Chapter 6
by @ummubasheer
*_MAHASEEM_*
{ ```Heart``` ```Touching``` ```Story``` }
_NA_
*_UMMU_ _BASHEER_*
```HASKE``` ```WRITER'S``` ```ASSOCIATION``` ...💡
{ _Home of Expert and Perfect Writers}_
_Wannan littafin na kud'i ne daga nan zan tsaya da yin free pages, Idan kuna son cigaba da karatanwa zaku iya turo 300 ta account, ko katin waya na airtel 300, *** banda kira pls, wannan labarin yanzu aka fara._
```Account Number
Fatima Abdullahi
Acc no 0592594133
GT Bank```
_Ku turo da shaidan biyar Ku ta wannan Number kamar haka ***, zan saku a paid group Insha Allah_
*Page 06*
Kowa ya watse Gudu sosai suke yi a dajin, Mahaseem da wata matashiyar budurwa ke bin duk inda Nibras yayi, Mahaseem ihu tayi lokacin da k'afar ta ya fad'a wani d'an rami ga k'ayoyi a ciki, yarinyar nan gaba tayi yayin da Nibras ma zai wuce da k'arfi tace"Dan Allah ka taimake ni"
Kamar zai tafi ya kara jin cikin kuka tace"ka taimake ni kar ka barni, Dan Allah kar ka tafi"
wani tausayin ta yaji ya kama shi bai kamata ya barta ba domin idan suka kamata bai san meh za suyi mata ba, nan yaji kamar kanwar shi Nawwal ce, Juyowa yayi ya karasa gurin ta , a hankali ya zaro kafar ta dake cikin ramin ga k'ayoyi suna sukar ta k'afar yayi jini sosai, bayan ya Ciro k'afar ne ya juya yace tayi sauri cikin kuka tace"bazan iya tafiya ba, wayyo zasu kashe ni"
Wani sanda ya d'auka yace ta rik'e sandar tana rik'ewa taga ya fara tafiya haka ta fara binshi tana d'ingishi, acan gaba suka tarar da budurwan nan, da sauri ta rik'e ma Mahaseem hannu suna gudu, can dai Nibras ya samu wani k'asan dutse yace suzo su buya, da sauri suka lab'e a gurin b'arayin ne suka zo suka jujuya basu ga kowa ba da alamu kamar ba wanda yabi ta nan, wani yace gaskiya su juya dajin bashi da kyau kar su shige sosai, tunda sun samu mutane a titi gara su koma kar a kawo musu farmaki, nan suka juya da Sauri, Mahaseem ta sauke ajiyar zuciya mai k'arfi domin ba k'aramin tsorata tayi ba, Kallon ta Nibras yayi ya kalli k'afarta yanda yaga yana jini yasa da sauri ya Ciro jakar shi ya bud'e ya Ciro first aid box dinshi, jawo k'afarta yayi bayan ya ciro cotton wool yasa spirit, duk kallon shi suke cikin Mamaki, yana fara goge mata ciwon tayi ihu da sauri dayar ta rufe mata baki"ki daure kar suji ki su dawo"
Cije lips tayi tana d'aga kai, Shi koh mamaki yake gata matsoraciya amma sai shegen Tsiwa,ita ma mamaki take ganin shi da kayan aikin hospital, sai lokacin ta kalle shi da kyau, farine kyakyawa sanye yake cikin Dark brown suit, lips dinshi ta kalla a zuciyar ta tace oh namiji da shafa jambaki toh ko ma dai Dan daudu ne,bayan ya gama mata dressing tace"Nagode sosai Yaya"
Bai kulata ba yana mamakin kiran shi da tayi da yaya, ya Ciro bottle water ya mik'a mata da sauri ta karb'a tasha sannan taba Matar nan ita ma tasha sukayi mai godiya, Mahaseem ta kasa shiru tace"amma kai likita ne koh, na ganka da wannan box dinne"
Bai amsa ba ya cigaba da danna wayar shi, yana neman network amma gaba daya ba service kasancewar daji ne,Matar nan ne tace"ai ba abinda zamu ce mai sai godiya"
Hararar ta Mahaseem tayi"Shine d'azu kika gudu kika barni ai shine ya taimake ni"
Dariya tayi ganin yanda Mahaseem tayi magana harda turo baki wai ita taji haushi"Kiyi Hakuri a rud'e nake, na ganki da lalle ne kamar wata amarya"
B'oye hannun ta tayi cikin hijab tace"Aa"
