Hoorain mai kusumbi (the hunch back girl)

13-14

by @nooriman


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓

(The hunch back girl)






_NoorEemaan_✍️📚





Chapter 1️⃣3️⃣⏩1️⃣4️⃣




Mintuna arba'in ya dauke shi shiryawa, kana ya dauki hanyar cikin kauyen oguma. Yana zuwa kofar gidan ya hangeta daga dan nesa da shi tana tafiya da bokitin rike a hannun ta, nan ya fahimci rafi zata je, wani iri ba dadi haka ya ji a ransa. So yake ya kira ta amma ya rasa ta yanda zai fara bude murya..., hakan ya sa cikin zafin nama irin na su na soldiers ya shiga bin ta, taku biyar zuwa shida ya iske ta...





*HOORAIN*


Ji tayi an karbi bokitin hannu ta, a tsorace ta juyi, ganin Hamdan ya sa ta sauke ajiyar zuciya mai sauti kana tayi murmushi.




Hamdan so yake yace mata sorry ya razana ta amma ya kasa.



Cikin sanyi da dadin Muryar ta tace "ina kwana ya Hamdan" ta ji sunan shi ne a lokacin da Ammi ta tambaye sa.




Wani yanayi na musamman yaji a zuciyar sa, kannen sa ya tuno, domin haka suke kiran shi, amma nata dabanne, domin tamkar da wani salo daya kawata sunan ta yi amfanin wurin kiran shi, wanda ya ji ya tsaru sosai a kunnuwan sa.




"Lafiya"



shine abinda yace cikin maganar sa da yafi kama da rada, domin idan baka da kunnen ji bazaka ji abinda yace ba.



Hoorain bata kara magana ba suka cigaba da tafiya, duk wanda suka hadu da shi a hanya su dinga bin su da ido kenan cikin mamaki, wasu har tuntube suke garin kallo, babban mamakin su shine ganin lafiyayyen namiji handsome uwa uba dan gayu a tare da Hoorain mai kusumbi.

ashe duk iya wakan Taheer dan mai gari da suke gani wasa ne, domin Hamdan ya dama ya shanye shi... Hamdan kuwa kara dinke fuskar nan yayi tsaf ganin kallon yayi yawa.




Bayan sun zo rafin Hoorain ta kalle shi, tace "ya hamdan kawo bucket din na debo ruwan"



Wani kallo ya jefa mata, shi ba harara ba gashi nan dai, kasa da tayi da kanta, domin k'wayar idanunsa mai kalar sararin samaniya yana matuƙar tasari a gareta tare da saukar mata da kasala, sam bata jurar kallon cikin su.





Kan wani babban dutse ya nuna mata yace "sit!" Ba musu ta zauna.



Kamar ruwa ya cinye Yammatan dake rafin nan, mutuwar tsaye suka yi ganin Hoorain da Hamdan, hassada k'arara ya bayyana a fuskar su, tsanar Hoorain ya kara cika zuciyar su.



Hamdan kuwa bakin rafin ya nufa, ba tare da ya kalli fuskar kowa ba, kamar kullum macijin 🐍 nan mai gadin ruwa na nan bakin ruwan...kallo daya yayiwa macijin ya dauke kansa, bucket din ya sa cikin ruwan ya diba kana ya nufi wajen da Hoorain ze zauna, alama yayi mata da ido kan su tafi ba musu ta tashi ta bishi, a ranta tana mamakin yau yammatan basu tsokaneta ba... Yau karon farko a kauyen oguma da bata yi kuka ba, sak'amak'on babu wanda ya nemi tsokanar ta.




Sun dan yi nisa da tafiya Hoorain taji an kwala kiran sunan ta.

A tare da suka tsaya, amma shi Hamdan bai juyo ba, murmushi Hoorain ta sakarwa Aramani daya taho hannun sa rike da kayan aikin gona.


Bayan ya karaso suka gaisa cikin yanayin su na shakuwa, sannan ya gaishe da Hamdan, gogan bai amsa ba, sai hannu daya bashi suka yi musabaha, wani dadi Aramani yaji ganin classic handsome guy ya bashi hannu sun gaisa ba kyama.


Kallon Hoorain yayi da yare yace

"waye wanna kyakkyawan?"



Murmushi tayi, cikin yaren ita ma tace "sabon yaya ne" ta fadi hakan domin bata san matsayin daya bata a zuciya ba kar ta zafafa da yawa.



"Gaskiya ya hadu, kuma wallahi kunyi kama fa"



Dan kwabe fuska tayi tace "dan'uwa Aramani haka zamu yi da kai, kai ma kasan ba gaskiya bane"




Dariya Aramani yayi kana ya yi musu sai anjima ya tafi... Kamar kullum taheer da mutanen sa na zaune, gaban Hoorain ya fadi a lokacin data hange su...amma abin mamaki har suka wuce bata ji ko gyaran murya sun yi ba, hakan yayi matuƙar daure mata kai, a yau duk masu tsokanar ta da ci mata fuska da lalurar da take da shi amma yau first in history Babu wanda yace komai, taji sanyi a ranta sosai, yau taji itama mutum ce kamar sauran mutane.


