WANI RABON........

CHAPTER 5

by @deejasmah

WANI RABON..............🦋🦋🦋


Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)


Elegant Verified Writers (E.V.W)


In dedication to all single ladies.........❤


Are you a writer or an aspiring writer but without an association ? Are you that one that writes but doesn't have much shares and less audience ? Have you been dreaming to be that great writer but you don't have anyone to review your write-ups and rate it ?

Then your time to rise and shine is here as Elegant Online Writers have given out that opportunity to young and talented writers to join its great platform to work towards achieving one's goals at the best rate you can ever get 


Pay 1k per form and the next thing is you are already in the platform !! 

They offer training and lectures for writers to make sure your write ups are error free and to prepare you for becoming that your dream writer 

Contact 

@ gimbiya : ***

@ Nimcyluv: ***


Don't miss this opportunity!!!!!!


CHAPTER 5 (Corper)


This page is dedicated to a friend more than a sister who lost her life in the early hour of today Allah yaji qanki safiyyah yai miki rahama yasa kyawawan halayyarki ya biki ya kuma sada ki da masoyinki annabin rahama 


Dan Allah in kaci karo da page d'innan kai mata addua Allah yasa tana cikin mafi yalwar dad'i da ni'ima 😢💖


Some months later 


Ranaku suna ta shud'ewa muna zaune a gida ban aikin komai hakan yasa nai enrolling a wani content creation class cikin saa kuma na fara k'warewa da gogewa a harkar cikin lokaci k'alilan aka yaye y'an set d'inmu na kuma zaman gida


Content na fara creating on my own kasancewar banda clients saidai inyi in ajiyesu a system saida na tara ne na bud'e sabon page a Instagram na fara d'aura contents d'ina costumers kad'an na fara samu sai a hankali due to refferals na fara samun wasu musamman da ya kasance akwai creativity a ciki kana inayinshi a farashi mai rahusa babu tsawwalawa 


List d'in Batch 1 NYSC ne ya fara fitowa hakan yasa nai gaggawar duba mana namu nida bestie cikin saa kuwa saiga sunanmu a batch d'in saidai ita Kaduna yayinda ni kuma gombe akai posting d'ina screenshot nayi na tura mata yayinda nawa kuma na jirayi dawowan Mamie 

Koda Mamie ta dawo ina parlor saida na jira ta huta kafin na nufi dak'in nata tana kwance ta mik'e k'afar ta akan rug kusa da ita na zauna ina sake gaisheta " naji ana cewa Batch "A" ya fito kin duba kuwa ?" ta

tambaya 


" Eh Mamie sun yi posting d'ina Gombe " na bata amsa ina mai bud'o mata pic d'in a wayata dubawa tayi kafin tace " I don't think you are going to Gombe " d'an kallonta nayi kad'an ganin yanda tai maganar amma fa nayi mamakin hakan don tace babu inda zata hana mu zuwa akan karatu ban wani damu ba nace " how are we going to do then Mamie kinsan dole sai na shiga camp kafin nai applying for redeployment "


"Send the details to me on WhatsApp u will be redeployed before camp insha allah " ta fad'a tana mai kallona "Toh" kawai nace cikeda ladabi sannan muka cigaba da firar mu a hankali har Areepha ta dawo muka d'aura da ita 


Harkokina na cigaba ba tareda na sake magana akan service d'inba bayan kwana biyu sai gashi ta dawo da deployment letter d'ina an maido ni kaduna godiya nai mata sosai akan hakan sannan muka fara shirye-shiryen shiga camp call-up letter naje nai printing sun canja komai ya bdawo Kaduna zanyi service d'in ne a Kaduna state markets development company (KSDMC) 


3 weeks mukayi a camp dukda cewa a cikin garin ne amma mun d'and'ana wuya saidai mun samu experience a rayuwa fiyeda baya bestie dai bata shiga camp ba saboda lokacin bata dad'e da yin miscarriage ba so bata da wani k'wari 


