Abraham

49-50

by @nooriman


🍇🍇ABRAHAM🍓🍓


*First edition*




***

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din






*WATTPAD*

@NoorEemaan





Chapter 49-50



*AYSHA*

Kallon dakin take ganin yadda ya hargitse ya tabattar mata da cewa an shigo dakin, amma bata ko yi magana ba ta shiga gyarawa, domin tambayar waya shigo ba hurumin ta bane.






Abraham kuwa zuba mata sexy eyes din sa yayi, Ya kuma fahimci abinda ke ranta, Amma Bai yi magana ba, tana cikin gyaran ne taji keypad dinta na ringing, sai a lokacin ta tuna cewa wayar na dakin Abraham, bata dauka ba, cikin sauri ta nufi Wajen wayar domin tana da tabbacin Inna ce, domin idan ma ba ita bace toh anty Bintu ce domin su kadai ke da numbern ta.





Tana dubawa kuwa ta ga Innar ce, cikin sauri ta yi picking Hadi da sawa a handsfree

"Ammuh!"

"Ammuh!!"

Muryan su Anwar ta cika wayar basu ma bari Inna tayi magana ba, siririyar dariya Aisha ta saki, hakan ya saka Abraham dagowa ya kalle ta, domin yau ne karon farko Daya ji dariyar ta haka, da alama tana matukar kaunar y'ay'an ta ya aiyana a ransa.

Tuno Nonye da cikin ta yasa ya hadiyi Wani abu Mai daci a ransa, yasan cewa da ace tana raye da yanzu yar su ko dan su tayi wayo, Jin muryoyin yaran yasa Wani mugun so y'ay'a da sha'awar su ya kama shi...




"Ammar! Anwar!!" Ku bari mu gaisa da Inna ko"


"Ammar!"



Abraham ya kira sunan da harshen sa na yan Igbo, tabbas wanna sunan yaji a bakin Aysha a ranar da ta fara shigowa dakin sa, a kuma duk lokacin da ta kira sunan sai zuciyar sa ta buga, me Hakan ke nufi kenan? Ya Yi wa Kansa tambayar da bai da amsar shi.



"Assalamualaikum, Innata! Ina kwana"


"Lafiya lou diyar albarka, yakike ya aikin?"


"Alhamdulillah Inna, fatan Babu wata matsala?"



"Alhamdulillah Babu komai, ya Mai jikin?"



Dan satar kallon Abraham tayi suka hada ido, saurin dauke kanta tayi kana tace "da sauki Inna"



"Masha Allah, toh Allah ya bashi lafiya, ki mai sannu"


"Toh inna"


"Yawwa, ga yaran ki ku gaisa, sannan ki dage dayi masa rubutun Nan da bashi maganin kinji ko" Inna ta fada daga dayan bangaren tana ajiye wayar gaban su Anwar domin raba rigima, saboda matuk'ar ta bawa Daya waya toh akwai rigima kenan...



"Toh Inna nagode, Yaran albarka, kun tashi lafiya?"



Hada Baki suka Yi wurin amsawa, "lafiya kalau Ammuh!" Nan suka shiga bata labari tana biye musu har kudin Inna ya kare, ba Dan sun so ba suka hakura.




Farinciki ne ya cika zuciyar Aysha Jin muryoyin yaran ta, ajiyar zuciya ta sauke murmushi dauke kan fuskar ta, sosai take kaunar su Anwar a ranta, domin kallon y'ay'a take musu da kuma kanne da bata dasu, ta dago kanta kenan taga sun hada ido, sauke kanta tayi kasa tace

"hmmm... Inna tace na Maka ya ji...." Sai kuma tayi shiru tuno cewa ba fahimtar abinda tace zai Yi ba, Abu mai sauki kawai ta dauki biro ta memo din shi ta rubuta, sannan ta hada da wayar sa dake gefen gado ta mika masa, domin sakon Inna ne dolen ta ta isar masa.




Karba yayi ya shiga app dinan mai fassara kalmomi daga Hausa izuwa turanci.