Kasancewar yanzu an saba kan sa tsaye ya nufi cikin gidan bakin sa dauke da sallama, Ya ajiye ruwan kana ya zauna kan matacciyar tabarman su da har ya saba da zaman kan sa yanzu, hakika babu abinda so baya iya mayar da mutum, bare shi da wannan ne farkon shigar sa, ba karamin kamu yayi masa ba.




"Thank you ya Hamdan" Hoorain ta fada.



Lumshe rikitatun idanun sa yayi batare da yace komai ba, yana kewar Ammi yana son jin Muryar ta, gashi garin saurin zuwa ganin Hoorain ya manta da wayar can gidan.



"Where is Mami?" Ya tambaye ta ganin bai ji motsin ta ba.


"Ta fita, amma bazata dade ba" ta karasa tana zama kan tabarman.




"Tell her abinda ke zuciyarka hamdan, for how long zaka cigaba da yin shiru" zuciyar sa ta bashi wannan shawarar.


Numfashi mai dumi ya furzar, cikin confidence din sa yace


"babe"


Da mamaki ta kalle shi jin sunan daya kirata. Hamdan kura mata ido yayi baya ko kyaftawa, saurin yin kasa tayi da idanun ta.




"I love You babe, did you love me?"



Kamar saukar aradu haka taji kalaman sa, shin kunnen ta ne bai ji daidai ba? *LOVE* dama akwai wanda zai so ta da wannan lalurar? ko mai nakasa bata taɓa kawowa zai so ta ba, balle had'add'en guy ajin karshe kamar Hamdan, wasu hawaye suka wanke mata fuska, Muryar ta na k'ak'arwa domin abin ya girmama brain dinta tace


"You love me ya Hamdan?"


Bata kaunar ganin hawayenta ta, domin ya na taba masa zuciya, a hankali ya sa babban dan yatsar sa ya dauke hawayen fuskar ta, cikin husky voice din sa yace "shhhh! Yeah i do, i Love You so much, i love You for no reason"



Wani sabon kuka ta rushe da shi, ta rasa wani yanayi take ciki, but all she knows this tayi farinciki da duk abinda yace, wacece ita da zata ki shi? shine mutum na farko a duniya ya ta6a furta mata kalmar so ba tare da ya damu ko duba lalurarta na kusumbi dake kara girma a kowacce rana ba....lallai wannan shine tsaftataciyyar soyayya da samun irin sa ke wuya a wanna zamanin.




Cikin muryar ta da bai dawo daidai ba tace "ya Hamdan....ina... ina...son ka nima" ta karasa tana rufe fuskar ta hadi da fashe masa da sabon kuka mai ratsa zuciya...





*MAMI*


Duk maganar su ta ji, domin tsaye take a soron gidan zata shigo ta ji abinda su ka ce. Hawayen idanun ta ta share, ta yi farinciki sosai wa tilon yarta, tabbas alamun Nasara ne wanna, yau taji abin farin ciki Wanda rabon da ta ji irin sa tun mahaifin Hoorain ya bar su, fatan alkhairi ta yi musu a ranta, maimakon shiga gidan da zata yi, sai ta juya waje.




*HOORAIN*


Ta ɗauki Mintuna tana kuka a ranta take furta "ya rabb! What a blessed day in my life"

Hamdan da kukan ta ke masa zafi a kirji ya kalle ta da idan sa da suka dan Sanja launin kadan Yace


"did i say anything wrong?"


"Nooo ya Hamdan, kukan farinciki nake" ta karasa tana share idanun ta, sosai idanun ta suka kumbura abin ka da farar mace.


"Stop those tears ok" ya fada mata calmly.



Jinjina masa kai tayi tana Murmushi mai tsayawa a rai.




Sai ta dan kalle shi da kumburarun idanunta tace "kayi hakuri ya Hamdan, na manta ban Maka ruwa ba" ta karasa tana ƙoƙarin mikewa.



"No Thanks" yace mata.


komawa tayi ta zauna, shi kam bazai iya shan ruwan garin nan ba, bare ya ga maciji a rafin nan, domin har yayi imaging cewa macijin na yawo cikin ruwan.



*BAYAN WASU MINTUNA*


Tsaye ya mike yana soke hannun sa cikin aljihun wandon sa, "i will see you tomorrow babe, i love You bye" yace yana barin gidan, ba tare da ya tsaya ba, wanda hakan yasa Hoorain bata samu nasarar amsa masa ba har ya fice...murmushi mai sauti ta saki sai ta sa hannu ta rufe fuskar ta cikin jin kunya, duk da ya Hamdan baya magana, amma yana burge ta, infact komai na shi na burge ta kuma tana son shi.

Bata wani jima da zama ita kadai ba Mami ta shigo, cikin farinciki tayi wa Mami sannu da zuwa, cike da kulawa Mami ta amsa ba tare da ta nuna ta ji maganar su ta dazu ba, amma kasan ranta farinciki ne fal cikin sa...




************



Zaune yake kan katifar dakin, wayar sa dake hannun sa ya shiga jujuyawa kana ya danna power button wayar ta kawo haske domin a kashe take.


