Hoorain mai kusumbi (the hunch back girl)
3-4
by @nooriman
🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓
(The hunch back girl
_NoorEemaan_
Chapter 3️⃣⏩4️⃣
"FIELD MARSHAL"
Shine sunan daya gani a rubuce baro-baro kan screen din wayar sa.
Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunne sa, cikin girmamawa wa marshal yace
"Good evening sir!"
"Evening captain, hope you are good?"
Hamdan yace "very well sir"
"That's nice, am... kan maganar da zaka jagoranci wasu sojas zuwa yaki ya tashi daga sati mai zuwa, domin mun samu labarin yan ta'addan nan sun sake kai farmaki wa kauyen, suna cikin wani hali matuƙa, dan haka jibi ne tafiyar ku in Sha Allah, domin gobe za a kamalla muku komai na tafiyar, all the Best captain Hamdan"
"Thank you sir" ya amsa yana taune jajayen labban'sa masu daukar hankali.
Ya jima yana tunane-tunane kana bacci ya dauke sa, kasancewar a matukar gajiye yake.
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
*WASHEGARI*
Misalin karfe goman safiya ce, zaune yake cikin motar sa yana sharara gudu kan lafiyayyen kwaltan, sanye yake da three quater wando na soja, sai singlet shi ma na sojas daya bayyana karfafan kafadun sa masu fadi, babu hula a kan shi yayi parking gashin sa as usually, kafar sa sanye da sandal fari mai igiyoyi, hannunsa dake murza sitiyarin cike da kwarewa sanye yake da tsad'add'en agogo, yayi mugun yin kyau...
Karatun Alqur'ani ke tashi cikin surutal Al-furqan, a nutse yake bi cikin zuciyar sa, wayar sa dake kan kujerar mai zaman banza ya dauka ya yi danne-danne kana ya kara a kunne sa, bayan seconds hamsin aka daga kiran daya ɗayan bangaren.
Kasa-kasa kamar mai tsoron kar a ji shi yace
"Assalamu alaikum, ina kwana first love, am on my way coming"
Abinda yace kenan ya katse kiran, bayan mintuna goma ya shigo unguwar su Nasarawa GRA, horn ya danna aka bude masa ya shiga, a tsakiyar gidan ya yi parking motar kana ya nufi part ɗin Ammi.
A bakin kofar glass ya tsaya, kofar ta buɗe ya shiga, runtse ido yayi sak'amak'on ganin Ayiyah a Zaune, a ransa yace
"damn it! Meyasa matar nan ta dawo" domin idan akwai abinda yake gudu toh Ayiyah ce, duk da kasancewar ta kakar sa, amma mugun ciwon kai take bashi.
Ware rikitattun idanun sa yayi, kamar yadda ya saba ciki-ciki haka yayi sallama, yana k'ara daure fuskar sa tamau, gudun kada Ayiyah ta kawo masa wargi amma bai tsira ba...
Cikin muryar ta mai cike da k'arsashi duk da ta tsufa tace
"fuska Fara, zuciyar ka baka, idan ka ga dama ka dawo da fuskar ka ta shanu bai dame ni ba, wallahi sai nayi magana, domin ni idan nayi shiru ban yi magana ba bakina wari yake, wanna gantalewa da bakin halin har ina, a cewa kullum mutum fuska a murtuke kamar na kashin asuba "
Ammi dake jin su kuwa matse dariyarta tayi, Hamdan kuwa kara bata rai yayi ya nufi wajen Ammi ya zauna kusa da ita, Cikin kaunar mahaifiyar sa ya kalle ta kana yace "Ammi hope you are Fine?"
"Am very fine Dan albarka, ya aiki?"
"Fine first love"
ya amsa yana ɗora kansa kan kafadar ta.
