SHAFI NA 11
````````````ZUMUNTA 馃 KO MUGUNTA 馃懞?馃摎
MARUBUCIYAR...鉁嶏笍
***Ashe ba so ba ne***
***Bayan wuya...***
***zumunta ko mugunta? On typing...鉁嶏笍
BY-Fatima Zara Alhassan 鉂わ笍
ARGUNGU WRITERS ASSOCIATION 馃挄
GARGADI!!!
Kagaggen labari ne,sabo da haka ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba ta re da izinina ba,akiyaye!!!
JINJINA 馃憣
Ga yan'uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma hada kanmu,muyi zumunta鉂わ笍馃挋
GODIYA
Ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi bi sa iyawar sa, da kuma yardarsa.Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai suna (ZUMUNTA 馃 KO MUGUNTA 馃懞?)
MATAIMAKA
**Abubakar Shu'aibu birnin tsaba**
**Usman isah Rio**
**iman fatima Ibrahim**
GA RE KU MAKARANTA
Ni mai neman gyaran ku ce, sabo da duk mutum mai kuskure ne, idan har kunga wani gyara toh kofata a bude ta ke(***).
Free Book
SHAFI NA 11
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
********************************************************
*************************************************kasan yadda tafiyar ya ke acikin tsakanin zafin sahara? Toh lallai wannan shi ne zanen kaddara, tafiya acikin sahara ga zafi , ga babu guzuri, kuma ba bu takalmin da zai rage ma ka zafin sahara, yunwa da kishirwa...sai ya rage ma ka taki ka蓷an domin cimma manufar ka da burikan ka na rayuwa,sai kuma kayi katari da alkalamin kaddara, wac ce ta ke rubuta fari da baki. A lokacin za ka ji duniya ta yi ma ka zafi , kowa ya koma ya zuba ma ka ido. Allah sarki! sai ka ga lokacin duk inda za ka nufa cike ya ke da azzalumai. Duk inda za ka dafa mugaye cike su ke a gurin, kowa kokari zai yi domin asami dama daya tal! Haka zalika za ka ga ma kusantan ka su ne miyagun mutane, sabo da hassada da MUGUNTA, ba za su du ba ZUMUNTAr da ke tsakanin ku ba.
Abdul'aziz kar ka sake lokaci ya yi ka na me jin haka, tabbas inaji ajikina wani abu zai faru da kai, amma ban san komai akan hakan ba,amma ina rokon Allah ya sa ko ma minene toh ya kasance alkhairi,sabo da haka kar ka yadda duniya ta ba ka damar amsar wasikar jaki, rayuwar da aka gina bayan an saka Allah acikin ta, ba ta lalacewa. Duk mutumin da ya dogara ga Allah baya tab'ewa, idan kaga abu ya sa me shi, toh ubangiji ya yi hakane domin ya gyara mishi lamarin shi...
A jiyar zuciya Abdul ya yi, ya na mai kallon mahaifinsa,ta re da nazarin maganganun sa, tabbas wannan ita ake cewa" Hausa mai ban haushi" Idan har mutum bai zurfafa tunani ba, ba zai gane inda maganganun nan su ka dosa ba, abu na karshe kuma da ya fahimta anan shi ne, mahaifinsa na son ya kula sosai akan yan'uwansa, sabo da kiyayyar da suke nuna mishi,wanda shi kansa ya san da wannan...amma har ga Allah ba zai ce ga dalilin mahaifinsa na yi ma shi wadan nan zantukan ba...murmushi Malam ya yi sabo da ganin halin da Abdul ya shiga, shi adole ya na son sanin ina maganar ta dosa. "Abdul sanin gaibu sai Allah, ban ce maka lallai wani abu zai faru ba, cewa na yi inaji ajikina, ka ci gaba da addua ni ma zan ta ya ka yi in-sha Allah. Ta shi ka tafi, Allah ya yi ma ka albarka...
A sanyaye Abdul ya fito daga dakin mahaifin na sa, ya shiga wajen mahaifiyar sa. d'aga kai inna zainaba ta yi ta na kallon tilon d'anta, ta na kuma hango tarin damuwar da ke kwance a fuskar sa. Bayan ya zauna ta gabatar ma shi da abinci, ta na mai kara nazarinsa da kyau.
Kadan yaci abincin ya rufe kwanon, sabo da ba ya da appetite. "Abdul me ke damunka? ka na kallon kanka kuwa? kaga yadda duk ka bi ka rame...? "inna nima wallahi ban san meke damu na ba, amma ina ga ciwon malam ne, kuma yaki ba ri akai shi Asibiti! Ajiyar zuciya ta yi "wallahi nima ciwon malam na damu na, kwanan nan wasu irin mafalkai na ke yi masu ban tsoro." cikin tashin hankali Abdul ya ke kallon mahaifiyar shi..."inna wane irin mafalki ki ke yi, wanda ya sa ki ke zubar da kwalla?" "Abdul kasan cewa malam shine uwata shine ubana? malam ya rikeni tsakani da Allah, ban ce ba bu maza irin malam ba,amma dawuya asamu masu tausayi, soyayya,wadata iyali, hakuri da mace, da sauran abubuwan da ke faruwa a cikin rayuwa, fashewa ta yi da kuka, Abdul idan na rasa malam ban san me zanyi ba! ina yawan mafalkan ku kai da malam, ina ji ajikina kamar wani abu zai faru da ku...! "``` YAR MUTAN ARGUNGU``` `````` ... 鉁嶏笍鉂わ笍
DOMIN BA DA SHAWARA KO GUDUNMUWA
馃憞
***