SHAFI NA 14
ZUMUNTA 馃 KO MUGUNTA 馃懞...鉁嶏笍
marubuciyar...鉁嶏笍
**bayan wuya**
**ashe ba so ba ne**
**zumunta ko mugunta? on typing...鉁嶏笍
writing-by Fatima Zara Alhassan 鉂わ笍
鉂わ笍ARGUNGU WRITER'S ASSOCIATION 鉁嶏笍
Gargadi!!!
kagaggen labari ne. idan ya yi dai-dai da rayuwar ku, toh akasi ne. kuma wallahi ban yadda a juya min littafi ba ta re da izini na ba! Free page ne, zai iya zama na kudi ako yaushe, akiyaye!!!
Jinjina
ga yan'uwa na Allah ya bar zumunci, ameen鉂わ笍馃挋馃挌
Godiya:
ga ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka muku da alkhairi nagode鉂わ笍
Ban manta da ke ba fatima iman Ibrahim 鉂わ笍
ta re da Abubakar Birnin tsaba馃憣
godiya ta musamman ga USMAN RIO馃憤
FREE PAGE馃摎
k/wata 3/10/2022
SHAFI NA 14
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
*********************************************************San nan su ka kama hanya sai birnin katsinan dikko...
Motar su ba ta tsaya a ko ina ba sai a Tashar NATO. Bayan sun sauka driver ya sauke mu su kayan su, kowa ya kama gaban sa, amma ban da Abdul. Samun wuri ya yi anan cikin tashar ya na tunanin rayuwa, duk wanda ya ce mi shi rayuwa za ta sauya mi shi haka wallahi ba zai yadda ba, amma ya san cewa dukkan tsanani ya na ta re da sauki, kukan yunwar da cikinsa ke yi ne ya dawo da shi daga duniyar tunani...Hannu ya sa ka acikin aljihun sa domin dauko sauran kudin da su ka rage mi shi, aka ce ya dauka in ya gansu ( watoh an sace kudin), kara dubawa yayi, da mamaki ya ke kallon kasan aljihun na sa, wanda aka yanke... murmushi ya yi wanda ya fi kuka ciwo, ya na aikin me hakan ta faru? zuciyar shi ce ta ba shi amsa "ka man ta mai son abun ka ya fi ka dubara?" Dogon numfashi ya ja...ya na mai jinjina al'amarin mutane, wato kowa kansa ya sa ni, ba bu wanda ya damu da halin da ka ke ciki. Tunawa ya yi kamar ya saka wa su canji acikin aljihun gaban rigar sa, ai kuwa ya na sa ka hannu sai ga wata tsohuwar d'ari biyu. Tun d'azu ya ke wannan tunanin ya kira ta ko kar ya kira? Sabo da rabon da su yi waya tun rasuwar mahaifiyar sa, a lokacin da ta kira shi ta yi mi shi ta'aziyya, sai kuma ya zo ya sayar da wayar sa sabo da bukatar yau da kullum...
Haka dai ya bi zabin zuciyar sa, ya ari wayar driver ya sayi katin naira dari(100) ya saka aciki...
Zaune ta ke akan makeken gadon ta, kallo d'aya za kayi ma ta kasan cewa akwai damuwa a tattare da ita, amma ta na kokarin boyewa...Da Sallama sister ta, ta shigo cikin d'akin san nan ta ce "yaya Lima mommy na kiran ki sabo da haka ta ke ce ma ta." A hankali ta bi bayan sister ta. A parlo su ka tarar da mommy zaune ta na kallon TV, zama su ka yi san nan Halima ta ce "Mommy gani"
"Halima ya kamata yanzu ace kin cire maganar Abdul'aziz ,acikin zuciyar ki, tun da ya zo gidan nan sau d'aya, har yanzu bai dawo ba, kullum sai kice ayi mi shi uzuri zai zo,Ha ba Halima! ya kamata ace yanzu ki yi wa kanki karatun ta natsu, ki fitar da miji cikin mane ma Auren ki, tun da ba ra sa su ki ka yi ba, toh magana dai ta karshe ita ce mahaifin ku ya ce in fada mi ki ya ba ki nan da wata daya,muddin ba ki tsayar da wanda ki ke so ba a cikin manemanki, toh wallahi za ki ga bacin ransa sosai! Sabo da haka ki cire wani Abdul daga ranki, ki rungumi kaddarar ki hannu biyu, amma idan kuma har Allah ya sa Shi Abdul din mijin ki ne, toh za ki ga kafin wa'adin da aka d'ibar mi ki ya cika zai zo, sabo da matar mutum kabarin sa."
"Insha Allah mommy ta, zan kasance mai biyayya a ga re ku, amma dan Allah ki ta ya ni da addua kin ji mommy?"