Muna fitowa da one week nai reporting babu wani b'ata lokaci a admin department aka ajiye ni babu wani k'alubale da nake fuskanta a wurin don 'yan office d'in ba k'aramar mutunci suke dashi ba 


Da yammacin laraba ne misalin 4:pm na fito daga office zan shiga kasuwa cefane kasancewar kasuwar wurin laraba take ci kasuwar tana a daidai bayan office d'in ta back gate zan fita Ina tafe kaina a k'asa wani k'amshi mai matuk'ar dad'i na jiyo hakan yasa nai saurin d'aga kaina ina kallon inda k'amshin yake fitowa 


Wani kyakkyawan matashi ne muka had'a ido dashi yana shigowa ta gate d'in hannunshi da counter da alamu daga masallaci yake don yanzu ne ma ake sallame sallahn la'asar saurin sauke idona nayi ina mai jin kunyan had'a ido dashi yayinda shikuma yak'i cire nashi a kaina ina jin yawon idanuwanshi a jikina ta gefen shi na wuce gaisawa mukayi da securityn kafin na fice 


Na d'an jima babu laifi danma a hakan inada wai'nda nake cefanen a wurinsu kayan miya ne seasonings spices da sauransu babu wani nauyi sosai dawowa nayi kafin lokacin tashi yayi in wuce dama haka nakeyi a reception nake ajiyewa in an tashi sai in d'auka in wuce 


Ina bud'e gate d'in na hango shi zaune a wani benchi shida securities wucesu nayi suna min barka da dawowa amsawa nai na shige ina ajiye kayan ne sai gashi ya shigo reception d'in Aisha ce ta gaishe shi yayinda ni kuma na wuce ina ce mata sai na fito ko sanda na fito zan wuce gida sai da na ganshi ban kalle shi ba na amshi kayana nai mata sallama kafin na fita titi na tsallaka na samu abin hawa 


Tun daga ranar kusan kullum sai mun had'u dashi sai dai bamu tab'a magana dashi ba saidai ina jin yanda yake bina da kallo wata ranar ma a stairs muke had'uwa abinda na sani shine baa office d'inmu yake ba 


Yau ban shiga office d'in domin secretariat na ke zuwa acan muke had'uwa da bestie muna zaune muna fira ina tambayarta jikinta mukaji sallama tareda wani familiar scent da hancina ya jima da haddace shi ina d'agowa muka had'a ido dashi yana sanye da kayanshi saidai white top d'inne kawai a jikinshi jacket d'in kuma tana hannunshi sai hula a kanshi 


A cikin abinda bai shige 10 secs ba na mai wannan kallon sauke idona nai saurin yi tareda kallon bestie da itama kallona takeyi gaisawa sukayi da bestie kamar sunsan juna harda ce mata Aunty (Sha'ani) ban tanka su ba saida naji yace " Anty k'anwar taki bata magana ne? " dariya ta k'umshe tareda cewa " ta nayi mana " rik'e baki yai tareda cewa " anya kuwa na fa had'u da ita kusan sau d'ari amma ban tab'a jin tayi magana ba 


Kallona tayi sannan tace " kodai kaine baka mata magana ba?" Turo baki yai kamar yaro "ke dai kawai kina goyon bayan ta ne " kallonta nayi tareda mamakin yanda suke Magana kamar sun san juna ganin bai shafe ni ba yasa na ciro wayata ina shafa screen d'in kamar ina wani abu ba 


Ji nai yace "Ina wuni k'anwar anty " hararar shi nai tareda cewa " 'yar anty dai ai nayi k'ank'anta in zama k'anwa " dariya suka fashe dashi bestie tana rufe bakinta shiko yi yakeyi kamar wani wanda ya tab'u saida yai mai'shi kafin yace " wallahi baki iya fad'a ba ki daina bai miki kyau ko k'adan ko anty ?" 


