Hoorain mai kusumbi (the hunch back girl)

15-16

by @nooriman


🍇🍇HOORAIN MAI KUSUMBI🍓🍓

(The hunch back girl






#sacrifice

#hotlove

#heart touching

#hatred

#betrayal





_written by NoorEemaan_📚✍️




Chapter 1️⃣5️⃣⏩1️⃣6️⃣




Safiyar alhamsin ne, jama'ar kauyen Oguma sai fitowa suke sak'amak'on jin Muryar dan baiwa Ashimi, domin su san matuƙar ya fito yana magana, toh fa yayi mafarki ne, kowa fargaban sa Kada a kira daya daga cikin sunan ahalin sa.




*TAKAITACCEN TARIHIN DAN BAIWA ASHIMI*


Asalin sa dan kauyen oguma ne, ya samo inkinyan sunan dan baiwa ne sakamakon idan yayi mafarki yana kasancewa gaskiya, tarin baiwa da ilimin sa ya sa ake ganin shi kamar wani sha takwas, wanda azahiri ba haka bane, tarin baiwa da ilimi ne ya sashi kasance hakan, farko idan yana sanar yayi mafarki, Zai kuma ce ayi sadaka mutane domin Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi, sai ana daukar abin wasa, har ya zama abin dariya ga yan kauyen.



Ranar da yayi wata mafarki basu ɗauke shi da Muhammanci ba, har abinda ba a so ya hafku, domin exactly munanan mafarkin da yayi ya faru a zahiri.


hakan yasa tun daga wannan ranar idan Allah ya sa yayi mafarkin mutum mara kyau, sai yace ayi sadaka, ko kuma yace a dage da tashi sallan dare, in Sha Allah sai mutum ya ga komai lafiya sakamakon addu'a da sadaka da ya yi, hakan yasa da yayi mafarki ya bayyana suna daukar shi da gaske...





*BACK TO STORY*



**********


Sai daya zo daidai kofar gidan su Hoorain ya ja ya tsaya, kana yace "Hoorain Yusuf a yau Allah ya bani ikon ganin maganin lurar ki a mafarki"




ya maimaita hakan sau uku abinka da yan kauye gaba-daya sun zagaye shi, ana ta kallon sa.




Ta bangaren Hoorain kuwa zaune suke ita da Hamdan da kullum sai yazo ya ganta yake samun nutsuwar zuciya.



Mami tana daki a zaune, yayinda Hamdan ke bare mata cashew nut da Aramani ya kawo mata soyayye tana ci, kawai kallon dan tsut din bakin ta yake with much admiring on his face, komai nata na burge shi, kamar ya hadiye ta ɗan so amma sam ba za ka taba gane hakan ta fuskar shi ba.




A lokacin da suka ji Ashimi dan baiwa ya kira sunan Hoorain gaban Mami da ita Hoorain yayi mummunan fad'uwa, cikin rashin fahimta Hamdan ke kallon hanyar soro ta inda yake hango kafafun mutane, gashi hayaniyar su ta cika wajen...




Mami ce ta fito daga daki, sannan ta mikawa Hoorain hannu domin taimaka mata wurin tashi, cikin mugun sanyi da jikin ta yayi ta kama hannu Mami ta mike...


cikin tafiyarta ta masu kusumbi ta bi bayan Mami, Hamdan ma mikewa yayi ya rufa musu baya, nan fa idanun yan k'auyen ya bisu Mami da suka fito zuuuuuuuuu




Cak Ashimi ya sayar da idanun sa masu kwarjini sosai ga fuskar Hoorain, kasa tayi da kanta domin idanun sa tsoro suke bata sakamakon tarin baiwa daya cika cikin su.




"A yau Allah ya nuna min ke Hoorain a mafarki"


Sai ya kalli Mami da idanun ta ke dauke da hawaye yace


"wannan kusumbi ba da shi kika haife ta ba, tana da Shekara daya a duniya aljanin daya yi sha'awar surar ta ya sanya mata sakamakon wata rana kin kwantar da ita tana bacci babu wando a jikin ta, kina band'aki, shi kuma ya bayyana gareta, surar Hoorain ya burge shi kana ya bashi sha'awa duk da karama ce, hakan yasa ya mika hannunsa daidai bayanta wani koren haske ya bayyana ya shiga ratsa bayanta, bayan wasu Mintuna ya bace bat.


