah kin kawo shawara toh dawa zamu had'a ta"


Da sauri tace"Garzali mana"


"Ke kinsan mai kike cewa Dan iskan yaro ne fa"


"Yo sai mene ai gara mu had'a dashi tunda yana sonta kullum sai ya aiko ayi mai salama da ita,kuma kaga ai ba zamu aurar da ita inda za taji dadi ba gara ta wahala, mu kuma muci dukiyar ta"



Cikin jin dadin zancen ta yace"kin kawo shawara mai kyau, anjima zan nema garzalin kawai ince ya turo"


Haka sukayi ta tataunawa Inna Ladi na bada muguwar shawara saboda ta tsani mahaseem sam bata son ganin ci gaban ta.




A ranar kuwa Kawu ya nema Garzali ya bashi izinin ya turo zai bashi Mahaseem, sosai garzali ya rude domin ba karamin so yake ma Mahaseem ba, a daren ranar yazo kofar gidan su bayan ya dau wanka,duk suna zaune a tsakar gida suna shan iska kasancewar ba wuta, amma akwai hasken farin wata. Yaro ne ya shigo yace"Wai Ana kiran Mahaseem inji Garzali"


Da sauri Mahaseem tace"kace baza tazo ba, shegen yaro mai kan goruba, kai ne Dan aike koh"


Kawu dake jinta yace ma yaron"ce mai tana zuwa" yaron ya amsa ya fita.


Kawu ya kalle ta"tashi maza kije"


Za tayi magana yayi mata wani mugun kallo ba shiri ta shige daki tasa hijab ta fito tana zuwa rai bace tace"Garzali zan maka rashin mutunci idan baka fita rayuwa tah ba, nace bana sonka koh ana so dole ne"


Murmushi yayi"yarinya daina wannan zancen domin an bani ke,goben nan iyayena za su zo asa mana ranar aure...."


Bai gama magana ba tace"Tirrr wallahi in aure ka ba dai niba yaro, jeka nema irin ka yar iska" tana fadin hakan ta shige gida, ba tare da ta dau maganar shi da muhimmanci ba.





Bayan kwana biyu


Kawu ne ya kira Mahaseem dasu Inna ya Sanar musu ansa ranar auren Mahaseem da Garzali, ansa sati biyu domin baya son a dauki dogon lokaci, wani irin ihu ta saki tana birgima a kasa, tana cewa ba zata aure shiba, Kawu sai da yayi mata shegen duka ta nutsu, sai kukan zuci take, Inna Jummai ta kaita daki tana mata nasiha ita kanta bata son auren domin tasan halin Garzali, amma tunda Kawun yace haka tasa shi da kafiya ba zai canza ra'ayi ba, haka tayi ta rarashin Mahaseem. Ita koh kuka take sosai tana cewa Dan anga iyayen ta sun mutu shiyasa za'ayi mata auren dole ita wallahi baza ta yarda ba.



Washegari sai ga k'anwar Maman ta tazo daga can Rugar su saboda jin auren Mahaseem da za'ayi, dama ita kadai ce ta rage yar'uwan Maman mahaseem iyayen su sun mutu,sauran yan uwan su kuma sun tashi a rugar, ita aure ne ya zaunar da ita lokaci zuwa lokaci takanje ganin Mahaseem, taso rik'e ta amma mijin ta ba zai bari ba, bashi da karfi ita ma managing rayuwa take, Mahaseem na ganin ta ta fara kuka tana cewa bata so, ita ma hakuri tayi ta bata, haka aka fara shirin biki, sosai Kanwar maman ta da take cema Mama ta fara gyara ta, nan da nan Mahaseem tayi wani irin kyau tayi haske ta fara fitowa Amarya, Garzali koh idan yazo bata fita,idan kawu na nan shine ke sata dole ta fita,ko ta fita shiru takeyi bata kula Garzalin har ya gama surutun shi ya tafi.




