Chapter 1 to end
☆“☆ª☆_☾`☆•`☆´-`☆´-
❉ *.¸¸.**.¸¸.**.¸¸*❆ *.¸¸.*.¸¸.*❆☆´-
*MATAR KAMAL*
.¸¸.**.¸¸*❆ ¸¸.¸* *.¸¸.** `☆´-`☆´-
Fasahar Rahma Muh'md Rufa'i Nalele... *Wattpad @rahamanalele*
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION 💡*
Home of expert and perfect writers
Kadda me karatu ya shagala, wannan labari kajeran labari ne, a page goma nake san gamasa, ko qasa da haka, ma'ana kwana goma😀.
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 01☆.
*Kwana na d'aya* 1.
Kwalliya takeyi sosai irin ta yara yaran mata masu kyau da aji, kyakkyawa ce ta qarshe, fara ce tas me dogwan hanci had'e da yala yalan gashin kai, doguwa ce me matsakaicin jiki, daga dukkan alamu zatayi fara'a Sannan baza ta cika surutu ba....
Yafa gyalanta tayi da fashe jikinta da turare, kana ta Saka takalminta me tudu ta d'auki wata qaramar jakarta me d'auke da wayarta da kayan tarkacen kwalliya irin namu na mata masu wayo idan zasu unguwa...
Haka tafito daga gidan nata wanda kallo d'aya zakama gidan kasan akwai rufun asiri daidai gwargwado..
Duk da cewar dare ne dan a lokacin tara da rabi ne na daran, amma hakan bai hanata tafiya a nutse ba...
"Sannu barwar Allah, ina za'a kaiki..
Wani me adaidaita sahu ya tambayeta ganin da alama leman abin hawa take, dan ganin sai warge warge takeyi akan titin layin nasu..
Ad'an tsorace ta kallesa dan bata san dashi a wajen ba, Ashe ta wuccesa dake hankalinta yana can inda take san zuwa...
"BSW nake san zuwa, "ok, shiga na kai ki.
Haka ta shiga yaja adaidaitan nasa, aiko bai direta a ko ina d'in ba sai a inda ta umarcesa..
Babban hotel ne, wanda ya amsa sunan sa, yana kyau sosai wanda baka isa kamai kallo d'aya ka wucce ba, manyan mutanan mu ne masu hannu da shud'i suka fiya zuwa wajen..
Dubu d'aya ta zaro a jakar tata ta miqa masa.. Nan ya karb'a da niyar nema mata canji a d'an cikin wannan ma'a danar tasu ta adaidaitan..
"No fah, kabarshi na bar maka canjin.. Aiko da murmushi akan fuskarsa ya kalleta da zuba mata godiya kana yaja adaidaitan nasa..
Sam bata motsa daga inda ya barta ba, saima kallan agogwan hannunta da tayi, tad'an ja tsaki da fara danna wayarta..
Kan ta cinma burinta akan wayar saiko ga wata zazzafar mota ta faka a gabanta, wata mata ce y'ar gaye haka kamarta, itama fara ce Sol tafito daga motar tana murmushi da cewa, Kiyi hakuri MATAR KAMAL, wallahi na tsaya lallab'a Salim ne yayi bacci..
Ta ce "Ya zanyi dake Safina, muyi ciki kawai dan sanyi ya fara takura min, takaicina d'aya nayi mantuwar suwaita. "Ba damuwa ai, tunda Oga yana nan saiya baki tashi, Safina ta bata amsa da fad'in, ta ce "Kumafa haka ne..
Nan suka shige cikin motar da shiga cikin Hotel d'in.
Can ciki Safina tayi parking motar, inda ba me takura mata da batun tazo ta gyara parking,, kana suka fitto da nufar wajen ma'aikatan wajen..
Dake sun san su mukullai kawai suka basu, da tabbatar musu matanansu suna d'akunan, duk da sun gaya muku hakan bai Saka su sun maida musu da mukullan da suka basu ba, haka suka haura saman inda d'akunan suke, waƴanda suke kallan juna, amma kafin su rabu sanda suka sumbaci junansu alamar sai da safe..
Yanda JAMILAH wato wacce Safina ta kira da MATAR KAMAL taga ogan nata kwance a kan gado haka itama Safina ayanzun taga nata kwance akan gadon..
Alamar jiransu kawai suke..
Safina matar Aure ce, dan tana da yaranta biyu, mijinta Soja ne, Sam baya tafiya da ita wajen aikinsu, gashi ita ta kasance mace ce me matuƙar sha'awa, shi kuma yana iban wata biyu ko uku acan wajen aikin nasu kafin ya dawo, hakan yasa data had'u da wata qawarta sai ta bata shawarar karta tsaya b'ata quruciyarta, kawai ta dinga lafewa da wasu mazen, tana samun biyan muqatarta. Da farko Safina taqi yarda amma daga baya da shed'an ya buga mata ganga saita yarda, yawancin mutananmu masu aji da dajin nera Safina ta san su, dan wannan dai qawar tata ita ce ta had'ata dasu, dama tana da y'ar aiki agidanta, wata Baba tsohuwa, tsohuwar banza ce, tunda tasan me Safinan take aikatawa amma bata tab'a tsawatar mata ba, tunda ta fuskanci ta qara mata albashi me yawa, itace dai take kula da yaran Safinan cikin dare tunda kwana takeyi agidan, shiyasa Safinan bata sharin kwana ako ina dan tasan Yaran nata na samun kulawa musamman da safe yayin zuwa skull..
Safina Y'ar gaye ce ta ƙarshe, tana da kyau daidai nata, mace ce wacce abinta bai rufe mata ido ba, tana da kirki sosai, dan daga danginta harna mijinta ƙaunarta suke, danta kasance me miqawa, ga ibada akan lokaci. Kawai dai ita matsalarta wannan harka dai ta takeyi, kuma tana jin tad'in harkar, bara mugu shin wannan jin daɗin nata zai d'aure kuwa...
Wannan shine labarin safina
Haka ayanzu taje ta rungume Alhajin nata, tana basa hakuri wai sanda ta tsaya Salim yayi bacci (wato qaramin yaranta) wannan ne yasata dad'ewa.
Shidai qara matseta yayi a jikinsa, dan Yasan ko tafi haka dad'ewa bazai damu ba, tunda yana samun yanda yake so..
JAMILAH ko yar da jakarta da wayarta gefe tayi, ogan nata ya tashi da farin ciki ya rungumeta yana me cewa, "sannu da zuwa MATAR KAMAL, meya dad'ar min dake ne haka..
Tace "kwalliya na tsaya yi maka. Ta kai qarshen zancen damar fari da ido wanda nan take yasashi yadasu akan wannan gado yana bata amsa da cewa, "Gashi ko kinyi kyau sosai, dole na biya wannan wankan..
Zata mai magana wayarta tahau ruri, sanda ta yatsina fuska dan gane me kiran, kana ta d'auka da cewa.. "Luvly, lefin me nayi yau kwata kwata baka kirani ba, bayan kasan ina a halin missing d'in komai da yake naka..
Acan b'an garan me kiran yace "Baby kiyi hakuri yau aiki ne yamin yawa, Sam kobi takan wayar tawa banbi ba, harna fara tunanin qila ko kinta kirana baki jini ba, Saidai kuma dana duba Miss call d'in dana samu na mutane babu naki a ciki..
"Tace haka ne Luvly, ban kiraka ba, yau dai rana d'aya nace bara na barka ka huta.. Danna fahimci kamar ina takura maka wajen yawan kiran naka da nakeyi.
Ya ce "Ba haka bane Baby, aiki ne yake mana yawa, kar kiyi fushi akan hakan, ta ce "Hmmm, zan kwanta Luvly bacci ya kusanto ni, yace "Dama muna tare da juna a daidai wannan lokacin, da kinyi min maganin gajiyar dana dawo da ita,.
Tayi murmushi da cewa, "karka damu zanyi maka maganinta ranar daka dawo, yace "Toh kidai kulamin da kanki, tace "yanda ka barni haka zaka dawo.ka sameni.
Yace "Toh Allah yasa, " Ameen.. tace
Daga hakan sukayi sallama..
Ogan nata ya kalleta rai b'ace yace "Yaushe zai dawo, tatab'e baki tace "jibi mana, me yasa kake mantawa ne, yace "Wallahi bani san dawowarsa, dan yana takura min..
Murmushi tayi da maida hankalinta gabaki d'aya kansa, ta Saka dukkan hannuwanta a kafaɗarsa suna masu kallan juna irin na waƴanda suka dad'e da sanin sirrin juna tace dashi, "nima yana takura min, ba yanda zanyi ne kaga ina maka shuru, amma yaci ace hakan ya dena damun ka, tunda ka fisa more duk wata albarka da Allah yayi min..
Jin hakan yasa shi sakin murmushi, da neman rabata da kayanta yana cewa, "Bakiyi qarya ba MATAR KAMAL...
Nan ko suka fad'a aikata aiki mummuna, wanda Allah yay hani dashi wanda zai zame musu dana sani anan gidan duniya dama can gidan lahira.
Sun b'atama juna tunani awannan dare kamar baza subar junan nasu ba, amma haka dai sukayi hakuri saboda bacci baya sallama..
_HASKE WRITER'S ASSOCIATION 💡_
Home of expert and perfect writers
☆“☆ª☆_☾`☆•`☆´-`☆´-
❉ *.¸¸.**.¸¸.**.¸¸*❆ *.¸¸.*.¸¸.*❆☆´-
*MATAR KAMAL*
.¸¸.**.¸¸*❆ ¸¸.¸* *.¸¸.** `☆´-`☆´-
Tare da alk'amin
Rahma Muh'md Rufa'i Nalele.
*Wattpad @rahamanalele*
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 02☆.
*kwana na biyu*
Washe gari da misalin qarfe goma sha d'aya da rabi ta fitto daga wanka tana zama gefen gado yahau shafa mata mai, Yana yaba naushin jiki da kyau da Allah yayi mata.
