49-50
by @nooriman
🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
*WATTPAD*
@NoorEemaan
EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌
Page 49-50
........Cikin sauri kana cikin girmamawa Habib Husain ya ƙatse shi ɗa cewa "kayi haku'ri Papi, wallahi da gaske ina son ƴarka da aure, kuma zan iya jira ta gama karatun sai ayi auren mu dan Allah ka amin....."
Tamk'ar saukar dalma haka yaji kalaman Habib Husain din, cikin kakausar murya yace "zan maimaitawa maka a karo na biyu, stay away from my daughter, bazan baka ita ba, idan na sake ganin ka a kofar gidanan or anywhere close to my daughter wallahi bazaka taba manta abinda zan maka ba"
Nu'aym na gama fadin haka ya shige cikin gidan a haukace...
Nu'aiymah na tsaye a dan haraban gidan tana sharan hawaye, Yayinda idanun ta ke fa kan gate din shigowa....
Ga kaka nata tambayar ta meya faru amma ta kasa magana sai hawaye da take ta faman share wa, a yanayin da ta ga Papi ya shigo ya kara tsoratata, cikin sauri ta nufi bayan kaka tana kara sautin k'ukan ta, domin a tunanin ta dukan ta zai yi.....
"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un! Miye haka wai? Kai Nu'aymu aljanu ne suka shige ƙa ne? Ka wani shigo kamar zaka tashi gidan gaba daya" kaka ta fada cikin dakewa amma tsoro ne fall cikin ta, domin duk wanda yaga yanayin Nu'aym din dole ya tsorata.
Bai kula kaka ba, ya zo har bayanta ya zaro Nu'aiymah data makalkale kakan, Sosai ta kara sautin kukan ta, abinka da farar mace gaba daya fuskar ta ta dawo jajur kamar tumatir...
Da hannu daya ya rike ta, kana ya daga dayan hannu zai wanke mata mari, sai kuma ya tsaya Cak! da hannun sa yana Murza wa
Nu'aiymah kuwa kamkame jikinta tayi hadi da runtse idanun ta, tana jiran saukan mari, ganin bai mareta ba, ya sanya ta fara bude Idanunta masu cike da hawaye, hade ido tayi dashi ta ƴi saurin sauke Idanunta kasa, sak'amak'on wani tashin hankali da take hangowa a idanun Papi'n nata....
Cikin fitar hayyaci ya dora hannunwan sa ɗuƙa kan kafadunta ya girgiza ta da karfi, idanunsa ya sanya cikin nata yace
"Waye shi!" a kausashe
Shiru tayi tana kuka kasa² kara jijigata yayi yace
"nace waye shi?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta karo sautin k'ukan ta, hannunsa daya ya cire kan kafadunta, ya hade babban dan yatsar sa data tsakiya ya dan harbe ta a kumatu, kifkifta Idanunta tayi, tana sakin shesheka kukan...
Nace "waye shi?" Ya kara tambayar ta.
Cikin rawar murya murya tace "y...ya Habib Husain ne?"
Wanna karon labb'anta ya harba yace "Idan kika ƙara ce masa yaya sai na zane ki"
"Nace waye shi? Kuma karki mun kuka"
"Ha....Ha...bib...Hu...sain ne" tace tana danne kukan ta.
"Good! Meya zo yi wajen ki?"
"Wai wai yace yana sona ne " ta fada gwanin tausayi.
Wani uban kishi ne ya tokare shi, cikin wata murya yace
"uhm! Kina son sa kema?"
Shiru tayi Hawaye na zuba a Idanunta.
"I said kema kina son shi ne?" Ya kara fada cikin daga murya...
"A.....a....a'a" ta fada cikin wata murya dake rawa sosai kana a cakude da kuka.
"Baby tell me nawa kike da har zaki fara zance? As small as you are kin fara sauraran namiji? Huh! Me nace miki kwanaki?" Ya fada cikin zallan kishi daya bayyana a muryar sa, sai dai Nu'aiymah sam bata fahimta, domin akwai ƴarinta a tare da ita.
"Cewa kayi karatu kake so inyi" ta fada gwanin tausayi.
"Kenan kin daina jin magana ta shiyasa kika fara bijirewa umarnin na, gayamin"
Nu'aiymah zata yi magana kaka dake gefe tun dazu ta kafa musu ido kamar ta samu Tv tace "yau naga ikon Allah! Miye yake damun ka ne d'an nan? Yanzu Nu'aiymahtou'n ce bata isa zance ba, ko a kauye irinta na da 'ya'ya uku ma, miye dan tayi zancen ko kana nufin har abada bazata yi aure ba? anan zata zauna, ko wani uba idan 'yarsa ta kai minzanin auren ya kuma samu suruki na gari abin farinciki ne, amma banda kai, yaron nan dan kirki ne har nan yazo ya tsugunna ya gaishe ni, wanna abin farincikin ne, ace 'yarka ta samu abokin rayuwa na gari"
Tamkar saukan tafashashen ruwa a jikin sa haka ya ji saukar kalaman kaka, wanda ya ƴi nuni da cewa ba yau ɓane farkon zuwan Husain din ba....
