39-40
by @nooriman
🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
*WATTPAD*
@NoorEemaan
EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌
39-40
............... Wata dariya suka sanya, Nu'aiymah har da kwallan mugun ta, kaka rigima, toh meƴe abin shiga dak'i har da sa key? Bayan Nu'aym ya gama cin egg roll din shi, ya ce ya ishe shi, kana Nu'aymah ta shiga dakin ta domin ta sanja kayanta, wasu riga da skirt na wani material mai taushi ta sanya daƴa fidda hadaddiyar surar ta, dankwalin ta yana a k'anta, domin tasan idan ma bata d'aura ba papi sai ya sa ta d'aura di'n, kasancewar bata son daura dankwali...
Turare ta fesa sama sama domin Nu'aiymah akwai son k'amshi, man zafin da take shafawa papi ta dauka kan dressing mirrow dinta ta fito, hakan yayi daidai da bud'e kofar da kaka tayi, wata dariya ce ta sake tahowa Nu'aiymah tuna abinda kaka tayi dazu, cikin tsokana tace
"kaka kin fito"
Bata rai kaka tayi tace "toh bazan fito ba? Kaji min ja'irar yarinya, bayan kin gama min rowa zaki min magana, yanzu dan baki da kirki 'yar nan akwai abin dadin nan amma bakya siyo min?".
Gimtse dariyar ta tayi, tasan idan bata amsawa kaka ba, tofah yau ta dinga mita kenan har dare, dan haka tace
"Toh kaka zan dinga siyo miki kullum kinji"
Washe baki kaka tayi kana tace "ko ke fa 'yar albarka" ta karasa tana shiga toilet.
Da kallo Nu'aym ya bi kaka yana murmushi, a ransa yana add'uar Allah ya kara wa kaka tsahon rai domin ita din farincikin su ce.....
"Papi bari na shafa maka man ka, na manta da safe"
"Ai dole ki manta da safe, baby rigima" inji Nu'aym idanun sa kafe k'anta, har yau ya kasa yarda cewa baby'nsa dake jaririya ce ta dawo budurwa mai kyawun gaske....
Boyayyen ajiyar zuciya ya sauke, ya lumshe idanun sa, kana ya ware su kan fusk'ar ta... Tana tsugunne gaban sa tana shafa masa man zafin, bud'e kofar bandakin da kaka tayi ya sanya shi dauke idanun sa... Yace "baby kinyi sallah kuwa?"
Kallon shi tayi tace "Papi nayi tun a masallacin school dinmu"
Jinjina kai yayi, ta cigaba da shafa masa man ta na zuba masa surutu, nan dai suka cigaba da Hirar su, harda da kaka dake basu labari suna ta dariya, bare ma Nu'aiymah har da kwalla, Nu'aym kam sai dai yayi murmushi.....
****** ******* ******
Bayan sati biyu Nu'aiym ya koma bakin aikinsa cike da kewar su.... Kamar koyaushe Nu'aiymah tayi kuka, hakan ke kara karya zuciyar Nu'aym.
Ɓabban burin shi yanzu ya siya musu gida a jigawan, domin su koma kusa dashi hankalin shi zai fi kwanciya idan yana ganin su tare a muhalli daya.
Bayan kwana biyar da tafiyar Nu'aym, kaka na zaune a parlour da misalin karfe sha biyu na rana tana kallon film a tashar MBC ACTION.
Wani film na fada suke haskowa, kaka fadi take "A'a a'a kai wannan mutanen baku da mutunci wallahi, sai fada kuke kuna zub da jini abu bai yi k'yau ba" wani ihu ta saki ganin an caka wa wani wuka tace
"karka kashe shi, karka kashe yi, wayyo! Kaga mutane masu zuciyar dutse kamar na firauna" abin dariya har rufe fuska kaka keyi, wai kada ta ga yanda aka cake wani da wuka...
Ringing d'in wayar ta ya dauke mata hankali daga kallon fim din da take, daukan wayar tayi, wanda yanzu Nu'aym ya sanja mata zuwa *infinix smart5* a kunne ta kara bayan ta daga tace
"assalama alaykum"
Daga dayan bangaren habib Husain ya gyara zaman sa kana cikin ladabi yace
"kaka ina wuni"
"Lafiya lau, manyan kalau? Sai dai ban shaida mai magana ba"
"Lafiya kalau kaka, sunana Habib Husain, Nu'aiymah ce ta bani number'n ki, na hadu ta ita lokacin data dawo daga makaranta, ban samu kira bane sai yau"
"Ai yo dan albarka, tabbas Nu'aiymahtou jika ta ce, Nu'aiymahtou! Nu'aiymahtou!! Kizo za a yi magana dake" kaka tace cikin daga murya fusk'ar ta a washe.
Nu'aiymah dake kitchen tana hada masu lunch(abincin rana) ta zo falon cikin sauri, a tunanin ta Papi ne, domin ita ta manta da wani shafi na Habib Husain
"Kaka Papi ne?" Tace bayan ta shigo falon
"A'a ba shine bane, karbi katinsa na tafiya a banza"
Amsa tayi ta fito waje, tana tunanin waye?