"MATAR KAMAL... "Kai kad'ai kake da mallakinta, ta bashi amsa da faɗin hakan, sai yayi murmushi da cewa, "Tunda nake wurd'a da mata ban tab'a cin karo da yarinya irinki ba, ga naushin jiki, ga kyau, ga dad'in harka...
"Hmmm, na lura da duk lokacin da kake shafamin mai saika fad'i waƴannan kalaman.
Cikin k'asa da murya irin nasu na manya yace "kina jin daɗin hakan, tace "sosai mah, ai duk lokacin da ka yabeni bayan jin daɗi qara ƙaunarka nake, yace "waini da Yaran nan wa kika fiso ne..
Maida kallanta garesa gabaki d'aya tayi da cewa, "Kasan dai nafi samun cikakkiyar kulawa da kyautatawa agunka fiye dashi, kuma kaji ance ZUCIYAH tafi san me kyautata mata..
Takai ƙarshen zancen da tashi ta suturta jikinta, sanda ta yafa gyalanta ta kuma rataya jakarta kana taci gaba da cewa, Ina sanka original KAMAL, ina ƙaunarka da kyau, dan Allah karka so wata mace fiye da san da kake min..
Yace "baki da matsala da wannan, dan ina tabbatar miki ko mamansu bana jinta kamar yanda nake jinki a raina...
Saita yatsina fuska alamar Sam bata so ya sako mata Sunan wata wai matarsa ba..
Hakan yasa ta fitta daga room d'in bata ko kallesa yana mata magana Sam bata kulasa ba.
Bai takura mata dasan saita kulasan ba, dan dama yafi kowa sanin halinta akan kishinsa, Sam bata san ya tab'o mata matarsa, koda ko zagin matar tasa zaiyi...
Safina na cikin motar tana jiranta, ta shiga tana jan tsaki.
"Ke lafiyar ki kuwa, ba farawa da gaisuwa sai jan tsaki, Safina ta gaya mata hakan tana me jan motar, "Kedai bari, KAMAL ne ya b'ata min rai, wai daga yin magana ya wani sako min zancen shegiyar matar sa..
Safina ta girgiza kai da cewa, "Wai me yasa matar nan ta dameki ne MATAR KAMAL, bayan kin fita more mijin nata, dan nayi imani saura kike bar mata tana tab'awa da hakuri, amma duk ran da ya kuskure ya fad'i sunanta a zancenku duk sai kibi ki d'auki zafi..
Tace "Nifa na tsaneta ne kawai, kuma qiris nake jira na wanketa soso da sabulu naga me tsaya mata,..
Safina ta sheqe da dariya tace "bame tsaya mata, dan shi me tsaya matan shi kika cafke, kina sha'aninki MATAR KAMAL, can KAMAL nan KAMAL wai ya abin yake miki ne...
Tab'e tayi, ta ce "Wallahi komai normal..
"Idan ko haka ne dan Allah kiyi hakuri karki kulata, dan kema kinsan had'a mata zafi zakiyi, idan dai har da gasken wanke ta da soso da sabulun za kiyi, dan Allah kiji tausayinta, dan kin Riga da kin gama da ita kwata kwata...
Dariya JAMILAH tayi da cewa, ai ban gama da ita ba, sai ran data ganni da cikin d'aya daga cikinsu, musamman original d'in...
Dariya Safina ta qara kwashewa da ita, tace "tab, ke akwai sauran dirama fah..
Shuru Jamila tayi mata kawai..
Sanda Safinan ta sauketa a kofar gidan nata Sannan tace da ita "kardar a wucce wani wajen, dan Allah kije kiji min da yarana, dan sun kusa dawowa daga skull, yanzu lokacin su ne,.
Dariyar dai Safina ta qara yi da cewa "Toh, baki da da matsala da hakan.
Minti goma da shigarta gidan nata saiga kiran sirikarta a waya wai tazo yanzu yanzu tana jiranta a gidanta, kuma bata jira cewarta ta kashe wayarta..
Tab'e baki JAMILAN tayi kana tashiga kiran wayan mijin nata, kusan kira uku bai d'auka ba, bata damu da hakan ba, haka ta yafa gyalanta ta nufi gidan sirikar tata wanda anan cikin layin nasu yake...
Datayi sallama agidan daqer yaran gidan suka amsa mata, saboda basa shiri da juna..
Kasancewar kafin auran nata da Yayan nasu mahaifiyar tasu bata santa, tace karya Aureta, shi kuma yace yana santa, Babansa kuwa yace tunda yarinyar arziqi ce, kuma daga gidan mutunci ta fitto ba abin dazai hana ya Aureta, haka ko ya shige ma d'an nasa gaba ya Aura masa ita..
Gane hakan da JAMILAH tayi yasa bata bin maman nasa sosai, irin dai kadaran kadaham d'in nan, amma tafi nunama qannan nasa bata sansu tunda suma nuna mata suke b'aro b'aro, kasan cewar mahaifiyar tasu ta dasa musu tsanarta...
Haka idan zasu gidanta sai taga dama take bud'e musu ƙofa, idan bataga dama ba bazata bud'e ba.
Rashin bud'ewar ma shiyafi alkairi, dan da fad'a ake rabuwa, dan shiga mata kitchen suke suyi abin da ransu ke so, su b'ata mata gidanta, idan tayi magana su mata rashin kunya, mamansu kuma tazo har gidan ta qare mata zagi, tana fitta su kuma su hau yi mata ruwan dutsuna. hakan yasa tadena bud'e musu kofar...
Sai mahaifiyar tasu takai ƙararta wajen Baban nasu, cewar bata san y'an uwan nasa dan haka yasa Kamal d'in ya sake ta, ce mata yayi dama can ba san Auran take ba, dan haka duk wani sharri dole zata had'a dan Auran ya mutu, to tasani idan Auran ya mutu nata ma zaibi sahu...
Kuma a gaban yaran ya fad'a mata hakan, hakan yasa daga ita har yaran suka qara jin tsanarta,
Sannan yace karya qara jin wani yaje gidan nata, da suka bud'e baki za suyi masa magana dan kare kansu, aiko ba qaramin doka sukaci bah..
Kasan cewar shi Kamal d'in aikinsa a Abuja yake, dan sai bayan qarshen wata yake dawowa yayi sati d'aya, su kuma a Kaduna suke, koda ya dawo hutun yaji labarin a bakin mahaifiyar tasa, baibi takan zancen ba, dan gani yake Kawai had'i ne, tunda tun farko ba san matar tashi take ba..
Wannan shine labarin mu'a malar JAMILAH da surukanta a zahiri..
Sanda Jamila ta kashe minti goma sha biyar a falan tana zaune zaman jiran saukowar sirikar tata kafin ta sauko...
Macece y'ar gajera haka amma tana da kyau daidai nata. Ta zaune kan kujera mecin mutum biyu fuskar nan tata babu wasa, JAMILAH tace "barka da Safiya mamah.
Cikin nuna isa da tak'ama tace mata, "Barka, shima daqer, dan wallahi bata qaunar yarinyar..
JAMILAH tatab'e baki tayin qasa da kanta.. Ganin hakan yasa taci gaba da cewa, Dama na kiraki ne danna gaya miki Aure zamma KAMAL, kuma ba wata bace zan Aura masa, y'ar Qanwata ce Zinatu. Wato Ummi..
JAMILAH ta d'ago da kanta tayi mata kallan kin isa, kana ta ce mata, "Wannan ba abu bane me yuhuwa mama, ni kad'ai ce MATAR KAMAL, dani kad'ai zaiyi rayuwa, kijimin mata, ke yanzu mama tsakaninki da Allah da kanki kike san KAMAL yayi min kishiya, ke tun k'uruciyarki har zuwa yanzu kinyi rayuwa da kishiyar ne, amma ni dan mugunta saboda ni ba y'arki bace sai kice wai zakima mijina Aure, Toh idan kin fasa masa kin raina Allahn daya halicceki... Takai ƙarshen zancen da qara kafe sirikar tata da ido..
Gabaki d'aya zuba mata ido sukayi, ina nufin daga yaran har ita kanta sirikar tatan..
Ai ba zato ba tsammani sai jin ruwan doka JAMILAN tayi akanta, dokan yaran gidan, fad'i suke.. "Ke kin isa kizo har gidan mu kiyima uwarmu rashin kunya, wallahi yau sai munci ubanki, shegiya y'ar iska wacce bata da tarbiya,..
Maman nasu ko cewa take "kuci ubanta da kyau ku mata raga raga inga uban dazai tsaya mata, jin hakan ya qara musu fawa, suka dinga dokanta tana ramawa, amma kunsan ance sarkin yawa ai yafi sarkin qarfi..
Ana cikin haka saiga Babansu ya shigo falan, ganin abin da yake faruwa yasa ya daka musu wata muguwar tsawa tare da mamakin ganin JAMILAN anan, cike da bacin rai yace dasu "Ku dan ubanku miye haka, ita d'in baiwar ubanku ce kota uwarku da zaku sata gaba da doka haka..
Komawa gefi sukayi dayin shuru, jikinsu ko ya d'auki b'ari, dan ba qaramin tsoran Baban nasu suke ba..
Ganin hakan yasa ya maida kallansa kan maman nasu yaci gaba da cewa, Ke kam anyi mutuniyar banza, dabba jaka wacce bata san me takeyi ba, da girmanki da mutuncinki akan idanki ki bari yaranki su dinga dokan sirikar ki...
Tace "Rashin kunya tayimin min, kuma banga amfaninsu ba idan har bazasu mata dokan tsiya ba, haba, wannan wane bala'i ne, Yarinya duk tabi ta zame min masifa da bala'i, daga mata zancen zan ma mijinta Aure saita bud'i baki dan rashin kunya da rashin tarbiya tace min wai ban isa ba ita kad'ai ce MATAR KAMAL ba wata bayan ita, har da cewa wai ni na zauna da kishiyar ne, da zanyo mata ita, Wai hakan mugunta ne tunda ita ba y'ata bace..