Cewa tai ai kuwa dai tana turo min message " bestie smile now wallahi bakiyi kyau ba " murmushi nai tareda replying " wai Ina kika samo wannan kuma harda kiranki Anty d'an uwanku ne ko kuma na Sahal ? " emojin dariya ta turo min tareda " Ko d'aya amma sanadiyar Babe na sanshi we will talk about that amma it seems like yayin falling miki " emojin gwalo nima na tura sannan nace "tab'b' wahalurrrr " daga nan na rufe datar ina kallonshi ya k'ure ni da kallo tab'e baki nai ina cewa "aiki jaa gashi ka zo sanda na rufe babin soyayya 


Katse shirun yai ta hanyar cewa " anty wai ya sunan k'anwar taki " kallonmu tayi kafin tace " mutum da bakin shi ? gaka ga ita ask her " turo baki yai da alamu sabon shi ne hakan yana cewa " to ai kinga baza tai min magana ba " nisawa yai kafin yai directing maganar zuwa kaina "Hey beautiful seems like you don't have a name but can i call you mine? " 


Zaro idanuwa nayi ina kallonshi kamar naga alien itako bestie cewa takeyi " awnnnn.......awnnnnn....awnnnnn" kamar wata ambulance cewa nai " my name is FAHEEMAH ABUBAKAR SADAUKI and I'm not yours don't call me that " daga haka na tashi na nufi gate ina jinshi a bayana sauri nakeyi kamar zan tashi sama ina fitowa na tare napep ina gayamai inda zai kaini ina mai jin wani zafi dan I'm very sure shima rabuwa zaiyi dani kamar yanda sauran suka yi 


SALEM'S POV


Tundaga randa naga wannan baiwar Allahn rabonda in samu wani sukuni a rayuwata wani yananyi nakeji a zuciyata wanda tunda nake ban tab'a jin irinshi ba duk 'yanmatan da na tab'a nema a rayuwata dalilin da yasa kenan nake zama a duk inda nasan zan had'u da ita na samu sunanta da kuma some informations like inda take ne a wurin Aisha receptionist d'in investment house d'in ita tace min she's a corp member a markets development wato 1st floor yayinda ni kuma nake 2nd floor KADRA 


Yau na shigo secretariat ne na hango su zaune ita da matar SMM wanda tsohon Vice President d'in Nigerian Students Association na Oxford university ne matsawa nai don mu gaisa da ita saidai tunda ta amsa sallama bata sake cewa uffan ba sai da matar SMM d'inme muke ta Magana sai sanda na nemi tsokana shima briefly ta tanka tana mai juya idonta wanda k'iris ya rage in zauce sakamakon wani kyau da naga tayi da kuma yanda kyan idanuwanta ya sake fitowa "ya ilahiy I love this girl " hakan ne yasa nai shiru ina kallon yanda take turo baki 


Katse shirun nai da tambayar Mrs SMM d'in sunanta ita kuma tace min in tambayeta mana mutum da bakin shi samun kaina nai cikin farinciki wato ta bani damar magana da ita kenan " Hey beautiful seems like you don't have a name, can i call you mine ?" na fad'a with the hope that she will accept my request sai dai reaction d'inta shows that I'm not welcome 


Mik'ewa tai tana cewa "my name is FAHEEMAH ABUBAKAR SADAUKI I'm not yours , don't call me that " kaina naji yana juyawa saidai gani nayi ta fara tafiya hakan yasa na bita a baya saidai kafin in isa gareta har ta tare napep tayi gaba ta barni a wurin duk'awa nayi ina mai jin wani irin ciwo a zuciyata I know I was a playboy nayi breaking hearts d'in 'yanmata da dama daga turawa har Afrikaans amma yau nasan zafin rejection ji nakeyi kamar heart d'ina zai rabe gida biyu dafe shi nai ina jin hawaye yana zubowa daga idanuna ......................


Deejasmah❤🦋🥀