Amsar da app din ya bashi ya kura wa ido, ashe matar da bata San ko shi wane ne ba ta damu da sanin lafiyar sa haka? Amma wacce ya dauka a matsayin mahaifiya bata ko damu da lafiya da lafiyar sa ba, bama ta kaunar ganin sa a doran kasa, ashe Aysha ta dauki shi da muhimmanci har ta sanar da mahaifiyar ta rashin lafiyar sa.


"Oh God! This people are damn amazing" ya fada a ransa cikin yabon kyawun halayen su.


Dagowa yayi ya sakar mata murmushin sa mai kyau domin yaji Dadi har ransa da kulawar Inna garesa, itama murmushi tayi kana ta bar dakin.





Da misalin karfe uku na yamma madam Gloria ta fito daga gidan,, sai dai bata dauki mota ba, a bakin gate ta tsaya bayan ta fito kana ta saki murmushin mugunta a Fili tace "wanna karon ba za ka Sha ba, duk taurin ranka dole ne ka mutu a duk lokacin Dana dawo, domin a mugun shirye nake yanzu"




"Bayan kwana uku*


Cikin kwanakin Nan Abraham na Jin sanje-sanje a jikin sa, domin sosai Aysha ke kokari safe, rana, dare wurin bashi magani da rubutu.


Ranar daya cika kwana bakwai da fara Shan magani Abraham yaji kamar an yaye masa ciwon cikin Nan, sannan ko da ya Dan motsa jikin sa baya Jin zafi kamar da, tamk'ar an dauke masa dutse daga kan cikin na sa haka yake jin shi qwanin Dadi, duk da Bai gwada mikewa ba, Amma tabbas farinciki ya cika zuciyar sa, domin tunda yaci gubar Nan Bai kara lafiya irin na yau ba, dama daurewa ciwon kawai yake.




A kuma daidai lokacin ne Aysha ta shiga dakin ta domin yin sallar magriba... sai a sannan Abraham ya gwada mikewa, iKon Allah buwayi gagara misali, kamar almara lo magic haka ya mike.




"Thank you Jesus Christ" shine kalmar daya fara fita a bakin sa, yayin da husky voice dinsa ke bayyana tarin farincikin sa.



Taku uku yayi, ya sake dawowa gaban well chair din sa, kamar karamin yaro haka ya fada kan gado ya dunkule hannun sa yace "yes! Am back on my feet, Jehovah thank you, oh Lord! Thank you" Ya ma rasa kalmar da zan fada saboda tarin farinciki, gaban gadon ya dawo yayi kneel down worship song na christian ya shiga Yi kana ya Dora da addu'a, bayan ya gama ya mike ya shige toilet, domin tsaftace jikin sa.






AYSHA

Bayan ta iddar da sallah ta sauko kasa domin karasa musu abincin dare, yau kam ta makara bata gama da wuri ba, Allah ya taimake ta Madam Gloria bata nan, da ta banu a hannun ta yau.



Sai da ta sake daukar wasu mintuna ashirin a kitchen din sannan ta gama, had'add'en spaghetti🍝 da miyar stew Daya Sha zallan sokan namomi ta girka, ta zuba masa a warmer, sannan ta daukar masa lemo da ruwa ta nufi dakin sa, kamar kullum bakin ta dauke da sallama ta tura kofar dakin ciki....




Sam bata lura Babu shi kan wheelchair din sa ba, sai da ta ajiye abincin a centre table kana ta dago kanta taga wayam Babu shi...



Gabanta ne ya fadi ganin Babu shi kan kujerar sa, "toh Ina ya tafi?" Ta San dai ba tafiya yake ba bare tace ko Wani waje ya tafi, gabadaya k'wak'walwarta ya toshe, hawaye suka cika idanun ta, kamar status haka ta tsaya bata motsa ba.


Wani sanyayyar kamshi taji ya bugi hanci ta, hakan yasa ta waiwaya da sauri, fidda manyan zararran idanunta tayi waje, cikin zallan mamaki da al'ajabi sak'amak'on abinda ta gani.







_hey fans! Hope you all enjoyed this episode? let me know In your comment_





Share fisabilillah


Comment




✨NoorEemaan✨

***




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or

*460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.


*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 0806626851