Abraham

21-22

by @nooriman


๐Ÿ‡๐Ÿ‡ABRAHAM ๐Ÿ“๐Ÿ“



*first edition*




*WATTPAD*

@NoorEemaan




*please Don't forget to vote my story and also follow me on WATTPAD @NoorEemaan*

love you all guys.





***


Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din






Chapter 21-22


(Not edited)




Lumshe sexy lulu eyes dinta tayi sak'amak'on sanyayyar kamashin room freshener daya daki hancinta, kana a hankali ta ware idanunta ta sauke su kan kayataccen falon daya gaji da haduwa, sai dai shiru ba motsin kowa sai k'aran Ac.





Wata kofa dake kallon gabas ta sauke idanunta a kai, a hankali ta fara takawa domin isa ga kofar, a gefe daya kuwa gabanta na tsananta fad'uwa...

Hannu ta dora kan handle din kofar da niyyar bud'ewa, sai kuma tayi saurin dauke hannun ta, a hankali ta fara knocking... Shiru ba amsa, sannan ba motsin kowa har na tsawon mintuna biyar, gajiya ta fara yi da tsayuwa kasancewar ta mutum mara jurar tsayawa, shahada tayi ta bud'e kofar a hankali, kana ta shiga....





Ya subhanallah! Ta fada tana runtse idanunta da karfi sakamakon hangoshi da ta yi kwance kasan tiles babu riga a jikin sa sai dogon wandon jeans kirar company'n gucci, wanda hakan ya bawa manyan six packs din sa bayyana hadi da karfaffan hayyensa daya yi mata shi dasu.





A kafatanin rayuwar ta bata taba ganin da namiji haka ba, duba da irin gidan da ta fito, ta dauki tsawon mintuna bakwai a haka, kana kamar mai tsoron ganin wani mugun abu ta shiga Bude idanunta a hankali ta sauke kan k'yak'yawar fuskar sa dake bacci a tunanin ta, wanna karon gabanta ya fi d'azu fad'uwa saboda ganin kamanin Ammar dinta da Abraham, ba tare da kuma ta san maganar ta ta fito fili ba tace "Ammarrr" cikin sautin amo dake bayyana zallan mamaki,

Ji tayi idan ta cigaba da tsayuwa a dakin komai zai faru, domin k'wak'walwarta ya gaza dauk'an abinda take gani, musamman kamanin su daya firgita ta, dan dai shi babba ne da ta ce tabbas Ammar din ta ne, cikin sassarfa ta juya domin barin dakin kamar a sama taji husky voice dinsa yace "hey! what did you want?" tilas ta tsaya cak! Gashi ya sake rudata da turanci sa da bata fahimci koda kalma daya ba... Abraham kuwa duk da yana cikin bacci, amma shigowar ta dakin ya sauya bugun zuciyar sa, wanda ya tilas ta masa farkawa daga dan baccin daya dauke sa, tabbas murya yarinyar daya ji a cikin adaidaita sahu ce, ya kuma sake tabbatar da hakan ta dalilin bugun zuciyar sa da ta sauya, wanda akan ta ne ya fara Jin hakan, mamaki yake kan meya kawo yarinyar cikin gidan su har dakinsa.





Jikin ta na bari, cikin rawar murya tace "ehm... Is your, is na mahaifiyar ka ta ce kazo kasan bene" ta fada cikin duburbucewa idanunta taf da k'walla...




Yamutsa fuska yayi domin ko kalma daya bai fahimta daga abinda tace ba, a hankali ya bud'e idanunsa da suka dan rine saboda jimawa da suka yi a rufe ya sauke su a kwanta, sai dai bayan ta kadai yake hangowa, ita kuwa jin bai sake magana ba yasa ta fita da gudu, ta nufi dakinta dake da dan nisa da nashi duk da saman bene ne.





ABRAHAM kuwa da kallo yabi bayanta, kana ya tabe bakin sa hadi da mikewa tsaye, toilet ya nufa domin yin wanka, shower ya kunna inda ruwan ya shiga dukan kansa zuwa jikinsa, a hankali muryata ya amsa kuwa a kunne sa "Ammarrr" ya maimaita kalmar can kasan makoshi, duk da bai san ma'anar sa ba, kawar da tunanin yayi ya cigaba da wankan sa inda mintuna ashirin ya dauka kana ya fito daure da farin towel.





Tsad'add'en lotion din sa ya shafa, kana yayi oiling kansa hadi da tajewa, gaban wardrobe din sa ya nufa, inda wayar sa ta fara ringing... Dubawa yayi ya ga MUM ce.


Amsawa yayi hadi da karawa a kunne sa,,

"Good morning Mummy"


"morning my son, I sent the house-maid to tell you breakfast is ready and.........."


"am coming mum" ya fada yana katse Kiran ba tare da ya bari ta karasa maganar ta ba, sai yanzu da mummy ta fada ya san dalilin shigowar Yarinyar nan dakin shi, wardrobe din ya bude ya fito da wani crazy Jean trouser white, sai bakin riga mai botira hadi da dogon hannu, cikin mintuna biyar ya shirya cikin su, gaban inda tarin takalman sa suke ya nufa ya dauki wani black palm sandals na company dolce and gabbana ya sanya, agogon zallan sliver ya manna a hannun sa, ba karamin kyau mai tsayawa a rai yayi ba , Bud'e kofar yayi ya sauko kasa...