Tsakanin su kawai suke hira shi kuma yana danna waya ya tura ma Abbi sak'o koda zai samu network a gaba, ya fara tunanin ya za'ayi su bar Dajin, Mahaseem da salima matar nan suke hirar su yana jinsu ya lura Mahaseem akwai yarinta daga yanayin maganar ta, can yace musu su tashi zasu bar gurin domin hatsarine cigaba da zaman su a gurin, Kamar za tayi kuka ta kalli k'afar ta Salima tayi sauri ta rik'e mata hannu suka fara binshi a baya, sunyi tafiya sosai ba kadan ba ga rana ya k'wala,Mahaseem ko takalmi ita da matar nan basu dashi tunda aka bisu suka watsar wake ta takalmi, Nibras koh yana sanye da Cover shoe ne,a haka suka cigaba da tafiya a wannan dajin Sosai Mahaseem ta galabaita kafarta na mata ciwo sosai kawai taja ta tsaya"gaskiya mu huta zan mutu, kallon ta yayi yaga duk ta fita hayyacinta ga zufa da tayi, bottle water d'azu ya mik'a mata tasha, bayan sun huta ne kawai sukaji tace"Allah sarki yar akuya tah,zanyi kewar ki"
Nibras duk da ranshi ba dad'i sai da ya kusa dariya, yarinyar nan akwai shirme suna ta ransu ita ta akuya take, Salima dariya tayi tace"akuya kuma"
Da sauri ta d'aga kai"eh yar akuya ta ina sonta wallahi ni damuwa ta wa zai dinga kular min da ita,koda yake Inna Jummai zata bata kulawa"
Dariya Salima tayi lalai yarinyar nan akwai yarinta za tayi magana taga Nibras ya tashi da sauri kamar zaiyi ihu yace"wayyo lizard a shoulder nah"
Mahaseem hannu tasa ta d'auki k'adangaren ta rik'e a tsorace ya kalle ta ganin yanda ba taji tsoro ba, ajiye k'adngaren tayi agefe ya gudu abinshi ta kwashe da dariya tana kallon Nibras"wai k'ato da kai kana tsoron k'adangare...."
Salima ce tayi saurin rik'e mata hannu alamar tayi shiru, shi koh daure fuska yayi domin baya son raini, bayan five minutes yace su tashi, bai jira su ba ya fara tafiya, sunyi tafiya mai d'an nisa sai gasu a titi, gaba d'ayan su ajiyan zuciya suka sauke ganin motoci na wucewa lafiya, da alamu yan fashin sun tafi, wata mota Nibras ya tsayar suka shiga ciki, network din wayar shi ce ta dawo yaji dad'i ko 1minutes ba'ayi ba sai ga kiran Abbi ya shigo d'auka yayi, Abbi hankali tashe yake tambayar shi yana ina, cikin kwantar mai da hankali yace sun kub'uta yanzu haka yana mota ya zai shigo Abuja, Abbi yace toh ya kirashi idan ya isa tasha da kanshi zai je d'aukar shi yayi godiya ya kashe, ba'a dad'e ba suka isa Abuja, suna sauka a tasha mutane duk suka fita Salima tayi musu sallama da godiya ta tafi,ganin Mahaseem na kallon shi yace"sai anjima"ya fara tafiya da sauri ta bishi, gate din fita tashar ya nufa domin jiran Abbi sai gani yayi tana ta binshi, cikin mamaki yace"Ki nema taxi ki tafi inda zaki mana"
Kamar za tayi kuka tace"nima bansan inda zanje ba"
Da mamaki yace"What!"
Hawaye ta fara"ni bansan ko'ina ba, ban tab'a zuwa nan ba"
Da mamaki yace"Toh meye yasa kika bar gida kika zo inda baki sani ba guduwa kikayi?"
D'aga kai tayi"Auren Dole za'ayi min shine na gudu Dan Allah ka taimake ni"
"Aure ke din?" Ya tambaya har lokacin yana mamaki, nan ta bashi labarin komi run rasuwar iyayenta zuwa auren da za'ayi mata da Garzali, sosai ya tausaya mata yanzu y'ar karamar yarinyar nan ace za'ayi mata aure, yanda take kuka ya k'ara tabattar mai da gaskiyar ta, nan ya tambaye ta sunan kauyen su tak'i fad'a mai yayi yayi ta fad'i tak'i tana tsoron kar ya maida ta k'auyen, gashi ta lik'e mai ko motsa kafa yayi zata motsa tana tsoron ya gudu ya barta, wayar shi ya d'auka ya kira Abbi tare da bashi labarin Mahaseem, nan Abbi yace gashi nan zuwa, ba'a dauki lokaci ba sai gashi a wata Babbar mota driver na tuk'i, nan yace su shiga motar, Baya suka shiga Mahaseem ta gaishe shi, ya amsa yana tausayin ta yarinya k'arama ace ta bar gidan su, bai kamata su barta ba dole su taimake ta, nan suka wuce Yero Mansion wato gidan su.
