15-16
by @nooriman
🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
Written by
Noor Eemaan
***
Wattpad
@NoorEemaan
Page 15-16
*JIGAWA*
Zaune Al'ameen, da Mariya suke kan dinning table suna breakfast cikin shigar al'farma. Dago kanta tayi a dame tace "haba Al'ameen, ya kamata ka rage damuwar da kake saka kanka a ciki zuwa yanzu fa, ka sani cewa damuwa baya gyara komai sai ma kara lalata abubuwa, ka duba fa ko abinci baka iya ci, rayuwa zata yu a haka?"
"Ki gafarceni Mariya, nasani cewa bana sauk'e dukkanin nauyi ki dake kaina a yanzu, na kasa jurewa ne, na kasa yarda cewa Raliya na cikin ciwon hauka, na kasa yarda cewa na rasa baby nah..." Yana kaiwa nan ya fashe da kuka, domin matuk'ar maganar matarsa Raliya da cikin jikinta daya rasa ne tofah baya iya jurewa, domin shi mai raunin ne a wanna bangaren.
Itama Mariya da idanunta suka ciko da kwallan tausayin mijinta tace "Na sani cewa da ciwo, rasa cikin da muka kwallafa rai a kansa, tabbas ina matuk'ar jin ciwo nima idan na tuna cewa kanwata(Raliya) na cikin halin ciwo, amma damuwa bazata kara mana komai ba face mu cigaba da add'ua akan Allah ya daidaita mana komai"
Numfashi mai zafi Al'ameen ya furzar kana yace "haka ne, nagode sosai da kulawarki uwargidana"
Wani fari Mariya tayi irin nasu na wayayyun mata tace "yanzu dai ka daure kaci abincin nan kada ka fita office haka ba komai cikin ka" ta fada cikin wata kissar ta wayayyun Mata.
Murmushi k'arfin hali ya saki kawai ya fara caccakan abincin domin bazan ce ci yake ba, bai wani taba da yawa ba, ya sha tea mai kauri daya ji su breavages(kayan shayi) kana ya mike yana goge bakin sa da tissue.
Mikewa itama Mariya tayi dauki da briefcase d'insa ta bi bayan sa har parking lot. Wata had'add'iyar mota kirar 4matic baka ya shiga, ajiye masa briefcase tayi a kujerar mai zaman banza kana ta rankwafo tace "Allah ya kiyaye ya bada sa'a sai ka dawo"
"Ameen ya Allah, nagode" ya fada hadi barin gidan a guje... Da kallo Mariya ta bi mijinta, soyaayyar sa na ratsa zuciyar ta, ajiyar zuciya ta sauke tana komawa cikin gidan murmushi d'auke a fuskar ta...
Al'ameen na tuki a nutse yayinda yake sauraran karatun qur'ani kirar Al ghamdi cikin suratul ma'ida yayinda yake bin karatun a hankali, har ya dan dota hanyar gidan su Raliya ya sake dawowa baya ya shiga layinsu domin so yake ya ganta ko zai sauki daga radadin dake damun zuciyar sa...
Kasancewar bazai dade ba yasashi barin motar sa a wajen gate din gidansu ya shiga ciki, a mutunci suka gaisa da mai gadi kana ya nufi cikin gidan....
Mama da baba ya tarar zaunen kasan centre carpet suna breakfast da kunun gyada da kosai sai kamshi mai dadi ke tashi... "Aminullah ne? maraba shigo" baba yace bayan ya amsa sallamar sa.
A nutse ya tsugunna yace "barka da safiya baba, barka da safiya mama kun tashi lafiya" a sake suka amsa tare.
"Bismillah, matso muyi Karin kumallo" Cewar baba.
Cikin kauna, kunya, da girmamawa surukan sa yace "Alhamdulillah, a koshe nake" sarai baba ya fahimce dalilin zuwan nasa, amma kasancewar shi mai kunya ya hanashi tambayar matar sa, gyaran murya baban yayi yace
"Aminullah shiga ciki, tana nan dakinta"
A kunyace ya mike yace "nagode baba, Allah Ya kara girma"
A nutse ya bud'e kofar dakinta ya shige, tana zaunen kan gado, gaba daya ta yayyaga kosan a kasa, hadi da zubar da kunun ta ko ina kasan tiles
Tausayin ta fall zuciyarsa yace "farincikina! Matso ga yayanki" Al'ameen yace yana ware mata hannun sa.
Shiru tayi tana kallon sa, kamar tana son tuno wani abu,... sai kuma ta fashe da dariya har da kwanciya kan gadon. Hawaye suka ciko idanun sa ya mayar, tsintsiya ya dauka ya tattare kosan data watsar hadi da goge kunun data zubar, domin yasan ta bata son kazanta ko kadan haka yasa shi gyara mata domin ta ji dadin zaman dakin, a hankali rayuwar da suka yi cikin farincikin da kauna a gidan sa ta shiga dawo masa...
Kan gadon inda take zaune ya hayo hadi da sanyata cikin jikin sa, yakushi hadi da cizo take kai masa ta ko ina. sai dai sam yaki sakin ta, sun kai mintuna goma sha biyar a haka kana ta yi shiru tana ta zare idanunta...
"Ina kaunar ki sosai Raliya, Allah ya baki lafiya, nayi kewar baby nah, ban san tayaya muka rasa ta ba, ke kadai ce zaki iya bamu amsar tayaya muka rasa baby da muka kwallafa rai a k'anta...."
Haka dai ya cigaba da maganarsa shi kadai, domin bata sam yana yi ba, karshe dai bacci ya d'auke ta, kwantar da ita yayi kan gado yana jin zuciyar sa na dan yi masa sanyi, blanket ya rufa mata, sai a lokacin ya ga ashe sha dayan tayi bai sani ba.
Fitowa yayi ya tarar da ba kowa a falon, hakan yayi masa dadi domin daya sha kunya kam, yana k'ok'arin fita daga gidan suka gaisa da ya Auwal amininsa cikin mutunta juna, sun dan bata lokaci suna hira duka dai kan lalurar Raliya kana suna yi sallama da juna...
*SOKOTO*
"Wai nikam Nu'aiymahtou haka nace ki tayani aiki ne? Kibar min wanke_wanke na zan karasa, yo Allah na tuba ai barna kike ba aiki ba" kaka take fama da hura wata tace da Nu'aiymah.
"Toh ki barni na wanke kwano na da na Papi nah" tace tana tura baki.
"Papo ba Papi ba, daman kuna da kwano a gidannan? Ai kwanukan gidanan na kowa ne, kinga tun muna shaida juna ki tashi, gaba daya kin jika kayanki da ruwa gaki da shegen jin sanyi, da kin fara tari da mura ki samu a damuwa ki hana mu bacci, ko nace ki hana uban ki bacci tunda tare kuke kwana nidai bacci na zanyi har da munshari ehe yarinya"
Suna cikin wanna dramar Nu'aym yayi sallama, da gudu tabar wanke _wanken ta nufi Nu'aym tana cewa "oyoyo Papi nah!" Cak ya daga ta sama yana juyi da ita hadi da dariya, manna ta yayi da jikin sa, ya bata rai hadi da cewa.....✍️
Share✔
Comment✔
Vote✔
Edit❌