Ganin kaka kara bata masa rai take yasanya shi cewa " A enough please kaka! a enough! Baby 'yata ce, na kuma ce bana son tayi zance yanzu, karatu zata yi, sannan nan ba kauye bane da zaki je sa'aninta sunyi aure, bana son ganin baby da ko wani da namiji! Nace bana so! Idan bazaki iya kular min da ita ba, idan kuma bazaki iya hanata sauraran ko wani da namiji ba, toh wallahi zan bayar da ita Jigawa, zan tafi da ita Jigawa domin na kula da 'yata".....
Ya fada cikin rawar murya kana ya ɓar gidan, domin baya son ya taba jikin Nu'aiymah ko kadan, idan ba fita yayi ba, zai iya dukan ta, wanda zai yi nadama mai tarin yawa...
Zubewa Nu'aiymah tayi a kasa tana kuka sosai, idan akwai abinda tafi tsoro a duniya toh fushin Papi'n ta ne, sam bata kaunar bacin ransa...
A hankali kaka ta karaso wajen Nu'aiymah ta daga ta suka shige falo, kan kujera suka zauna Yayinda Nu'aiymah ta kwantar da kanta kan cinyar kaka tana cigaba da rera kukanta.
Kaka an nutsu, yau kam ba rikici, sosai ta ke fassara kalaman Nu'aym din kashi² a matsayin ta na babba ta fahimci wasu abubuwan daga kalaman Nu'aym din, ita kam ba zata so Nu'aiymah tayi kukan maraici ba, sam bata so Nu'aiymah ta san cewa su din ba ahalin ta bane, bazata so farinciki su ya yanke ɓa, sai dai ta lura Nu'aym ya dauko hanyar da zai sa Nu'aiymah ta fahimci cewa ba shi ne ubanta, ba tare da yasan cewa ya fara yin hakan ba, bubbuga bayan Nu'aymah ta fara yi alamun lallashin, da tunanin idan Nu'aym din ya dawo zasu yi magana.....
Bangaren Nu'aym kuwa wani wajen shakatawa ya nufa, VIP ya nufa domin baya son hayaniya a halin da yake ciki, sosai yake kokarin controlling temper d'insa, wanda kaso arba'in na cikin fushi da damuwar sa ya gushe, sai ɗai daya runtse idanun sa babu abinda yake hangowa sai baby'n sa tare da Husain tana sakar masa ƙƴaƙƴawawan murmushin ta....
Sai karfe tara ya bar wajen ya nufi gida, a keke napep ya tafi, dama bai fito da lifan din sa ba, babu jimawa ya iso gidan....
Zaune ya tarar dasu kan sallaya a dan farfajiyar gidan sunyi shiru, wani tausayin su ne ya dake sa, domin yasan cewa rashin dawowar sa ya sanya su shiga wanna yanayin.
Dauke kai yayi kamar bai gan su ba ya nufi dakin sa... Kuka Nu'aiymah ta fashe dashi, ganin bai kula su ba...
Kaka tace "yi Shiru abin ki, zai sauko kinji, tafi dak'i ki kwanta, tunda ya dawo Alhamdulillah, zuwa gobe zai sauko kinji ƙo" kaka ta fada cikin lallashi ta nufi dakin ta, duk da tasan muyuwan ci ne Nu'aym ya hakura a gobe, tabbas ta san halin jikan nata, ba shida hakuri idan ransa ya baci....
Zaman wajen Nu'aiymah ta cigaba tayi tana hawaye Yayinda take tunanin yanda zata je wajen Papi domin tsoro take ji, can ta tuna da wayar sa daya bata dazu da ƴamma, mikewa tayi ta linke sallayan kana ta nufi parlour, ajiye sallayan tayi kan kujera kana ta dauki wayar ta fita.... ta zo daidai dakin Nu'aym Nepa suka dawo da wuta, a hankali ta murda kofar dakin ta shige bakin ta dauke da sallama da amon sa ke cike da kuka......
Zaune yake daga shi sai wando 3quarter na jeans, hadi da bakin singlet da alama wanka yayi, cikin dar²
tace "p...pa...pi ga wayar ka"
Wani uban harara ya jefa mata kana ya haura gadon yana mai juya mata baya, kuka sosai ta sakar masa har da dirdire kafafu, pillow ya sanya ya toshe kunnewansa........✍️
Thank you for reading my novel Papi ne!
Share fisabilillah
Comment
Vote
Show some love😍 by following me on wattpad @NoorEemaan
Noor loves you all
***