ZUMUNTA KO MUGUNTA

SHAFI NA 15

by @yarmutanargungu

```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺?📚




MARUBUCIYAR...✍️


***Ashe ba so ba ne***


***Bayan wuya...***


***zumunta ko mugunta? On typing...✍️


BY-Fatima zara Alhassan 💖

(ƴar mutan Argungu)


ARGUNGU WRITERS ASSOCIATION 💕



GARGADI!!!

ƙagaggen labari ne,sabo da haka ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba ta re da izinina ba,akiyaye!!!



JINJINA 👌

Ga yan'uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma haɗa kanmu,muyi zumunta❤️💙



GODIYA

Ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi bi sa iyawar sa, da kuma yardarsa.Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai suna (ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺?)



MATAIMAKA


**Abubakar Shu'aibu birnin tsaba**


**Usman isah Rio**


**iman fatima Ibrahim**




GAREKU MA SU BIBIYAR LITTAFAI NA.

Ni mai neman gyaran ku ce, sabo da duk mutum mai kuskure ne, idan har kunga wani gyara toh kofata a buɗe ta ke(***).




29/10/2022




Free Book



SHAFI NA 15


BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM

*************************************************Cikin tashin hankali iyayen Aneesa, su ka nufi wajen, domin kaiwa tilon ƴar su ɗauki. Zuwan su ne ya sa macijin saurin buɗe kansa da nufin ya kai wa ZOMON nan sara.  Abdul bai san lokacin da ya yi tsalle ta re da sandar da ke riƙe a hannun sa ba, ta re da kiran sunan Allah, ya bugawa macijin akansa. Wani irin tsalle macijin ya yi da nufin ya koma kan Abdul, amma Allah bai ba shi sa'a ba. Da sauri su ka ɗauke Aneesa, wadda sam sam hankalin ta bai tashi ba, sabo da ba ta ma san abun da ke faruwa ba..


A haka ma su gadin gonar su ka bazama wurin neman wannan macijin, amma ƙasa ko sama ba su gan shi ba...



wannan abun da ya faru, shiyasa su ka tattara kayan su za su wuce gida. Bayan sunyi sallama da ma su gadi. 


Sun fito kenan za su wuce sai ga wasu zomaye su biyu macce da namiji, ɗaya babba ɗayan kuma bai kai shi ba, can kuma sai ga wancan zomon da Maciji ya tashi cizo, shi ma ya zo ku sa da wanɗan nan ya tsaya, sai su ka taru su na kallon su Aneesa har su ka ɓacewa ganin su...



Bayan shekaru huɗu, abubuwa da yawa sun faru, ciki har da rasuwar iyayen Halima, bayan sun yi haɗarin mota, da kuma zuwan Abdul JADA, sabo da jin hukuncin duk mai yanke ZUMUNTA da kuma falalar da ke cikin sada ZUMUNTA



ganin yadda yan'uwansa su ke rayuwar ƙasƙanci da kuma zallar talauci, sai a lokacin ne ya ke jin labarin, Inna Atika ta haukace kuma an neme ta ba a ganta ba...


Kun san ance zuciya ba ta da kashi, haka ya sa, Abdul ya ji tausayin su, ta re da yi mu su alƙawarin zai samo mu su mafita.



Bayan ya koma katsina ya yi shawara da matar shi, Halima akan halin da ƴan uwan sa su ke ciki, ya na kuma neman shawarar ta...


Ta na jindadi duk lokacin da mijin ta ya zo neman shawarwari awurin ta, da wuya ya zartar da hukunci ba ta re da ya nemi jin ta bakinta ba, hakan na yi ma ta dadi sosai, shiyasa ta ke natsuwa ta ba shi shawara mai kyau,  toh hakan ce ta kasance a yanzu ma...



Ta nu na mishi cewa ya samar mu su gonaki acikin garin JADA, san nan ya saya musu gida ko ya gina mu su wani, sabo da wancan tsohon gidan na su na Da, sisi ma albarka. sabo da ita har ga Allah tafi son ya bar su acan JADA ɗin, ba wai don ba ta son su ba ko kuma don su na dangin mijin ta ba, a'a sai dan ganin cewa duk mutumin da ya ce baya son ka, daga baya kuma ya dawo ya ce yana sonka toh wallahi karyane...



amma ga mamakin ta, sam Abdul bai yi na'am da zancen ta ba, abun da kuwa bai taɓa faruwa a tsakanin su ba.Ta nu na mishi illar ɗauko su, amm sam ya yi kunnen uwar shegu da zancen ta. A haka ta koma gefe ta zubawa sarautar Allah ido.



Alokacin da ya ɗauko ƴan uwa shi, Aneesa ta gama primary school going to secondary school. Bayan ya nu na mu su wuraren da za su yi na su aikin, ya kuma haɗa su da ƙwararrun maaikatan sa, domin su nu na musu abubuwan da ba su sa ni ba...


