27-28
by @nooriman
🍇🍇ABRAHAM🍓🍓
*First edition*
*WATTPAD*
@NoorEemaan
***
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
Chapter 27-28
Tamk'ar barauniya haka ta fito cikin sanda, jin shiru babu motsin kowa a falon ya sanya ta sakin ajiyar zuciya, kana ta ci mur ta nufi kitchen kai tsaye, nan ma shiru babu kowa, hakan yasa cikin sauri ta shiga bud'e poison din, amma ta kasa, dogon tsaki ta saki, saboda ba karamin dauri aka masa ba, karshe dai wuka tasa ta yanke saman robar da k'yar, atishawa ta jera sau biyar, saboda karfin gubar da ta shak'a, gumi ta share, kana ta mayar da kallonta ga tukunyar dake ta tashin k'amshi mai dadin gaske...
Leka waje tayi ta ga babu alamun tahowar kowa, hakan yasa ta bud'e tukunyar, inda porridge yam din ke ta tafasa, murmushi ta saki, domin hakan yayi mata daidai, juye robar guban gabadaya cikin tukunyar mai dauk'e da porridge yam din tayi, inda dama ta cewa Indo ayi wa Abraham shi kadai, dama ka'idar gidan ne mai girki bata d'and'ana abincin da za ta yi wa masu gidan, idan ma ka yi tasting a bakin aikin ka.
Babban spoon ta saka ta jujjuya, rufe tukunyar tayi ta fita da sauri, inda taje toilet din dakinta ta yi flushing robar hadi da wanke hannun ta da hand-wash sosai saboda karfin gubar, fadawa tayi flat kan gadon ta, yayinda katon cikin ta da kamar ana kara masa girma kullum yayi tsalle, dariya zallan mugun ta ta saki tace "you re dead already Abraham hhhhhhhhh"
★★★
Aysha da ta fito daga toilet kuwa, cikin sauri ta sauko tuno abinda ta dora kad'a ya kone...
Shigar ta kitchen ya haddasa mata wata fad'uwar gaba da har yasa ta dafe kirjin ta, "Ya Rahman" ta furta saman labb'anta masu taushi da kyalli.
Idanunta ne ya kai kan saman murfin robar guban da madam Gloria ta yanke, wanda ta manta bata dauka ba, a hankali ta tsugunna hadi da dauko shi, while kirjinta ke cigaba da bugu kallon robar tayi ta ga anyi rubutun, amma ko harafi daya bazata iya pronouncing ba, cilli tayi dashi cikin dan kwand'on shara dake kitchen din, ganin wuka cikin sink ya bata mamaki, domin ita dai ta wanke komai ta mayar muhallin sa, ganin spoon again gefen sink ya kara bata mamaki....
"waya shigo kicin (kitchen) din nan?“ ta fada cikin karyewar zuciya..
Bude tukunyar girkin tayi, kana ta mayar ta rufe tana sauke numfashi, ganin kuma ya dahu ne yasa ta yi turning off gas hadi da dauko had'add'en warmer ta juye ciki...
Wanke komai tayi ta kara kyar kitchen din, dama ta gama girkawa madam Gloria abinda take so, fito da komai tayi kan dinning table, sannan ta koma dakin ta saboda lokacin magriba ya kusa...
*6:55pm*
Cikin sassarfa ya shigo cikin falon, idaunsa har lumshewa suke, ga wata azababben yunwa da yake ji, domin tun safe ruwan Black tea ne kawai a cikin sa, a matuk'ar gajiye yake sosai, sak'amak'on gajiyar daya kwaso, domin bai taba zirga-zirga irin na yau ba...
Cikin kulawa madam Gloria ta tare shi hadi da bashi side hug, "welcome back my son, my son has suffered today, Undu nwamu nkwo (Sannu yarona kaji) " ta karasa da yaren igbo.
Murmushi saman labb'a kwai yayi, yayin da idaunsa na kara lumshewa, kamar wanda aka tilasta wa yin magana yace "mum am badly hungry"
Wani irin sanyayyar dadi ne ya ratsa zuciyar madam Gloria, kansa ta shafa tace "toh son bari na kira Aysha tayi serving dinka"
A hankali ya bud'e idanunsa kana ya lashe labb'ansa da suka dan bushe kadan yace "lemme fresh up first"
"OK son, zan sa ta kawo maka dakin ka"
Ta fada tana bin bayan shi da wani mugun kallo hadi da murmushin samun nasara, sai daya bacewa ganin ta sannan ta saki wata katuwar dariya amma kasa² har da buga cinyar ta, duk da bai kai ga cin abincin ba, amma wani dadi ne ke ratsa ta, domin ta hango alamun NASARA a yau, domin abu ne mai wuya Abraham ya nemi Abinci a k'aran kansa...
*ABRAHAM*
Yana shiga dakin sa ya shiga toilet hadi da cika ruwan dumi a bathtub ya fada ciki, ya dauki tsahon mintuna goma a ciki, yayin da yake jin gajiyar na warware wa yana barin jikinsa a hankali...
Madam Gloria kuwa sawa ta yi lubabatu Kiran mata Aysha, inda babu bata lokaci suka sauka tare da ita, a yatsine ta kalli Aysha tace "ki dauki Abunshin (Abinci) yarona ki kai masa part din sa"
Cikin ladabi Aysha ta amsa da "toh" duk da fad'uwar gaban da take fama dashi, wanda sai kara tsananta yake...
