ZUMUNTA KO MUGUNTA

SHAFI NA 16

by @yarmutanargungu

```


ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️



marubuciyar...✍️


**bayan wuya**


**ashe ba so ba ne**


**zumunta ko mugunta? on typing...✍️




writing-by Fatima Zara Alhassan ❤️


ARGUNGU WRITERS ASSOCIATION 💕


Gargadi!!!

kagaggen labari ne. idan ya yi dai-dai da rayuwar ku, toh akasi ne. kuma wallahi ban yadda a juya min littafi ba ta re da izini na ba! Free page ne,ban ya fe ba, duk wanda ya sayar da shi,akiye!!!




Jinjina 👌

ga yan'uwa na Allah ya bar zumunci, ameen❤️💙💚



Godiya:

ga ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka muku da alkhairi nagode❤️



Ban manta da ke ba, fatima iman Ibrahim 😘



K/wata: 30/10/2022



Free Book📚



SHAFI NA 16



BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM


**********************************************************A jiyar zuciya su ka yi, ya yin da ita kuma Aneesa ta sa ka tafin hannun ta domin share ƙwallar da ke zubowa a fuskar ta, ta re da son yi mi shi magana. Du ban ta ya yi da kyau ya na mai ƙara jin tausayin ta, san nan ya ce "ki tashi mu tafi, na san yanzu haka sarauniya tana can ta na dubin hanyar mu. A'a Aneesa ba sai kince komai ba, ki aje duk wa su tambayoyin ki har mu isa masarauta, na tabbata sarauniya ba za ta ƙi amsa mi ki duk wa su tambayoyi da ke cikin zuciyar ki ba."


Ba ta re da ta yi mi shi gardama ba ta ce " toh". 


Hakan ya sa shi miƙewa tsaye, ta re da girgiza jikin sa, ya na wa su irin surutai...


gefe ɗaya ta koma ta na kallon ikon ubangiji, ganin abun ta ke tamkar a majigi, ganin ta ke yi kamar mafarki ne, wanda ako wane lokaci ta na iya farkawa...


A tsorace ta ke kallon sa, ganin ya koma wata halitta ta daban. Ya lura ta na son sume mishi ne, shiyasa ya su re ta( ya ɗauke ta) da hannun sa, sai akan fukafikin sa, nan ta ke su ka lula sararin samaniya, yau ga Aneesa a cikin gajimare. Tun ta na ɗarɗar har tafiyar ta yi ma ta daɗi sosai....


cikin saa'a( 1 hour) sai ga su a bakin masarautar su fu'ad. Masarauta ce mai girman gaske, daga shigowar ka cikin masarautar za ka fara jin kiɗan algaitu ma su sauti mabambanta.


A hankali ya saukar da ni daga kan bayan sa, nan ta ke kuma ya rikiɗe zuwa fu"ad ɗin da na sa ni, haka mu ke ratsa wurare ma su ban sha'awa da ɗaukar ido, ka na ƙara shiga cikin masarautar ta na kuma ƙara yi ma ka kyau. wata hanya ce yarima fu'ad ya bi da ni, sai da numfashi na ya tsaya na wa su daƙiƙu,wuri ne wanda tun da na ke a duniya ban taɓa mafarki ko jin labarin wuri mai kyau da ban sha'awar sa ba, ga furanni ma su ƙamshi launika iri-iri, ƙorama ta na kaiwa ta na kawowa gwanin ban sha'awa, ga ƴaƴan itatuwa nan iri- iri,ga tsuntsaye nan su na waƙoƙi da mabambantan sautuka ma su natsar da zuciyar mai sauraro. kai a taƙaice dai irin wannan wuri alƙalami na ya yi kaɗan wajen rubuta mu ku irin tsaruwar wajen...Wani irin taku ya ke yi irin na ƴaƴan sarakuna, duk inda mu ka ratsa Bayi ne ta ko ina birjik su na kawo mi shi gaisuwa, haka ya ke ɗaga mu su hannu ya na wucewa,. Isarmu kofar palace ɗin ke da wuya, sarauniya Ayra ta re da gimbiya Hoor, su ka rungume shi, su na yi mi shi lale marhabin da sarkin farisa...


San nan su ka da wo kaina su ka rungume ni su na cewa " barka da zuwa masarautar farisa, mu na farin ciki da zuwan ki" Jarumta na aro, san nan na ƙawa ta fuska ta da murmushi, na ce "nagode" hannu na su ka riƙe mu ka shiga cikin gida.