Wani tabe baki Ayiyah tayi tace " haka fa, sai karyar turanci, yanzu fisabilillahi ko kunya baka ji, katoto da kai ka wani zo ka manne wa uwar ka, ko su Abbas da suke kannen ka basa wanna iyayin, ko da yaƙe laifin uwar ka nake gani, domin ita ke shagwaba ba" ta bantali goro tana tauna, jikake karas karas ta kuma baza kunne domin jin yayi magana amma bai kula ta ba, hakan ya dame ta, domin ita kam bata iya shiru ba, ba kuma ta so a yi shiru, "nayi magana kayi shiru kamar baka ji ba, gaskiya dai sai na fada, kuma bari ka ji ka yi ka nemo matar aure domin mun gaji da ganin ka haka, ko kuma na je kauyen su wata kawata na samo maka mata a can...."
Daga kansa yayi daga kafad'ar Ammi ya watsa wa Ayiyah, tilas ta tsuke bakin ta, domin tsoron kwayar idanun sa masu launin sky blue (kalan sararin samaniya) take, domin duk masifar da take mishi bata kallon fuskar sa.
Daga karshe ma mikewa tayi ta fara tafiya tana kananun surutai, Hadi da kwala wa mai aiki kira kan ta kawo mata abinda tace ta dafa mata.
Tana barin wajen Ammi ta saki murmushi mai sauti, sannan ta kalli Hamdan tace "ka dinga hakuri da halin Ayiyah son, ka san rikicin tsufa ke damun ta, kaji ko"
Jinjina mata kai yayi alamun toh.
Nan ya sanar da ita cewa an dawo da tafiyar su gobe, sosai Ammi tayi masa addu'a tare da fata na gari, duk da jikin ta yayi sanyi.
Suna zaune a haka su Abbas suka shigo, cikin girmamawa suka gaishe shi, hannu ya mika musu alamun su yi musabaha ba tare da yace komai ba, dadi ya kama su, Anas shine farkon mika hannun sa saboda farinciki, duk ranar da Hamdan ya shiga harkan su dadi sosai suke ji
Kallon su Ammi tayi cikin burgewa, da godewa Allah daya bata zaratan samari masu kyau da nutsuwa, duk da cewa Hamdan baya shiga harkan su, amma yana matuk'ar kaunar kannen sa, halin shi ne haka, baya shiga harkan mutane sam, ga wanda bai gane ba sai ya dauka wulakanci ko girman kai ne dashi, shiyasa a kullum take rokon Allah ya bashi mace da zata Sanja masa wanna halin nasa ko da ba duka ba, but at least ya kasance mai walwala kamar kowa..
"Anas, kabeer, Omar."
"Yes Ammi" suka amsa a tare.
"Kuyi wa Captain addu'a gobe zai jagoranci wasu sojas zuwa kwantar da tarzoma da yan ta'addan suka tayar a garin Kogi" kasancewar labarin a bayyane yake, domin duk wata kafa ta sadarwa sun fadi halin da wannan yan garin suke ciki.
"Addu'a sosai suka yi masa, a kasan makoshi ya amsa da "Ameen" sun karanci hakan ta lips din sa, sai suka kalli juna suka yi murmushi...
Anas daya fisu surutu ne yace "Ammi, ina Ayiyah?"
"Yanzu ta gama drama da yayan ku, ina tunanin tana dakin ta"
Dariya suka yi, kana suka mike, domin tafiya wurin ta, su kam suna kaunar Ayiyah a gidan, ko ba komai zasu ci dariya.
Hamdan bai bar gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan ya bawa Ammi makud'an kudade, sannan ya bawa su Anas har ma da Ayiyah, duk da basu rasa komai ba amma hakan baya hana shi ya basu kudi.
Domin har yau akwai kamfanunuwan mahaifin su daya bari kafin ya rasu kuma su Anas ke kula da shi.
Addu'a Ammi ta kara yi masa, ya rugunme hallita mafi soyuwa a rayuwar sa cikin jin dadi samun ta a matsayin uwa mai kulawa da tsananin son y'ay'an ta.
Da haƙa suka yi sallama Ammi na daga masa hannu har ya fita kana ta share hawaye tana rokon Allah ya dawo mata da shi cikin koshin lafiya.
*BUKAVU BARRACKS*
Hilux Masu dauke da zanen sojoji hadi da motocin amoka da yawa suka jeru reras, kimanin soldiers da zasu kai dubu dari biyar ke tsaye ko wanin su ya kame cikin kayan sojoji, sai jaka irin na sojas dake rataye a bayan kowanne su, ga bindigan AK-47 dake rataye a kafadar su, kawai jiran umarni suke domin su fara tafiya.
