Papi ne!

5-6

by @nooriman

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

Written by

Noor Eemaan


Wattpad

@NoorEemaan




This book this dedicated to all orphans in the orphanage home.


Page5-6

........Ciƙin ikon Allah k'uwa bata ƙara tashi ba har gari ya waye, sai takwas na safe nu'aym ya fito daga dak'insa baby'n dauk'e a hannun sa.


Ƙo ina tsaf tsaf alamun an gyara, gama shatin tsintsiya kwance kan jar kasar, d'aga gefen wajen mad'afa kuwa kaka ce tsukunne ta dora musu d'umammen tuwon su da yayi ragowa jiya, "my kakus ina kwana" ya fad'a cikin tsokanar ta.

Shan toka/kunu kaka tayi ba tare da ta bashi amsa ba, kan yaloluwar tabarman su ta nufa da kwanon tuwonta ta fara ci....Dariya ya saki d'omin ya san dole dama za a yi hak'an

Kan tabarman ya zauna gefen ta ya kara cewa "haba tawan kiyi haku'ri kinji"

Sai data kai wata katukar loma kana tace" k'ullum sai ka gama yin son ranka sai ka wani ce in yi haku'ri, toh baru kaji a yau sai ka fitar da yarinyar nan daga gidannan bazata sake kwana a nan gidan ba, ko tausayin ta baka ji, jaririya da ko cibiyar bai gama nuna ba ka dauko, nama rasa wacce uwa ce mara tunanin ta baka 'ya sabuwar haihuwa har ka kawo ta gidan nan cik'in ruwan sama, fisabilillah fa" kaka ta karasa maganar cik'in masifa kana cik'in daga murya.


Jikinsa yayi sanyi, d'omin d'uk rigimar su yana matuk'ar son kakar sa haka itama. Cik'in muryar daya san zata tausaya masa yace "ki gafarceni k'aka, banyi da niyyar bata miki rai ba, sannan tsananin tausayin wanna baby'n yasa na har na d'auko ta a hanyar dawowa na daga gareji Cik'in kwali...."

"Cik'in kwali kuma kuma Nu'aymu?" Kaka ta ce tana tsame hannunta daga Cik'in tuwon

"kwarai kaka Cik'in kwali ,nan ya shiga bata labarin yand'a ya tsince ta.....

K'uka mai ciwo k'aka ta fashe da shi tace " Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan minha, duniya ina zaki damu ne? Yanzu saboda rashin imani uwa ta yar da dan data haifa da cikinta, shin yaushe zamu yi hankali ne, tayaya masifu da rashin cigaba bazasu iya mana yawa ba, muna aikata manyan laifuka, yanzu meye laifin wanna jinjirar da bata san komai ba, wai saboda toshewar basira da tunani kayi cik'in da wata tara ka haifeshi tsannan ki ce zaki ji kunyar rainon dan ko yar dazai iya jikan ki a duniya, wasu na nema ido rufe wasu na yar wa, shin wanna data yar da jaririya, bata san wani hali zata shiga ba, zata rayu ko zata mutu, hannu na gari zata fada ko akasin haka, kuma mace ce fa, mace da rayuwar ta ke bukatar kulawa, sanya ido, hadi da bata tarbiyya ingantacciyar domin matukar ka tarbiyan tar da ya mace tamkar ka tarbiyarta da Al'ummah ne, shine ta yar da ita bako tsoron Allah, idan Allah ya dauki ranta wani amsa zata bawa ubangijin ta? kai jama'a mu ji tsoron Allah" kaka ta karasa cik'in amo dake nuna cewa tana matuk'ar jin haushin da tsanan wadannan halaiyan daya addabi al'ummar mu a yau...

take wani matsanancin tausayi, da son wanna jaririyar ya ratsa zuciyarta, d'omin shakka babu ta yarda da jikan ta, sannan ta san cewa bazai taba kowa abinda zai cuce ta har gida ba, kawai da farko taji tsoro ne saboda yand'a duniya ta lalace yanzu...


