SHAFI NA 12
```ZUMUNTA 馃 KO MUGUNTA?馃摎
Marubuciyar...鉁嶏笍
***Ashe ba so ba ne***
***Bayan wuya***
***zumunta ko mugunta*** on typing...鉁嶏笍
BY-Fatima Zara Alhassan 鉂わ笍
ARGUNGU WRITERS ASSOCIATION 馃挄
DOKA!!!
Wannan littafi kagagge ne,sabo da haka
ban yarda wani ko wata su yi amfani da kalma daya daga cikin littafi na ba, ba ta re da izinina ba,akiyaye!!!
SADAUKARWA
Ga iyaye na domin nuna godiya ta a gare su鉂わ笍
GAREKU MASOYANA鉂わ笍
Ni mai neman gyaran ku ce, sabo da duk mutum mai kuskure ne idan har kunga wani gyara, toh kofata a bud'e ta ke domin ga number waya ta nan don isar da sako kai tsaye zuwa gare ni...***(WhatsApp number ***)
SHAFI NA 12
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
**********************************************"Ina ji a jikina kamar wani abu zai faru da ku...!" Rungume mahaifiyar shi ya yi, ya na cewa "Inna ba ko yaushe mafalki ya ke zama gaskiya ba, mu ci gaba da yin sadaka domin ita ce ke kore duk kan masifu, idan kuma wannan abun na cikin kaddarar mutum, toh sai ya kasance abun ya zo mishi da sauki..."
Bayan ya ba ro d'akin inna, directly na sa d'akin ya wuce, ya zauna ya na tunanin maganganun da iyayen shi su ka fada mi shi,ta re kuma da nazarin su, toh me hakan ya ke nufi? Du ba agogon hannun sa ya yi, 11:30pm na dare, hakan ya sa ya tashi ya je ya d'auro alwala domin gabatar da sallar nafila, ba zai yi wasa wajen fad'awa ubangiji bukatun shi ba...
Yau gidan malam Abubakar cike ya ke da tashin hankali, sakamakon rasuwar malam,wanda ba iya kacin iyalansa ba,har ta mutanan gari sun ji wannan mutuwar! Haka aka yi jana'izar sa, ta re da d'unbin mutane, ta ko ina jama'a sun taru, sai dai muce Allah ya jikansa ya kuma sa ya huta tare da dukkan kulumin musulmai baki daya...
Bayan sati biyu aka shiga rabon gaado, amma Abdul hankalin sa ba ya kan rabon gaadon, sabo da mahaifiyar sa da ke kwance a gadon asibiti ba ta da lafiya, kamar tasan lokacinta ya yi, ha ka za ta saka Abdul gaba ta na yi mishi wasiyya. Allah sarki inna zainaba, ita ma kwanan ta biyar cif a Asibiti ta ce ga garin ku...
Dauko gawar ya yi, ya zo gida da ita aka yi ma ta wanka, sannan aka yi ma ta sallah aka kai ta makwancin ta, wanda duk mai rai sai ya riski haka, ya Allah ka sa mu gama da duniya lafiya,mu cika da imani...
Duk wanda ya Kalli Abdul zai san cewa ya yi babban rashi, ba bu iyaye sannan ba bu dangin iyaye, a gefe d'aya kuma ga rashin mutuncin da Brothers din sa , su ke yi mi shi, hatta gaadon sa da ya ke da hakki akan sa, duk sun tattara sun handame, sai sauran filayen su na noma, ya kai karar su amma abanza, kun dai san yadda azzalumai su ke a wannan lokacin...a lokacin ne ya dauko takardun shi na makaranta domin neman aiki, amma bai samu ba. Duk manyan mutanan da ya san ya yi huld'a da su a baya, haka ya dinga bin su domin samun madafa amma shiru ka ke ji " kamar an aika bawa garin su" sabo da a wannan zamanin na mu, sai ka na da shi ake yi da kai,wallahi da zarar ba ka da shi, toh kai da ban za duk d'aya ku ke, mai karfi shi ake k'arawa k'arfi, kai kuma talaka a k'ara durk'ushe ka. Toh hakan ce ta faru ga Abdul'aziz Abubakar mai Noma; Cikin iyawar ubangiji sai ga shi wa su mutane sun ba shi aron gonakin su ta re da ba shi gudunwar kudi, wa su kuma su ka ba shi iri na shuka, ya yi murna sosai fiye da tunanin mai karatu...
lokacin damuna, haka ya kwashi ma aikata, su ka yi aiki sosai, gona biyu ce d'aya ya shuka shinkafa d'aya kuma waken soya, kuma kowa ce gona ya na saran ya samu buhu saba'in ko sittin,in Allah ya yar da....
Allah sarki! rayuwa kenan," kana ta kanka,a lokacin kuma wani ta taka ya ke yi" toh hakan ce ta kasance ga Abdul, bayan amfanin gonar sa, sun isa cirewa, kwatsam sai ga wani babban al'amari ya faru....!
*****************************************
My dear Readers, wlh ku na raina a ko da yaushe, dan Allah ku yi hkr kwana2 ban yi muku post ba,hakan ya na da alaqa da rashin lfyr da na yi,amma in-sha Allah daga yanzu za ku dinga ji na akai-akai
FISABILILLAH...COMMENT,SHARE,FOLLOW
鉂わ笍Y**A**R**MUTAN ARGUNGU``` ...鉁嶏笍馃摎鉂わ笍