Yau biki saura kwana uku an kawo lefen ta, tana zaune a daki daga ita sai Indo ta share hawaye tace"Indo aradu ban son auren nan, kuma bazan yarda ayi min shi ba"


Cikin tausayin kawarta Indo tace"Nima bana son ki aure shi Dan iska ne, ance yana ma mata cikin shege"


Tsaki Mahaseem tayi"gashi kuma d'an kauye, jahili, mumuna, kazami kuma, idan yana magana rufe hanci nake kamar inyi amai, Indo kwarankwatsi ban yarda a aura min shi, guduwa zanyi!"


Da sauri Indo ta rufe mata baki"Ki rufa mana asiri, karki sake fad'a ma aji"


Cire hannun ta tayi"Indo so kike in zauna ayi min auren dole kawai saboda an tsane ni,idan da Bibalo ce kinsan ba zasuyi mata ba, kuma wallahi harda had'in bakin massifafiyar nan Inna Ladi"


Indo dai hakuri tayi ta bata, jinta kawai Mahaseen take, Washegari akayi ma Amarya lalle.Gaba Daya da kun ganta kunsan bata son auren.Inna Jummai koh takai ta dawo tana rarashin ta, domin tausaya mata take.









 ```Maitama Abuja```




Yana Zaune a Parlour yana jiran sakowar Abbi domin yace yana son ganin shi,Nawwal na zaune tana fama buga game a wayar ta, Abbi da Ummi ne suke saukowa daga Upstairs, Ummi cikin farin ciki take kallon yaran nata, nan tace su zo suyi Dinner,suka nufa Dining table Nawwal ce tayi serving dinsu, bayan sun gama ne Abbi da Nibras suka koma Parlour nan Abbi ya fad'a mishi cewa yana so gobe zaije Kauyen nan domin ganin yanda abubuwa ke gudana a hospital sai kuma gashi wani Urgent meeting ya taso mai Dan haka yace Nibras ya wakilce shi yaje Kauyen ya bashi address din kauyen da Hospital dinshi sam Nibras bai so hakan ba amma yayi ma Abbi biyayya yace Insha Allah da safe zai kama hanya, Nan yayi ma Ummi sallama ita ma tayi mai addu'a domin Abbi ya fad'a mata komi.



Washegari karfe tara na safe Nibras ya dauki hanyar Kaduna state, bayan ya dauki abubuwan bukatun shi domin dole ya kwana biyu, saboda ba zai yuwu yaje ya dawo a ranar ba, koda ya isa Kaduna bai tsaya ba ya kama hanyar Kauyen, aroun 2pm ya isa, already Abbi ya bashi number wani doctor, yana zuwa ya kira shi shima ya kara mai kwatance, Parking yayi cikin hospital din, sai ga Wannan Doctor Imran din, suka gaisa yayi mishi jagora zuwa ciki, Ya zazaga yaga marasa lafiya ya duba komi aka kira mai sauran doctors nurses da staffs suka gaishe shi, a Office din Doctor Imran ya zauna kasancewa shine Babba da aka daura akan hospital din, Abinci yasa aka siyo ma Nibras amma kadan yaci domin abincin baiyi mai ba, around 7pm suka bar Hospital din shida Doctor Imran, gidan shi ya kaishi can yayi mai masauk'i, gidan flat ne ba laifi yana Da dan kyau, matar shi daya da yaron su, wani bedroom aka bashi inda zai kwana, akwai toilet a ciki ya shiga yayi wanka, yasa kaya marasa nauyi, bayan yayi sallar isha'i ya dauki wayar shi ya kira Abbi suka tatauna akan abinda ya kawo shi, Sun Dade suna waya Kafin ya ajiye wayar, ya dauki system dinshi yana wasu bincike, Doctor Imran ne ya shigo ya kawo mai abinci yana cewa"Doctor Nibras ya kaji kauyen namu, akwai dad'i koh"


Murmushi yayi yace"Uhm Thanks Doctor Imran"