Yace "mugunta ne mana, inda y'arki ce zaki mata hakan ne, koni nayi miki kishiyar ne, da zaki Saka y'ar mutane a gaba dan baqin hali kice zakima majinta Aure, ina ruwanki da sabgar gidan d'anki ban da zubda mutunci da jama kai raini......
"Toh,🤔 ikwan Allah, wato ni banda iko akan d'ana kenan, ban isa dashi ba kenan. Ta katse shi da faɗin hakan tana me zuba masa ido tare da mamakin dukkan kalamansa..
Yako qara tsaida idansa akanta yace "baki da da iko dashi idan dai akan hakan ne, idan har ina amsa Sunan ubansa bazan yarda kisa JAMILAH cikin k'unci ba, tunda tace bazata zauna da kishiya ba wallahi bazata zauna da ita ba, ko shi KAMAL d'inne yazo yace zai mata bai isa ba, dan bazan yarda ayi mata abin da bata so bah.
Tace "ikwan Allah, wato ka fifita bugatarta fiye da abin da Allah yace, yace "kin fini sanin Allahn ne, shi KAMAL d'inne yace zai qara Auren, ina kece yanzu kikace zaki masa, kinga kenan idan ya dawo daga baya yace yana san yayi ke kika sa shi, dan haka nace bazan barshi yayin ba..
Kuma Wallahi kibi a hankali dan kika fiya matsama yarinyar nan, zan iya rabuwa dake akanta....
Ba ita ba har y'ay'an nasa sanda suka kallesa..
Yaci gaba da cewa, Eh haka nace kina da abin da zaki ce ne..
Shuru tayi, nan kuma take ita da yaran nata suka qara jin tsanar JAMILAN...
Ganin hakan yasa JAMILAN tashi a gajiye, dan da gaske tad'an daku a hannunsu, direct fitta tayi daga falan ba tare datace komai..
Shiko ganin hakan yasa yayi part d'insa ransa a mugun b'ace...
Yaran suka bishi da kallo, ita kuma maman nasu d'aga waya tayi rannan nata yayi mata baqiqirin tahau kiran KAMAL d'in..
KAMAL na d'aukar ta fashe mai da kuka da zayyane mai dukkan abin daya faru..
Duk da Cewar ba yau bane karo na farko da hakan ta saba faruwa, amma haka kawai yau d'in yaji babu dad'i akan maganganun da mahaifin nasa ya gaya ma mahaifiyar tasa, duk da ya fahimci lefinta ne, saidai fa yaji haushin rashin kunyar da matar tasa tayi mata, amma daya tuna Sam fa mahaifiyar tasa basan matar tasa take ba sai yayi tunanin kodai ta shirya hakan ne danta rabasu kamar yanda ako wane lokaci take yunk'urin yin hakan.
Dan haka lankwasar da murya yayi ya dinga bata hakuri da nuna mata zai gamu da JAMILAN..
Haka dai Sukayi sallama, duk da tasan ba wani kula JAMILAN zaiyi ba, amma taji daɗin kwantar mata da hankalin da yayi..
JAMILAH ko tana komawa gidan nata bayan ta zauna saiga kiran Alhajin nata a wayar ta, bata d'auka ba, haka yata kira taqi d'auka, 7 miss call ya mata sai kuma miss call d'in mijinta 2, taja tsaki zata tashi sai taji shigowar message d'insa, ta duba taga dai magana yake mata akan dan Allah ta d'auka, ganin hakan yasa ta d'auka, tana me cewa "Wai menene..
Yace "Am so sorry MATAR KAMAL, dan Allah kar kiyi fushi dani, kar ki bari abin ya shafe ni, tace "Wallahi KAMAL Na tsani matarka bana santa na tsaneta sosai..
Yace "Na sa'ni ai, ni dai kiyi hakuri...
Tace "hakuri ai ya zama dole, amma yau bazan zo gareka ba, Saidai kazo gidana ka same ni tunda kasan shi gobe ne zai dawo...
Sauke ajiyar zuciya yayi jin ta hakura, dan Wallahi shi dai kam bashi da matsala a rayuwarsa sai ita, idan yaga ranta ya b'aci hankalinsa tashi yake
Yace "Yanzo ai baki da matsala da hakan....
Tana jin haka ta kashe wayar tana tuna gaskiya ba qaramin so take masa ba, yanda take jinsa a ranta ko KAMAL mijinta yaro me jini a jika bata jinsa a ranta kamar shi..
Tashi tayi ta shiga toilet d'inta ta watsa ruwa me zafi, bayan ta fitto ta shafe jikinta da man zafi kana ta haye gado..
Baccin gajiya take san yi amma saita tuna taga miss call na mijin nata d'azu
Hakan yasa ta shiga kiransa, yana d'auka yace meya kaita gidansu d'azu..
Tace mai ai ta kirasa sau uku bai d'auka ba kafin taje gidan, mamansa ce ta kirata. Nan dai ta kwashe komai daya faru ta gaya masa, amma ta b'oye rashin kunyar datama mahaifiyar tasa..
Shuru yayi, can yace "Abin da nake so dake, daga yau karki qara, suwa gidan, tace "toh insha Allah bazan qara zuwa ba...
Yace "Gud, Sannan kifa fara shiri tun yanzu dan kinsan ina kan hanya gobe, yakai ƙarshen zancen da murmushi..
Tace "Ai ina sane da hakan, dan kullum a cikin k'irge nake, baka da matsala da hakan, komai na gama shirya maka shi..
Yace "Allah ya barni da Matata, tace "A nan gidan duniya..
Yace "Har ma acan Gidan lahira..
Dariya sukayi gabaki d'aya..
Daga haka kuma sukayi sallah
Sanda ta kira qawar tata Safina ta gaya mata yau bazata Hotel ba, dan a gida za'a sheqe ayar..
Dariya kawai Safinan tayi..
Daga haka maida hankalinta tayi akan baccin da take san yazo mata..
Sai bayan Sallar Azahar tatashi.. Nan ta hau yin sallah da sauri dan har a zuciyarta bata so sallar d'in ta wucce ta ba.
Tana ko idarwa ta shiga kitchen dan fara had'a girkin dare.
Bayan Isha'i taci kwalliyarta ta qananun kaya tayi kyau sosai. A haka gwanin nata yazo ya sameta saboda tsabagen sabo ba kunya ba jin tsoran Allah haka ya baje a gidan kamar irin ya samu gidan san nan..
Ita kuma ta sake kamar dai da mijinta take tare...
Suna had'e da juna sukaji ana kwankwasa ƙofar get d'in gidan
Muje zuwa..
Fallow me kawai y'an hannuna
_HASKE WRITER'S ASSOCIATION 💡_
Home of expert and perfect writers
☆“☆ª☆_☾`☆•`☆´-`☆´-
❉ *.¸¸.**.¸¸.**.¸¸*❆ *.¸¸.*.¸¸.*❆☆´-
*MATAR KAMAL*
.¸¸.**.¸¸*❆ ¸¸.¸* *.¸¸.** `☆´-`☆´-
Tare da alk'amin
Rahma Muh'md Rufa'i Nalele.
*Wattpad @rahamanalele*
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 03☆.
*Kuyi hakuri sister na rashin jina da bakuyi ba jiya*
Dake Mara gaskiya ko a ruwa yake gumi yake, hakan yasa hankalinsu tashi ba d'an kad'an ba, cikin tashin hankali JAMILAH tatashi ta cintsa kanta da sauri shima ya shiga gyara kansa ta nuna masa wajen b'uya kana ta fitto bakin get d'in tana cewa waye..
Wani saurayi ne ya amsa mata da cewa, dan Allah nan ne gidan Alhaji Muktar..
Sanda ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "ba nan bane gidan gaba ne... Yace "Toh na gode..
Haka ta koma taga ogan nata duk ya had'a gumi, tamai dariya da cewa, "Toh bashi bane saika fitto, yace "dan Allah kibar maganar wasa ki gaya min gaskiya, tace "Allah da gaske nake, kasan bazan maka wasa irin wannan ba..
Fitowa yayi da rungumarta yana cewa, gaskiya duk ran da asirinmu ya tonu akwai matsala Babba, tace "Kai zakaga hakan, danni ko kad'an bani tunanin zuwan wannan ranar..
Murmushi kawai yayi mata, da haka kuma suka qara bajewa.
Washe gari *kwana na uku*
Basu rabu da juna ba sai kusan goma da rabi..
Sam basu so hakan ba, dan basu gajiya da junan nasu..
Haka ta gyara gidan ta shiga kitchen tahau dafe dafe dan tayi waya da mijin nata yace mata yana kan hanya..
Can wajen qarfe uku ya iso, KAMAL yaro ne nutsattse me hankali, ga kyau ga d'an abin hannunsa, yana san JAMILAH fiye da komai a rayuwarsa, dan ta cika dukkan wasu sharid'ansa, tana kyau sosai, wanda hakan yana cikin burinsa nasan Auran mace me kyau over, gata da iyayi da kisisina da shagwab'a irin ta yara yaran mata, uwa uba ba ƙaramin jin daɗin harka da zaman takewa yake da ita ba...
Mace ce wacce bata da qiwa akan tsabta dayin duk wani abu dazai d'auke hankalin duk wanda take tare dashi, ga ibada dan ba lefi tana da ibada sosai..
Gane hakan yasa ya qara jinta da ƙaunarta aransa...
Cike da so da ƙauna take ta faman tararrayarsa, tsayawa kallanta kawai yake, dan shi dai kam komai take burgesa take..