Messages masu yawa ya fara gani a inbox din shi amma bai duba ba, manjahar WhatsApp ya shiga Bayan ya kunna datar sa, massages masu yawa ne suka dinga shigowa....


Ajiye wayar yayi for like two minutes har massages din suka gama loading... Sakon abokon sa Corporal Imran ya shiga, domin shi ne a farko, yaga ya rubuta masa




_hey dude! Kwana biyu shiru hope You re fine_?





Dubawa Hamdan yayi ya ga yana online, hakan yasa ya fara yi masa reply kamar haka




_my fine Imran, what's up_?



Typing Imran ya fara masa kamar haka...



_dude wai bazaka dawo bane? ana ta neman ka anan barrack, Please come back, wai me kake a kogi ne?_




_you won't understand imran_


shine amsar da hamdan ya bashi.




_then make me understand_

Imran ya fada.




Shiru Hamdan yayi for some minutes har Imran ya fidda rai da jin reply din sa sannan ya ga yace



_i love her Imran_



"What!?"

Imran yace a zabure yana mikewa tsaye, shin mafarki yake, CAPTAIN HAMDAN MALEEK BUMSA ne ya furta yana son wata, duk zurfi ciki hadi da miskilancin sa?

Murmushi Imran keyi hannunsa na rawa wurin rubuta masa reply...


_wait! Are You sure is person iam speaking with is Captain Hamdan?_


ya karasa yana saka emojin tsokana (😜)



Share sa hamdan yayi ya mayar da idanun sa ya rufe.



Karan sakonin yaji sun dame shi, sai ya sake buɗe wayar...



_Am sorry dude! Wasa nake, Please gayamin who's the lucky girl data samu gagarumin nasarar sace zuciyar da yammata bila adadin ke rububin saman sa_?



Abinda Imran yace kenan cikin zallan zumudi, dama gashi mayen love ne .




_*The hunch back girl*_ hamdan ya bashi amsa.




_what! Like seriously You mean tana da kusumbi a baya_? Imran ya tambaya da zallan mamaki yana saka emojin dariya.





_yeah! You think she's no body on the outside? Well I can assure you that on the inside... She's the whole fucking queen👑 that rules the kingdom of my heart_




Daga haka ya sauka a online gabadaya hadi da kashe mobile data din sa, yaso kiran Ammi amma baya so yaji muryar ta da damuwa a dalilin rashin dawowar sa.


duk son da yake wa aikin sa na soja a yanzu bai damu ko da ya daina saka kaki ba, ba kuma zai bar kauyen nan idan ba tare da Hoorain ba, bai san yadda zai kasance ba, amma bazai iya tafiya ya bar ta ba.




Daga bangaren Imran kuwa wani abu ya ji game da kalaman hamdan na karshe, sosai kalaman suka taba masa zuciya, hakika so yayi wa abokin sa mummunan kamu, wanda zallan soyayya ne da babu algus a Cikin ta, kamar karamin yaro ya dinga tsalle yace


"yes!" Kana ya dunkule hannu irin abin ya mai sugar, Sannan ya kara da cewa "Ina tare da kai dude, indeed this is true love"




*NASARAWA GRA SULTAN ROAD*


5:09pm

Omar, Anas da kabeer ne suka dawo daga kamfanin da mahaifinsu ya bari kamar yadda suka saba, sallama dauke a bakin su suka shigo part ɗin ammi, a sanyayye Ammi dake zaune kan kujera ta amsa tana ƙoƙarin boye damuwar fuskar ta bayan ta amsa sallamar su...



Duk kusa da ita suka zauna, sai ya zamana tana tsakiyar su.


Anas yace "Ammi You look cold, har yanzu wayar ya Hamdan bai shiga bako?"


Ajiyar zuciya ta sauke tace "i just hope and pray yana lafiya Anas, yayanku na da zurfin ciki, na san akwai wani abu a kasa definitely"




"Kiyi hakuri Ammi in Sha Allah yana lafiya, kin san yaron ki jarumi ne, he can take care of his self". Cewar kabeer



"i know, Amma kun san baya son cin abinci, kila yana can yana barin kan sa da yunwa" ta fada cikin karyewar zuciya.




"Ammi karki damu zai ci da yawa saboda ke, You know yaya na kaunar farinciki ki" Omar ya fada domin kwantar wa Mata da hankali



"Allah yasa" Shine abinda

Ammi tace tana dan murmushi, ta ɗan ji sanyi a ranta sak'amak'on abinda su Hamdan suka ce.



Hira suka dinga jan ta da shi har Ayiyah ta fito daga dakin ta zo aka cigaba hira, tana musu halin nata ana dariya.





*_Thanks to everyone for the warm prayers, Ina muku fatan alkhairi tare da fatan gamawa da duniya lafiya, fans dina dana sani da wanda ban sani ba alkhairi Allah ya kai mu a duk inda kuke, masu tayani sharing novels nawa jazakallahu khair Habibte's_* 🙏🥰






NoorEemaan

***




Thank you for reading my story

🍇#hoorain the hunch back girl🍓




2:48pm

Tuesday 24/5/2022