29-30
by @nooriman
ππABRAHAMππ
*First edition*
*WATTPAD*
@NoorEemaan
***
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
_kuyi hakuri Na san page din yayi kad'an sosai am sorry, dan nayi alkawari ne shiyasa na cika, at least da babu gwara ba dadi , ba haka na so ba wlh, amma banda zabi daya huce haka, domin babu lokaci, kuyi manage da wanna in sha Allah ranar lahadi zan Baku update, karku yi korafi please_π€
Chapter 29-30
(Not Edited)
Sandarewa tayi a tsaye sak'amak'on abinda take gani, "mike shirin faruwa ne yau ya Allah " ta aiyana a ranta yayinda hawaye wani na bin wani a fuskar ta, jin ya kara sakin wani karan hadi da sulalewa kasa dafe da cikinsa da yake jin wasu azaba a cikin su.
Cikin firgicewa hadi da tsantsar tsoro daya bayyana a fuskar ta karara ta nufi wajen shi da gudu, cikin rud'ewa ta tallafi kansa da ke kansa tiles ta rike a tafin hannun ta, fashewa tayi da kuka tace "Dan Allah yallabai ka tashi, ka rufa min asiri, ni Dama ban yarda da wanna abincin ba, duk da ni na dafa, dan Allah ka tashi wayyo Inna ta!!!" ta karasa cikin amon sauti mai matuk'ar taΙa zuciya, Abraham kuwa wata mahaukaciyar yamutsa cikin sa ke yi, yayinda yake jin kamar ana saka wuka mai kaifi Ana dasa ko wani jijiya dake cikinsa, kasan maransa kuwa ji yake kamar ana diga masa narkakiyyar ruwan dalma a kai...
Still idanunsa na kan Aysha da yake bin ta da wani irin kallo dashi kan shi bai San ma'anar sa ba, ruwan hawaye ne suka taro a cikin kwarmin idanunsa, amma basu zubo ba, duk da sanyin air conditioner dake dakin, hakan bai hana jikinsa hadi da singlet din jikin sa sun jike da gumi daya karyo masa all of a sudden ba, saboda tashin hankali mara misaltuwa da yake ciki.
AYSHA
Kuka sosai take tana jijjiga kansa, fadi take ya rufe mata asiri ya tashi, ganin abin kara gaba yake yasa ta ajiye kansa a hankali ta fice da gudu zuwa downstairs....
Madam Gloria da ta yi pretending cewa tana kallo TV , amma azahiri Sam ba haka ne, ta kasa kunne ne taji kyakyawar labarin cewa Abraham is no more...
Jin takun sauk'owar Aysha yasa ta dago kanta da sauri, yayinda ta saki boyayyen murmushi, domin tsantsar tashin hankalin data hango a fusk'ar Aysha wanda ko tantama bata yi, alamun samun nasarar ta ne.
Gabanta Aysha ta zube, cikin shesheka take nuni da hanyar step din, kana ta fisgo maganar daya makale a makoshin ta... "zai mutu, ki taimaka min ki zo, yana kwance cikin mayuwancin hali"
"ke nutsu ki fadamin, me yana faruwa, waye zai mutu, me kika yi wa yarona, ki sani duk abinda ya samu yaron na bazan bar ki ba" madam Gloria ta fada hankali a tashe, kamar gaske.
Cak kukan Indo ya tsaya sak'amak'on jin abinda madam Gloria tace, wani sabon kukan ta kara sawa, kana cikin raunataciyyar murya tace "wallahi Allah na rantse ban yi masa komai ba"
Madam Gloria bata kara cewa komai ta nufi hanyar step da gudu, burinta ta kawai ta isa dakin, ba Wai dan ta damu da halin da yake ciki ba, a'a a k'age take ta je domin ganin halin da yake ciki, wanda take fatan ransa ya bar gangan jikinsa...
A tare ita da Aysha dake biye da ita suka sanya kansu dakin, sai dai shiru dakin, ba motsin komai, rarrabe ido madam Gloria tayi har ta hango shi kwance flat a can gefe idanunsa a Lumshe inda zuwa yanzu dishi-dishi yake gani.
Da gudu madam Gloria ta kara sa gareshi, kukan zallan tuggu da makirci ta fara yi tana fadin, "please son wake up! don't do this to me, somebody help me oo!" ta karasa tana jijjiga Abraham, amma daga ta cikin zuciyar ta farinciki ne fal cikinsa.
