Abraham

53-54

by @nooriman


🍇🍇ABRAHAM🍓🍓





*WATTPAD*

@NoorEemaan




***

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Page 53-54



"'ple.... p...le...ase can i see your boss, i mean Abraham"


Cikin rashin fahimta mai gadi ke kallon ta, domin iya sanin sa ba sunan uban gidan sa Abraham ba, ita kuma Anty sarah ta gane shi tsaf domin shi ne dai mai gadin Abraham na da, amma bata nuna ta gane shi ba.


Shiru mai gadi yayi kamar yace batan gida tayi, sai kuma yayi saurin cewa "oh! Oh!! Oh!!!" Alamun ya tuna Abraham tsohon mai gidan sa, nan ya shiga bawa Anty Sarah labarin tashin sa daga garin ba kuma ya san ina suka koma ba, yana gama bata labari ya rufe gate din ya ruga cikin gidan da gudu sak'amak'on kiran da matar gidan ke masa.



Anty Sarah sulalewa kasa tayi ta ɗora hannun ta akai ta sa kuka mara sauti yayinda hawaye ke sulalowa daga idanun ta, gwanin tausayi, ita kam ina zata je? Ta ina zata fara neman su a fadin duniyar nan?

Ta jima zaune a wajen cikin rashin sanin abin yi, ga duk wanda zan wuce sai ya dinga kallon ta, hakan yasa a sanyayye ta mike ta shiga tafiya domin komawa garin su....




••• ••• •••



Zaune yake a had'add'en office din sa dake cikin ma'aikatar sa, yau kwanasa uku da dawowa aiki, inda sosai ma'aikatan sa suka yi murna da dawowar sa.


A shirye yake cikin suit baƙi, sosai hakan ya fito da kwarjinin sa hadi da haibar sa, Google ya shiga yayi searching wani abu sannan lambar dake karshen rubutun ya dauka, wayar sa yasa ya danna kiran lambar, magana biyu zuwa uku ya ajiye wayar, sannan ya mike ya dauki key din mota da waya, sake gyara zaman rigar sa yayi, murya kasa-kasa yace "yeah! I guess this is the only solution" ya karasa fada yana bude kofar office din ya fita, parking space dake company ya nufa ya shiga Mota, security da masu gadi na masa a dawo lafiya, hannu kawai ya daga musu kana ya fice...



Tafiyar mintuna arba'in ya kawo shi babban ginin mai dake da rubutun *MM HARUNA ENGLISH ACADEMY* kallo daya yayi wa ginin kana ya dauke kansa, lambar dazu yayi dialling, bayan anyi picking ya fada musu yana wajen ginin...


Mintuna uku kacal wani matashi ya fito, cikin girmamawa ya gaishe da Abraham, fuska a sake Abraham ya bashi hannu ya suka yi musabaha, sannan suka jera cikin wajen, office din shugaban su matashin nan ya nuna masa kana ya koma...


Bayan sun gaisa da shi, Abraham yayi gyaran murya yace "am.... I want to register a girl here, i don't mind to pay extra money if she can be fluent in speaking English" Ya karasa Yana dan bugu teburin office din da yatsun sa biyu a hankali, bai sani ba ko Aysha zata yi na'am da wannan makarantar ta koyan turanci da zai sa ta ba, kawai yana so ta iya ne domin ya saukaka musu wajen magana da juna, ya lura cewa bata yi karatun boko ba, matuƙar ta bashi hadin kai, tana kuma kaunar karatun zai bata dukkan wata gudunmawa domin ta cigaba, domin tana daya daga cikin halittun da bazai iya taɓa mantawa ba a rayuwarsa, shiyasa take da dubbin darajar a idanunsa.


Maganar shugaban makarantar ce ta sa shi daga kansa, sannan ya daina buga yatsun sa kan teburin, cikin turanci mutumin yace...

"In Sha Allah zaka yi mamaki yanda zata kware a fannin turanci, karka damu, sannan kamar yadda kace za ka iya ƙara kuɗi domin ta fi saurin kwarewa. Toh zan yi making arrangement a saka ta a special class domin a koya mata komai yanda ya kamata, sannan yace zata iya farawa ranar juma'a, tunda yau Laraba, domin dama kwana uku kaɗai ake karatun juma'a, asabar, da Lahadi"


Hannu Abraham ya bashi suka yi musabaha, sannan ya biya dukkanin kuɗin da ake bukata, sannan aka bashi Form ya cike mata sannan a yi attaching passport din ta da filling foam din, karba Abraham yayi, domin bai san sunan ta ba, bare ya cike mata, baya ga haka ma babu passport din ta a wajen sa, hakan yasa ya karbi Form din yace zai je gida ya cike gobe zai dawo dashi, da haka ya bar wajen


Bayan ya koma office, babu jimawa P.A dinan na shi ya shigo bayan ya bashi izinin shigowa, a sake suke tattauna da Abraham kan abinda ya shafi business din su musamman da bayan nan, yana masa bayanin komai da komai, bayan sun gama maganar business din yace "boss!"