Cikin tafiyar nan tasa ta lafiyayyen namiji mai ji da kuruciya hadi da takama ya nufo inda motocin suke,...
Wajen commander dake tsaye ya nufa, ya kame hadi da tsara masa, hannu shi commander ya kama suka dan koma gefe, yayi masa wasu maganganu da basu wuce mintuna uku ba sannan suka dawo inda commander'n ya tsaya dazu, wani Kurt soja ya bude wa hamadan kofa, cikin jarumta ya yi tsalle ya fada cikin motar amoka domin irin mai tsayin nan ce, umarnin tafiya ya bayar, nan motocin suka fara tafiya, a jere...
Sauran sojas da babu su a yak'in tsaye suna daga musu hannu hadi da yi musu fatan dawowa lafiya, haka suka ratsa gate suka fice...
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
*KOGI STATE*
*(Kauyen Oguma)*
Kauye ne mai girma hadi da tarin jama'a, ga ni'ima mai sanyi da Allah ya albarkaci kauyen da shi.
A yau ya kasance ranar cin kasuwar su ne, amma babu halin hakan, saboda tashin hankali da tsoro da suke ciki, sakamakon yan ta'adda da suka kawo wa kauyen farmaki, wanda hakan ya sa suka rasa kwanciyar hankali, fuskar su a lullube da tsoro kallo daya za ka musu ka fahimci hakan, ko yaran su basa iya zuwan makaranta, dare da rana cikin addu'a suke kan Allah ya kawo musu dauki, domin har sun rasa yan'uwa da abokan arzikin da yawa.
Gida ne dan madaidaici mai dakuna biyu ginin jar kasa, irin na kauye, har rubewa ginin ya fara yi, kallo daya mutum zai yi wa gidan ya fahimci cewa ko a talakawan kauyen, wanna gidan nasu talaucin ya munana.
Yarinya ce yar shekara goma sha bakwai ta buɗe wata kod'add'iyar zanin atamfa daya kasancewa kofa ga banɗakin su da ko rufin sama babu ta fito.
Abin mamaki da al'ajabi ga wanna budurwa mai kananun shekaru shine Bata tsaya kan kafafun ta ba, ta tsunkuya irin yadda tsofaffi masu tarin shekaru da basa iya tsaye kan kafafun su haka take, sakamakon kusumbi (hunch back) dake bayanta, kusumbin ya kumburo sosai a bayanta tamkar an kifa katon kwarya.
Kyakkyawar ce, sannan fara ce, sol irin mai daukar idon nan, duk da cewa suna fama da talauci, amma skin dinta na nan fresh wanda hakan baya rasa nasaba da ni'imar kauyen da suke dashi
Butar hannun da ko albarkan murfi babu, ga shi duk ya faffashe ta ajiye a gefe kana ta yi tafiya irin na masu kusumbi ta zauna kan matacciyar tabarman dake shimfide a gefen dakin su.
Numfashi ta sauke bayan ta juya lulu eyes dinta masu girma hadi da haske...
tagumi tayi, bazata ce rayuwa bata mata adalci ba, sai dai akwai tarin kalubale a rayuwarta da take fatan ya zama nasara ko samuwar farinciki ga rayuwar ta, duk da hali da lalurar da take ciki tana godewa Allah, domin akwai wadanda suke cikin hali daya fi nata muni, sai dai raunin ta na bayyana ne a duk lokacin da ta fita, yammatan kauyen ke sata a gaba da tsokana da kiran ta *HOORAIN MAI KUSUMBI* ga zallan kishi da take hangowa a idanun su wanda bata san ko na menene ba, duk da lalurar ta...
Kara juya fararren idanun ta tayi, wanda hakan dabi'a ne a gareta, sannan ta rufe idanun ta ruf, tunanin tashin hankali da suke ciki a wannan k'auyen take, addu'a take a ranta kan Allah ya kawo musu mafita da kwanciyar hankali.
"HOORAIN!"
Taji an kira sunan ta...
Share share share
fisabilillah 🙏
NoorEemaan
***