Haka ya zauna yana mai hira shi kuma Nibras gaba daya jin shi take a takure gaba daya ya dame shi ya lura yana da surutu, abincin ma sakura yayi, sai 9 yayi mai sai da safe, Doctor Sahal ne ya kira shi tsaki yayi ya d'auka, suka gaisa yayi mai ya hanya kasancewar ya fad'a mishi yayi tafiya, saboda ya kula da wacce su kayi ma aiki jiya, nan yaga shima zai cika shi da surutu yace"wai kai baka gajiya da magana ne"


Sahal dariya yayi"anyi baki Dan magana ne meyasa zanyi shiru toh"


Cikin haushi yace" toh ai sai kayi, good night I'm sleepy" bai jira amsar shiba ya kashe wayar, ya kwanta, cikin dare sai juyi yake ya kasa bacci saboda sauro da suke ta cizon shi ga azabar zafi an dauke wuta, gaba daya bai samu isashen bacci ba, washegari da sasafe ya shirya komawa Abuja domin ba zai iya kara kwana a kauyen ba, idan ko ya kara ya tabbata ciwo zai fara gaba daya k'yamar kauyen yake,ya kira Abbi a waya ya sanar mai zai juyo, Abbi yayi mai addu'a, Around 10am ya bar kauyen ya kama hanya.






Mahaseem Tun ana gobe daurin aure take kuka daren ba tayi bacci ba gaba Daya hankalin ta a tashe yake, ta tsani auren nan, haka tayi bacci cikin tunane tunane ta sak'a wannan ta warware wannan a haka sai kusan 5am bacci ya dauke ta, around 5:30 Inna jummai ta tashe ta tayi sallah, gaba daya Mahaseem a rikice take abu daya tasa a ranta shine kawai ta gudu idan ba haka ba kuwa tana ji tana gani ba wanda zai hana za'a aura mata Garzali, da safe mutane nata shigowa ana girki, gurin karfe tara aka gama shirya amarya, gaba daya mahaseem a firgice take karfe biyu na rana za'a daura aure dole ta gudu kafin mutane su fara cika a gidan, agogo ta duba karfe 9:40 buta ta d'auka Inna Jummai tace" Mahseem lafiya na ganki duk a firgice ne? ", 


Cikin tsoro tace"Aah...ba komi fah...Inna Cikina ke murd'awa bari in shiga bayi" da sauri ta shige kar zuciyar ta ya karye taji kamar kar ta bar Innar ta mai sonta, haka ta shige bayin kasancewar gajeran katanga ne kuma ta baya, bayan gidan ne kawai sai ta dira, dama ta rataya hijab dinta a bayin tun tuni, tana sakawa ta haura, dama ta kulle yan wasu kud'adenta a zani, tabi ta lungu har ta bar unguwar su tana fita direct tashar kauyen ta nufa, tana zuwa taji wani yana cewa"Kaduna Habuja, Kaduna Habuja"


Mutumin ne yazo kusa da ita"yarinyar Ga motar Habuj zakije ne"


"Eh" kawai tace mai domin ita kanta bata San ina zataje ba, kawai zuciyar ta taji tana son Habujan da akace ne,Ita yanda take ji ma burin ta kawai shine ta bar kauyen nan, nan ta shiga mota ta biya kudi, aka k'ara passengers, zuciyar ta cike da bakin ciki da tunane tunane, saukin da take ji kawai shine na ba zata auri Garzali ba tunda ta gudu ai sai ayi auren ta gani.







Nibras ya d'anyi nisa da kauyen kawai motar shi ta tsaya,yayi yayi motar tak'i tashi, motar ta samu matsala dole ya nemo mechanic, machine ya samu ya hau ya koma kauyen ya kira mechanic, tare suka o da Mechanic din ya duba motar yace mai gaskiya sai anyi gyara cikin damuwa Nibras yace "kamar wani lokaci gyaran zai d'auka?"


