ZUMUNTA KO MUGUNTA

SHAFI NA 10

by @yarmutanargungu

``````


ZUMUNTA 馃 KO MUGUNTA 馃懞...鉁嶏笍



marubuciyar...鉁嶏笍


**bayan wuya**


**ashe ba so ba ne**


**zumunta ko mugunta? on typing...鉁嶏笍



BY-Fatima Zara Alhassan 鉂わ笍

(拼ar mutan Argungu)


ARGUNGU WRITERS ASSOCIATION 馃挄

Gargadi!!!


kagaggen labari ne. idan ya yi dai-dai da rayuwar ku, toh akasi ne. kuma wallahi ban yadda a juya min littafi ba ta re da izini na ba! Free Book ne, ban ya fe duk wanda ya sayar da shi,akiye!!!




Jinjina 馃憣


ga yan'uwa na Allah ya bar zumunci, ameen鉂わ笍馃挋馃挌



Godiya:


ga ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka muku da alkhairi nagode鉂わ笍




Ban manta da ke ba fatima iman Ibrahim 鉂わ笍


ta re da Abubakar Birnin tsaba馃憣




FREE BOOK 馃摎



SHAFI NA 10



BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM


**********************************************************300level ta ke...


A cikin shekara daya abubuwa da yawa sun faru, ciki har da zuwan malam makkah da kuma Auren su Tukur da Adamu, da kammala bautar kasar Abdul. A gefe daya kuma Abdul ya aje takardun sa, zai kama wa malam aikin noma,a cewar sa ya kamata yanzu malam ya huta haka nan... Haka Abdul ya dinga shige da fice akan har kan Noma, duk wanda ke cikin JADA ya san Abdul sabo da kwazonsa da kuma sauki da ya ke wa jama'a akan kayan abinci...


shiyasa babba da yaro ba bu wanda bai san Abdul'aziz Abubakar mai Noma ba,ya yi fice sosai a yankin Arewa...hakan ya jawo mishi bakin jini a wajen yan uwansa, a cewar su, su ne manya su ya kamata a fi sa ni, ba kanensu ba!!! Tun su na boye kiyayyar da su ke yi mishi, har su ka fitoh fili...


Malam yayi na shi kokarin ya fahimtar da su cewa kowa rabon sa ya ke ci,ba bu mai cin arzikin wani aduniya, kuma wannan abun kunya ne ace su rasa wanda za su yiwa hassada sai dan uwansu! Amma haka za su bad'awa idanuwan su toka, su ta ke zancen malam...


Yau kusan sati d'aya malam bai da lafiya, kuma yaqi ba ri akai shi Asibiti, haka kullum ya ke ta ra iyalansa, ya na bar musu wasiyya, da su rike ZUMUNTA 馃 a tsakanin su, kar su bar shedan ya yi tasiri a cikin zuciyoyin su...


Tun d'azu malam ya ke kallon Abdul wanda ya yi rama kad'an, akan ciwon malam. Har ga Allah ya na tausayawa Abdul, sabo da irin yan 'uwan da Allah ya ba shi, sam ba su da tausayi koh jinkai ga kanensu, kan su kawai su ka sa ni, ga shi yanzu baya da lafiya amma Abdul kawai ya damu da shi sai kuma mahaifiyar shi,wallahi ya na tausayin zainaba, shine uwarta shi ne ubanta, amma ya san ko bayan ransa, ba za ta yi rashi ba, sabo da ya na da yakinin Abdul ba zai taba barin mahaifiyar shi, tayi kuka ba, idan ya tuna wannan yakan ji dadi...


Abdul ne ya dafa shi yana cewa " Baba ya na ganka ka na kuka kuma kana dariya? Murmushi malam ya yi san nan ya ce " ina farin ciki ne da Allah ya ban D'a mai hankali da kuma hangen nesa, haka kuma ina kuka ne sabo da zan bar ka ta re da kuraye, ma su farautar rayuwar ka,a yayin da kai kuma ba ka ma san da su ba, Abdul kar ka yadda Allah ya jarabce ka da laluran da ba ta da magani, kar ka yadda Allah ya daure maka kaddara da ba ta da iyaka, duniya cike ta ke da mugaye,kowa da ka gani son kanshi ya ke, kowa da ka gani son abin duniya ya ke yi,kasan dai rijiya mai gaba dubu, idan ka fada kafin aciro ka ai kasan ka shek'a lahira, toh haka tafiyar kaddara ta ke, na farko ba a tanada ma ta wuri,san nan tafiya ce da motar da ba bu matuki,tafiya ce da koh kana hanya koh ba ka hanya idan motar ta lalace tafiyar kafa za ka koma yi...


kasan yadda tafiyar take a cikin tsananin zafin sahara? Toh lallai wannan shi ne zanen kaddara...




Domin shawarwari koh gudunmuwa 


pls ***


***************yar mutan Argungu``` ``` 鉂わ笍馃挋鉂わ笍