Haukar da na yi a waje a she bakomai ba ce, wani irin parlor ne mu ka shiga wanda zan iya cewa duk faɗin nigeria ba za asamu parlor mai girma da faɗi, uwa uba akai ga kayan more rayuwar da ke cikin sa ba, gaskiya ba za a samu ba.A hankali sarauniya Ayra ta zaunar da ni a ɗaya daga cikin kujerun diningtable ɗin da ke wurin wanda aka cika shi da kayan abinci nau'i daban-daban, wannan shi ake kira in ba ka ci ba ni waje...


Gimbiya Hoor ta zubamin abin da ta ga kamar shi zan iya cinsa, ta aje mini a ga ba na, ta re da sakar min murmushi, wanda na lura yin murmushin kamar a jinin su ne, da fa kafaɗa ta tayi ta na mai cewa "sister bismillah" nima murmushin na sakar ma ta ina mai cewa " nagode"


Bayan mun gama cin abinci, aka kaini ɗakin da zan zauna, uhum ba a cewa komai ( idan na ce zan zaiyano mu ku haɗuwar ɗakin, wa su sai su ce na yi ƙarya, shiyasa zan bar ku da kan ku, ku ƙiyasta kyansa).


Ina gama wanka na rama sallolin da ake bi na, san nan nayi azkar,ina mai ƙara jinjina hukuncin ubangiji, wallahi har yanzu ganin na ke yi kamar mafarki ne, har yanzu na ka sa yarda abun da ke faruwa gaske ne. Da wannan tunanin ne barci ɓarawo ya yi gaba da ni...


Kiran sallar magrib ya sa ka Aneesa miƙewa daga kwancen da ta ke, ta nufi banɗaki (toilet) domin ɗauro alwala.Ba ta tashi akan daddumar ba har sai da aka kira sallar isha'i, ta miƙe domin gabatar da sallah. Sallemewar ta ke da wuya, ta ji an turo ƙofar ɗakin a hankali, gimbiya Hoor ce ta shigo ta re da mai da marfin ƙofar ta rufe, da sallama ɗauke a bakin ta. Miƙewa Aneesa ta yi ta na naɗe dardumar sallan, murmushi ta sakawar gimbiya Hoor ta re da cewa "ina wuni gimbiya," " lafiyalau Aneesa ya baƙunci?" 


Murmushi kawai Aneesa ta yi, san nan gimbiya Hoor ta ce " Sarauniya ta ce ki zo ki ci abinci ke kaɗai ake jira...


Kai tsaye su ka nufi ƙayataccen diningtable, a zaune su ka iske sarauniya ta re da yarima fu'ad, da alamu su kaɗai ake jiran isowar ta su...


Cikin ladabi Aneesa ta durƙusa har ƙasa ta gaishe su, amsa ma ta su ka yi san nan , sarauniya ta ce ta tashi ta hau kujera su ci abinci. Bayan sun fa ra cin abincin ba ka ji sautin komai, kowa ya mai da hankalin sa wajen ƙoƙarin ba wa cikin sa haƙƙin sa. Sarauniya ce ta fa ra miƙewa, ta re da kallon ɓangaren yarima fu'ad san nan ta ce " yarima idan ku ka gama cin abinci ina son yin magana da ku, ku sa me ni a ɓangare na." San nan ta wuce ba ta re da jiran amsar su ba.


Wu cewar sarauniya ba da jimawa ba, su ma su ka kammala, san nan su ka nufi ɓangare ta...


Wani babban parlor Aneesa ta ga sun shigo, a jiyar zuciya ta sauke a lokacin da ƙafar ta, ta lotse cikin wani lallausan kafet(carpet) lokaci ɗaya kuma wani ƙamshi ya bugi hancin ta, mai sanyayyen daɗi, ( sandal nur kenan,  turaran wuta ne amma kamar na feshi, ya na sanya kwanciyar hankali a cikin gida. Ma za ku garzaya Hway incense🌹 domin ɗauko rabon ku, ana sayar da ɗaiɗai ko sari. )



zama su ka yi akan lutsa-lutsan kujeru.


San nan sarauniya ta fa ra da cewa...




HAR WA YAU DAI KAR KU GA JI DA NI, WAJEN YI MIN 👇


        **comment**


        **share**



ZA KU IYA SAMUN LITTAFI NA #Wattpad#


  


SAI NA JI KU❤




DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA PLS


   👇


***




TA KU HAR KULLUM📚


                     ❤ƳAR MUTAN 


                   ARGUNGU``` ❤