SHAFI NA 08
```ZUMUNTA 馃 KO MUGUNTA 馃懞...鉁嶏笍
MARUBUCIYAR...鉁嶏笍
**Ashe ba so ba ne
**Bayan wuya**
Zumunta ko mugunta on typing...鉁嶏笍
NA
Fatima Zara Alhassan 鉂わ笍
GARGADI!
Kagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata su juya shi,ba tare da izinina ba, akiyaye. Idan kuma ya zo dai-dai da rayuwar wa su, toh akasi ne!.
GODIYA
Ga mabiya littafai na, Allah ya barmu ta re,ya kuma kara dankon zumunci 馃挋鉂わ笍
FREE BOOK馃摎
TSOKACI AKAN LITTAFIN
LABARIN ANEESA ZAI FARA NE TUN DAGA KAKANNIN TA.
SHAFI NA 8
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
********************************************************
WACE CE ANEESA?
JADA, kauyane acikin kebbi State,
Haba zainaba saunawa zan fada miki, ki daina damuwar kan ki, akan wannan batu, fisabilillahi! Ko yaushe ke ce cikin damuwa akan wane dalili? Haihuwar nan dai ta Allah ce ba wani ne ke ba kan sa ba, ballan ta na ki ce in kin damu za ki samu, duk abun da ki ka ga Allah bai ba ka ba, toh akwai dalilin sa na yin hakan. Indai ni ne wallahi bazan taba yi miki gorin haihuwa ba, sabo da nasan komai lokaci ne,toh akan me zan sa ka kaina cikin damuwa...Matsala daya ce kuma akan iya ce, na san kina hakuri akan abubuwan da take yi miki, kuma na yaba na gode,. Tun dazu da malam Abubakar ke magana ta na gefe daya zaune akan gadon kaara, ta yi tagumi...Sai yanzu ta samu damar yin magana bayan ya kai aaya."Malam nifa ban ki ta taka ba, kawai ina tunanin abun da zai kai ya komo ne akan maganar da IYA ta yi, na cewa ka kara Aure! Ba cewa na yi ka bijirewa umarnin mahaifiyar ka ba, ina dai duba makoma ta ce muddin aka yi wannan Auren, Sabo da ba lallai ne ayi min adalci ba, ta na mai share hawayenta....
Rike hannuwan ta biyu ya yi, yana cewa..."Idan ki ka yi mi ni haka wallahi ba ki yi min adalci ba! A kullum ina rokon Allah kar ya ba ni ikon juya miki baya zainaba...muryar IYA ce ta katse mu su zancen da su ke yi...cikin tashin hankali su ka mike a lokaci daya. Ah,a Iya sannu da zuwa, bismillah ga wuri zauna...
"kai dallah tafi can kaban wuri, shashasha wanda bai san ciwon kansa ba! Tun yaushe na ke binka akan ka kara Aure ,amma kayi kunnen uwar shegu da ni. Sabo da ga ka isashshe mijin isassa koh? Sai kuma ta fashe da kuka... jama'a ku kawo dauki Dana ya bijire min, wallahi nidai lokacin mu ba haka ake yi ba, da zarar ka ce wa yaro kar ya tsallaka wallahi ba zai tsallaka ba....ta jawo gefen hijabin ta, ta na sharar majina...
Iya dan Allah ki yi hakuri, cewar zainaba."Ai dole ki ce inyi hakuri tun da an cuce ni! Atoh an cuce ni mana,shiyasa ki kayi sumi-sumi da kai ana cewa Iya ayi hakuri, salon jama'ar gari su ji su ce ni ce muguwa, ba su san cewa nan kuwa ni ce wadda ake cutarwa ba, ko wane gida ka shiga, sai ka ga yara dugui-dugui, ni kuma gani am mai sheni yar iska gantalalliya, mutum ya yi magana ace mishi rigimammiyar tsohuwa, kin dai san can da ina son ki,ganin ba ki aje mini jikoki ba ne ki kaga na sako ki gaba kamar figargiyar tantabara,amma yanzu duk abun da ku ka yi min wallahi na yafe muku duniya da lahira,toh bayan kai da matar ka wa ag gareni? Dole ne inso abun da ka ke so Abubakar,ai kana kokari da ni sosai Allah ya biyaka. Toh nidai yanzu ba wannan ne ya kawo ni ba,mai zai hana ka Auri Atika yar gidan malam Tukur, yarinya ce mai hankali,Toh ni dai ba hankalin ne ya burge ni ba, kasan danginsu irin haihuwa ne, akan haihuwar su kowa ya san duk shekara sai anyi suna a gidan...
"Iya mun fa dade da wuce wannan wurin, haihuwar nan ba fa mutum ke ba kansa ba,ko mata nawa zan kawo cikin gidan nan, idan Allah bai nufa ba, ba yadda zamu yi, sabo da haka komi lokaci ne, maganar wata Atika a ajeta gefe gaskiya...
Haka iya ta fita daga gidan ta na kuka, wai Abubakar ya ci ma ta mutunci shi da matar sa...Bayan fitar iya, zainaba ta kalli mijinta, dan Allah malam ka je ka ba ta hakuri, in dai sabo da ni ce wallahi na yadda ka Kara Aure. Ba ason bata ran mahaifa, hakuri ake da su...amma ki na ganin abun da iya ke yi dai-dai? A dai yi hakuri kasan sha'anin tsufa...
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUN MUWA
PLS
***
YAR MUTAN ARGUNGU``` 鉂わ笍馃挋