ZUMUNTA KO MUGUNTA

SHAFI NA 7

by @yarmutanargungu

```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️



Marubuciyar...✍️



**Bayan wuya**


**Ashe ba so ba ne**


**Zumunta ko mugunta on typing...✍️

NA


Fatima Zara Alhassan ❤️



ARGUNGU WRITERS ASSOCIATION


GARGADI!!!


wannan labarin kagagge ne. Ban rubuta shi don cin zarafin kowa ba, idan yazo daidai da rayuwar ka, toh akasi ne, sabo da haka a kiyaye!!!



Godiya ta musamma ga mabiya littafi na, nagode sosai Allah ya sa ka mu ku da alkhairi 👌




Fatima iman ibrahim ina godiya sosai❤️



SHAFI NA 7



   Bismillahir- rahmanir rahim



kuma da sharadin duk ranar da kika dawo wallahi sai na sare kan ki, kuma bazan yi kaffara ba!! Na ba ki rabin saa'a ki yi nesa da kasar, komai kama da ke aka ce angani, toh kiyi kuka da kanki,. San nan sarauniya Ayra ta sa ke juyawa gefen dakaru, ta fitar da duk wadanda su ka bijirewa mijinta, ta sallame su, ta re kuma da gargadin su, matukar su na son ran su, toh kar ta kara ganin su acikin wannan nahiyar. Ta ce wa sauran su fa ra shirye- shiryen nada Yarima fu'ad akan karagar mulki....Wannan shi ne takaitaccen tarihi na...


A jiyar zuciya Aneesa ta yi, ta re da kara kallon fuskar fu'ad, ita kam tasan wannan kyau haka sai dai aljani. san nan ta ce: "ina yi ma ka ta'aziyya akan rasa mahaifin ka, da kuma ta ya ka murnar kifar da zalunci kadaura adalci. Hakan ya sa nasan ba bu MUGUNTA acikin zuciyar ka, dama ace kowane jinsin Aljanu haka su ke...da an samu zaman lafiya a duniya, sabo da dayawan su, su ke kara ba da gudunmuwa wajen tashin hankulan bil'adama... 


Murmushi ya yi, ta re da jinjina waayo irin na ta. "kai komai murmushi? Amma kuma wallahi ya na ma ka kyau... kin ganki ko? Surutun ki ya yi yawa, kuma kar ki sa ke cemin KAI, daga yanzu ni yayan ki ne, kinji ko? "Toh mai martaba sarkin farisa...hararar ta ya yi, shiyasa tayi saurin cewa: Wai...yaya fu'ad. Dariya su ka yi gaba dayan su...



"Amma yaya fu'ad, ya aka yi kasan suna na, da kuma sunan iyaye na? Wannan ba abun mamaki ba ne, dan nasan sunanki.


Tun kina yar karamar ki, nasan ki.


Baki bude ta ke kallon sa, san nan ta jeho mishi tambaya. Tun fa ina karama ka ce? Toh ta ya ya kasanni? Sabo da ke na ke zaune a wannan wurin, kin ga kuwa ai ba abun mamaki ba ne, sanin sunan ki?



"Amm... Aneesa surutu...zan fada miki amma sai nan gaba.Kuma kema sai kin bani labarin ki...


Yanzu dai kika ce mu jinsin mu, mun fiye MUGUNTA ko?! Kai yaya fu'ad, har fa maganar ta wuce... a wurin ki ba, kamar yadda ki kasan akwai azzalummai acikin mu, haka kuma akwai su acikin ku, son zuciya da neman duniya, shiyasa bil'adama ke tsoron aljannu, amma maganar gaskiya aljanu su ke tsoron mutane, amma fa ada can... kafin zamani ya canza. Yanzu sabo da neman bukatu wajen aljanu da mutane ke yi, shiyasa aljanu ke juya su yadda su ke so, sabo da ba Allah acikin zukatan wasu. Amma da ace za su rike Allah kuma su dage da adu'a toh wallahi da ba bu wani aljani da zai rabesu da nufin cutarwa...sai dai kash! wasu mutanen sun mai da aljanu abun bautawar su...sun manta cewa akwai Allah a madakata ya na jiranmu.... Allah ya sa mufi karfin zuciyoyin mu, ameen...


"Haka ne yaya fu'ad, mutane na manta cewa addua takobin mumini, Allah ya ganar damu gaskiya ya kuma ba mu ikon aiki da ita amin.


SUNANA ANEESA ABDUL'AZIZ ABUBAKAR MAI NOMA...Kamar yadda ka fada abaya...




MUHADU A SHAFI NA 8 DON JIN LABARIN ANEESA...✍️





DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA


PLS


***



YAR MUTAN ARGUNGU``` ❤️🥰📚