Ajiyar zuciya ya sauk'e maganganun kakan na ratsa zuciyar sa, duk da yana da karanci shekaru amma yana da kaifin tunani. Yana shirin yin magana baby'n ta saki wata atishawa a tare suka kai kallon su gareta

"Nu'aymu sanyi ya shiga jikin yarinyar nan, ooh yarinya Allah ya saki miki" kaka tace tana rike haban ta

Sannan ta kara cewa "in sha Allahu, da hannuna da k'arfina zan taya ka rikon wanna yar, d'omin yanzu girma ya hau kanka ka zama uba, d'omin zata taso da sanin cewa Kaine ubanta, sai a nutsu, eh sai a nutsu saboda kada yarinya ta gado rashin jin magana Allah ya raya mana ita ya taya mu riko, Allah yasa mai taimakon addinin islama ce" kaka ta karasa karshen maganar a zolaye...

"Murmushi kawai ya saki, wani girma na kara shigar sa, farincikin mara mitsaltuwa na ratsa shi jiyake tamk'ar ita din diyar sa k'amar yadda kaka tace...

Kasa kasa da muryar k'aka tayi tace " yawwa wani hanzari ba gudu ba, duk wanda ya tambayi ka cewa yar waye kace diyar kanwata ne d'a ta rasu, duk da ba wanda zai tambaya, tunda bamu da abun duniya babu mai rabar mu, kawai inkas(in case) idan sun tambayeka shiyasa na fad'a, kuma koda wasa bana son wanna yarinyar tayi k'ukan uwa a duniya, don haka zamu rufa mata har duniya ta nade kaji ko?"

Jinjina kai yayi Cik'in gamsuwa, karban ta kaka tayi domin yi mata wanka, duk tattalin kaka sai gata ta fidda dari biyun ta tace "kaje kantin iliyasu ka siyo pampas(Pampers) lamba daya ka kawo min maza"

Amsar kudin yayi yace "yau yaushe kaka?"

"Yau asabar, lafiya kake tambaya Nu'aymu"

"Tab... wallahi za'a yi ruwan sama yau, kaka da kanki kika fidda kudi a siyi abu wa mutum, ina mammakon na ki ya tafi?"

"Kaji min dan bazan yaro, yo kayan jikinta ma atika kawata da diyar ta ta haihu zan kaiwa, wallahi da nace sai ka biyani amma yanzu na yafe, don inason wanna diyar sosai mai madarar kyau"

Dariya ta bashi, ficewa yayi yana jin kaunar kakarsa a ransa...



*ASALIN SU*

Malam jafaru dikko dan asalin garin katsina ne, shine da na uku wajen iyayensa kuma auta, bayan ya girma ya fara fita neman na kai, daga kano har Sokoto, wanda a nan ne ya hadu da wata yarinya mai suna zainab, tak'e ya kamu da sonta saboda tarbiyar ta, ba a dauki tsahon lok'aci ba aka daura musu aure kasancewar suna son junan su...

Kasancewar yafi dan samu kudi a sokoto ne yasa ya siyi dan karami fili yayi gininsa dai dai talaka suka ciga'ba da rayuwar su, bayan shekaru hudu zaynab ta haifi da namiji ranar suna yaro yaci suna AHAMADU wanda daga shi Allah bai kara basu haihuwa ba....



BAYAN SHEKARU ASHIRIN DA TAKWAS

A cikin tsayin shekarun nan abubuwa da dama sun faru , wasu sun mutu ciki harda malam jafaru, wanda mutuwar sa ta dakesu ba kadan ba, a cikin tsayin shekarun nan dai Ahamadu yayi aure, ya auri wata yar nan sokoto, suka ciga'ba da rufawa juna asiri cik'in kaunar juna... Bayan shekara daya matar Ahamadu mai suna Amina ta haifi yaro K'yak'yyawan gaske, ranar suna yaro yaci suna *NU'AYM* wanda duk suka dora masa son duniya, sai dai kwana arba'in da haihuwar, mahaifiyar Nu'aym ta koma ga Allah....

Sosai sukayi kukan rashin ta bare ma zainab(kaka) haka kaka ta ciga'ba da rainon sa har ya girma kuma alhamdulillah bai yi wata rigima ba. Haka ta ciga'ba da rainon sa har ya kai shekaru uku, mahaifinsa Ahamadu ya sa shi makarantar private....

