Hoorain mai kusumbi (the hunch back girl)

7-8

by @nooriman


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓

(The hunch back girl)






# _NoorEemaan_




*DEAR LOVELY FANS DA MA MAKARANTAN HOORAIN PLEASE KU KARANTA WANNAN BAYANIN NAWA IT'S VERY IMPORTANT*


_Zan yi wanna dan tsokacin ne idan ma akwai mai irin wanna tunanin a ransa_.

_Kila wasunku zaku ce meyasa Noor ta rubuta cewa HAMDAN yana da gashi, bayan ba a san sojojin da gashi ba_.


_Yeah it's possible soldiers su tara gashi, amma mafi yawa na nan Najeriya basa yi_...

_Abin da ya saba dokar soja shine askin banza ne ba a so_... _Amma bawai basa tara gashi bane, sai dai mafi yawan su basa tara mai yawa_...


_Dan haka Habibte's ina sane da abinda na rubuta, domin ina da experience a akan soldiers, ina da friends da yan'uwa sojas, and also tun Ina pre-nursery har na gama secondary school a barrack din sojoji nayi karatu na, to Cut it short_...

_Haka nake son HAMDAN ya kasance a littafin HOORAIN, shiyasa na rubuta cewa yana da suma_.

_Abu mafi muhimmanci a novel shine sakon da marubuciya take son isar wa yaje inda ake so_.


_A karshe dai makaranta na da suke bibiyata tun daga farkon book dina sun san cewa duka book dina fictional story's ne, ban taba rubuta true live story ba, Dan haka a Novel ba komai ne dake faruwa a gaske za a rubuta ba, dole akwai nishadantarwa domin kawata Labarin_.



*Thank you all da yanda kuka karbi littafin HOORAIN MAI KUSUMBI Allah ya bar kauna, son so nake Muku.💞




Chapter 7️⃣ ⏩ 8️⃣


Tafiyar da ya kamata yayi a Mintuna talatin, a 20 minutes yayi shi.

A lokacin daya isa wajen yayi mamakin yadda abu ya ɓaci haka, ba tare da bata lokaci ba ya shiga cikin sauran soldiers aka cigaba da fafatawa cike da kwarewa wanda hakan ya nuna cewa sun sha training mai zafi...



A takaice dai sai karfe hudu saura aka samu komai ya lafa, inda yan ta'addan nan da suke rage takwas har da shugaban su suka yi kokarin guduwa, domin bullet din su ya kare.


Cikin sa a hamdan ya samu nasarar sakarwa biyar arbi a kafafun su biyu, sauran ukun ma wasu soldiers din suka karbe su, hakan yasa suka zube a kasa suna ihu azaba...


Umarnin Hamdan ya bayar cewa a kamo su duka. Sannan ya ce wa wasu soldiers din su tsaya a kauyen har safiya domin tabbatar da tsoro, cikin girmamawa suka amsa da "yes sir!"

Bayan sun isa gidan da suka sauka nan aka kulle yan ta'addan nan a wani daki.



*WASHEGARI*

Kusan ko wani kafa da sadarwa sun samu labarin abinda ya faruwa, sun kuma bayyana wa jama'a, zuciyar mutane cike da farin ciki nasarar da Allah ya bawa wadanda jaruman sojas din masu kishin kasar su.


Field marshal wanda shine mai 5 star rank general, haka kuma shine highest rank a Nigerian army, Ya kira Hamdan ya yaba masa.



Ammin ma ta gani a news din karfe shida da ta kalla, ta kira hamdan tayi masa murna sosai da addu'ar Allah ya dawo da su lafiya.



Da misalin k'arfe taran safe yan jaridu sun cika k'auyen oguma domin cigaba da daukar rahoto, Sannan an kai yan ta'addan nan babban kotun Abuja kasancewar daga kogi zuwa Abuja babu wani mugun nisan, an saka su a prison zuwa ranar da za a yanke musu hukunci...