Ta kallesa da fararan idanta masu qara burgesa tamai fari dasu tace, "Gaskiya dole na qara godema Allah daya halicceka yasa kuma ka zamo miji gareni, wallahi Baby ba ƙaramin sanka nake ba, ina sanka ina ƙaunarka sosai fiye da komai na rayuwa ta, tunda na rasa iyayena bayan Aure na dakai, na qara maka wani Babban matsayi cikin raina.... Tana zuwa anan cikin kalaman nata da matso kusa dashi da sakala dukkan hannuwanta biyu akan kafaɗinsa taci gaba da cewa, bakaji yanda ayanzu nake ji a raina bane, ji nake kamar na cinyeka d'anye, kullum maganata da zuciyata dama kana kusa dani, dama dama dama aikin naka ya dawo nan, danafi kowace mace murna da farin ciki a rayuwa..
Murmushi yayi mata da cewa, "Insha Allah zan dad'a dagewa da Addu'a kan Allah yasa fatan ki ya tabbata, dan nasan dole na fiki farin ciki, kasancewar har gobe bazan yarda da cewar kinfi ƙaunata akan ƙaunar da nake miki ba..
Wani shegen murmushi tayi dajan hannunsa zuwa bedroom dan ya watsa ruwa ya kuma ci abincin data girka masa..
Safina ko dake jiya a hotel ta kuma kwana, hakan yasa tana komawa gida tafara baccin gajiya, har yaranta suka dawo daga skull me aikin nata ta shiryesu suka tafi madarasa bata tashi ba, sanda tayi mararta ta murd'a kana tatashi a gigice..
Ganin Lokacin sallah yasa tatashi a daddafe, tayi sallar, Saidai me kamar jira ake ta idar da sallar ciwan ya qara ram da ita fiye dana d'azu..
Safina tana da tsoran ciwo, tunda aka tab'a cire mata afandis shekarun baya take jin tsoran ciwan ciki, dan ba qaramin azaba taci ba, Toh yanzu jin ciwan cikin tayi kamar na afandis d'in, wannan yasa ba shiri ta zura doguwar riga sai asibiti, Allah yasa asibitin ma kusa ne nan takai kanta cikin lokaci qanqani..
Doctor Aminu ya duba ta ya tabbatar mata ba afandis ke damunta ba, Ciki ne da ita na wata d'aya da sati biyu....
Ai saiga Safina ta gwalalo ido, tace "Ciki ciki wane iri.. doctorn yayi murmushi da tabbatar mata ciki ne, har ya fara bata shawarar ta kula da shi da kyau dan Wannan baya san wahala, ba irin cikin da tayi abaya bane, wato na d'anta Salim da yayarsa Hanifa...
Safina fa ba sauraran doctor d'in take ba, dan tuni ta shiga tunani a burkice , Rabanta da mijinta wata uku, yanzu idan ya dawo ya ganta da cikin wata d'aya da sati biyu tace mai me, bama wannan ba, ita Sam kanta kullewa yayi tayo asibiti batare da tayi lissafin kwanakin al'adarta ba.. Sannan ta manta lokacin da tayi cikinta na fari na Hanifa ciwan cikin ne yasa suka gane tana d'auke da cikin...
Gashi doctorn daya dubatan ayanzu abokin mijinta ne, dan asibitin nasa tayo, nan take ba tare da b'ata lokaci ba taji hawaye ya zubo mata, ta qara yarda Allah ba mutum bane, cikin lokaci qalilan shimai iya tona asirin ka ne, idan kuma yaso ya rufa maka asirin..
Dan ita ko a mafarki batayi tunanin za'ace mata ciki ne da ita ba, tunaninta ko ace ciwan cikin ne daga Allah ko wani afandis d'in...
"Lafiyarki kuwa Safina, meke damunki kike hawaye, ke da zakiyi murna...
Saurin kallansa tayi da qirqiru wani murmushi tace, "Aminu kamin rai, kaga Salim bai wani girma ba, ina ni ina masa qani, dan Allah kaban maganin da zan zubar da cikin ka kuma yimin Allurar fulanin na shekara uku amma dan Allah hakan ya zama sirri tsakani na da kai...
Murmushi doctor Aminun yayi da cewa, "Ku mata baku da wayo, haba Safina, da wayanki da iliminki kike san tun yanzu ki fara lalata mahaifarki, yara nawa gareki da Zaki fara tunanin zubda ciki da fulanin, ga mijinki na san yara sosai me zaisa kimai haka, bayan ba ƙaramin sanki yake ba da san duk wani abu dazai zo daga gareki musamman ma yaran..
Tace "baza ka gane bane Aminu, wallahi akwai muguwar matsala, kuma gaskiya ni banda ra'ayin tara yara, nafi san yara kad'an, kuma ya kasance akwai tazara tsakaninsu, akan wannan buri nawa zan iya basa goyan baya kan ya qara Aure..
Murmushi yayi da cewa, "Gaskiya bazan iya miki abin da kike so ba, dan akwai amana tsakanina da SA'EED. Bazan iya cin amanarsa akan banzan tunaninki ba....
Jin hakan yasa ta saki murmushi da cewa "toh ba damuwa zan bar cikin Allah yasa mai albarka, amma dan Allah karka gaya mai komai akan hakan, zan gaya mai da kaina dan Allah..
Yace "Baki da matsala da hakan, ga magungu nan da zaki sha yanzu, Sannan kifa rage aiki, dan zaki iya jama kanki matsala akan hakan, tace "Toh Nagode..
Da haka sukayi sallama..
Tana dawowa gida tahau safa da marwa, duk duniyar sai tai mata zafi ta rasa me yake mata dad'i...
Nan ta kira Alhajin nata wanda take da tabbacin cikinsa ne ta gaya mai, nan ko hankalinsa ya tashi dan yasan tabbas mijinta baya gari tsawan wata uku, ya kuma yarda cikin nasa ne, dan haka yace mata ta bari sai dare idan tazo Hotel sa yanke shawarar abin yi, toh tace mai...
Abin da Safina bata sa'ni ba shine, tana barin asibitin, doctor Aminun ya kira mijinta SA'EED d'in, suna gaisawa yake cemai sun kwan biyu basu gaisa ba kuma basu had'u ba, yace mai dan baya gari ne amma insha Allah satin da za'a shiga yana nan kan hanya, yace mai masha Allah Allahn ya kawo shi lafiya, kana yace, "dama na kira ka ne dan na gaya maka ka rage yawan rayawa sunna da matar ka dan hakan zai iya jawo sanadiyar zubewar cikin dake jikinta yanzu
Da bazan gaya maka ba, dan ta rok'eni akan hakan, amma dana tuna dole saina gaya maka dan ka kiyaye hakan shiyasa banbin takan rokwan nata ba, fatana dai Allah ya sauketa lafiya...
Waro ido sosai SA'EED yayi da cewa "what, Safina na da ciki..
Yace "Yes kayi mamaki ne.😃
Yace "No, yanzu tazo ka duba ta. Yace "Eh, cikin wata d'aya da sati biyu gareta, dan Allah ka kula da ita sosai, dan Wannan ba irin nasu Salim bane..
Ai SA'EED najin hakan yaji zufa na tsattsafo masa, yace "Nagode Nagode Abokina..
Yace "Ba komai SA'EED ai ana tare..
Daga haka suka ajiye waya..
Jifa da wayar tasa SA'EED yayi, hankalinsa ya tashi sosai, dan rabuwarsa da ita yama barta tana al'ada, kuma wai cikin wata d'aya gareta da sati biyu, wato wani ne ya mata kenan..
Bai ankare ba yaji hawaye na zubo masa, dan ba qaramin tashin hankali bane ya kama sa
Nan yahau shiri shirin tawowa gareta ayau, dama wani abokin aikinsa zai tawo garin nasu yanzu bara kawai ya biyosa, dan shi dai kam bazai iya toqi acikin wannan halin da yake ciki ba, Sannan baya buqatar rakiyan yaransa bare yace musu su kawosa, dan kallo d'aya kowa zai masa yasan akwai gaggarumin abin da yake damunsa
Wannan shine abin da Safina bata sani ba.
Toh dake ogan nata me cikin yace mata sai sun had'u da dare hakan yasa data sha maganin da doctor Aminun ya bata ta kwanta saita hau kiran wayar MATAR KAMAL..
Lokacin tana maqale da KAMAL mijin da yake hakkinta, ai ganin kiran wayar Safina saita zare jikinta daga nasa taje can kitchen d'inta ta d'auka tana cewa, "k'awata lafiya...
"Inafa lafiya MATAR KAMAL, ciki ne dani...
JAMILAH ta waro ido waje tace "what, ciki Safina, cikin wah, kar kice min cikin Alhaji Nura mijin Yayar mijinki, dan nasan yafi like miki, kuma kema kinfi jin daɗin harka dashi...
Safina tace "Cikinsa ne JAMILAH, har munyi magana dashi yace mu had'e kawai yau da daddare, wallahi MATAR KAMAL damuwata d'ayace doctor Aminu ya sa'ni, ina tsoran karya gayama SA'EED..
Tace "Baki rok'esa ba. Tace "Na rokesa amma ai banda tabbas, dan kinsan Aminu bai zama lalle yaqi gaya masan ba..
JAMILAH taja numfashi tace mubar komai zuwa gobe, kafin nan kun gama tattaunawa da shi d'in, dama ni bana wani sanki dashi, ban san meyasa kikafi lik'emai ba, tace "Hmm ya iya da mace ne k'awata bazaki gane ba, saina baki shi ya d'and'ana miki zaki san me nake ji, kidai gaishemin da wanda kika raina, dan nasan yanzu kuna tare..
JAMILAH tayi dariya tace, "Hmmm, kamarku kin sani, duk yabi ya isheni, wallahi kawai ina biye mai ne, amma zuciyata tatafi ga shegen tsowan cen....