Yana jss3 a makaranta Ahamadu ya rasu, sak'amak'on ciwon ciki daya yi kwana daya tal, wanna karon Nu'aym yaji mutuwar mahaifin sa kasancewar sa yaro mai wayon gaske

Haka suka haku'ri suka ciga'ba da rayuwar su cik'in rufin asirin Allah, saidai daga baya komai ya fara kare musu, ko a cik'in yan'uwa babu masu waiwayon su balle har su taimak'a musu k'asancewar yanzu zumuncin da taimkon juna yayi karanci...

Ganin halin babu da suke ciki yasa Nu'aym fara tunanin abin yi domin taimaka musu, sosai yake da tunanin tamk'ar babba, kaifin tunanin da zafin zuciyar nema...

K'asancewar yanzu an cire shi daga private school ya dawo na government saboda rashin kudi, sai yaje wani gareje dake gaba da unguwar su, ya roki ogan zai dinga zuwa koyan aiki, babu musu ogan ya amince, bai rufa wata biyu ba ya fara iya aikin domin har yan kananun gyare gyare zai iya yi, idan ya tashi ogan zai bashi dari uku, hudu haka wata rana har dari biyar....


Da wanna kudin suka dinga rufawa juna asiri har ya bawa k'aka jarin dari hudu, ta kuwa auno lalle ta fara kullawa goma goma kuma alhamdulillah ana dan siya, kullum idan ya tashi daga boko baya dawowa gida direct gareji yake tafiya, domin yana da izu arba'in a kan shi yana kuma fatan matukar abubuwa suka dan daidaita musu zai koma islamiyya, da bayan magariba yake tashi daga gareji, sai yaki dawowa gida su zauna hira shi da abokansa, har tara, goma, yana kaiwa wani zubin, babban abokinsa shine Abdul -hafeex, domin Abdulhafeex na son abota da Nu'aym, amma Nu'aym bai fiye sake masa sosai, k'asancewar Abdul-hafeex dan masu kudi ne...

Kullum haka kaka ke fama da shi kan dawowa gida da wuri, wani zubin har fad'a suke, domin kaka akwai rikici duk da haka dai suna da matuk'ar son junansu wanna kenan...


*CIGA'BAN LABARI*

Zaune suke a dakin kaka, tana shirya baby'n cik'in wasu kaya masu kananun kudi domin baza su fi dari hudu ba, ba laifi baby'n ta rage k'uka domin k'ullum Cikin dare sai ta tashi tana kuka sai dai Nu'aym na daukar ta zata yi shiru ta ciga'ba da baccin ta har mamakin hak'an yake, duk ranar da bai samu kudi masu yawa a gareji na siya mata madarar yara ba, sai ya siya mata nono na saba'in haka wurin masu fura kuma alhamdulillah tana karba ta sha.


Bayan kaka ta gama shirya ta ya karbeta ya rungumeta a jik'in sa, murmushi kaka ta yi tace "toh mai 'ya wani suna ka zaba mata ne?"

Lumshe idanun sa yayi kana ya ware su kan baby'n yace "BABY NU'AYMAH"

Dan tabe baki kaka tayi tace "meye wani bebi (baby) kuma sai kace wata yar tsana"

Murmushi yayi yace "toh NU'AIYMAH nake nufi"

"Yawwa yanzu naji batu, Allah ya raya mana Nu'aiymah, sai kayi mata hudu ba ko?" Take kuwa ya yi mata, "Allah ya raya ta" kaka ta kara cewa

"Ameen ya Allah kaka" yace yana kara kamkame ta a jikinsa, shi dai yana jin wani abu da bai san ma'anar sa ba a jikin sa...

"Sai dai dole mu yanka mata ragon nan nawa a sunan ta, tunda ina da guda daya Allah ya hore min, idan yaso sai a dinga siya mata madarar yara har Allah yasa ta kai minzanin cin abinci..

Dariya yayi yana mamakin yawan sakin hannun ta a yanzu yace" hak'an yayi dai dai kaka" Allah ya kara miki lafiya da Nisan kwana"

"Ameen dan jikana".....tace cik'in farincikin.



Share✔

Comment✔

Vote✔

Edit❌