ZUMUNTA KO MUGUNTA

SHAFI NA 06

by @yarmutanargungu

```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️



Marubuciyar...✍️



**Bayan wuya**


**Ashe ba so ba ne**


**Zumunta ko mugunta on typing...✍️

NA

Fatima Zara Alhassan ❤️


GODIYA

ga Aunty sadiya Alhassan. Allah ya shirya mi ki zuri'ar



SHAFI NA 6


   Bismillahir- rahmanir rahim


An koya mu su yakii sosai. Haka ta samu mahaifin ta, ta ce mishi nan da sati huɗu ta na son zuwa kasar Farisa, ta re da yaran ta. Bai jaa zancen ba ya nuna ma ta amince warsa, ta re da ba ta ƙwarin guiwa, "idan su ka je, kar tabar Sarauniya Samee akan karaga, sabo da duk zaluncin da sarauniya samee ke yi, ana faɗa mi shi. Amma yanzu lokaci ya yi da za ki je ma ta a makance,ma'ana duk wata hanya da za ta san da zuwan ku, zan rufe ta,sabo da ta saka matakan tsaro sosai a ƙasar ta. Ko ƙwaro ya bi ta gefen kasar ta sai ta sa ka an kashe shi... ballan ta na ke da tasan cewa ko bajima ko badaɗe sai kin kai ma ta farmaki, sabo da haka je ki kira mini jikokina...? Bayan mun bayyana agaban kakan mu. Sai ya ɗauko ƙwarya, ya yi addu'o'i acikin ta,san nan ya ba ni ya ce, "karba kasha ka ba kanwar ka, wannan tsarine da yardar ubangiji, duk wani girman al'jani ko muninsa ko kuma tsafinsa, wallahi bai isa ya tsaya agaban jinina ba,matukar ya ce zai cutar da su, sai dai ya tsaya a gaban ku da alkhairi ba dai sharri ba. Dan haka ku tashi ku tafi, in-sha Allah ku ke da nasara! Amma ku sa ni, na hane ku da yin zalunci tun daga jinsin ku, har na bil'adama, Allah ya yi mu ku albarka!" Ameen Kakan mu, mun gode sosai da dawainiyar da kayi damu, Allah ya saka ma ka da alkhairi ya kuma kara ma ka lafiya. kuma in-sha Allah mu ma su biyayya ne akan umarnin ka, ma'assalam...


A hankali su ka koma farin hayaki,su bace bat! A kasar farisa kuwa, kwanan nan wasu irin mafalkai ta ke yi mai ban tsoro...wai an shigo masarautar ta an hallaka ta, am ma ta kisan gilla. Wannan abun na ta da hankalin ta ainun, ta kuma yi iyya binciken da za ta yi, akan gano dalilin wannan mafalkin amma ta ka sa ga ne komai akai!!! Hakan ya sa ta ƙara yawan dakaru ma su tsaron lafiyar ta. Wannan kenan....


Saukar mu kasar Farisa ke da wu ya, mu ka kutsa kai tsaye cikin masarautar. Duk yadda dakaru ke son tsayar damu, abu ya faskara. Dalili kuwa shi ne, da zarar sun nufo wajen mu da niyyar kai mana farmaki sai su jaa baya,haka mu ka dinga yi da su har mu ka isa cikin fada.... 


Sarauniya samee na ganin mu, ta mike tsaye cikin mugun firgici!!! Yau me zan ga ni, ni sarauniyar FARISa?! Me ku ka dawo yi a kasata?! Cikin tashin hankali ta ke kallon su, cikin kuma kaɗuwar hanta.


Ba ta tsinke da lamarin ba, sai da ta juya ta ga Yarima Fu'ad zaune akan karagar ta.


"Tashin hankali wan da ba a sa ma sa rana" Tabbas! mafarkin ta ya tabbata, amma wallahi sai dai su kashe ta ,ba za ta ba su mulki ba. Duk cikin zuciyar ta,ta ke wannan zance...


Ki samu wuri ki zauna, magana zamu da ke ta fahimta,amma fa idan kin bamu hadin kai. cewar yarima fu'ad,. cikin tsawa ta ce ," kai har ka isa ka zo gabana ka ce wai in zauna?! Waye kai kuma tashin yaushe da za kaban umarni, kuma kayi tunanin in bika, toh ko uwarka Ayra ba ta isa ba, balle yaron da aka haifa a ga ba na!!! Ke Samee... sa ka idanuwan ki cikin na wa, nine dai-dai yin ki, ba mahaifiya ta ba, dan haka umarni ne na ba ki, kuma dole ki bi...azuciye ta yi wurinsa, amma ga mamakin ta, ta ka sa hada ido da shi, sai ma wani shegen tsoron sa da ta ke ji. Toh me hakan ya ke nufi?!! Ta tambayi kan ta.


Murmushi Sarauniya Ayra ta yi, irin na ya'yan saraku na, san nan ta ce, "ai dama na fada miki, idan muzuru na yawo, shaho na yawo wata ran, za su hadu" yanzu kin yadda da magana ta? Ta muzance sosai, ace kamar ta sarauniya samee,wai yau ita ake ciwa mutumci agaban dakarunta!!!. A yau ba sai gobe ba,za ki bar wannan karagar mulkin, za kuma ki bar wannan kasar gaba daya, kuma da sharadin duk ranar da kika dawo wallahi sai na sare kan ki, kuma bazan yi kaffara ba!! Na ba ki rabin saa'a ki yi nesa da kasar, komai kama da ke aka ce angani, toh kiyi kuka da kanki,. San nan sarauniya Ayra ta sa ke juyawa gefen dakaru, ta fitar da duk wadanda su ka bijirewa mijinta, ta sallame su``` ...


DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA PLS

👇***


COMMENT

SHARE

FOLLOW

FISABILILLAH ❤


TA KU HAR KULLUM

❤ƴar mutan Argungu ❤