ZUMUNTA KO MUGUNTAFree

ArewaPen original

MysteryFreeOngoing

ZUMUNTA KO MUGUNTA

  • 1views
  • 26chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

Sample · SHAFI NA 01

```MARUBUCIYAR...✍️Bayan WuyaAshe ba so ba neZumunta ko Mugunta📚      Writting-by Fatima Zara Alhassan ❤️GARGADI!!!   Kagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata, su juya mi ni littafi, ba ta re da izini na ba!! Sabo da haka a kiyaye👂!!!JINJINA Ina jinjina ga mabiya littafai na, nagode sosai Allah ya barmu ta re🥰💛💙SADAUKARWAga yan' uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma qara hada kanmu, mu yi zumunci🤝❤️     MY FANS WANNAN SALON NA DABAN NE. KAR KU BA RI ABAR KU A BAYA🤪    Free pagesSHAFI NA 1    BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMGudu ta ke yi sosai acikin dajii. ƙafafunta duk sun farfashe, ya yin da ƙafarta ta hagu jini ke zuba. Da alama wani ƙwaro ne ya cije ta awajen. kayan jikinta duk sun yayyage, kan ta ba bu dankwali. kallo ɗaya za ka yi wa kan ta, kasan cewa ya yi watanni sabo da daddagewar da kitson ya yi, ba bu kyan gani. Alamu sun nu na cewa ita kan ta yarinyar ba ta san ina za ta je ba.A daidai wurin wata ƙatuwar itaciyar kuka ta faɗi, sabo da juuwar da ta ɗibeta . Nan da nan guguwa ta tashi a wurin ta lullube yarinyar. Bayan daƙiƙa biyar guguwar ta laafa. Tun shigowar ta cikin dajin ya ke kallonta, ta re da mamakin wannan al'ajabi! Tun zaman sa a jejin bai taba ganin wani mahaluki wai shi bil'adama ya shigo jejin ba, sai yau da Allah ya hada shi da wannan yarinya. Duk gudun da ta ke yi akan idonsa, har kawo yanzu da ta fadi a gabansa.Ba din da ya yi saurin ta re ta ba,Allah kadai ya san raunin da za ta ji, idan ta fadi a kasa. Tsura ma ta ido ya yi yana kallonta, dududu ba za ta wuce shekaru shaa shida ba(16 years) wadda ba ta wuce renon iyaye ba, shi ne aka samu wa su azzalummai su ka gunguntar da rayuwar ta. Tafaa hannuwan sa ya yi, sai wurin ya koma wani babban falo ta re da kayan alatu na rayuwa. Fadin haduwar sa bata lokaci ne . Tafaa hannuwan sa ya yi akaro na biyu, ta ke duk rauni kan jikinta su ka bace, ta re da canza ma ta kayan jikinta. . Masha Allah, yarinya ce kyakkayawa , alkalami na ba zai iya bai ya na mu ku kyanta ba. sai dai mai karatu ya ƙiyasta...Abun tambaya anan shi ne, wanene wannan mutumin? kuma yarinyar daga ina ta fito, san nan me ya faru da ita?A tunanin ku, wane irin firgici yarinyar za ta shiga, idan ta farka ta ga kan ta a wannan wuri kuma ta re da wannan mutumin? kar ku damu, ni Fatima Zara Alhassan ashirye na ke tsab domin kawo mu ku wadan nan amsoshin.DOMIN GUDUnMUWA KO SHAWARWARI PLS   ***YAR MUTAN     ARGUNGU ✍️📚ya ku ka ji wannan salon,Ina fa tar salon ya kayatar da ku?Comments Share```

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters26
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play