Aysha da ta kasa kunne, jin motsin ya fito ya sanya ta fitowa da sauri, duk da faduwar gaba da Tsoron da take ji amma dole ta gyara masa dakin tunda aikin ta ne, baya ga haka bata ma so abinda zai hada ta da madam Gloria, dakin sa ta koma ta fara gyara falon da sauriยฒ inda ba wani datti yayi sosai ba, bedroom dinshi ta nufa shima ta gyara kana ta yi mopping a ranta tana mamakin yanda ya iya kwanciya kan uban sanyin da tiles din ke da shi, domin ita kafar ta kadai dake taka shi yanzu ya sa ta jin Sanyi.




Bayan ta gama, ta wanke toilet ta fito, wani kofa ta gani by the left, Bude kofar tayi ta ga kitchen ne, a gyare yake babu wani datti, wani kofa ta sake gani ta cikin kitchen din ta bi, take ta bayyana a gyming room dinshi wanda ke gyare tsaf, "Dama makeri ne shi" ta fada tana kallon karafunan da abubuwan motsa jikinsa, wanda ita bata San amfanin su ba.






Sosai ta shagala ta kallon dakin motsa jikin, can ta tuno cewa zai iya shigowa yasa ta fita cikin sauri, dakinta ta koma tana sauke ajiyar zuciya, yayin da har yanzu tana mamakin wannan kammanin, daga kashe dai ta basar, tasa a ranta cewa kawai kama ce....





ABRAHAM kuwa tea kawai ya sha, dama shi ba ma'abocin cin abinci bane sosai, madam Gloria tayi-tayi yaki ci, dole ta hakura, fita yayi zuwa unguwar rimi, domin so yake ya je su yi magana da wani attajiri mai harkan filaye wanda ya ga ya dora wani fili mai girman gaske a Instagram din shi wanda na siyarwa ne, wanda tun yana dubai yaga tallan, luckily kuma yaga kaduna state ne , so yake ya siya domin ya gina company a nan kaduna, wanda hakan zai yi keeping dinsa busy...






Babu jimawa da fitarsa professional chef din da zata fara koyawa indo girki-girki tazo mai suna miss Zaynab Akindele yar jahar ogun ce, ba bata lokaci madam Gloria tayi Kiran Indo ta sauko suka shiga kitchen....




____________________





*Gombe State*


Bangaren su innah kuwa sosai suke fama da tsananin kewar Aysha indo, bare ma su Anwar, ranar farkon da basu kwana da Ammuh din su ba, cikin dare Inna ta ga ta kanta, domin zazzabi ne ya rufe su, babu abinda suke kira sai Ammuh! Ammuh! Suna kuka, innah bata taba sanin cewa haka suke da Wayo ba, domin ta yi iya yinta sun ki hakura...





Washegari da asuba zazzabin ya sauka, suka fara dan wasan su, amma abu kadan sun kira sunan Indo ko su je dakinta, lallaba su innah ta dinga yi tana musu Wayo da haka ta samu dan sauki.





โ˜…โ˜…โ˜…








*KADUNA STATE*


Kiamanin sati daya Kenan da miss Zaynab Akindele ta fara koyawa Indo girki, kuma ba laifi tana fahimta sosai wanda hakan ke sa miss zaynab kara himma wurin koya mata, domin ita macece mai son ta koyawa mutum abu ya dauka da wuri, ta bangaren Aysha kuwa tana jin nishadi a duk lokacin da ake koya mata girkin, karin dadi kuma miss Zaynab na jin hausa sosai duk da kasancewar ta yare, wanda hakan ke sa Indo saurin fahimta.





Ta bangaren Abraham kuwa yayi nasaran siyan filin nan, inda babu bata lokaci aka fara gini, abinka da kudi, sosai ya zama busy baya samun zama...





Ta bangaren madam Gloria kuwa tana nan tana shirya yanda zata kashe Abraham, sai dai kwatsam wani tunani ya zo ranta yasa ta dan dakata, domin tabbas Abraham ya wuce duk tunanin ta, shi din ta kasa kashewa har yanzu saboda taurin ransa, da asirin ta ya tono a idon duniya bata more dukiyar da ta dade da burin mallaka ba gwara ta sanja salo, sai kawai ta yanke shawarar amfani da AYSHA Wacce tasan yar gidan talakawa ce, domin kashe shi, ko da bincike yayi bincike aysha za a kama...






KO TA YAYA MADAM GLORIA ZA TA YI AMFANI DA AYSHA WURIN KASHE ABRAHAM??? KU BIYO ALKALAMIN NOOR...โœ๏ธ๐Ÿ˜Š





Shareโœ…

Comment โœ…

Vote โœ…





Editing is not allowedโŽ






NoorEemaan๐Ÿฆ‹

***




Thanks for reading my novel ๐Ÿค

๐Ÿ‡๐Ÿ“ABRAHAM ๐Ÿ‡๐Ÿ“





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or

*460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.


*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 0806626851