*BAYAN KWANA ƊAYA*.


Ta bangaren yan k'auyen oguma kuwa sosai suka tashi da nishadi a safiyar yau, tsoron da fargaban su ya kau, sun dawo hada-hadar su kamar yadda suka saba cikin walwala.




********


Tafe take cikin tafiyar ta irin na masu kusumbi, hanyar rafin kauyen su ta nufi, duk da yanda mami ta hanata zuwa, amma bazata iya kallon Mami da girman ta na zuwa diban ruwa yayinda ita ke zaune ba.



Jefi-jefi tana haduwa da mazan garin suna gaisawa a mutunce. Allah yayi wa Hoorain wani mugun farinjini wanda hakan ke bak'anta ran yawancin yammatan kauyen, ganin su lafiyayyu marasa nakasa mazan basa Kula su kamar yadda suke wa Hoorain magana.



***


babba rafi ne wanda yake kashi uku, bangaren daya wasu na wanka, dayan wasu na wanki, dayan kuma na diba ne, a sha a kuma yi girki ba a shiga cikin sa.



Ga wani babban maciji mai jan abu a kansa kamar hula yana gefen ruwa ba tare da yayi wa kowa komai ba, haka ma mutane dake rafin basa tsoro, abu ne wanda sun riga sun saba da ganin sa, domin duk wani d'a ko y'a a k'auyen haka ya tashi ya tarar da macijin nan a rafin.



Sannan abin mamaki da tsoro, ga wanna macijin shine matuƙar mace na period bata wanka cikin rafin, sannan idan akwai janaba ko da datti a jikin Mutum ya shiga rafin dan wankan toh sai macijin nan ya sare shi.



Ga yammatan nan da yawa wasu na wanki, wasu na wanka, wasu na hira a tsakanin su.


Ko kallon su Hoorain bata yi ba ta cigaba da tafiyar ta a hankali domin isa wajen diban ruwa, tana jin yammatan nan na mata dariya, ta gefen ido ta ga wata na k'waik'wayon irin tafiyar ta, Murmushi Mai ciwo tayi wanda ya taho da zubar hawaye mai dumi daga idanun ta, hannu tasa ta share fuskar ta.


Saka madaidaicin bucket Mai hannu tayi ta diba ruwan ta kana ta fara tafiya domin barin rafin, ta ji sun sakar mata ihu suna karin "Mai kusumbi" cikin shekiyanci hadi da tsokana, hadiye kukan ta tayi har ta ɗan yi nisa da rafin kana ta ajiye bokitin ta fashe da kuka mai ban tausayi hadi da taba zuciyar mai sauraron ta, har wani shesheka take saki..



Ji tayi an dafa ta a baya, cikin sauri ta juyo, "Aramani!" Ta kira sunan matashin daya dafa ta tana sakar masa Murmushi, a kokarin ta na boye damuwar ta.


Wanda aka kira da Aramani ya dauki bokitin data ajiye, cikin tausayawa ya ce "hoorain kada ki min murmushin da bai kai zuciyar ki ba, bayan ga tarin damuwa kwance cikin idanun ki, kiyi hakuri da abubuwan dake faruwa watarana komai zai wuce, ki daina barin maganganun wasu yana damun ki, domin ke din ta daban ce, kin fisu komai, ki manta da lalurar ki, You re a special Creator from God, Dan haka cheers ok?"




Hannu ta sa ta kara goge fuskar ta da kyau, bayan Mamin ta, Aramani kadai ne mutum na biyu dake son ta hadi da bata karfin guiwan ta da rasa, take kuma kan rasawa a duk lokacin da aka tozarta ta a kauyen oguma.



sanyin ta ji a ranta, atleast ta dan samu karfin guiwa, cikin sanyin Muryarta tace

"Nagode omaye mie" Aramani"(omaye mie na nufin dan'uwana da Yaren Igala)


Murmushi kawai ya sakar mata, suka fara tafiya yana jan ta da hira hadi da bata labarai masu ban dariya domin ta saki ranta.