"kar ki damu Halima kullum cikin yi muku addua mu ke yi, Allah ya yi mu ku zabi na alkhairi ke da yar' uwarki"
"Amin mommy, su ka rungume ta a ta re...
Haka su ka zauna su na firar su ...karar wayar Halima ce ta cika parlon, tun d'azu ake kira amma ba ta dauka ba, kasan cewar number ce ba bu suna, "Halima ba ki ji ana kiran wayar ki ba ne? ki dauka ma na". mommy ba suna number ce , toh idan number ce shine ba za ki dauka ba? kubar yin hakanan!. sa ke kira aka yi akaro na uku...Dauka tayi ta na jin muryar mai yi ma ta sallama, cikin kaduwar jiki ta furta Abdul! a bangaren Abdul kuwa murmushi ya yi san ya ce ma ta ya shigo katsina amma yanzu zai zo gidan su, cikin murna ta ce toh sai ka zo...
Bayan sun gama waya ta juyo ido biyu su ka yi da mommy, nan ta ke kunya ta kamata, murmushi mommy ta yi san nan ta ce addua ta, ta karbu kenan ta na dariya.
Bayan daddy ya dawo, mommy ta fada mi shi Abdul'aziz zai shigo zuwa anjima, ya yi farin ciki sosai, ya kuma yi fatar Allah ya sanya alkhairi.
Da kyar Abdul ya samu mai mashin ya dauke shi akan naira d'ari zuwa Barhim estate. Bayan ya isa gidan su Halima, da mamaki ta ke kallon shi, kamar ba Abdul dinta mai gayu ba, ko kadan ba ya wasa da tsafta, amma kuma idan ka dube shi da kyau za ka ga akwai damuwa a tattare da shi, wanda idan ba kallon tsaf ka yi mi shi ba, toh ba za ka ga ne ba...
Haka ta yi mi shi jagora zuwa cikin gidan su, daddy da kansa ya tarbe shi hannu bibbiyu, sabo da akwai shi da son mutane, ballan ta na wanda ke son yar' sa, bayan sun gaisa aka gabatar mi shi da abinci ta re da abun sha,bayan ya gama su ka kara yi mi shi gaisuwa akan rashin iyayen sa...
San nan daddy ya nemi karin bayani akan Abdul, duk da yana jin labarin Abdul d'in amma bai san shi ba, sabo da wancan zuwan na sa ba ya gari, amma duk da haka ya na son takaitaccen tarihin sa, kun san waka a bakin mai ita tafi dadi...
Sunana Abdul'aziz Abubakar mai Noma...
haka ya kwashe labarin sa ya fadawa su daddy,kowa ya tausaya mi shi, shiyasa aka ce ku ji tausayin mai mulki idan ya rasa ko mai dukiya, su din abun tausayi ne.
Wannan shi ne farkon zaman Abdul a karkashin daddy, duk wasu gonakin daddy ba bu wadda Abdul bai san da zaman su ba, arzikin daddy ya ninka na da, shiyasa ya ware wa Abdul gonakin sa na shuka AYA, ko kafin ka ce kwabo! katsina tafi ko wace jaha noma AYA a cikin Arewa.
Shima Abdul'aziz arzikin sa ba a cewa komai. Haka akayi bikin Abdul da Halima, su na zaman su cikin kwanciyar hankali da kuma kaunar juna...Bayan shekara daya Allah ya azurta su da samun k'aruwa, yarinya ta ci sunan mahaifiyar sa, amma su na kiran ta da Aneesa.
Duk ranar asabar Abdul na zuwa da iyalan shi gidan gonar sa, wadda ta ke a malumfashi, domin shakatawa, yauma hakan ce ta kasance, su ka shirya su ka tafi, gona ce babba sosai, gefe daya anyi ginin zamani, mai kyau kamar ba daji ba, sai kuma d'ayan gefen wanda d'akin mai gadi ya ke a wurin, a gefen haggu kuma itatuwa ne daban-daban na kayan marmari( Ya'yan itatuwa)..
Aneesa ce ke rarrafe a farfajiyar wajen, idon ta ne ya kyalla akan wani Zomo fari fat mai d'aukar ido , gefe d'aya kuma ga wani katon maciji na son sarar wannan zomon, abun ka da k'urciya, don a lokacin watan ta 7, kamar ance iyayen su kalla, aikuwa su ka yi ido biyu da wannan macijin wanda ke son sarar zomon da ke hannun Aneesa...
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA
PLS
***
KAR KU MAN TA DA:
**COMMENTS
AND
**SHARE
TA KU HAR KULLUM...
鉂わ笍YAR MUTAN ARGUNGU``` 馃摎鉂わ笍