Dan tunani yayi yace"awa biyu dai haka"


Gaskiya ba zai iya tsayawa na two hours ba duk ya k'osa ya bar kauyen, nan ya kira Abbi a waya ya sanar mishi halin da yake ciki, Abbi yace bari ya turo mai wani driver yace Aa kawai bari ya nema wata mota, Abbi yace bai kamata ya hau motar hayya ba, gara ko daga Kaduna yasa Kanin shi ya tura mai private car, Amma Nibras yak'i amincewa saboda ba zai iya jira ba, Abbi addu'a yayi mai tunda yaga hankalin shi yayi gida gara kawai ya dawo,Nan yaba mechanic Car key dinshi yace ya duba za suyi waya kawai ya karbi Number shi, ya dauki karamin bag dinshi dake dauke da system dinshi da ruwa da first aid box karami saboda baya tafi babu first aid box, ya rataye jakar a baya tare da tsaya kan titin jiran motar da zai kai shi Abuja, wata mota tazo Amma an cika shi kuma baya son ya matsu, nan yace su tafi kawai, wata motar ya tsayar, motar na tsayawa yayi magana da driver din, yace ya hau akwai space din mutum daya dama, shiga motar yayi nan idanun kowa ya kai kanshi, ganin shi kyakyawa Dan gayu, Mahseem nakan kujera ta rufe fuskar ta da hijab kawai sai ji tayi an taka mata k'afa, azaban zafi yasa ta mik'e ganin Kyakyawan saurayi yana shirin zama yasa cikin tsiwa tace"Kai Makaho ne baka gani ka taka nine"


Tsayawa yayi cikin mamaki yana kallon ta, jin yayi banza da ita ta kara cewa"bayan makanta halan kai Kurma ne"


Tsawa ya daka mata"Ke ni sa'ar kine baki da kunya"


Rik'e Kugu tayi cikin tsokana"bansan shiba, ka taka ni kuma zaka min massifa, dama Ku maza yan iska ne........ "Tasss taji saukar mari a kuncin ta wani ihu tasa mutanen motar sai kalon su suke ganin meke faruwa wasu maza ne suka fara bashi hakuri ganin irin rashin kunyar da Mahaseem tayi mai, ranshi ya baci ganin yar karamar yarinya tana Gaza mai magana, Ko kanwar shi Nawwal zata girme ta, Mahaseem kunsan ta da tsiwa ga tsoro, duk da Marin da yayi mata ta tsorata amma hakan bai hana ta cewa ba" Allah ya saka min wallahi mugu kawai...." Haushi da Bacin rai yasa zai k'ara mata wani ya rik'e shi yana bashi hakuri, wata tsohuwa dake gefe ta kalli mahaseem"ke yarinya ki bar mai rashin kunya, ina ke ina fad'a da namiji ai sai yayi miki lahani"


Cikin tsiwa tace"Inna duk Baku gani bane taka min k'afa yayi fah, toh ni an fad'a mishi tsoron shi nake....."


Nibras ya kara yo kanta aka sake ririk'e shi, ita kuwa sai tsiwa amma zuciyar ta cike da tsor kawai Dan taga an rik'e shine ta samu bakin magana, da kyar aka basu hakuri, driver ma yasa baki aka fara tafiya.





Amma Mahaseem sai hararar shi take, bai kara bin takanta ba, yasa wayarshi a jaka, sunyi nisa sosai suna gab da shiga Abuja kawai sai ganin motoci dayawa sukayi an tsatsaya, driver shima tsayawa yayi, Nibras tunani yake ko checking point ne amma kuma ai basu tsayawa anan kafin ya gama tunani sukaji harbi, ai gaba daya suka rude suka bud'e motar, mutane dayawa sukayi cikin daji a guje, ciki harda Nibras da Mahseem, barayin hango mutane da sukayi sunyi cikin daji sai suka fara harbi wasu suka bisu dajin.............













 

 ```TAKU CE UMMU BASHEER```