5-6
by @nooriman
๐๐ABRAHAM๐๐
WATTPAD
@NoorEemaan
***
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
Chapter 5-6
Sai da anty Sarah ta fito babban titi kana hankalin ta ya kwanta, ba tare da ta bata lokaci ba ta nufi tasha domin hawa mota da zai sadata da asalin kauyan su, Sam bata damu yamma tayi ba, haka zalika bata damu ko jin tsoron tafiyar dare ba, duk da yanda ta kai ga tsanar zaman kauye amma shine waje da zai sa hankalinta ya kwanta, domin bata son abinda zai sake hada ta da madam Gloria, ta kuma sani cewa har abada zasu da sauran kwannciyar hankali, domin kashe rai ba abun wasa bane.
Fatan ta daya mutanen nan su rike yaran amana, kuma in sha Allah zata yi kokarin sada Abraham da y'ay'ansa a lokacin daya dace matuk'ar tana raye, hawayen nadama ne ya saukar mata tuno cewa sune silan mutuwar Nonye, yanzu meye ribar su?
*GOMBE*
Baffa ne ya fito daga daki inna na biye dashi, "indo! Indon Baffa!!" baffan ya kira ta yana lekan Dan karamin dakin ta
"na'am baffana" ta fada cikin murya kasa-kasa wanda ke nuni da bacci ke shirin daukar ta.
Fitowar ta yayi daidai da dariyar da Baffa ya saki, kana cikin tarin kaunar tilon 'yarsa yace" shalelena ba dai bacci kike shirin yi ba ga magriba ta gabato"
"wallahi baffana bacci nake ji sosai" tafada a shagwabe tana dago lumsasun fararren idanunta da ya dan rine kadan sak'amak'on baccin da take ji.
"kinga ki danyi hakuri kiyi sallah idan yaso sai ki kwanta, zo mu zauna a tabarma kafin ayi kiran"
"toh Baffa bari nayi fitsari Ina zuwa" tafada tana daukar buta domin shiga bandakin.
Inna dake garken dabobbi tana tasar nonon shanu ta saki murmushi hadi da girgiza kai, domin sosai indo da Baffa ke kaunar juna wani zubin 'yar kallo take zama...
Kafar hagu indo ta saka a bandakin bakinta dauke da addu'ar shiga bandaki, sai dai addu'ar makalewa yayi sak'amak'on abinda tayi tozali dashi a kasan bandakin, shin mafarki take ko gaske? Ko ko shin aljanu ke kokarin bud'e mata ido?
Sanin cewa bata da mai bata amsa ya sanya ta kwala ihu daya yi matukar gigita su Baffa, hankali tashe suke nufi bandakin dan ganin abinda ke faruwa, ya kuma saka Indon su ihu...
*IMO STATE *
Zaune madam Gloria take sanye da bakaken kaya kamar yadda yake al'adarsu idan anyi musu rasuwa, idanunta sunyi luhuยฒ sakamakon kukan karyan da take yi ba dare ba rana matukar a idon jama'a ne, sosai mutane ke tausaya mata, domin har tafi iyayen Nonye nuna mutuwar ta girgiza ta...
Wata yar'uwar su ce ta kalli madam Gloria hadi da cewa "Gloria kiyi hakuri hakan nan, sannan ya kamata zuwa yanzu ki kira ABRAHAM domin ya sani, saboda babu amfanin cigaba da boye masa"
Wani kuka madam Gloria ta saki har da majina tace "tayaya zanyi in sanar da dana wanna mummunan labarin? Banason hankalin shi ya tashi" ta karasa cikin kuka tana bubbuga kafafunta a kasa, riketa duk sukayi suna bata hakuri hadi da karfafa mata guiwan ta kira shi kan cewa ya dawo gida amma kada ta sanar dashi mutuwar Nonye sai idan ya dawo kasar.
Tana Jan majina ta fara dialing number'n shi kana ta daidaita muryar ta...
