JAMILA

8&9

by @rabiattu0444

*JÂMÊÊLÊR*

 


  Na💖

(Ummu Maher)Miss green💚

*MATAR BASH*💡


My

 Wattpad:Rabiatu333





  🟨8&9



Wani gumi ne ya shiga karyomin ta ko INA jin furucin Yaya Deen akan Yaya ta,ga wani kishi da naji yana Neman kassarani duk kuwa akan furucin da naji Yaya Deen ya yi ne,bayan mun koma gida kuwa hankali na ne ya nemi barin jikina yadda naga Yaya Deen yana lallab'a Aunty Safiyya har da ce mata dole a yi maganin zazzab'in nan saboda kar suyi aure ta na yi,don asatinnan zai kawo kud'in saka rana Dana komai kuma ba yaso bukin ya wuce wata 1kacal.



 Fatima ce ta ringa tausar zuciya ta akan inyi hak'uri komai yayi farko yana da k'arshe, hakan ce kuwa ta faru dani domin a kaso 100 acikin son da na ke yiwa Yaya Deen sai naji bai fi kaso 40 ba,don arayuwa ta na tsani mutum mayaudari maci amana.


 Ai kuwa kwana uku da faruwar wannan al'amari naje gaida Babanmu naji yana fad'awa Mamanmu CE wa,wai jiya Yaya Deen ya kai kud'in Aure har da nasaka rana kuma nan da wata 1 za'ayi bukin,duk da gabana ya fad'i sosai da jin maganar Amman ban nuna ba ko alamu.


 "Fatima kinga cin amanar da akayi min ko?wai yaya ta uwa d'aya uba d'aya Amman ki duba kiga irin cin amanar da ta aikata a gareni ko?" Wallahi haryau ban San me na aikatawa Yaya Safiyya ba take nunamin muguwar tsana haka ba,a iya sanina ban tab'a k'inta ko muzanta mata ba,Amman ki duba kiga yadda ita kullum ta ke nema taci min mutunci,ta hanani farin ciki don ita ta samu farinciki.



"Kiyi hakuri Jamila tabbas Yayarki taci amanarki sai dai kiyi hakuri ki fawwalawa Allah shi zai shige miki gaba aduk inda kike,kuma Allah zai fito miki da Wanda yafi Yaya Deen da komai,nidai ina rok'onki da kada ki nunawa kowa sirrin dake cikin zuciyarki,yin hakan shi zaisa kibawa Yayarki kunya."



 To da wannan dad'ad'an maganganun na Fatima ne zuciyata ta samu salama sosai don sai in kwana in yini banyi tunanin wani Yaya Deen ba,balle Yaya Safiya wacce ayanzu gaba ki d'aya ta zama busy saboda bikinta daya gabato,kullum suna yawo ita da Sabuwa narasa inda suke zuwa.



 Yadda Yaya Deen ya shareni ya fita daga rayuwata nima kuwa hakance ta faru a nawa b'angaren don ko kallonshi yanzu ba na yi,don akwai ranarda suna zaune shida Yaya Safiyya suna zance naje wucewa,ko kallonsu banyi ba na fara tafiya zan wucesu,kawai sai naji muryar Yaya Safiyya tana cewa,ke Jamila wani irin iskanci ne muna zaune Zaki wuce ba tare da kin tsaya kin gaida Yaya Deen ba,ko kuwa shima mugun halin irin naki zaki gwada mai?.


 Ban saurareta ba na k'ara kama hanya zan wuce tasha gabana tare da d'aga hannunta ta wanke ni da wani mahaukacin mari wanda sai Dana ga wucewar taurari ta masu haske,sannan ta nuna ni da ytsanta tace"daga yau sai yau duk ranar da kika k'ara wucewa muna zaune baki gaishe muba to wallahi na lahira ma yafi ki jin dad'i.



 Zuciya tace ta tsinke na kalli Yaya Deen naga ko kallo ban ishe shi ba, wani malulun bak'in ciki ya tsaya min a k'ahon zuciyata,ban k'ara magana ba na shige cikin gida ina kuka,koda Mama ta tambayeni ban bata amsa ba kawai sai na fad'a d'akinmu INA kuka mai tsuma zuciya.




