53-54
by @nooriman
🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
*WATTPAD*
@NoorEemaan
EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌
*ban tace ba (editing) idan kun ga typing error kuyi hakuri🤒*
Page 53-54
.......Babu jimawa NU'AIYM ya shigo ciƙin kananun ƙaya masu masifar kƴau ɗa alama wanka ƴayi....
"Sannu kinji baby'n papi'n ta" ƴa faɗa yana saƙe fita, bai jima ba ya shigo ɗa tray mai ɗauke ɗa tea mai kauri, sai golden yam hadi da kawai....
Mikar ɗa ita zaune ƴayi, bayan ya ajiƴe tray din a gefe, kana ya sake dauko tray din ya dora kan cinyar sa, "Haaaaa!' yace yana kai yanka daya na golden yam din bakinta, ciƙin shagwaɓa tace "A'aaaaaa papi bazan ci ba, bakina daci" ta faɗa tana ɓata fuska...
" ki sha ko tea ne, domin idan muƙa je hospital kaɗa liƙita yace ki ci abinci kafin ayi allura" Nu'aym y faɗa cikin lallaɓawa..
"kai papi allura faaaaa, ni ni ni ban so" ta faɗa har hawaye na ciko idanun ta, domin ta ƙi jinin allura.
Ciƙin wayo yace "toh shikenan ki sha tea din ƙawai, iɗan yaso sai ƴa duba ki kinji"
"toh papi" tace tana karban mug din hannun sa bata wani sha da yawa ba, ta dire.
"taso mu tafi"
"a'aaaa" tace a shagwaɓe, tana makale ƙafada.
murmushi ƴaƴi yace "baby rigima menene?"
"ni ɗai kaci abinci kafin mu tafi, zaka ji ƴunwa"
bai musa ba, yaci yanka hudu na doƴar kana ya sha ragowar tea din data rage, hannun ta ya riko suƙa fito waje...
"papi mu hau keke napep, kada mu hau machine, zan ji kamar zan faɗi ne"
"Toh! yanɗa ƙiƙe so haka za aƴi"
********************
Bayan sun je asiɓiti basu wani tarar ɗa layi ba, bayan liƙita ya dubata yace sai an yi mata allura domin zazzabi yayi sauran sauka, nan fa shagwaɓaɓiƴƴar ta fara kuka ita baza a yi mata allura ba.
Ɗa kƴar papi ya lallaba ta, amma ɗa nurse din ta nufo jikinta da alluran sai ta zille, nan nurse din tace Nu'aiym ya rike ta sosai gudun ƙada garin wanna zillewar tata a samu matsala....
Nan fa Nu'aym ya riketa sosai ko motsi ta kasayi har aka yi nasaran yi mata alluran, nurse din sai tsokanar ta take...
Bayan sun biya hospital bill aka basu magunguna suka nufo gida, a bakin layin su mai adaidaita sahun ya tsaya, dama kafin ya dauke su yace baya shiga cikin layi....
sun dan yi tafiya kaɗan Nu'aiymah ta tsaya tace "Allah papiiiiii na gaji" ta faɗa kamar zata saki kuka, ɗama tunɗa aka mata alluran take jin wani jiri_jiri.
hannunta ya saki yace "toh hau bayana in goƴa ki" mutuniyar ba kunya ta dane ɓayan papinta suka je har giɗa, nan kallo ya dawo kansu, masu kus kus nayi....
Kaka ma salati ta saki a lokacin ɗata gan su tace "oh yaran nan, yanzu babu kunƴa katuwa ɗake kika hau baya, kamar jaririƴar goƴe"
"toh ai ɓayan papi na ne" NU'AIYMAH ta fada.
"eh na sani ai, aku mai magana, wato bakin ki ya fara dawowa ai"
Murmushi Nu'aiym ƴayi, ya sauke baby a hankali ya sauke ta kan babban sallayan ɗake shumfuɗe a haraban gidan....
parlour ya nufa ya bude madaidaicin firji ya dauko table water mara sanyi, nan ya balla magunguna ya bata ta sha, bayan ta sha babu jimawa kuwa ta bingile ɗa bacci ɗa bata yi ba jiƴa.
Mikewa ƴayi ya dauketa zuwa ɗakin ta ya kwantar kana ya fito, yana shirin shiga ɗakin sa domin ƴa kwanta, saboɗa sosai bacci ke cike a idanun sa...
kaka ɗake zaune ƙan sallayan tace "zo! ɗanan"
ƁA musu ƴa dawo ƴa zauna, a nutse kamar ba kaka mai rikici ba tace "Ɗanan kana lura da matsalan ɗa kake son kowa mana kuwa? kasan cewa yarinƴar kai taƙe kallo a matsayin asalin ubanta, sannan ɗuƙ wani uba na gari iɗan ƴarsa ta samu kamili mutum dake son ƴarsa abin farin ciki ne a gare shi, toh ƴanzu ɗaƙa fara wanna halin tofah babu tamtama Nu'aiymahtou zata fara zurfafa tunani, kila har ta gano sirrin boye, wanda haƙan na nufin katsewar farincikin mu gaba ɗaƴa, na kuma san ba zaka so haƙan ba, dan haƙa ka bi komai a sannu kaji ko?"
Ajiƴar zuciƴa ƴa sauƙe, bai ce ƙomai ba, bai san cewa raunin ɗa ƴaƙe dashi akan baby'n tasa har ta kai ƙaƙa ta fahimta, domin duƙ ɗa bata fito fili ta faɗa ba, amma taɓɓas ya san ta gane wasu abubuwan, ya kuma san kalaman ta ɓabu karya a cikin sa, amma ya zai ƴi ɓaƴa iƴa controlling ƙansa iɗan yaga Nu'aiymah'nsa tare ɗa wani ɗa namiji.....
"nagoɗe kaka" yace yana shiga ɗakin sa, da kallo tausayi ta bishi, tana musu fatan alkhairi gaba daƴa....
***********************
JIGAWA
BAYAN WATANIN BIƳAR
"malam kaga yarinyar nan tun safe na lura jikin ta ba ɗaɗi, ga kuma taki cin abincin, ina tamtama ɗai kamar nakuda take ya kamata........"
Ihun Raliƴa ya hana mama karasa maganar ta, haƙan ƴasa suka nufi dakin a 360.......
muje zuwa fans🔥
SHARE
COMMENT
VOTE
NOOR
EMAAN
***