Manufar sa ta yin hakan shine saboda kada wani da namiji ya aure ta ko ya so ta, shi kadai ne zai mallake ta. Kamar wasa a hankali kusumbi ya fara tsiro wa har yayi wanna girman, a ko wacce rana wannan Aljani mai suna mushkaf sai ya zo ya kara mata girman sa, shiyasa kullum kusumbin ke cigaba da mamaye bayan ta, idan kuma aka cigaba a haka watarana zai rinjaye ta ta yanda ko tashi zai gagare ta..."





Salati, ihu, hadi da surutai kala-kala ke tashi a wajen, Mami hawaye take abin tausayi, tabbas Ashimi dan baiwa bai yi karya ba, ba haka ta haife yar ta ba, nadama sosai ya rufe ta, domin bata manta lokacin da mahaifin Hoorain ke yawan cewa ta daina barin Hoorain ba kaya, ashe ita ta ja wa yarta wanna lalurar sai ta rushe da kuka hadi da saka matacciyar hijab dinta da shi kadai ta mallaka ta toshe bakin ta dashi ....



Muryar ASHIMI dan baiwa daya cigaba da tashi ya sa wurin ya dawo so slient kamar ba hallitu a wajen duk suka kasa kunne suna sauraron sa



"Alhamdulillah! Allah ya nuna min maganin, wanda maganin warakar kusumbi Hoorain yana world of dead (duniyar mutuwa)"




Salati aka kara saki, wasu har da dora hannu a kai.


Ashimi dan baiwa ya cigaba da cewa "world of dead na da matuƙar hatsari fiye da tunanin ku, mugayen Aljanu, mayu masu shawagi da rana hadi da wasu hallitu marasa kyauwu ne suka cika duniyar mutuwa, duk mun san cewa babu wanda ya taɓa zuwa ko yin hanyar duniyar mutuwa. Toh anan maganin warkar da kusumbin Hoorain yake cikin wata kwarya a karkashin bishiyar kuka..."



Shiru ya dan yi yana bin mutane da kallo kana ya cigaba da cewa "zaratan samari bakwai ne zasu yi wanna tafiyar zuwa duniyar mutuwa domin dauko kwaryan nan, ba karya zaku hadu da miyagun hallitu da zasu yaudare ku, domin da siffa mai kyau zasu zo muku amma kada ku yarda da su daidai da ƙwayar zarrah, ku karfafa zuciyar ku, ku rike addu'a, ga wadanda suka shirya wannan tafiya zan baku wasu addu'o'i domin kare kanku, Hoorain na da kyakkyawar zuciya, ga duk wanda ya ga zai taimaka mata Allah ya biya shi, jibi ne tafiyar, na barku cikin aminci" yana kaiwa nan ya juya cikin tafiyar sa ta sauri_sauri ya bar wajen...




*HOORAIN*

Kamar wacce aka datsa haka ta cigaba da tsayawa idanunta kurrr kan dan baiwa Ashimi har ya tafi ta kasa kyafta idanun ta a wajen da ya tsaya, tsananin shock yasa ta kasa motsi, sai ruwan hawaye dake bulbulowa daga idanunta kamar an kunna famfo...




*HAMDAN*

Kallo daya zaka masa ka hango tsantsar damuwa daga cikin blue eyes dinsa daya Sanja launi, gaba-daya ransa a bace yake, duk da kasancewa mushkaf ba a jinsin bil'adama yake amma wani mugun kishi ke caccak'ar zuciyar sa game da shi, tausayin babe din sa ya kara yawaita a zuciyar sa.




Mutane ne suka fara watsewa kowa da abinda yake cewa, cikin sauri Hoorain ta fada cikin gidan tana kara sakin kuka mai tsuma zuciya, Mami ta biyo bayanta, kana Hamdan ya mara musu baya... hannunsu zube cikin aljihun wandon sa ya kafe ta da idanun sa masu ɗauke da tausayi, tsananin so, zallan kishi, hadi da bacin rai amma bai ce komai ba.




Abin tausayi haka Mami ta zube gaban Hoorain hadi da dafa ta, cikin sauri ta dago, ganin Mami ce yasa ta fada jikin ta hadi da kiran "Mami mie" cikin kwarewar zuciya.




Hugging dinta back Mami tayi tana rarrashin ta, kana tace "Hoorain haka Allah ya ƙaddara Maki, amma har da laifina ciki domin tabbas kina yar karama ban fiye son saka Miki kaya ba, ki yafe....."




