Papi ne!

13-14

by @nooriman

๐Ÿ‡๐Ÿ‡PAPI NE!๐Ÿ“๐Ÿ“


Written by

Noor Eemaan

***


Wattpad

@NoorEemaan





Juma'at Mubarak to all my fans, Allah ya sada mu da Alkhairi cikin ta.







Page 13-14


.............da suka shiga gida kuwa sai da kaka ta fuskanci ba lafiya, domin ba haka suka saba shigo mata ba, k'ullum cikin nishadi suke shigowa cikin gidan da tsokanar ta, duk sai taji ba dadi, kasa hak'uri tayi tace "ya dai kuka shigo kamar kun ji sakon mutuwa ta"

Nu'aym bai kulata ba ya shige dak'in sa ya kwanta, da kallo ta bishi kana ta dawo da Kallon ga Nu'aiymah da har ta fara matso k'walla tace "Ke miye sameku?"

Shiru Nu'aiymah tayi tana cigaba da kukan ta da sautin sa ya fara fitowa fili, tabe baki kaka tayi cikin jin haushin ganin duk sun mata shiru, mita ta shiga yi duk sun mayar da ita mahauk'aciya sun ki kulata.



Nu'aym na daga dakin kwance ya rufe k'unnewansa da tafin hannun sa, sam bayason jin k'ukan ta domin har kahon zuciyarsa yake jin zafi idan tana kuka.....



*JIGAWA*

Zaune suke gabadaya a falon gidan, baba, mama, Usman, Auwal, da Juwairiyya dukkaninsu 'ya'yye ne ga Raliya dake zaune kan kujera fes da ita, bazaka taba tunanin cewa tana da ciwon hauka ba sai dai halaiyen ta ya nuna, sosai suke kama dukkanin su tamk'ar an tsaga kara, sai dai Raliya tafi su kyau nisa ba kusa ba.

Muskutawa Aunty juwariyya tayi tace " ya Auwal, ya Usman ni a shawara ta mezai hana mu kaita asibitin a duba k'wak'walwarta a tabbatar da ainihin matsalar" ta karasa tana duban yayyen nata tare da iyayen ta.



Ya Auwal daya kasance babba ya fara magana kamar haka "Bamu ki taki ba juwairiyya amma, bazamu aiwatar da hakan ba sai da amincewar mama da baba" ya Auwal ya karasa cikin yanayin girmamawa wa iyayen sa.




Murmushi mama da baba, suka saki a tare, sun sani cewa 'ya'yansu na matuk'ar bin umarnin su, hakan baya rasa nasaba da irin jajircewa da suka yi wurin basu tarbiyya, hakan yasa yanzu suke cin moriyarsu duk da sunyi aure harda 'ya'ya amma yawanci duk abinda zasu yi sai da shawara da amincewar iyayensu...




Gyaran murya baba yayi, cikin dattako yace" Allah yayi muku albarka 'y'ay'a na gari, ita din kanwar ku ce, munyi muku izinin kaita domin duba lafiyar ta, Allah ya sa a dace, kuna tare da add'uar mu akodayaushe".




Cikin alfahari da iyayen su, suka hada baki Wurin fadin "Ameen ya Allah" kana suka mike hannun Raliya, Aunty juwairiyya tayi niyyar kamowa alamun ta mike ta kuwa boye hannun ta tana turo baki hadi da bata fuska, da kyar aka lallaba ta tashi, sai kuma ta ruga a guje ta fice haraban gidan, da gudu duk su ya Auwal suka bi bayanta, rikota suka yi suka shigar da ita cikin mota, ya Usman, da anty juwairiyya suka zaunan a kujerar baya Raliya a tsakiyar su, yayinda ya Auwal ya ja motar suka fice....




A hospital bayan su samu ganin babban likita, aka shigar da Raliya dakin za'a duba ta da kyar, bayan kamar awannin uku likita ya fito yana sharce gumi, yace su biyo shi office...




Numfashi doctor ya fesar domin al'amarin yayi matukar d'aure masa kai duk da yana fuskantar case masu yawa, amma wanna na daban ne. "Am... maganar gaskiya duk iya binciken mu bamu gano komai ba, haka result din ya nuna, duk da cewa alamun ciwon Hauka, am sorry to say ya bayyane a tare da ita, sai dai nayi matuk'ar mamakin ganin result d'inta, zan rubuta muku magani ku siya a gwada bata, bayan wasu lokuta ku dawo a sake duba ta, amma gaskiya bamu gano komai ba". Likitan ya fada yana rubutu kan farar takarda...




Cikin al'ajabi suke kallon doctor, sun ma kasa magana, daga karshe dai barin asibitin suka yi bayan sun biya kudin ganin likita da maganin.... Gani suke likitan bai iya aikin sa ba, hakan yasa suka je wani asibitin, duka dai Maganar iri daya ce, asibiti uku suka je duk abu daya ake fada musu...



Asanyaye suka dawo gida, suka sanar wa da iyayen su komai, sosai suma suka jajanta, har magariba suna kan tattauna maganar, bayan duk sunyi sallar magariba kowannensu ya nufi gidan shi bisa umarnin iyayen su....



