SHAFI NA 13
```ZUMUNTA 馃 KO MUGUNTA?馃摎
marubuciyar...鉁嶏笍
**Bayan wuya**
**Ashe ba so ba ne**
**Zumunta ko mugunta on typing...鉁嶏笍
Writing by-Fatima Zara Alhassan 鉂わ笍 (Yar'mutan Argungu)
ARGUNGU WRITERS ASSOCIATION 馃挄
GARGADI!!!
Kagaggen labari ne. Sabo da haka ban yarda wani ko wata su yi amfani da kalma d'aya daga cikin wannan littafi ba, ba ta re da sanin marubuciyar littafin ba,haka kuma duka sunayen da ke ciki kagaggu ne. A KIYAYE!!!
GODIYA!
Ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi bisa iyawarsa da kuma yardar sa. Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai suna( ZUMUNTA KO MUGUNTA)lfy.
SADAUKARWA
ga yan'uwana, domin nuna mahimmancin ZUMUNTA, da kuma kaucewa rud'in zuciya domin kar ta kaimu ga yi wa yan'uwan mu MUGUNTA
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA PLS *** KO KUMA WHATSAPP NUMBER ***
FREE BOOK
SHAFI NA 13
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
********************************************* Kwatsam! Sai ga wani Babban al'amari ya faru...
Tun jiya Abdul ya yi magana da ma aikatan da za su yi mishi aikin cirar amfanin gonakin sa. Yau tun da safe ma aikatan su ka iso kofar gidan su Abdul don tafiya gona,su ka yi sallama, Adamu ne ya fito ya na huhura hanci yadda kasan bututun mai haka ya ke d'age hancin shi sama, "uban waye ya ke damun mu da sassafen nan?!!" Gaishe shi su ka yi, san nan su tsaya yi mi shi bayanin wurin wanda su ka zo nema, "oh kune ma aikatan wancan yaron koh?" a ta re su ka ce ehh ranka shi dade... Murmushi ya yi wanda ake cewa na ciki na ciki, san nan ya ce ku bari in kira mu ku shi..bayan ya shiga cikin gida ya iske inna Atika a bakin murhu san nan ya ce "inna wai ina d'an banzan yaron nan ya ke ne..kafin ya kai karshe sai ga Abdul ya fito daga cikin d'akin sa ta re da shirin zuwa gona, a hankali ya tako har gaban inna Atika ya duka " inna ina kwana" kallon shi ta yi shekeke tun daga kai har kafa, san nan tace " da ban kwana ba za ka ganni, ka ga ka fita daga ido na in rufe!wlh da kasan yadda na tsani in bud'e idanuwana in gan ka acikin gidan nan, na tabbata da ba za kazo ku sa da ni ba, sabo da kai kowa ya tsani ya'yana, duk wanda ya tashi Abdul kowa Abdul sai ka ce kai kad'ai ne yaro acikin garin nan...za ka tashi kaban wuri ko sai na shuka maka rashin mutunci a anan wurin!!!'
Cikin sanyi jiki ya tashi ya fita,yana mai kara jinjina kiyayyar da matar baban sa ta ke nuna mi shi,amma ya san duk wannan abun ba komai ba ne fac ce hassada...
Bayan ya wu ce,Adamu ya dubi mahaifiyar su, ya ce "inna, wallahi na tsani wannan shegen yaron, mune manya amma Abdul ya fimu masoya, wani lokacin kuma wallahi ya na ba ni tausayi...kai dallah tafi can sakaran banza wanda bai san ciwon kansa ba!!
tausayi, wallahi yanzu ya fara gani indai ni ce Atika, ba yana takama ya samu gonaki har yayi shuka ba? Toh yau zai je ya girbe shukar sa mai kyau, dan wallahi mud din ina cikin duniyar nan toh Abdul da shi da arziki sai alahira acan d'in ma dan ban da yadda zanyi ne da na yi wallahi!!! amma da ni ya ke wasa, zaman garin sai ya gagare sa, da kafarsa zai fece kuma ina zaune ka ce ni na fad'a ma ka!!" Shewa sukayi san nan su ka tafa(kunji wani zance na inna Atika,sai ka ce a hannun ta kaddarar Abdul ta ke? Amma muje zuwa duk zakaran da Allah ya nufa da caara...?)
******Bayan fitowar Abdul daga gida, su ka kama hanyar gona, isar su ke da wuya
Abdul ya yi tozali da gonakin sa duk sun k'one bakikirin,har ta kasar wurin za a sha fama kafin a iya sake noma awurin, ba bu abun da ya fito daga bakin shi sai kalmar. " Innalilllahi wa inna ilaihir raji'un脳3
mamaki da al'ajabi su ka kama ma' aikatansa, sabo da ganin yadda gonar ta koma, wannan ko rantsuwa mutum ya yi ba zai yi kaffara ba, saka wutar aka yi... rike shi su ka yi ganin cewa ya yi suman tsaye. A haka su ka dauke shi sai gida...ko kafin ka ce kwabo! labari ya cika gari, wa su ma har kara gishiri su ke yi a labarin
Ma su yi mishi jaje na yi, suma yan'Allah kara na yin na su...
Wasa-wasa sai da zaman garin JADA ya gagare shi, haka ya tattara komatsen sa ya fice daga garin, bai zame ko ina ba sai tasha wajen shiga mota, shi kan shi a lokacin idan ka tambaye sa inda zai je bai sa ni ba, kwatsam! ya ji conductor na cewa "katsina...katsina, hakan ya samu kansa da cewa katsina zai tafi(wannan shi ne farkon zanen kaddarar Abdul).
Bayan motar su ta cika,san nan su ka kama hanya sai birnin katsinan dikko...
LITTAFIN ZUMUNTA KO MUGUNTA, YA NA IYA KASANCEWA NA KU茒I, A KO WANE LOKACI KU ZAMA CIKIN SHIRI, AMMA IDAN NA GA RUWAN COMMENTS,KILA INA IYA CANZA RA'AYI BA SAI NA SAYAR BA馃摎
COMMENTS
AND
SHARE```
YAR'MUTAN ARGUNGU 馃摎鉂わ笍馃挋鉂わ笍