 Fatima CE ta ringa rarrashi na,akan da na yi hak'uri kada kuma na sakata acikin raina har abin ya dameni,kuma idan nayi hak'uri ta kusa barin Gidan nan na dad'ewa ba.






   <★>

Yau take ranar D'aurin Auren Yaya Safiyya da kuma Yaya Deen,idan ka gansu ko wannensu baki har kunne saboda murna,ya yinda ni kuma na ke cikin wani hali wani irin zazzab'i mai mugun zafi ne ya rufeni y'an buki sai sannu suke zubamin tare da tausayamin don ina shan wahala,Amman Yaya Safiyya ko kallon arzik'i ban isheta ba,saima kallon banza da take bina dashi.




 K'anwar Mama nace ta fad'awa Mahaifiyarmu aka kirawo min Family doctor d'inmu don yazo ya dubani,bayan ya gama dubani ne ya bani magani sannan na yi bacci,har akayi dinner aka kai amarya ban San me ke faruwa ba,domin kuwa inata bacci Fatima na kusa dani tana kallona tare da tausayamin.



 Sai k'arfe goma na dare na tashi,ina tashi Fatima ma ta tashi tana yimin sannu, abinci ta kawomin da ruwan tee harda maganina,sannan na tashi na rama sallolin da ake bina zuciyata tana yimin k'una yanzu shikkenan Aunty Safiyya ta Auri Yaya Deen?kuka ne naji ya kwace min Fatima ta ringa tausata har na samu na kwanta bacci.



*Bayan kwana biyu*


Itace kuma ranar da k'addarar Jamila ta soma.



"Jamila!Jamila!!da sauri na fito daga cikin d'aki har ina had'a hanya don amsa kiran umman tawa,a farlo na sameta da wani Abu a cikin kwali Wanda ban San ko meye ba.



" tashi ki shirya Fatima ta rakaki Gidan mami,don haka ake kiran Aunty Safiyya,ki kai mata wannan sak'on sannan ki tayata gyara kayan".


To nace sannan na tashi zuciyata babu dad'i,don araina ban tab'a kawo zanje Gidan Aunty Safiyya da wuri ba, na samu Fatima ta fito daga wanka tana waya da Lamir,saurayinta ne Wanda suka had'u da shi ranar bikin Aunty Safiyya abokin Yaya Deen ne.



Dariya nayi sannan na ce"Miss soyayya ta shi kiraka ni Gidan Aunty Safiyya,sauri tayi ta kashe wayar sannan ta ce"rufamin asiri yanzu Yaya Lamir ya CE min yana hanya sai dai idan ya tafi sai muje."


"A'ah gwara ba tafi kada dare yayi idan yazo kya mik'amin gaisuwa".





 Kallon Gidan na farayi tun daga k'ofar gate d'in har ko'ina na Gidan, ina tuna ranar da Yaya Deen ya nunamin Gidan a wayarsa yana gayamin irin rayuwar da zamuyi a Gidan,wasu zafafan hawayene naji suna fito min har na shiga Gidan ban San na fito ba kawai sai ganina nayi a cikin Gidan.



 Tunda ta taho Deen ya hangota tun daga nesa tana takunta mai tattare da nitsuwa acikinsa,ya rasa me yake yi mai dad'i aduk sanda yaga Jamila sai yaji wutar sonta tare da sha'awarta Amman baya jin zai iya Gaya mata kuma aduk sanda yaganta sai yaji bazai tab'a iya yi mata magana ba.



 Ko kallonshi ban yi ba na yi shige wata ciki,sallama na ringayi a tsakiyar farlon babu Wanda ya amsa min,na shiga wani d'aki Wanda nake tunanin shine d'akin Aunty Safiyya,nanma babu kowa juyowar da zanyi kawai sai naga Yaya Deen daga shi sai boxer ajikinshi,hankalina ya tashi sosai na tsorata da ganin Yaya Deen a haka,ban sanda na bud'e baki zanyi ihu ba kawai saiya shek'amin wani Abu a hancina,daganan ban k'ara sanin inda nake ba...








Idan kin karanta don Allah kiyi share.👏🏻