Dariya sosai Safina tayi da cewa "Allah ya kyauta mana.. Tace "Amiien kekam sai goben idan kinzo kinsan bazan samu damar fitta a goben ba bare ni nazo, Saidai kinzo kawai.. "Toh ba matsala saikin jini..
Da hakan suka sauke wayah
KAMAL yayi saurin komawa falan nasu, gabansa na bugawa fat fat fat, dan lokacin data tashi tayi kitchen d'in biyota Yayi, danya had'a Lipton, Sam bata san ya biyo bayanta ba, jin irin maganar da take yi yaja hankalinsa har ya koma baya dan karta juyo ta gansa, a haka yaji duk amsar da take bama Safina, shi dai ba Yaro bane bare ya kasa ganeni me hakan ke nufi..
Ganin duk yabi ya rikice yasa ya tashi yayi bedroom d'insa dan ta iso falan, Sam baya san tasan yaji wayar tata...
Tace "Ha'a, Honey, ya katashi.. Bai juyo ya kalleta ba, yace "toilet zan shiga bani minti biyu. Tace "OK saika fitto, amma karka dad'e, dan haushi nake ji idan naga kana gida ka barni koda ko barin na dalili ne kamar wannan...
Baice mata qala ba yayi ciki abinsa..
Itako bata damu ba dan bata wani fahimce sa bah.
Sanda ya bari ya dawo normal kana ya fitta daga toilet d'in, danya yan ke shawarar abin yi, zai bi wasan nasu ya tabbatar da abin da hirar tasu take nufi...
Tara da rabi SA'EED ya iso, dake zuwan nasa bana shiri bane hakan yasa daga shi sai wayarsa da kayansa kala biyu, abokin nasa na saukesa a kan layin nasu ya tsaya bakin wani shago dan Siyan kati, aiko juyowar nan da zaiyi saiko ya hangi Safina a motar ta wacce ya siya mata ta nufi arewa....
Cikin sauri yace ma me shagon yana zuwa, ya tsaida wani me kekenafef yace mai yabi mai bayan motarta.
Itako Safina tsakaninta da Allah take nuqinta burinta takai hotel d'insu...
A haka ko takai, SA'EED yace ma me nafef d'in ya jirasa yana zuwa, haka yata bin bayanta har tayi parking dayin wajen ma'aikatan wajen, mamakinsa Bai gama tsayawa ba sanda yaga ta karb'i key agunsu tayi sama Sannan yasan eh lalle bashi kad'ai yake kid'ansa da ita bah..
Haka ya shiga wajen nasu da murmushi yace dasu, "Barkanku sisters.. Suka kallesa cike da kulawa suka ce "Barka dai..
Yace "ina san d'akin da waccar matar take ciki, ya musu nuni da hanyar da Safina tayi, murmushi suka mai d'aya daga cikinsu tace, "Oga ai ba'a haka, tana da oganta, dan dashi take kwana, da ace ita kad'ai ce dasai mu had'aka da ita tunda duk abun d'aya ne, duk da hakan yana a matsayin katsalandan ga rayuwarta da zamu mata.
Murmushin yaƙe ya mata da cewa "Okay, zanje na dawo dan nayi mantuwa, inna dawo saiku bani d'akin dake jikin nata, amma zaku temaka min wajen had'ani da ita da safe ko, tace "Baka da matsala Oga, dan akwai wata ST qararrawa, idan ka danna zata baka sautin bud'ewar ƙofar su da rufewarta ta hakan zaka iya ganinta inta fitto saika kaima ka fitto ku dai-dai ta, ammafa bazata amince da kai lokaci d'aya ba zaka sha fama, dan tanaji da wannan ogan nata...
"Ya kike karya doka ne, kinsan ba'a faɗin sirrin mutum ga wani bak'o ko, ko kin manta hakan ne, abokiyar aikinta ta katseta da faɗin hakan..
Shuru tayi, shima ganin hakan yasa shi yin murmushi da ficcewa daga gun, yayi wajen me nafef d'insa yace mai ya mai da shi inda ya d'auko shi.
Muje zuwa.. Kudai bini kawai.
*KUNDIN HASKE*
Alk'aluman marubutan Haske
_Babi na goma sha tara_
_HASKE WRITER'S ASSOCIATION 💡_
Home of expert and perfect writers
☆“☆ª☆_☾`☆•`☆´-`☆´-
❉ *.¸¸.**.¸¸.**.¸¸*❆ *.¸¸.*.¸¸.*❆☆´-
*MATAR KAMAL*
.¸¸.**.¸¸*❆ ¸¸.¸* *.¸¸.** `☆´-`☆´-
Tare da alk'amin
Rahma Muh'md Rufa'i Nalele.
*Wattpad @rahamanalele*
” بسم الله الرحمن الرحيم
☆page 04 qarshe da yardar Allah☆😂
*Yau dai na sauke nauyi na huta da yawan tambaya*
Yanzu har ƙofar gidan nasa ya kaisa, yako masa kyakkyawar biya, sanda ya buga ƙofar gidan sosai sannan baba me aikin nata ta fitto bud'e mai, daga ciki tace "waye ne haka, yace "me gidan ne, tana jin hakan gabanta ya fad'i, nan dai ta bud'e mai jiki a sanyaye, ya shiga da rufe gidan...
A tare suka jero dan shiga ciki tana mai sunnu da zuwa, ya amsa ba yabo ba fallasa, kana yayi shashinsa yana sak'a abubuwa da dama, wanka yayi da canja kaya yayi sallah kana ya fitto falan, tsohuwar nanan inda ya barta, dan hankalinta ba qaramin tashi yayi ba, tana da waya amma ba kud'i a ciki, dan ita Sam bata saka kud'i a waya tunda ba kowa take kira ba, bare ta kira Safinan ta gaya mata megidan nata ya dawo, dan tasan me zata ce mai idan ya tambaye ta ita, dan tasan dole zai tambayeta, toh yama za'a ya dawo gidansa bai tambayi matar sa ba...
Aiko katse mata tunanin nata yayi wajen cewa, "Har tsawan wane lokaci Safina ta d'auka tana fitta kwana a waje wajen tarewa da wasu mazan.
A furgice ta kallesa, yako d'aure fuska alamar babu wasa cikin tambayar da yayi matan.
Cikin in i na, tace "Allah ya wucci ranka uban gidana, gaskiya bazan iya tunawa ba, amma nasan, dai Salim da Halifa yaranka ne, dan bayan yaye Salim d'in ne abubuwan suka fara canjawa..
Yace "Me yasa baki tsawatar mata ba, Sannan baki gayamin ba, tace "Afuwa ranka ya dad'e nifa a qarqashinta nake, yin hakan gareta shish shigi ne, baya ga hakan ta qara min albashi, kuma anan kad'ai nake samun biyan buqatata na yau da kullum..
Yace "Wannan ba Hajju bace, Safina da yaranta dani kaina duk amana ne tsakanin mu, kinci amanata kin kuma ci amanar ita kanta Safinan, wai ina kwad'ayi da san zuciya zasu kai mutane ne...
Ba irin abun da bana miki a rayuwa, amma saboda kwad'ayi da buri kin manta haka kin tsaya duba qarin d'an abin da tayi miki, wanda na tabbatar ba abun kirki bane, wai shine yasa ki qin tsawatar mata.
"Kayi hakuri ranka ya dad'e, insha Allah bazan qara aikata wannan kuskuran ba..
SA'EED ya tab'e baki yace "Ai da gaske kam bazaki qara aikata hakan ba, kin kira Safinan ne shigata ciki, tace "aa wallahi, dan wayar tawa babu ko sisi, yace "Ok, bani aran ta zuwa gobe, dan nima ba kwana zanyi a gidan ba, ina dai cikin unguwar, dan zan aiwatar da wani binkice ne, ya kai ƙarshen zancen da tashi, saita miqa masa wayar tata jiki a sanyaye..
Bayan ya karb'a shashin yaran nasu yayi, suna bacci hankali kwance, duk saiya manna musu kiss ya qara gyara musu kwanciya daja musu bargo, kana ya fitto yana ce mata suje ta kulle gidan..
Tace mai toh duk jikinta a sanyayen.
Wata motarsa yahau ya ficce ita kuma ta kulle gidan kamar yanda ya umarceta, mamaki take akan me yasa ya karb'i wayarta. "Allah dai ya nuna mana gobe naga mezai faru. Ta faɗi hakan abayyane.
Shiko dalilin dayasa ya karb'i wayar tata shine, baya san ta kira Safina ne ta gaya mata dawowar tasa, wannan yasa ya karb'i wayar tata, duk da yaji tace ba ko sisi acikin ta, zata iya fitta ta nemi yaro ya siyo mata kati ta kira ta idan taga ya fittan, wannan tunanin da yayi ne yasashi ce mata zaiyi bincike a unguwar tasu, dan ma karta fitto ta nemi wata wayar ta kirata...
Komawa Hotel d'in yayi kamar yanda ya gaya ma waƴannan y'an matan kan zai dawo, haka suka bashi d'aki a jikin nasu Safinan..
Ita ko Safina tana jikin Alhajin nata yana kwasar d'uminta, kwantar mata da hankali yake yi kan karta damu zasu zubar da cikin, tace "Gaskiya Baby ina tsoro, dan ban tab'a zub da ciki ba, wannan ma bansan ya akayi haka ta kasance ba, dan kaga ina amfani da magungunan hana d'auka.. Yace "tabbas haka ne, amma karki damu dan ina tabbatar miki ba abin dazai faru dake, doctor Ozi ya san kan aikinsa, zan masa magana gobe insha Allah, tace Allahn ya kaimu, amma ya zanyi da doctor Aminu bana san ya gayama SA'EED komai.
Yace "Wannan ma karki daku tunda yace bazai gaya mai ba Sam bazai gayamai ba, kinfa san mu maza ba kamar ku bane masu canja magana..
Jin hakan yasa hankalinta ya kwanta, haka suka ci gaba da budirinsu.