"A'a A'a Mami, wallahi bazaki taba Zama mai laifi a gareni ba, ke ce duniya ta, ke kika kila da Ni har na kai iyanzu, Mami kada ki ci komai dan Allah, ina son ki Mami mie"




Kuka Mami ta sa, kauna da tausayin tilon yarta na kara mamaye zuciyar ta.


Hamdan kuwa bai taba ganin abinda ya ta6a zuciyar sa hadi da bashi tausayi kamar Hoorain ba, karamar innocent girl da take cikin K'addarar rayuwa.




Kasa jurar kallonsu yayi ya fita waje ya samu wani benchi na karfe a dan nesa da gidan su Hoorain ya zauna hadi da nausa hannunsa cikin sumar kansa yana mai rufe idanun sa.




****************



Da misalin K'arfe biyar din yamma, sai ga Aramani tare da wasu samari biyar sun zo gidan su Hoorain.


Abin mamaki suka sanar cewa zasu je duniyar mutuwa domin dauko maganin nan da zai warkar da kusumbin ta, sun kuma sanar da su cewa zasu Yi wannan sadaukarwan domin son fisabilillah da suke wa Hoorain, hakika ta sha gwagwarmayar rayuwa da tarin kalubale, ya kamata zuwa yanzu ta ji dadi ko yaya ne. Suka kara da cewa suna saka ran in Sha Allah su samu cikon na Bakwai din zuwa gobe tunda jibi ne tafiyar.




Mami tsabagen al'ajabi yasa ta kasa magana. Hoorain kuwa kuka ta samu musu tana cewa "Aramani, Danjuma, salihu, yakubu, oshimana, Abu, dan Allah karku je, bana so ku mutu, karku jefa rayuwar ku cikin hadari saboda Ni, ina farinciki da godewa Allah a yanda nake, dan Allah bazan iya jurar rasa ku baaaaaa" ta ja karshen maganar sakamakon mugun kukan daya kufce mata.




"Tafiya babu fashi Hoorain yar'uwar mu, matukar kana son mutum zaka iya sadaukarwa mai girma domin shi, ki mana addu'a kin ji ko? In Sha Allah zaki mike kina tafiya kan kafafunki kamar kowa"



samarin suka hada baki wurin fadin haka, daga nan suka fice a gidan.




****



A ranar kam har dare Hoorain idanun ta jike suke da ruwan hawaye, ta kasa daina kukan, Mami kallon ta kawai take cikin tausayawa domin babu wani karfin guiwa a tare da ita, jikin ta gaba-daya ya mutu, a ranar sun manta sunan abinda ake cewa *YUNWA* saboda tsananin damuwa daya cika zuciyar su, ko lokacin da Hamdan ya tafi ma basu sani ba.






Ta bangaren yan kauyen Oguma kuwa, ko wani gida da ko wani majalisa hirar Hoorain ke tashi kowa na fadin albarkacin bakin sa.



*WASHEGARI*



*HAMDAN*


Tun ranar da suka gama chat da Imran bai kara kunna wayar ba sai yanzu, kallon percentage din wayar yayi ga sauran masa 10% a hakan ma ya ga kokarin ta, domin iPhone baya mugun rikon chargi, gashi tunda yazo kogi bai yi mata chargi ba.




Contact list ya shiga, inda ya tsayar da idanun sa kan number'n Ammi, wata karfafar ajiyar zuciya ya sauke, kana ya danna number'n ta hadi da kara wayar a kunnen sa yan sauraron ringing din da yake...








*Mun fara shigowa cikin labarin, i swear basan yadda zan kwakwanta zafin book din nan ba. Abubuwan ciki na daban ne, just continuing following my pen, sahihiyyar kauna Noor ke wa masoyan ta na fili dana boye*



*Naso kara yawan typing amma banda a enough charge*



*_guys Meye ra'ayinku kan page din yau_?*






*Two free page left karku ji dif*🤸💃





Wanna littafin paid book ne akan dari daya, 2261488155

Rukayya Haruna zenith bank, ko katin MTN na dari, yan Nijer kuma zasu turo katin Airtel na 200cf. Nayi wanna ragin ne saboda fans dina musamman makarantar Abraham, ina godiya sosai da comments, ina kuma godiya da yanda kuke so books dina.




NoorEemaan

***




Thank you for reading my story

🍇#Hoorain the hunch back girl🍓




Share

Share

share


Please🙏




9:07

26/5 2022