*KOREA*
Kwance yake gefen beach a wani had'add'en kujera sanye da boxer, sai sunglass dake manne a idanun sa, haka zalika sauran mazan sanye suke da boxer musamman masu shiga ruwan yayinda matan ke sanye da bikini wanda daga kirjinsu sai al'auransu ya rufe. Kyakyawane, chocolate color mai haske, yana da kirar nan da akewa lakabi da *giant* sai had'add'en six-packs dinsa idaunsa bai fiye girma ba, amma suna da matukar jan hankali, hancinsa dogo ne mai dan kauri, yana madaidaicin lips daya kara fuskar tasa kyau ainun, akwai wani karamin dankunne a kunnensa yayinda ya rataya cross + a wuyansa wanda hakan ke nuni da cewa shi din mabiyin addinin chirista(Christian) ne.
Burinsa yanzu ya gama abinda ya kawo shi kasar nan ya tafi domin yayi kewar gida sosai, kasancewar agajiye yake dawowa ko damar Kiran nonye da mummy baya yi, dan karamin tsaki yaja wanda sautinsa bai fito ba sai labb'an bakin sa ne suka motsa.
Haka kawai yake jin ranshi ba dadi, latsa wayarsa yake kokarin yi Kiran madam Gloria ya shigo, yaji dadi sai dai Sam babu alamar hakan a fuskar sa, domin shi mutum ne miskili da zurfin ciki wanda kai tsaye mutum bazai iya karantar abinda ke fuskar sa ba.
Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunnensa "good evening mummy, I was trying to call you guys now" ya fada da turanci.
Daga bangaren madam Gloria kuwa sosai ta daidaita muryar ta kana tace " yes son! Ya kamata ka zo kawo gida hakan gobe, idan yaso ka koma daga baya" ta fada masa da yaren igbo
"mummy is everything alright? How's Nonye and my baby doing?" kit madam Gloria ta kashe wayar ta, domin batasan sauran amsar bashi ba.
Haka nan yake Jin cewa there's something wrong Dan haka babu bata lokaci ya shirya kana yayi booking flight Inda yaci sa a samun jirgin da zai je Nigeria, amma sai karfen taran dare.
Dan haka gida ya dawo ya shirya cikin wasu had'add'un kaya da ganinsu kadai zai tabbatar maka da tsadar su, wayoyin sa hadi da system dinsa kadai ya dauka kana ya tura sakon Gmail ga company daya zo takanas domin su cewa akwai dalili mai karfi daya sanyashi komawa kasar sa, amma zai dawo as soon as possible, daga nan filin jirgi ya koma domin zuwa lokacin takwas ta wuce, ba kuma yaso yayi missing flight.
*NIGERIA*
IMO STATE
Bayan ya sauka a airport ya kira lambar driver gidan hadi da sanar dashi yana Airport, babu Jimawa yazo amma wanna karon driver'n bai yi masa surutunsa irin yanda ya saba ba, hakan ya dan bawa Abraham mamaki domin yasan driver akwai surutu sosai, amma Sam bai nuna ba
Tafiyar mintuna ashirin ya sada su da Abraham mansion, sauka yayi, bai jira driver ya Bude masa ba, direct ya shige general parlour sai dai abinda ya gani ya sanya gabansa fad'uwa sosai domin a iya saninsa a kuma al'adar su ta igbo sai idan mutum ya mutu ake sanya bakakken kaya irin haka, toh me yasa duk suka sanya bakin kaya? Waye ya mutu? Yayi duka tambayar a ransa yana bin fuskar kowa da kallo
Da sauri madam Gloria ta taso, ta isa gareshi kana ta fashe da kuka sosai tace....
_A GASKIYA COMMENT DINKU YANA KADAN HAKAN KE SANI RASA KARFIN GUIWAN TYPING DAN ALLAH IDAN KUN KARA YAWAN COMMENT ZAN DINGA YI MUKU KODA BAYAN KWANA DAYA NE, IF POSSIBLE KULLUM, DOMIN INA DA AIKI SOSAI NAKE DAUREWA NAYI MUKU DAN HAKA KUMA KU FARANTA MIN DA COMMENT DINKU_
Noor๐ฆ
26/12/2021
9:41am
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851