KAMAL kam kamar yanda ya udirce aransa kan bazai nuna mata komai ba, hakan yayi, ya sake sukaci gaba da mu'a malarsu..
Sai yanzu wanjen baccinsu ne yace mata "Honey, tace "Na'am, yace "Nayi mantuwar qarasa wasu aikina a Abuja dan haka gobe zan koma, Saidai bazan samu dawowa ba sai qarshen sati, ma'ana nan da kwana biyar, dan Allah kiyi hakuri karki b'ata ranki, dan aikin yana da matuƙar mahimmanci ne, dan dole sai an buqacesa nan da kwana uku, gashi yana da yawa, kiyi hakuri kinji...
Wani shegen murmushi ta sake da cewa "Ai ka kashe ni tunda kace dan Allah, kaci darajarsa, dan haka fatan ailkairi ne kawai tsakanina dakai, amma ka sa'ni idan har kasake ka qara kwana d'aya akan yanda kace, zamu samu matsala..
Yace "baki da matsala MATAR KAMAL..
Anan ko har qarfe hud'un dare SA'EED ya kasa bacci, dan Sam bai runtsa ba, zuciyar cike tam da b'acin rai da baƙin ciki, wai ace matarsa ta sunna itace tare da wani k'atan gardi suna aikata abin da shi shi kad'ai ne yake da hakkin yi mata...
Ya kammala tunaninsa tsaf lalle ba kowace mace bace ake tafiya a barta har tsawan wata uku, ya qara tabbatar wa abin dana miji zai iya jurewa mata d'ai da'i kune zasu iya jurewa...
Wannan shine kuskuran wasu mazan kuma ya kamata su hankalta su gyara, yanzu kam har dashi acikinsu, bazai qara tafiya yabar matarsa haka ba, wannan ma qarin wani ilimi ne, da ace yana tafiya da ita qila da bata fad'a cikin wannan hali ba, tunda yasan halinta da nace masa shi kansa shedane akan sha'awarta, amma duk da haka ai sanda yaji ra'ayinta..
Haka dai yata tunani kala kala, daga bisani ya tashi da d'aukar wata shegiyar dodonarsa ya saka a ajjihunsa kana ya fitta daga room din da yake ciki yaje ya tsaya a ƙofar d'akin dasu Safinan suke. Ya juma kafin daga bisani ya saka wani shegen mukullinsu na sojoji wanda idan sukaje waje wanda wajen yake a kulle sukan iya bud'ewa da mukullan, toh a yanzu ma hakan ce ta kasance, yana saka nasa mukullin, sai nasu na ciki ya fad'i, hakan yasa kofar ta bud'e..
Yamai da ita a hankali ya rufe, ganinsu yayi sunata sharar baccinsu hankali kwance, ga launin wutar da suka bari blue, kallo d'aya zaka musu kad'auka ma'aurata ne, idan kuma ka musu kallo na biyu kabasu suna da masu qaunar junansu, idan ka musu kallo na uku, kace ba qaramin ji da junan nasu suke ba, dan yanda suke maqale da junan nasu abin a kalla ne.
SA'EED ya rintse idansa da bud'ewa wanda ya kad'a yayi jajawur, baƙin ciki da b'acin rai suka qara kamasa, nan cikin fusata ya kunna ainihin wutar da zata bashi haske me yawa, yanda komai zai bayyana..
Aiko nan suka fara mummutsa idansu, can Safina ta bud'e nata tar.. Daidai lokacin ogan nata shima ya bud'e nasa suka had'a ido yace "Baby me kike so kika kunna wutta, zata mai magana kenan idanta ya sauka akan SA'EED....
Ai wata wata zabura tayi da kwalla qara tana faɗin Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, shima ogan nata a rikice ya tashi da kallan inda ya bata tsoran nan shima idansa ya shiga cikin na SA'EED d'in, aiko shima a bala'in tsorace ya zaburan yana wulwulla ido.
SA'EED yayi murmushi yace "lalle kun cika matsiyata, yanzu ke ki rasa wanda zakiyi wurd'a da shi sai mijin Y'ar uwata, kaima karasa wacce zakayi lalata da ita sai Matata...
Nan hawaye ya fara ambaliya a fuskar Safina, ta fara zan bargo tana rufe jikin nata, dan babu komai a jikin nasu daga ita har shi..
SA'EED ya galla mata wata shegiyar harara daci gaba da cewa, Bar wani suturta jikin ki munafuka, dan sai kunyi abin da kukeyi akan idona dan naga jin daɗin da kike samu agunsa, shima naga jin daɗin da yake samu agunki, amma kafin nan sai kun sauko kunyi min tsallan kwad'o kafin ku fara iskancin cikakkun matsiyata..
Kuka sosai Safina ta fara, shiko magiya ya hau yima SA'EED d'in kan yayi hakuri wallahi bazasu qara ba, sun tuba..
SA'EED zaiyi magana yaji ana kwankwasa kofar tasu..
Nan yace "Waye... Wani ma'aikacin Hotel d'in ne yace "Dama camera ce ta nuna mutumin da yake jikin d'akin nan naku ya shigo naku d'akin da fatan ba wani abu zai muku ba...
Kallansu SA'EED d'in yayi murya can qasa yace "kuce ni abokin ku ne kune kuka kirani..
Cikin sauri Alhaji nura kwartan yace "Babu abin dazai mana, Abokina ne mune muka kirasa.
Safina tace "Babu matsala mune muka kirasa...
Jin hakan yasa shi cewa "Toh kuyi hakuri dama nazo naji ne, atashi lafiya, sukace Allah yasa. Yace Ameen da tafiya..
SA'EED ya zaro wannan dodonar tashi da nufar wajen kayan kallo ya kunna kallan, setilai ce, dan haka ya shiga wata tashar waqa ya bud'e volume sosai tayanda duk abin dazai musu bame jin ihunsu, Sannan bazata damu mutane sosai ba, ya kallesu da cewa "Saiku sauko ku fara tsallan kwad'an....
Anan ne fa Nuran ya fara hawaye, nadamar duniya ta kamasa. Safina ko dama tuntuni hawayen yake amfaliya a fuskar tata..
"Dan Allah kayi hakuri wallahi mun tuba bazamu sake ba, sharrin shed'an ne... Suka had'a baki wajen bashi wannan amsar..
Aiko a fusace yayi kansu da yaye musu bargwan jikin nasu, nan babu b'ata lokaci, yahau tabka musu wannan dodonar, tsuka hau ihu neman temako, dan ba komai bane a jikinsu kamar yanda kuka sani, gashi abinka da Soja, duk wata hanya da sukayi qoqarin bi dan tsira mangara d'aya yake musu su zube ya kuma ci gaba da zanesu, sanda yaga jini na fitta daga jikinsu fata fata kana ya barsu da daka musu tsawa yace suyi tsallan kwad'an daya sasu..
Jiki babu kwari haka cikin tsoro suka hau yin tsallan kwad'an, suna kukan da tunda suke a rayuwarsu basu tab'a yin irinsa ba, sunayi yana ci gaba da zanesu, da musu nuni suyi dakyau..
Nadana sa'ni
Nadama
Kaico
Duk sanda suka kamasu...
Nan tausayin Safinan ya kama SA'EED, hawaye ya zubo masa yace ta bar tsallan kwad'an danya tuna da cikin matsiyacin a jikinta, nan ko ta koma gefe ta dungule hawaye naci gaba da zubo mata..
"Wallahi nayi nadama kayi hakuri SA'EED na dena neman mata...
SA'EED ya galla mai wata muguwar harara yace."shege d'an iska matsiyaci mazinace annamimi wanda bashi da hankali, yanzu ku tashi ku hau gadan kuyi basik'an cin naga yanda kuke ji...
Safina tace "Wallahi SA'EED na zab'i ka kasheni da dai na aikata basik'ancin a gabanka, akan idan ka kuna kana gani na...
Matsawa kusa da ita yayi da cewa, "Me yasa kika min haka Safina, me yasa, bayan lokacin da aka canja min wajen aiki sanda na gaya miki kina da sha'awa ki yarda na dinga tafiya dake wajen aikin amma kikace ke Sam baki yarda ba, Ashe dama danna dunga tafiya kina kefewa da wasu mazan ne....
Cikin sauri tace, "wallahi da zuciya d'aya nace maka bazan bika ba, ganina zan iya jurewa, Ashe abin ba haka yake ba, lokacin dana gane hakan sai naji nauyin gaya maka, dan Allah dan Annabi SA'EED ka yafemin ka rufamin asiri wallahi na tabka Babban kuskure...
Yace "na yafe miki Safina, amma ki sani zaki kotum musulunci a yanke miki hukunci akan hakan da kuka aikata...
Tace "zanje, wallahi zanje..
Cikin kuka sosai Alhaji Nuran yace "Nima zanje, dan na zab'i jin kunyar duniya data lahira, wallahi ban tab'a yin nadamar gaskiya irin tayau ba, dan Allah dan Annabi Muhammadu sallallahu-alayyiwassallam ka yafe min SA'EED.
Tausayinsu ne ya kama SA'EED d'in, hawaye ya qara zubo masa a karo na biyu, yace "Na yafe maka... Sannan ke daga nan gidanku zaki wucce na sake ki sakin da babu dawowa,...Ya faɗin hakan ya kashe kayan kallan da bud'e ƙofar room d'in ya ficce.. Dama kiran sallah akeyi dan haka alwala yayi da d'aukar keys nasa da wayarsa da dodonar tasa ya fitto da biyan ma'aikatan Hotel d'in kud'insu kana ya shiga motarsa yaje can wajen masallacin da suka kira sallar...
*Kwana na Huɗu*
Bayan sun idar sanda ya tsaya yayi su rikirorinsa ga Allah, kana yayi gidan nasa..
Anan yaga yaran nasa suka rungumesa suna masu murnar ganinsa...