*SOKOTO*

Rarrashen Nu'aiymah Papi yake fusk'ar cikin damuwa, kuka take sosai a dalilin fushin da Papi'nta ke yi da ita " it's ok my baby, papi ya daina fushi dake kinji?" Dif ta dauke kukan tana sauk'e sheshek'ar k'uka yayinda fuskar nan tayi jawur, ga majina kaca kaca a hancin ta, kamar kullum baya taba share mata majina da wani abu face da bakinsa yake zuke mata, wanna karon ma hak'ane bayan ya gama zuke mata ya tashi da ita a jikinta ya zubar kana ya kuskure bakinsa da ruwa ya dawo ya zauna, kan cinyar sa ya dora ta, ya fara bata danwak'en data kici tun d'azu, k'aka dake kallon su ta tabe baki hadi da yatsina fusk'a tace

"wai wanna kazantar badani ba, zuke majina da baki" ta fada tana kama haba


"Papi kaga kaka ko?"


Bubbuga bayanta yayi yace"don't mind kaka, she's jealous of you" Nu'aym yace yana sanya mata danwak'en a baki, amsa tayi tana murmushi hadi da yiwa k'aka gwalo.



Kaka dake kallon su, domin sam bata fahimci maganar su ba sai *kaka* data ji ya fada tace "in ba tsoro ba ku fada da yaran da kuka san ina ji mana, ni zaku nunawa karyar boko"



Shiru suka yi mata ya ciga'ba da bawa baby'nsa dan wake, sai data ce ta koshi ya bata ruwa a Kofi ta sha, tace "Papi kawo nima in baka kajii"

Ba musu yace "toh" murmushi dauke a fuskarsa. Dan waken ta sanya masa a baki ya k'uwa bud'e baki ya karba, sai ya kamo yan kananun yatsar ta ya tsotse man jan hannunta, sai ta kyalkyale dariya, data sake bashi sai ta sanya masa hannunta duka a baki ya tsotsa, ta kuwa sa dariya, haka ya dinga biyewa shiriritar ta har ya cinye sauran ya sha ruwa kana suka wanke hannun su da omo, kan tabarman suka dawo suka cigaba da hira, Nu'aiymah na jikinsa har ya fara jin saukar numfashin ta alamun tayi bacci

Kallonsa kaka tayi tace " 'yarka fa bata yi fitsari ba, kada ku kwanta ta tsula maka fitsari akatifa" kasancewar bata yarda ta kwana da kaka sai da Papi'n ta.



Kallon Nu'aiymah dake bacci hankali kwance ajikinsa yayi kana yace "eh idan zamu shiga daki, zan tashe ta tayi kafin mu kwanta, sannan ya d'ora da cewa kaka dan miko min zanin ki can na rufe jikin baby saboda sauro"


Ba musu kaka ta mika sa, sai daya tabattar jikin ta ya rufu yanda yake so, kana yace "wato kaka abinda ya dame ni shine Nu'aiymah ta fara tambayar wacece *mahaifiyarta* na sani cewa duk wani 'da a duniya dole ya nemi sanin mahaifan sa, ba wai ina bakin ciki bane da hakan, sanin kanmu ne cewa ban tsinci komai tare da baby face kwalin datake ciki ba, da ace na samu wani abu a tare da ita a lokacin, da ni da kaina zan fara neman mahaifan ta da dukkanin iyawata kafin ta girma, ina tsoron kada wata rana idan ta girma ta sake min wanna tambayar na *ina Mummy na*, ina jin tsoron ranar kaka wani amsa gareni dazan bata?"... Ya karasa idanun na tara k'wallan domin abinda yafi tsana a rayuwar yaga baby'n sa cikin damuwa bazai iya jurewa ba...



" Allahu akbar, tabbas iyaye daban suke, kuma dole zata sake neman mahaifiyar ta, tunda kaine a matsayin ubanta, kamar yadda muka binne wanna sirrin mu cigaba a haka, Allah ya iya mana ya kawo mana mafita" kaka fada tana kallon Nu'aym.



"Ameen kaka" yace yana k'ok'arin sake magana kawai yaji shaaaaaaaaaa Nu'aiymah na sakin fitsari, lumshe ido yayi dumin fitsarin na taba fatar jikinsa, dama yasan Zata iya yin fitsarin tunda ta sha ruwa da yawa yau...

"Ta saki ko? ai daman sai dana fada, sai shegen son shan ruwa, idan na yi magana ya zama laifi tunda ba'a taba yar gwal"

Bai kula kaka ba, domin bai ga abin fada ba acewar sa, daga ta yayi ya shafa mata ruwa a fuska, take ta bud'e idanunta tana kananun koke_koke alamun baccin bai ishe ta, "sorry! yanzu zaki koma bacci, kinga kin jika kayanki da fitsari bari na sanja miki" yace cikin rarrashi yayinda yake watsa mata ruwa a jikin....



wasu kayan ya sanja mata kana yakaita daki ya shiga lallaba ta babu jimawa tayi baccin ya fito cikin sanda domin tana jin ya fita itama Zata tashi, wani wanka ya sake ya sanja kaya kana suka yi sallama da kaka kowannensu ya nufi makwancinsa......



Gobe in sha zan sake baku sabon update da sannu zamu shiga cikin labarin...


Share fisabilillah


Comment


Vote


Editing is not allowedโŒ