Murmushi take yi kasancewar aramani na da barkwanci sosai.



Tun daga nesa hoorain ta hango Taheer dan mai gari da zugan sa a zaune suna kallon duk wata mace data wuce, kuma matukar yana son mace dolenta ta amince masa, kasancewar baban sa mai kudi gashi kuma a Abuja yayi karatu hakan yasa matan kauyen ke rububin sa, wasu ma da gangan suke hucewa sau goma domin ya kyasta.



Gaban Hoorain ya fad'i, tana matukar tsoron Taheer domin sam baya da d'aa bare Magana mai dadi a bakin sa, sannan ta rasa me ta masa, da duk lokacin da ya ganta sai ya jefa mata kallon tsana, bata mantawa ranar da ya ke faɗin

ya tsane ta, ita din mummuna ce, mai tawayar hallita baya kaunar ganin ta, haka ya disga ta cikin tarin jama'a a ranar tayi kuka kamar ranta zai fita, ta rasa me ta tsare masa, haka suka wuce sam bata bari sun hada ido ba, sai dariyar abokan sa data ji cikin tsokana, alamun yayi wata magana data shafe ta, duk hirar da Aramani yake mata sam bata fahimta a yanzu.



Har cikin gida Aramani ya shigar mata da ruwan, suka gaisa da Mami kana yayi musu sallama ya tafi...



⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐



Press up yake cikin sauri-sauri ya had'a uban gumi domin kimanin mintuna talatin ya dauka yana yi, sai daya gaji dan kan sa kana ya mike yana goge fuskar sa zuwa wuyan sa da farin towel dake rataye a wuyan sa, direct toilet ya wuce ya yi wanka, kana ya fito, cikin blue jeans da farar T-shirt ya shirya, gashin sa daya zo masa saman wuya ya cire rubber band daya riƙe gashin, kana ya shafa oil ya taje...

As usually ya kara parking gashin a kasan keyar sa, facing cap ya sanya, ya fashe turaren sa, palm sandal ya saka a kafar sa sannan ya dauki wayar sa ya fito...



Wajen gidan da suka sauka ya tsaye, haka kawai ya ji yana son zuwa kauyen, cikin tafiyar sa ta birgewa ya shiga taka wa yana jin yanda idanun jama'a ke yawo a kan sa, bai damu ba duk da baya son kallo... abinda ya faranta masa rai shine ganin yanda yan kauyen ke ta walwalar su ba kamar ranar da suka zo ba, a ransa ya raye cewa zaman lafiya ya fi komai dadi, haka kuma yana saka al'umma samun cigaba.



*HOORAIN*

A hankali ta fito daga cikin gidan su tsintsiya dauke a hannun ta, share kofar gidan su ta fara yi...

hakan yayi daidai da lokacin da hamdan yazo wucewa, bai san me ya kai idanunsa kan farar kagun ta dake sanye da jigida(waist bead) ba, wanda ita Hoorain bata san cewa rigarta ta ɗan dage ba, saurin dauke idanun sa yayi, ya cigaba da tafiya, zazzak'ar Muryar ta ya ji tamkar busar sarewa... cak ya tsaya da tafiya saboda yanda wakar ke fita daga bakin ta kamar haka...✍️




hoorain mai kusumbi na kudi ne akan dari daya kacal₦100, ainihin kudinsa 300 ne, haka na siyar da shi ga wadanda suka siya a baya, nayi wanna ragin ne saboda fans dina, musamman makarantar littafin Abraham.

2261488155 Rukayya Haruna zenith bank.

Or katin MTN, yan Nijer kuma zasu turo 200cf na Airtel.







Ga masu son shiga hoorain group ga link👇

***



NoorEemaan

***