ZUMUNTA KO MUGUNTA

SHAFI NA 05

by @yarmutanargungu

```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️



ARGUNGU WRITERS ASSOCIATION❤


    MARUBUCIYAR...✍️



***Bayan Wuya***


***Ashe ba so ba ne***


***Zumunta ko mugunta*** On typing...✍️


BY- FATIMA ZARA ALHASSAN ❤️💙💛





GARGADI!!!


Kagaggen labari ne. Sabo da haka, ban yadda wani ko wata su juya min littafi, ba ta re da izinina ba, a kiyaye!!!



     JINJINA:


Ga yan uwana👍 Allah ya barmu ta re, ya kuma kara ma na son yin zumunci 💛💙❤️




GODIYA:


Ina miika gaisuwa ta zuwa ga masoya na, ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka mu ku da alkhairi 👌




     Ita din kanwata ce, kuma kawa ta ce, wani bangaren kuma Uwa ta ce FATIMA IMAN IBRAHIM 🥰❤️



FREE PAGES



SHAFI NA 5



     Bismillahir Rahmanir- rahim



A rana ta uku ne labari ya shaa bamban...



*************************


                **********************


Sanadiyyar halaka junan su da su ka yi. Hakan ya sa garin ya yi tsit...ba ka jin motsin komai, sai koke-koken iyalan sarki Baqeer.


Bayan kwana uku, garin ya laafa. Sarauniya Samee ta hau kan karagar mulki,sabo da ba wanda ya isa ya ha na ta,a cewar ta, ita ke da karfin dakaru, duk abun da ta sasu, shi su ke yi. Hawanta karagar ba wu ya ta dinga shinfida zalunci, da mugunta, ta re da kuma ka fa dokoki tsaurara a cikin mulkin ta. Daga karshe kuma ta koori Sarauniya Ayra ta re da yaranta daga cikin masarautar, kuma da gargadin kar su kuskura su waiwayo wannan kasar. 


Ha ka sarauniya Ayra, ta kwashe yaranta su ka lula birnin misra ( EGYPT) Ba wai don ba ta iyawa da sarauniya samee ba ne, a'a kawai dai ta ba ta lokaci ne. kuma in har "muzuru na yawo shaho na yawo dole su hadu wata rana". A birnin misra kuwa, mahaifin ta ya karbe su hannu bibbiyu. A nan birnin misra ta sa ka yaranta makaranta,a cewar ta ga ra su samu ilmi sosai, domin ƙwaato/karɓo hakkokin su, ta re da kuma taimakawa al'ummar su. Sabo da ta na da tabbacin da ace kasar su, su na da ilmi sosai da duk hakan bai fa ru ba. Shiyasa ta zaunar da ya'yanta ta ce mu su ta na son su sa mu ilmi na addini da kuma na zamani, sabo da ilmi bargo ne ga duk wanda ya lulluba da shi, ba ya tozarta . Sai ka ga shi ba kowa ba,amma matukar ya sami ilmi sai ya zama babba a cikin Al'umma....



******************************************


        *********************************


     Dai-dai wani ƙaton get na ga an rubuta KAMBUN SARAUTA da manya baqi, shiga ciki na yi, a she Makaranta ce ta ya'yan sarakuna (aljannu) sarauniya Ayra ce bakin ta ba ya rufuwa sabo da farin cikinta, yaron ta ya ga ma makaranta! Burinta na gab da cika, amma za ta kara lokaci kaɗan kafin nan gimbiya Hoor ita ma ta gama karatun ta. 


Akwana atashi asarar mai rai...ga shi Hoor har ta ga ma karatun ta. sun yi murna sosai. Bayan wa su yan kwanaki, ta sa aka fa ra koya mu su yaƙi ta re da dabarun ka re kan su....



SADAKA FISABILILLAH

👇

***Comment***

***share***

***follow***


DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA


   PLS


***


  


YAR MUTAN ARGUNGU``` ❤️💙