**************


           Rayuwa kenan, ance kasha daɗi kasha wahala. ko kafin kace kwabo, su Adamu sun zarce yadda ku ke tunani. Amma kun san mai hali ba ya fasa halin sa, sabo da har yau da na ke faɗa mu ku , su na nan da ƙudirin su a cikin zuciyar su...


A ranar da Aneesa ta kammala secondary school ɗin ta, da wata biyu, wanda ya yi dai-dai ga ranar da ba za ta taɓa mantawa ba, shi ne lokacin da aka kashe ma ta iyaye...


Sabo da a lokacin idan har ba ta manta ba, akwai ranar da ta dawo daga islamiyya, ta iske ran Baffan ta a ɓace, ummanta kuma ta na zaune ku sa da shi, ta na ba shi haƙuri. "cikin nuna abun da aka yi mi shi ya ɓata mishi rai sosai! Halima har yaushe ne ni kam zanji daɗin ƴan uwana? yanzu abun da su Yaya su ke yi min dai-dai ne fisabilillahi!? su sa yar min da gonaki biyu, san nan su ce ban isa inyi mu su magana ba akan me! toh wallahi nagaji, su tattara inasu-inasu su wuce, tun da su ba za su taɓa canza hali ba, dama tun farko sai da ki ka gargaɗe ni, amma na yi kunnen uwar shegu da zancen ki, Halima wannan wane irin ZUMUNTA ne ko ince MUGUNTA? 



A jiyar zuciya Halima ta yi, san nan ta ce " Abban Aneesa dan Allah ka kwantar da hankalin ka, duk abun da zaman lafiya bai ba da ba, wallahi tashin hankali ba zai ba da shi ba, duk abun da ya yi tsanani maganin sa Allah, amma kam tabbas ba su kyauta ba, kuma ba bu inda ake sayar da abun wani ba ta re da izinin mai shi ba, kuskure dai ne sun ri ga sun yi shi ayi haƙuri a ta ri gaba."  


Sun yi wannan maganar da sati ɗaya. Kwatsam! Sai ga su kawu Adamu, da daddare ta re da ƴan fashi, abun da ya tada hankalin mu ainun, bayan sun nemi Baffa na da ya saka mu su hannu akan takardun dukiyar shi, waɗanda su ke mallakin sa, amma yaƙi, sabo da a cewar sa, ba zai yi yu kura da shan bugu gardi da karbe kudi ba, ba zai yarda a ce duk gwagwarmayar da ya sha a rayuwa, amma wai lokaci ɗaya ace ya bayar da dukiyar sa, wallahi sai dai duk abun da zai faru ya faru.Hakan ne ya fusata wa su ƴan fashi biyu dake can gefe ɗaya harbin mahaifina a ƙirjin sa, mahaifiya ta kuma akai, hakan ya sa na gigice ta re da ɗimaucewa, duk da a lokacin ba na cikin hayyaci na, amma ba zan taɓa manta muryoyin da ke magana a gaba na ba. Ɗagowar da zanyi, ya yi dai-dai da cire baƙin ƙyallen da ke ɗaure a fuskar su, kawu Tukur da Adamu... harbin da aka yi min ne a ƙafar hagu,  shiyasa na sume a wurin,ban sa ke sanin inda kai na ya ke ba.


A ɓangaren su kawu Adamu, bayan Aneesa ta sume a wurin, tabbas sauran ɓarayin da su ka zo da su, sun so abar Aneesa a wurin su wuce kawai. Amma kawu Tukur ya ce sam, ba za a bar ta ba, sabo da ba ta mutu ba, idan su ka bar ta asirin su zai tonu, kawai su kashe ta su huta. Har ya ɗana kunamar bindigar sa, sai ɗan fashin ya ce kar su kashe ta, sabo da jin jiniyar motar ƴan sanda. Amma sabo da ƙarfin haki irin na Tukur sai da ya ɗauki Aneesa, su ka wuce da ita. Haka ya jefar da ita a cikin daji. Duk wannan abun bai isheshi ba, sai da ya koma wajen malamin sa na tsibbu, ya sa aka haukatar da Aneesa.


Wannan shi ne labarin rayuwar Aneesa...



GODIYA TA MUSAMMAN GA MASOYA NA MA SU BIBIYAR LITTAFAI NA. ❤ALLAH YA BAR MU TA RE DA KU


INA MAI FARIN CIKIN SANAR DA KU CEWA, DAGA YANZU ZA KU IYA SAMUN LITTADI NA A @WATTPAD


sai na ji ku


DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA


    PLS


     👇


***



KAR KU MAN TA KU YI MIN


***VOTE***


***SHARE***


***COMMENT***




  Ta ku akullum


            ƳAR MUTAN ARGUNGU``` ❤📚