Kitchen ta shiga, ta d'auko wani k'yak'yawan tray, dinning area ta d'awo ta saka warmer din cikin tray hadi da plate da spoon, sai roban ruwa, sama ta hau dashi, madam Gloria dake binta da kallo ta saki dariya kasa² cikin farinciki.
Knocking tayi har sau uku shiru, hakan yasa bakinta d'auke da sallama d'aya zame mata sabo ta tura kanta ciki, Lumshe ido tayi, domin kamar kullum dakin na wani irin kamshin na musamman, ware idanunta tayi, daram! Kirjinta ya buga da k'arfi sak'amak'on hango faffad'an bayansa da tayi, wanda babu riga, domin tsaye yake da towel a gaban dressing mirror yana shafa lotion, duk da yaji shigowar mutum, sannan kirjin sa ya buga domin ta, amma ko juyowa bai yi ba....
Aysha kuwa kamar Wacce aka dasa, kasa dago kanta tayi, tun kallon farkon da ta yi masa, domin sosai ya cika mata ido, controlling kanta tayi sak'amak'on hannun ta dake rawa, gashi ta kasa ajiye tray din, kamar yanda ko motsi k'wak'wara bata yi.
ABRAHAM kuwa hankali kwance ya shirya abinshi duk da tana dakin amma ko a jikin shi...
Cikin dagon wandon fari kal, hadi da black singlet ya shirya, roll on mai suna *Old spices* ya Murza a hammatan sa hadi da taje kansa sama² ya dawo bakin gado ya zauna tsahon mintuna biyar ba tare da yace komai ba....
A hankali ya sauke ganinsa kan ta, inda baya ganin fusk'ar ta sak'amak'on kanta dak'e tsunkuye, dan cizan labb'ansa yayi ba tare da kuma ya sake kallon ta ba, yace
"Am hungry, serve me!"
Rud'u ta shiga saboda jin amon husky voice dinsa, da kuma turancin sa da bata fahimci ko kalma daya daga ciki ba.
Amma sai tunanin ta ya bata cewa abinci yake nufin ta tabatar masa...
Dan haka tamk'ar mai tausayin taka saman tiles din ta nufi inda yake zaune, a hankali ta dire tray din kan Wani tum-tum dake gabansa, plate ta dauka ta fara serving din shi...
Sirarran hannun ta dake ta faman rawa ya shiga rarraba idanun sa a kansu, yana mamakin meke haddasa mata wanna rawan jikin...
Aysha kuwa abubuwa da dama sun dame ta, na farko kusancin su dake haddasa mata shiga wani yanayi na loosing control, na biyu kuma haka kawai kallon Abinci ke sata fad'uwar wanda bata taba Jin hakan ba, hakan nan bata yarda da abincin ba, duk da kyau, hadi da haduwar abincin...
Bayan ta zuba masa ta ajiye gabansa, gefe tayi ta shiga murza hannun ta, domin ta kasa barin dakin, a hankali ta Lumshe idanunta hawaye suka gangaro kuncin ta, hak'ik'a abinda take ji a zuciyar ta ba karami bane a yau, saboda bata taba faduwar gaba irin wanna ranar ba.
Share hawayen ta tayi, ta Bude idanunta inda ta sauke su kan doyar daya raba biyu da spoon, maimakon taga cikin doyar fari sai ta ganshi yellow shaar, ga wani kyalli da cikin doyar keyi kamar maiko-maiko...
kanta ne ya kara d'aurewa domin lok'acin da take fere doyar fari kal sosai yake, ba wanna ba, iya Sanin ta dai ko an dafa doya cikin shi baya wanna yellow'n ko da faten sa ne kuwa...
Take k'wak'walwarta ta kara hasko mata yanda ta ga kitchen dazu, so take ta furta wani Abu amma ta kasa ganin ya kai lomar farko bakinsa...
Wanda ya kara hadd'asa mata wata faduwar gaba mai tsanani, ganin yana kokarin kai loma ta biyu bakinsa yasa da gudu ta nufe shi, ta ture hannun shi, inda Abincin ya zube har kan farin wandonsa...
AYSHA
duk da tsananin tsoron da take ji a dalilin abinda ta yi masa, amma bata da zabi, sannan bata damu da hukuncin da zai biyo baya ba matuk'ar ta samu ta hanasa cigaba da cin Abincin...
"ka... ka... ka... yi hakuri dan Allah da Annabi, wallahi hankalina bai kwanta da Abincin nan ba, duk da ni na dafa, kayi hakuri yanzu zan je in dafa maka wani Abu mai sauri kaji" ta karasa cikin yanayi na rud'ewa da zubar hawaye masu zafi...
*ABRAHAM*
Zuba mata ido yayi, yana kallon kananan labb'anta masu moving very fast, ba dan ya fahimci ko kalma daya daga maganganun ta ba, illa yana mamakin dalilin barar da lomar Abincin da yake kokarin kai bakinsa...
Me hakan yake nufi?
Aysha kuwa cikin sassarfa ta nufi hanyar fita daga dakin, har ta dora hannun ta a handle ta ji ihun sa...
"Arrrrrrrh!!!“
A razane ta juyo, inda ta gan shi har ya sauko kasa kan guiwar sa hannun sa biyu dafe da cikin sa, yayin da ya zuba mata idanun sa da suka yi wani irin jaa tashi daya hadi da tara ruwan hawaye cikin su...
(Not edited) 🤒
What's your opinion on this episode reader's???
Share✅
Comment✅
NoorEemaan🦋
***
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851