17-18
by @nooriman
🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
Written by
Noor Eemaan
***
Wattpad
@NoorEemaan
Godiya mara adadi ga masu bibiyar novels dina da wadanda nasani da ma wadanda ban sani ba, ina godiya sosai Alkhairi Allah ya kaimu a duk inda kuke masoyana❤
Page 17-18
........"Baby bakya jin magana ko? Bana hana ki wasan ruwan ba?"
"Gaya mata dai, ai ni bata jin magana ta Saboda ni ba Papi'n ta bane, tun dazu nake gaya mata taki ji" kaka ta katse masa sauran maganar sa.
"Kayi hak'uri Papi nah, na daina kaji karka yi fushi dani kaka ta mun dariya" domin idan akwai abinda bata so to bacin ran Nu'aym ne.
Dariya taso ba shi saboda maganar ta ta karshe, "promise bazaki sake ba?" Ya tambayeta yana kallonta.
"Yes Papi, kawo hannun ka mu kulla ma" ta fada cikin yarinta tana bashi karamin yatsar ta wai su kulla yanda dai yan yara kan yi, tsad'add'en murmushi ya sakar mata kana ya bata karamin yatsar sa suka kulla.
Sauk'e ta yayi yace " maza dauko wata rigar na sanja miki kada sanyi ya shige ki, na siyo miki chocolates da ice cream"
"Yeeeehhyy" tace tana yin daki da gudu cikin murna ta dauko kayan ya sanja mata kana ya bud'e ledan.
Fan ice ne dan karamin robar nan dabai fi dari da ashiri zuwa da hamsi ba, ya bude mata hadi da sanya mata dan cokalin nan ciki. Ai yawunta dilala yake Saboda kwadayi sai chocolate masu sauki kudi kwaya uku.
"Allah ya sauwake maka, gaba daya ka koya mata shan zaki, kadai yi a hankali 'ya mace ce dai ehe..."
Nama balangun daya ajiye a tsakiyan su yasa ta yi shiru da sauran maganar ta kana ta hadiye miyau tace "A'a dan nan, yau dai kace dadi zamu ci, da alama aiki yayi kyau"
Dariya sa ya boye yace "Alhamdulillah kaka, yau kam na samu dubu biyu sak'amak'on wani aiki dana yiwa wani mutun ya bani kyauta" Nu'aym fada yana sanya wa Nu'aiymah nama yanka daya a bakinta.
"Masha Allah, Allah yayi masa Albarka, kaima Allah ya bud'a maka yanda kake k'ok'arin faranta mana, hakika baka baro komai daga cikin halaiyan mahaifin ka, kuma dana Ahmadu ba Allah ya jikan shi " kaka tace tana kai nama yanka har hudu bakinta.
"Kai papi kaga kaka tasa nama da yawa a baki"
Dariyar da yake k'ok'arin rikewa ce ta subuce masa, kullum kaka da salon datake yi wurin basu dariya.
Bakin kaka cike da nama tace "kaji min jar'irar 'ya daya siyo miki kayan yan gayun ki nayi magana ne? Shine yanzu kike mun sa ido, toh yanda kike takamar ubanki ne toh nima jika na ne, kin ga k'uwa dole naci iya son raina"
"Kaka! Kaka!!Kaka!!!" Nu'aym ya kira ta sau uku cikin gajiyawa da maganar ta.
"Meye toh, wato kada nayi magana ko, ita data yi magana meka ce?" Tace tana sake kai wani naman bakin ta.
"Ji yanda kikewa Baby magana kamar wata babba fa, yarinyar ce ki dinga yi mata a hankali banason bacin ranta"
"Iyeeh sannu uban zamanin, toh wallahi sai dai superglue zaka manna min a baki amma matuk'ar na gani sai na tanka yawwa" tace tana tura daurin ta gaban goshi.... Haka dai suka cigaba da hirar har suka cinye naman wanda yanka d'aya ya samu yaci, bai kuma damu ba domin Saboda farincikin su ya siya.....
*BAYAN SHEKARU HUDU*
Zuwa yanzu baby Nu'aiymah nada shekaru goma cif a duniya ba laifi ta dan yi wayo da girma kadan, wanda yayi daidai da gama karatun Nu'aym har an tura su serving (bautar kasa) inda gobe zai tafi sai dai basu yi maganar gaban Nu'aiymah ba, domin matuk'ar taji tofah bazasu yi bacci yau ba...
Daddare suna zaune kan tabarman Nu'aiymah na kwance a jikin sa, domin tana da sauri bacci idan tayi dadewar duniya to ta kai tara bata yi bacci ba. Nasiha hadi da add'uar kaka ke masa yana amsawa,...
ajiyar zuciya ya sauk'e yace "kaka ki lallaba min Baby please, nasan zata sha kuka idan taga bana nan gobe, dole zan yi fitar asuba domin bazan juri ganin tana kuka ba....
Murmushi kaka tayi tace " in sha Allah zan kula da ita karka ji komai, kuka kam dole ne zata yi shi, amma da an kwana biyu zata saba ne, ni dai fatana ka kula ka rike addinin ka kaji ko?"
"In sha Allah kaka zan kula nagode "
Haka suka cigaba da hira kewar juna har karfe goma sha d'aya na dare kana ya d'auki Nu'aiymah ya kaita dakin kaka a hank'ali domin tunda takai shekaru goma suka daina kwana tare, duk da cikin wayo yake samu ya gudo nasa dakin kasancewar har yanzu bata yarda, sai yayi kamar a dakin kaka zai kwana sai tayi nisa a bacci sai ya lallaba ya fito
Idan ta farka da asuba bata ganshi ba daya dawo daga sallar asuba tayi masa korafin bata gan shi ba, sai yayi mata wayon masallaci ya tafi...
Haka ya koma dakinsa ya kwanta tunani hadi da kewar su baby'nsa har ya fara kama shi, karshe dai ya hakur'a yana lumshe ido fatan sa bacci ya d'auke shi Saboda ya tashi da wuri....✍️
Kuyi haku'ri ya jama'a, wallahi duk yanda naso baku pages masu yawa akan bai samu ba sakamakon uzirori dasuka min yawa, in sha Allah a page 19-20 zan baku masu yawa both papi ne da kyautar koda.
Comment✔
Share✔
Vote✔
Edit❌