"Assalama alaykum" tace cikin zazzak'ar muryar ta.
"Wa'alaikumu salam mai kyau nah" cewar Habib Husain cikin taushin murya.
Take ta fahimci mai magana, a fili tace "ina wuni"
"Lafiya lau mai kyau nah, ya kike haba gaɓa daya kin manta dani ko? Gashi ni kin sace zuciya ta, kin hana ta sukuni, tun daga ranar dana ganki kullum cikin begen ki nake, na azabtu da rashin ko da jin muryar ki ne, amma yanzu naji sanyi a raina, fatan kina cikin koshin lafiya?" Ya fada cikin iyakar gaskiyar sa kana cikin kulawa.
Lumshe lumsasun idanunta tayi, masu kama da mai jin bacci, wani yanayi taji a jikinta, domin kalaman sa suka tsaru sosai a kunnuwan ta.
Ware idanun tayi tace "Alhamdulillah ina lafiya"
"Masha Allah naji dadi jin haƙan mai kyau nah, gaskiya naji dadi yanda kaka ta amsa gaisuwata"
Murmushi Nu'aiymah tayi, ba tare da tace komai ba.
"Ki sa min rana mai kyau nah domin in zo gareki, idanuna cike suke da kwadayin ganin ki, please and please karki ce min a'a " ya karasa cikin wani salo mai tafiya da zuciyar wacce aka yiwa.
Murmushi ya subuce mata, ba tare da sani ba, a fili tace "ni ban sani ba, duk ranar da ka so zuwa"
Cikin jin dadi Habib Husain yace "wow! Nagode da wanna damar da kika bani, in sha Allah zaki iya ganin na akodayaushe, bye take care, I Miss you" kit ya kashe kiran.
Ajiyar zuciya Nu'aiymah tana jin wani yanayi a tare da ita, kaf din rayuwar ta babu namijin data saba dashi, sannan yake gaya mata magana mai dadi sama Papi'n ta, amma yau da Habib Husain ya gaya mata kalamai, wanda ba wai tafi jin dadin na Husain din bane fiye da na papi, a'a kawai salon sa ne ya sanya kalaman suka tsaru har suka samu muhallin zama a zuciyar ta...
Falon ta koma domin mayar wa kaka wayar ta, bayan ta duba girkin ta.
"Kaka ga wayar"
Ba tare da kaka ta karbi wayar ba tace "ke! 'yar nan, dama kinyi saurayi ba labari? Oh duniya yarinyar nan akwai ki da zurfin ciki, yanzu da bai kira waya ta ba, bazan sani ba"
Turo baki Nu'aiymah tayi tace "kaka ni fa ba saurayina bane"
"Kaji min ja'ira, idan ba saurayin ki bane, meye na bashi lamba ta? Kinga banason iyayi idan ma kina so, ai ba wani abu bane, daga jin muryar yaron nasan yana da kirki, dan haƙa ina miki add'uar Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ai wanna abin farinciki ne"
"Nifa kaka ba fa cewa yayi yana sona ba, kawai ranar nan ne, na dawo daga makaranta shine ya biyo ni, daya matsa min da yawa shine na bashi lambar ki" Nu'aiymah ta fada tana Turo bakin shagwa'ba
Dariya kaka tayi tace "yaro yaro ne, yaro man kaza"
Nu'aiymah bata fahimci maganar kaka ba hakan yasa tace "kaka kin ji wai zai zo"
"Ai ba matsala, Allah ya kawo shi lafiya, yaushe zai zo di'n"
" kaka bai fada min ba"
"Toh ai shikenan, yanmmatan kaka, wai yarinya ta girma, mun kusa samun suriki" ƙaka ta faɗa a zolaye.
"Kai kaka dan Allah faa" Nu'aiymah tace cikin kunya tana barin dakin...
Da kallo kaka ta bi ta tana Dariya, ita kam zata so Nu'aiymah tayi aure a kananun shekarun ta....
Bayan kwana uku, da magriba Nu'aiymah da kaka na zauna kan sallaya sanye da hijab da alama sallar suka gamawa iddar wa, da carbi a hannu su suna ja. Suna a haka wayar kaka ta fara ringing, alamun ana kira, kasancewar wayar na gefen Nu'aiymah ya sanya ta ga sunan mai kiran kamar yanda tayi saving da * Ya Habib Husain.....
Manage please🙏
Afuwan habibtie's in sha Allah daga yanzu ranakun posting sun dawo sau uku a sati, domin wallahi busy da nake ciki ya sanya hakan, bana da lokaci kwata kwata wallahi, ku tayani add'ua kan abinda nake yi yanzu, Allah ya bani sa'a.
ina fatan zaku min haku'ri... Ranakun posting din sune kamar haka monday, Thursday, Sunday. Amma matuk'ar na samu lokaci a sauran ranakun da ban ambata ba, toh zaku iya ganin update, amma kusa a ranku cewa ranakun dana ambata wato litinin, alhamsi, da lahadi suna ranakun da tabbas zaku ga posting.
Ngd sosai da kauna da kuke nunawa books dina, ku sani a addu'oi'n ku👏 Noor na muku sahihiyar kauna💞
#Share
#Comment
#Vote