Abraham ya dage girar sa alamun amsawa.

"Wallahi matar ka tana da kirki sosai"...

Dan waro ido Abraham yayi saboda mamakin kiran kalmar *mata* da personal assistance din sa yayi, shi kuwa P.A bai lura da yanayin fuskar Abraham ba, nan ya shiga bawa shi labari tun daga zuwan sa gidan da karramawar da Aysha tayi masa, sannan maganar da suka tattauna kan yana k'asar waje, komai dai bai boye ba...


*Some minutes later*

Bayan fitar P.A "What!" Abraham yace Yana sakin murmushin gefen baki, "so this Hausa girl is smart as this, oh my goodness" sosai ta burge shi, musamman karkashin ta, dakewar ta, hadi da boye rashin lafiyar sa da ta yi, ya jima yana tunanin a kanta da irin hallacin data yi masa...





••••••• ••••••• ••••••




Da misalin ƙarfe hudu ya bar company'n sa zuwa gida. Biyar saura mintuna k'alilan ya iso gida saboda dan hold up dake hanya, a parking space ya faka motar sa, kana ya fito rike da brief case din sa, har ya fara tafiya ya tuna da Form din, ya kuwa ya d'auka sannan ya nufi cikin gidan.....



Kamar kullum fakon shiru sai plasma dake aiki she kad'ai, kamshi yaji ya bugi hancinsa wanda ya tabbatar masa da cewa tana kitchen kenan, bai ce komai ba, ya haura sama, bayan ya ajiye Form dinan a dining table ya ɗora remote control akan takardan.



_7:55pm_

A daidai lokacin Abraham ke saukowa sanye da fararen kaya na shan iska da suka yi matukar karban chocolate skin din sa, kan dining table ya zauna, yana jiran Aysha tazo tayi serving din sa, domin sosai ya fara jin yunwa tun abincin safe, a hankali ya daga kansa ya kalli sama, a ransa cewa kila sallah take yi.


Bayan mintuna goma ya ji takun tafiyar ta, sanye take da hijab ja har kasa, yayi matukar karban farar fatar ta, tamkar wata zinariya haka ta yi kyau.


Kallon ta Abraham ke yi, maganganun da P.A yayi masa ke dawowa ƙwaƙwalwar sa, innocent face dinta ya ke kallo, ba tare da sanin sa ba, murmushi ya subuce masa, tana da sanyi sosai, yayi mamaki kwarai data samu kwarin gwiwa har haka.


Gefen sa ta tsaya tace " sannu da zuwa! Ina wuni"


Daga maka kai kawai yayi, domin bai ji abinda tace ba, kwara ina kwana yafi gane mai, Aysha bata kara cewa komai ba shiga serving din sa, bayan ta gama ta fara kokarin barin wajen.


"Hey! Sit" yace Yana nuna mata kujeran dining table, a sanyayye ta dawo ta zauna, alamu yayi mata kan taji abinci, girgiza masa tayi sannan ta motsa kananan lips dinta tace "Na koshi"


Bai kara magana ba ganin har ta fara raurau da idanu, sai da ya ci fiye da rabi sannan ya mika mata wata takarda, Domin kafin ya sauko ya shiga app dinnan, yayi typing da turanci kan bayanai abinda za a cike Form da shi, abun ya fito da amsa da turanci, ya yi coping a paper, idan ta rubuta masa, she kuma sai ya cike mata Form din da kansa.


Duk da tayi mamakin mezai yi da sunan ta, shekaran ta, da sauran personal details dinta, amma bata tambaya ba ta shiga rubuta komai a inda ya bar space gashi rubutun da Hausa wanda Hakan yayi mata sauki kwarai...