Cikin son juye komai ya dawo kan Aysha baiwar Allah tace " kin k'ade, kin shiga goma sha biyar bama uku ba, matuk'ar komai ya samu son, zaki gaya min me kika saka masa a abinci, ji ki kira min driver da mai gadi su tayani kai shi mota" ta karasa a tsawace mai hade da kuka.
Da gudu Aysha ta bar dakin gwanin tausayi, madam Gloria kuwa ta dire kan shi da karfi cikin halin ko in kula, wanda hakan yasa idanunsa dake Lumshe suka dan bud'e kad'an amma Sam mutum bazai lura ba ya bi madam Gloria dashi, cikin sauri ta Bude drawer din shi ta yi sa'ar samun wani kyakyawan farin leda, abincin cikin warmer hadi da na plate din ta juye cikin ledar, kana ta kulla da kyau ta jefar cikin karamin kwandon shara dake dakin, wanda tayi hakan ne domin koda za a yi bincike bata so ya tsananta, domin tasan dangin mahaifin Abraham basu da wasa, baya ga haka, matukar aka gano kalar guban, ba karamin matsala bace...
Dariya ta saka, wanda yasa Abraham mamaki kwarai, Sam baya son k'wak'walwa da zuciyar sa su yarda da abinda suke son bijiro masa, so yake ya furta wata kalma amma labb'ansa sun yi masa nauyi ainun, wani bakin duhu ne ya rufe idanunsa, samaΒ² yaji tace "Dan banza mai tarin rai, dama ka mutu na huta" daga nan bai kara sanin inda kansa yake ba....
Jin takun haurowar su Aysha yasa da sauri ta koma kan Abraham tana jijjiga shi, sannan ta cigaba da kukan ta.
Hankali a tashe suka kama Abraham da kyar zuwa kasa, domin ginanen jikinsa yasa yake da weight, ba kuma dan yana da kiba ba, a'a kasancewar sa giant ne kuma mai gymming yasa haka.
Babu bata lokaci suka bar gidan, yayinda Indo dake tsaye a compound din gidan ta bisu da kallo hadi da zubewa kan guiwar ta ta saki kuka mai tab'a zuciya, taso bin su asibitin amma madam Gloria ta ture ta cikin shammata a lokacin da take k'ok'arin shiga motar, ta jima sosai tana kukan, kana ta ja kafarta daya yi sanyin kalau zuwa cikin gidan, cike da fatan Allah yasa ya rayu, domin Sam bata son shiga tashin hankali har yaje ga kunnen Inna da ta dan samu farinciki, kuma ko da wasa bata son wanna farincikin ya gushe.
Ta bangaren su madam Gloria kuwa gudu sosai driver yake falfalawa yayinda madam Gloria ke kuka tana surutai cikin yaren igbo, wanda ba komai take fadi ba illa jifan Abraham da kalamai marasa kyau hadi da yi masa fatan mutuwa, driver dake tuki ya kalle ta hadi da girgiza kai cikin tausayin ta, tabbas a yanayin yanda take kuka tana maganganun dole ta baka tausayi, domin mutum zai yi tunanin abin arziki take fadi, sanin cewa driver baya jin yaren Igbo yasa ta fadi abinda take so babu ko sha yi
Tafiyar mintuna ashirin da biyar ta kawo su wani had'add'en private hospital, cikin sanin makamin aiki nurses din suka tura shi zuwa emergency ward ganin halin da yake ciki, kasa zama madam tayi, burinta kawai Doctor ya fito ya sanar mata mutuwar sa, da babu abinda zai hana ta fasa kukan murna...
_5 hours later_
Dare yayi sosai, kuma har zuwa wanna lokacin babu wani doctor ko nurse daya fito daga emergency ward din bare ta samu damar tambayar sa, safa da marwa kawai take a matukar kage, sai da aka sake dauk'ar wasu mintuna talatin din sannan doctor ya fito yana sharce gumi, kai kace ruwa ne a fusk'ar sa, cire medicated glass din idanunsa yayi ya kalli madam Gloria yace "madam follow me to my office"
**** fans keep the comment going and please don't forget to follow my account and also vote my stories thank you*
Share to other group's please π
NoorEemaan
O7082281566
10:41pm
Friday, 18 February.
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851