Anan yayi breakfast d'in da tsohuwar tayima yaran dan tafiya skull, sanda ya bari motar skull d'in su ta d'auke su Sannan ya biya tsohuwan kudin aikinta, yace tatattara tabar masa gidansa..
Tana kuka haka tatattara kayan nata tabar gidan...
Bayan yayi wanka gidansu ya nufa, wato gidan iyayensa, A takaice dai ya gaya musu abin daya faru, sunyi baqin ciki Sosai da hakan, dan da gaske suke san Safina, mahaifiyarsa tace ya kawo mata yaran nasa ta rik'e...
Anan ya kira yayar tasa ya gaya mata komai, ita kam sumewa tayi, sanda Babban d'anta yasamu kanta kana ta samu bakin yin kuka, tana me tsine musu, wai mijinta ne da matar qaninta suke aikata fasik'anci....
Su Safinan ko tunda taji batun saki dama ta qara volume d'in kukanta, sanda tayi me isarta ita da kwartan nata kana tatashi a daddafe tayi toilet tayi wankan ta gabatar da sallar asuba, lokacin qarfe takwas da rabi, haka ta shirya ta jira kwartan nata ya gama nasa shirin kana tace mai, "Na qara yarda Nura Allah ba mutum bane, dan ako wane lokaci yakan iya canja ma rayuwarka, ka duba ko a mafarki ban tab'a tunanin ƙarshen wasan namu haka zaizo ba, duk da nasan Dole ƙarshen yazo dama da muni, amma ban bashi har haka ba...
Nadamar gaskiya nayi ba nadamar ƙarya ba, zanje asibiti yanzu a duba min lafiyata dan cikina ya fara min ciwo, bazan zubar da cikin ba kamar yanda kace, wasan namu ya qare daga yau... Takai ƙarshen zancen da zubo da hawaye, sai yace "Na cutar da rayuwarki Safina, da ban nemeki ba da wata qila baki fad'a wannan halin ba, tace "kafin kai nayi mu'amala da wani, amma yanzu baya qasar, kadena zargin kanka dan bakai ka bud'emin hanya bah, cutace dai na cuci rayuwata, dana yarda da shawarar mijina da yanzu bana cikin wannan halin, dan sanda ya gaya min gaskiya kan na bisa dan yasan halina, amma nace mai aa... Tana kawowa nan cikin zancen nata tatashi tabar room d'in.. Kuma direct gidanta ta wucce, dake tana key d'in gidan haka ta shiga ta kwashe dukkan kayan sawarta kaf, ta zuba cikin motarta, kana taje gidansu, Sam babu tsoro ta gaya ma mahaifiyarta komai bata b'oye mata ba, dan mahaifinta baya raye ya rasu tun tana yarinya....
Kuka sosai mahaifiyar tata tayi, ba abin daya burgeta da Safinan kamar yanda tace zata bi dokar muslinci, tabbas da ace ana bin hakan da iskancin bazai ya waita bah, dan ba abin da musulincin ya bari...
Safinan ta kira SA'EED tana mai magana akan Yaranta, ya bata labarin yanda sukayi da mahaifiyarsa kan zata rik'e yaran, dan Yanzu haka ma ayau zai kwashe dukkan ka yayyakinsu ya kai mata...
Murmushin baqin ciki kawai tayi...
Ta kira number na MATAR KAMAL dan taga miss call nata biyu, amma Saidai kusan kira shidda bata d'auka ba...
Abin dayasa hakan kuwa shine.. Bayan KAMAL yayi shirin sa da safe da misalin qarfe bakwai yayi mata sallama kan tafiyarsa daya gaya mata jiya, tayi mai shagwaɓar kissa kan bata san tafiyarsa yadai lallasheta anan dai sukayi sallama, direct gidansu yayi nan kamar yanda ya gaya mata haka ya gaya masu, kana yayi musu sallama bai zame ako ina ba sai'a wani Hotel me suna Habib anan dai kusa dasu.. ya kama d'aki yana jiran lokaci yaga me zai faru...
Danya shirya mata wani mugun taget, wanda duk wanda zatayi waya dashi saiya shigo wayarsa ya gani, ta hakan ne zaisan me yake faruwa...
Ilai kuwa ko cikakken minti talatin baiyi da zama ba, saiga shi yaga tana kiran wata number ta cikin application d'in daya had'a target d'in nata
Toh da gaske kiran wayan oganta take, dama yana fitta, tayi saurin gyara gidan nata dajin kwad'ayin ogan nata, wallahi Sam bata gajiya da Tsowan, kamar yanda tasan shima baya gajiya da ita, saikace sun dad'e basuji junan nasu ba..
Shine yanzu da take kwance akan gadanta ta kirasa, shine ai KAMAL d'in yaga kiran da take mai..
Dama shima tsowan banzan yana office d'insa dan shigarsa kenan, saiya d'auka wayar da cewa, "Baby nasan albishir d'in da zaki min, wato wannan yaran ya qara komawa Abuja d'azu ko..
Tace "Haka ne, dama yanzu nake san nad'an jika kad'an dan duk sha'awar ta baibayeni..
Yayi murmushi yace "Wallahi na fiki jin hakan, amma dan Allah kimin hak'uri zuwa nan da qarfe biyu, idan muka d'an tab'a dare mayi me dalili, tace "Oh Baby banso hakan ba, amma na maka hakurin, dan ban sani ba ko ka zube ma shegiyar matarka ruwan ne...
Dariya yayi, da cewa "Tausayi ta bani, sai bina take kamar jela hakan yasa nad'an kulata, Sam babu dad'i haka take kamar dusa... Dariyar itama tayi da cewa "kai dai ka sa'ni, Sannan idan zaka tawo ka kawo min da kayan fruit nawa ya qare.. Yace "Baki da matsala akan hakan, amma me yasa bazamu had'e a hotel ba, kinga yanzu rana ne, kuma kinsan nifa ba cika san zuwa gidan naku nake ba, tace "Kawai bazan fitto bane, dan kwana biyun nan sanyi akeyi, kuma kasan bana san sanyi, yanzu duk sai kaga mura na kamani, a takaice dai banda ara'ayin zuwa can kazo gidan kawai ka sameni, ai ta ƙofar baya zaka shigo, dan yau na cire d'aya daga cikin key d'in wajen a cikin keys nasa, kuma har na bud'e maka.
Yace "Toh ba damuwa zaki ganni kafin ma lokacin..
Da haka sukayi sallama...
Gumi da zufa ne suka dinga karyoma KAMAL, shi dai kamar yasan muryar wanda ta kira d'in...
Yanzu JAMILANSA ce take mu'a mana da wani namijin a waje...
Hawaye ne ya zubo mai, shiko zaiga ikwan Allah, bari k'arfe biyun tayi zaije yaga meke faruwa...
A wannan lokacin ne ta kira Safina kira biyu bata d'auka ba, shine taje tasa wayar tata a caji acan falanta, ta miqe kan duguwar kujera sai kuma taji bacci nasan kamata, hakan yasa tatashi taje gadanta ta kwanta..
Wannan shine dalilin dayasa Safina tayi mata kira har shidda a wayar tata bata d'auka ba...
Wato ita dai kofar bayan da JAMILAN take gayama ogan nata wata ƙofa ce da KAMAL ya fittar da ita dan yafi jin sauƙin shigowa ta ita, musamman idan shigowar dare yayi, basai yasha wahalar zagaye ba, kuma tafi sirri ba kowa bane yake gane ka dawo...
Qarfe d'aya da rabi yabar abin da yake a office d'in nasa ya iso Gidan nata kamar yanda ta umarce shi ta ƙofar bayan ya shigo da kayan fruit d'in data buqata..
Kai tsaye ba wani batun tsoro ko shakka bedroom d'inta ya shiga, nan ya ganta kan Sallaya ta idar da sallar azahar, dan tashinta kenan tace bara tayi sallah..
Ai suna had'a ido suka sakarma kansu murmushi, sanda ta shafa addu'arta kana suka rungume juna...
"Baby d'an kwana d'ayan nan wallahi bakaji yanda nayi missing d'inka ba, yace "Nima haka Wallahi *Matata* kuji wai matarsa ko agidan ubansa tazama matar tasa🤔 ( Rahama Nalele tace bar mutumin banza mana😡 )
Haka kamar wasu jarababbu suka fara harkan tsiyarsu..
Sun shagala sosai dan babu komai ajikinsu haka suke kamar yanda sukazo duniya, daidai lokacin ko shima KAMAL ya shigo gidan ta ƙofar bayan...
A hankali yake shiga cikin gidan har ya iso ga falan nasu, tun anan yake jin gurnaninsu da magana qasa qasa irin ta waƴanda suka shagala, jiki a sanyaye ya qarasa bedroom d'in nata, dake sun san bame zuwa musu ko d'an sakaye kofar basuyi ba, haka KAMAL ya gansu aihuwar uwarsu da ubansu...
Sun sake tsakaninsu da Allah kamar ma'aurata.
Jiri ne ya fara kama KAMAL yaji kansa na juyawa saboda tsabagen tsoro da furgicin daya kamasa a lokaci d'aya.🤞
Mahaifinsa da matarsa ta sunna suna aikata Zina acikin gidansa.
Kansa ne yaji yana Sara masa, zuciyarsa ta d'auki zafi, k'afafuwansa suka kasa d'aukar jikinsa, nan take kuma gabaki d'aya illahirin jikin nasa ya d'auki karkarwa yace "Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un.. Yana faɗin hakan ha yanke jiki ya fad'i sumamme...
Sam basu san da tsayuwarsa ba sanda sukaji ya furta kalmar Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un d'in sannan suka farga dashi, dukkansu zubamai ido sukayi...
A lokaci d'aya kuma suka saki junasu, nan take kuma damuwar duniyar nan ta diran musu..
Ba batun b'ata lokaci sukayi saurin kintsa kansu, hankalinsu ya bala'in tashi...