Mahaseem tun a mota ta fara gyangyad'i taji sanyin AC, can taga driver yayi horn a wani katon gida, ga makeken gate, bata k'ara rud'ewa ba taga sun shiga cikin gidan, sai kace sun shiga cikin Unguwa, had'adun gidaje take hangowa , can taga sunje gurin parking ga motoci dayawa, sukai parking ta fito a tsorace, Nibras dake lura da ita a hankali yace"Calm down and feel free"duk da yasan ma kila bata jin English shi dai yayi mata, straight side din Ummi suka nufa suna zuwa nan ta k'ara rud'ewa lalai nan shine aljannar Duniya, kalle kalle take tana juya kai can sai ga Ummi ta sauko ita da Nawwal ganin kyawawa mata yasa Mahaseem tace"ko dai na mutu ne tun a daji, halan Aljanna ne nan"
Murmusawa sukayi Abbi yace"kwantar da hankalin ki nan gidana ne, Baki mutu ba"
Ummi data karaso cikin mamaki take Kare ma Mahaseem kallo cewa tayi"Wannan kuma fah daga ina, Alhaji ko y'ar aiki ka kawo min nifa inada da Mariya ta isa banson tara yan aiki" ta k'are cikin nuna kyamar Mahaseem.
Abbi yace"ba y'ar aiki bace mu zauna pls" da mamaki ta bishi da kallo toh idan ba y'ar aiki bace wace ce ita.
Zama su kayi dukan su a kujera Mahaseem ko da sauri ta zauna a carpet tana jin laushin carpet din, Nan Abbi ya basu labarin komi harda yan fashin da su bisu daji, Ummi hankalin tane ta tashi ta fara tambayar Nibras ba abinda ya same shi koh yace he's fine kar ta damu, nan yace yana so Mahaseem ta zauna nan ta huta kafin su San inda take a maida ta, Ai nan Ummi ta mik'e cikin haushi tace"Abbu Nibras sai dai idan aiki zata dinga mana koh?"
Da mamaki duk suka kalle ta, Abbi ya mik'e yayi hanyar stairs yana cewa"a bata abinci da masauki"
Ummi haushi yasa tabi bayan shi domin ba zata yarda a kawo mata tsintaciya ba, Nibras ya kalli Nawwal"take her to ur room, ki bata kulawa"
"Okay broh"
Fita yayi zuwa side dinshi, ita kuma ta kalle ta sosai taji tausayin ta nan tace ta taso suje, binta kawai Mahaseem take tana kalle kalle, koda suka hau upstairs corridor ne inda taga white doors, sai taga Nawwal ta bude d'aya sun shiga sosai dakin yayi mata kyau komi milk and pink, ta shiga toilet ta had'a mata ruwan wanka mai dumi tace ta shiga, a toilet dinma sai da tayi kauyanci ta tab'i wannan ta tab'i wannan, sosai tayi wanka sai taji dadi, tana fitowa daure da towel Nawwal ta bata wasu kaya tace tasa idan ta gama ta sauko k'asa taci abinci toh kawai tace mata domin tunda tazo gidan bakin ta ya mutu ganin aljannar duniyar data shigo, doguwar rigace na lace tayi mata kyau kadan ne yayi mata tsawo saboda Nawwal ta Dan fita tsawo, kallon dressing mirrow tayi taga kayan kwalliya jibge sai tab'e tab'e take amma ba tayi kwalliyar ba domin yunwa take ji sosai, ta feshe jikinta da turare ta fito ta inda taga sun biyo d'azu, a parlour taga Nawwal, ta karasa Nawwal taja hannun ta zuwa Dining tana fad'a mata yanda tayi kyau, haka ta zuba mata abincin tana mata hira, ita dai jinta kawai take domin abinci ya tafi da tunanin ta, said santi take, white rice ne da stew da yaji naman kaza sai cowslow, ga Pineapple juice mai sanyi sai data k'oshi ta kalli Nawwal"yauwa mai kike cewa ma"
Dariya Nawwal tayi sosai tace"tunda baki jiba ai shikenan, yanzu dai muje muyi sallar la'asar sai mu fita in zazaga dake cikin gidan, har gurin granny sai munje"
Cikin murna tace"Gaskiya naga kina sona,Wannan da muka zo Yayan kine"
Murmushi tayi"Eh yaya nane mu biyu iyayen mu suka haifa Abbi da Ummi da ki gani sune iyayen mu" murmushi Mahaseem tayi tace"amma yayan ki ya fiki kyau"
B'ata fuska tayi"ai koh zamu kwance k'awancen"
Dariya Mahaseem tayi"yi hakuri aradu na daina"
Da mamaki tace" meye aradu kuma, kinga tashi muje na kosa mu fita har gurin Hibban zan kaiki ince munyi sabuwar k'awa" dariya sukayi dukan su tare da nufar Upstairs.................
```Shin ya rayuwar Mahaseem zata kasance a cikin wannan Gidan?
Ummi zata karb'e ta koh kuwa?
Ya labarin Kauye, bayan tafiyar Mahaseem mene ne ya faru, shin an daura mata aure da Garzali ko kuwa?
Mahaseem zata yarda ta koma kauye kuwa?
Ya sauran jama'ar y'an gidan Yero zasu karb'e ta?
Wannan amsoshin tambayar duk yana cikin page na gaba , Ku biya 300 kacal domin zaku nishad'antu sosai a wannan litafin na Mahaseem yanzu labarin ya fara Ku biyo ni don jin yanda zai kasance.
```
~Last Free Page~
_TAKU CE UMMU BASHEER_