Bayan ta gama rubutuwa ta lura da wasu rubutu still da Hausa a kasan takardan "Ban san yanda zaki dauki abun ba, amma na saki a wata makaranta ta koyan turanci, inda zaki dinga zuwa juma'a asabar da Lahadi, gobe zamu je ayi miki passport idan na dawo, amma idan bakya so zaki iya fadamin"



A hankali ta dago kanta fuskar ta dauke da murmushi, kasancewar ita yake kallo yasa shi ganin murmushin, wani sanyi yaji a ransa, hannayenta ta dage alamun godiya kana tace

"Nagode sosai, Allah ya saka...."


Hannun ya ɗora a lips din sa alamun tayi shiru, saboda ya fahimci godiya take kokarin masa.


Bayan ya gama ya sha lemo sannan ya janyo Form din da abinda ta rubuta ya shiga cike mata.

Aysha kuma ta mike ta gyara dining table, sannan ta kai plate da cups da yayi amfani dasu ta wanke kana ta fito...

"sai da safe" tace tana hayewa sama, bai je komai, domin bai fahimta ba, sai bin ta da ido yayi har ta bacewa ganin sa...


Numfashi ya furzar, kana ya kai idanun sa kan dakin Madam Gloria, wani abu ya daki zuciyarsa tuno wacce mummy, domin sai Yanzu ainihin hallayen ta suka bayyana, ashe duk zaman da suke fuska biyu ce! Bai sani ba, bata kuma taɓa nuna wata alama ba, ganin ransa zai fara ɓaci yasa shi daina tunanin Madam Gloria, sannan ya raya a ransa cewa da safe kafin yaje office zai biya bank ya sanja pin account din sa, saboda a ranar data kwashe ATM din duk yana jin ta, dama pretending baccin karya yayi...


Yana jima a zaune yana sake-sake kana ya kashe duka kayan wutan dakin da plasma ya nufi dakin sa domin bacci...



*WASHEGARI*

Hudu saura mintuna takwas Abraham ya dawo, domin ya yi alƙawarin cewa yau zasu je tayi passport, cikin dan sauri-sauri yake tafiya.

Dakin sa ya shiga dake a kimtse gwanin burgewa sai kamshi ke tashi, kayan jikin sa ya cire, daura towel, sannan ya jefa wanda ya cire a laundary basket kana ya shiga wanka, mintuna goma kacal yayi ya fito ya shiga shiryawa...


Bayan ya gama ya fito, har zai leka dakin ta ya kira ta, sai kuma ya hango ta zaune a downstairs, da alama shi take jira, bayan ya gama saukowa ba tare da ya kalle ta ba yace "let's go"


Duk da bata gane abinda yace ba, amma haka ta bi bayan sa ganin ya nufi waje, sai Yanzu take jin son turanci a ranta, musamman da Abraham ke yi, domin sosai take dad'i a bakin sa...



Har zata shiga baya, taga ya buɗe mata gaban motar, ba musu ta shiga ta zauna. Wani babban gidan hoto Mai suna *INFINITY* ya kawo su, Bayan yayi parking, kusan a tare suka fito daga motar, cikin wajen suka nufa, cikin girmamawa ake karɓe su, nan mai yin passport din ya sanar dasu cewa passport takwas 3,500 hake yake yin sa...


Wani had'add'en dakin hoton aka shigar da Ita, mintuna biyar ta fito ta zauna gefen kujerar da aka tanadar wa Abraham two sitter.


Bayan an gama hada komai aka saka mata envelope, Ya mika mata, karba Aysha tayi ta ɗan buɗe ta ga yayi kyau sosai kamar dai hoto normal saboda haduwar sa.


Maimakon su koma gida sai ta ga ya nufi wani restaurant yayi musu takeaway, domin sam Yau baya son tayi girki, yana matukar ganin kokarin ta wajen iya girki da kula da gida tamkar babbar mace, at least once in the while ya kamata tana hutawa.




•••••. ••••••. •••••


MADAM GLORIA

Tafiya take cikin wani kusurmin daji mai matukar ban tsoro da abubuwan al'ajabi kala ² tun jiya take tafiya amma har yanzu bata kara so inda take so ba, ko wahala bare tsoro bata ji saboda mugun nufin daya cika zuciyar ta...


Tana cigaba da tafiya taji wata murya ta fara dariya cikin wata amo mai ban tsoro hadi da ruda ƙwaƙwalwar mutum, juye juye ta shiga yi ko zata ga mai dariya amma bata kowa ba, can kuma dif cikin wata murya da amon sa ke fidda zallan fushi taji an ce....







Share


Comment







NoorEemaan

***





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or

*460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.


*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 0806626851