Tare suka kinkimeshi suka kaishi motar ogan nata wato Baban nashi, still tare suka kaishi asibiti...
Nan ko doctors suka hau bashi temakwan gaggawa..
Haka dai Baban nashi ya kira matarsa wato mahaifiyar KAMAL d'in ya gaya mata wai KAMAL na asibiti, mamaki ya kamata, tace meya same shi, kasa ce mata komai yayi, jin hakan tace Toh ya gaya mata wane asibiti ne.. Nan ya gaya mata, dake ba kowa a gidan duk qannan nasa sun tafi skull hakan yasa ta kulle gidan ta nufo asibitin...
Zuwanta yayi daidai da fitowar doctorn dayafi dubasa, sukayi kansa da sauri suna tambayarsa lafiyar KAMAL d'in....
Jiki a sanyaye, yace "Saidai kuyi hakuri, KAMAL ba rayuwa zaiyi, dan yaga abin daya furgitasa sosai, hakan yasa zuciyarsa kamuwa, munyi iya qoqarinmu dan ganin munyi controlling d'inta amma abin ya faskara, dan haka ku shiga kawai ko zaku iya sallama dashi...
Ai har suna bangaje doctor d'in. Haka suka shige cikin d'akin...
Mahaifinsa ya durƙusa a gabansa cikin kuka sosai yace "ka yafe min KAMAL na cutar da rayuwarka, na maida matarka Matata, dan Allah dan Annabi ka yafe min...
KAMAL ya rintse idon sa, wanda hawaye yake zubar mai, ya kalli JAMILAH wacce itama kukan take sosai tana cewa, "Na shiga uku, dan Allah KAMAL ka yafe min, wallahi nayi nadama, karka mutu da baqin ciki na, idan ka mutu da hakan bazan ga kyakkyawan ƙarshe ba, ba irin Soyayyar dabaka nuna min ba, amma sanda naci amanarka, amanar da duk wanda yaji saiya tsine min da tsinema rayuwata, dan Allah ka yafe min KAMAL...
Wani kyakkyawan murmushi KAMAL d'in ya sake, jini na fitto masa ta baki ta hanci, yace "MATAR KAMAL, kowane lokaci k'awayanki da wannan sunan suke kiranki, kuma ba ƙaramin farin ciki kike shiga ba idan sun fad'in miki hakan, ayau ki duba girman Allah ki gaya min gaskiya shin waye fek waye original tsakanin ni da Mahaifina, idan akace miki MATAR KAMAL wa kika bama wannan sunan tsakanin ni dashi..
Cikin kuka sosai tace, "Allah ya sani Annabi ya sani jama'a sun sheda Kaine original, Amma dake shed'an ya buga min ganga, Wallahi bana tunaninka idan aka kira ni da MATAR KAMAL, Mahaifinka shi nake tunawa, danya tsaya min arai fiye dakai, kuma na saka a raina ni MATAR MAHAIFINKA ce ba MATAR kaba KAMAL, kayi hakuri tambayana gaskiya kayi, toh wannan itace gaskiyar, amma a yanzu na tsani Mahaifin naka, ni kai nake so, dan Allah ka rayu mu sake sabuwar rayuwa...
Murmushi yayi da cewa, "kin rigada kin b'ata komai MATAR KAMAL, ni ba rayuwa zanyi ba, sai dai zan baki shawara, wallahi qarshenki bazaiyi kyau ba idan har baki je kotun musulunci ta zartar miki da hukunci ba..
Yana Faɗin mata hakan ya kalli mahaifinsa wanda banda kuka ba abin da yakeyi, yaci gaba da cewa, Dady bana san kace min komai, kaje na yafe maka, Nima ka yafe min, yace "Ba abin da kamin KAMAL imma kayimin wallahi na yafe maka....
Nine naja ra'ayin JAMILAH, wata ranah datazo min da qarar mahaifiyar tasa ta a gaba, saina fahimci tana matuƙar san rayuwa dakai, shine nayi amfani da wannan damar na nuna mata zaka rayu da ita ita kad'ai ba batun matsawar uwar miji bare kuma wata kishiya, amma Saidai in zata amince da buqatata, ta d'auki lokaci me kafin ta amince min, dan Allah ka yafe min KAMAL...
Hawayen dai sune suka qara zubo ma KAMAL, baice masa komai ba saima maida kallansa ga mahaifiyarsa da yayi wacce itama sai zubda hawaye take, tunda ta gama gane me yake faruwa, bata jira ya fara mata magana ba, tace "Na yafe maka KAMAL.., insha Allah baka ba samun matsala acikin kabarinka, albarkacin Annabi Muhammadu sallallahu-alayyiwassallam...
Tana fad'in hakan kuwa, sai KAMAL d'in yayi kalmar shahad'a nan dai rai yayi halinsa...
JAMILAH ta zambad'a ihu tana ta shiga uku, mahaifiyar KAMAL ta kalleta a fusace tare da galla mata wata shegiyar harara tace "ai baki shiga uku ba, tunda kin had'a nan kin kuma had'a can, nan KAMAL can KAMAL, d'aya ya musu sai kici gaba da mu'amala da d'ayan, dama ni nasan ba banza ba nake jin muguwar tsanarki a raina....
Fitta daga d'akin JAMILAN tayi... Direct gidanta tayi, ta kulle kanta a gidan ta dinga kuka, sanda tayi me isarta, kana taje toilet ta tsaftace kanta, bayan ta fitto taji ana kwankwasa mata kofar get d'inta sanda ta saka kaya Sannan tazo ta bud'e, Safina tagani,.. Aiko saita rungumeta ta rushe mata da kuka, itama Safina jin kukan kawai tayi yazo mata, haka suka dinga yi sanda sukayi me isarsu, kana Safina ta tambayi JAMILAN meya faru da ita haka...
Aiko nan babu b'ata lokaci JAMILAN ta bata labarin dukkan abin daya faru, ta qara dace nata "meya faru dake ke kuma, naga duk jikinki a farfashe..
Hawaye ne ya zuboma Safinan, itama ta kwashe dukkan abin daya faru da ita ta gaya mata, ta qara da dace mata, "Yanzu haka daga asibiti nake, doctor ya duba ni sosai yace min nayi hankali da cikin jikin nawa, dan na qara bari aka kuma min irin dukkan da SA'EED yamin toh ba shakka cikin zai fitta, shine ya rubutamin magunguna naje na siya, nace bari na biyo tanan na gaya miki abin dake faruwa...
Wallahi JAMILAH, nayi nadama, kuma shima Alhaji Nuran na yarda da nadamarsa dan ya kirani d'azu yace min yaje kotun musulinci da maganar tamu d'azu, sunce muje jibi ni dashi..
JAMILAH tace "Nima zanje su yanke min hukuncin, dan na tabbatar idan banyi hakan ba bazanyi kyakkyawan qarshe ba, bani da uwa bani da uba, sai dangi, idan nace ma zanyi rayuwa da dangin rayuwar unci zanyi, tunda bani da qanne bani da yayu..
Haka suka dinga tattaunawa suna kuka, da amincewa zasubi duk abin da musulinci ya zartar musu, kana suka rabu, JAMILAH ta kwashe kayan sawarta itama taje gidan qanwar mamanta, haka itama ta cire kunya ta gaya mata komai, itama ta tausaya mata..
Aiko kwana uku Safina da Alhajinta Alhaji nura sukaje kotu ta yanke musu hukuncin jefewa, amma banda Safinan a yanzu dan saita haihu...
Jin hakan yasa JAMILAH kiran Baban KAMAL ta gaya mai itama zata idan zaije sai suje bayan arba'in din KAMAL..
Haka ya gayama matar tasa cewar zeje kotun musulinci a zatar mishi da hukunci, dan kwata kwata taqi kulasa dan tace saiya bata takardar sakinta, amma tana jin hakan sai hankalinta ya tashi tausayinsa kuma ya kamata, tace "da baka aikata hakan ba, da yanzu muna tare...
Kuka take sosai ita da yaran nata, way'anda suma suka san me yake faruwa,...
( Rahma Nalele tace Oh wannan abin kunya dame yay kama )
Sanda ko akayi arba'in d'in Sannan sukaje, suma yanke musu jefa akayi, nan da kwana uku...
Jama'ar musulmai haka tsoran aikata Zina ya qara kamasu, musamman yara yaran nan, irin su SAMARIN BANAH, nan suka k'yamaci aikata zinar, suna masu tsoran idan sukayi idan har suna san kyakkyawan qarshe toh fa Saidai suzo a jefesu...
Haka ko y'an uwa da abokan arzik'i suna kallo yara suka jefesu, kamar yanda dangin Alhaji Nura suma suna kallo aka jefesa..
(Rahama Nalele tace da haka masu aikata lefin suke, watoh idan sunyi suje a jefesu da zinan tayi qaranci cikin al'uma, Amma ina yanzu waye yake zuwa amai haka, jama'a muji tsoran Allah. Wallahi Allah ba mutum bane, Wallahi Akwai kwanciyar kabari da tashin alqiyama)
Safina tasha kuka sosai jin an jefe babbar qawarta JAMILAH...
Kwana uku tsakani cikin jikinta ya zube, sakamakwan fad'uwa da tayi a toilet, bayan tasamu kanta a asibiti haka taje itama kotun, aka zartar mata da nata jifan..
Allahu Akbar, jama'a muji tsoran Allah, mu gujema aikata Zina, dan babbar MASIFA ce a garemu...
Alhamdulillah, Anan na kawo muku ƙarshen wannan gajeran labari nawa na MATAR KAMAL, Allah ya yafe mana kuskuran da mukayi cikinsa, Nagode fans nawa, kubini a saban littafina na gaba, wanda Soyayyace zallah da ƙauna acikinsa...😍😍😍 Rahama Nalele dai taku ce.
*** mata zallah banda namiji danni matar Aure ce...