Papi ne!

55-56

by @nooriman

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓







*WATTPAD*

@NoorEemaan












EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌






Page 55_56





.........kwance Suka tarar da ita ruwan paya ya fashe, sai juye² take, duk da halin tabin k'wak'walwar da take ciki hakan bai hanata jin zafin nakuda ba...







Cikin dan rud'ewa mama tace "malam haihuwar ce ta zo fa"






Cikin sauri malam baba yace "toh! toh!! bara na Kira wayar yaran nan su zo muje asibiti"






Mama bata amsa ba, sai faman sannu² take wa Raliya dake faman fisge_fisge cikin tsananin jin zafi....







Can mama ta dago tace "malam ka Kira shi yaron nan Al'ameen domin yafi kusa, kuma ina kyautata zaton bai fita daga gida ba"







Ba bata lokaci malam baba ya Kira Al'ameen ya sanar dashi......






Bangaren Al'ameen kuwa daidai lokacin yana zaune a dinning area tare da uwar gidan sa Mariya suna having breakfast.





Bayan malam baba ya Kira shi, a sukwane ya mike yayin da gaban sa ya Fadi, mukullin mota ya dauka kana yayi hanyar waje da gudu² sauri²...






Cikin sauri itama mariya ta bi bayan shi tana tambayar sa lafiya? Ba tare da ya tsaya ba ya bata amsa...





Itama hankalin ta a tashe ta bi bayan shi suka bar gidan a guje...





Bayan sun isa gidan su Raliya, Al'ameen da kan shi ya shiga ciki ya dauko Raliya kana ya shimfida ta a bayan mota, ganin yadda take fisge² hadi da son guduwa ya sanya Al'ameen yace mariya ta koma bayan mota ta rike ta, ba musu mariya ta yi yadda yace, da haka Suka bar gidan....







Bangaren malam baba kuwa Yaya Auwal, da Yaya Usman, hadi da yayar Raliya mace ya Kira ya sanar musu, kana yace su ma asibiti suka nufa, dan haka su hadu a can....







Nan malam baba da mama suka fada motar gidan driver ya ja suka nufi asibitin.





*HOSPITAL*



Kowa ka gani hankalin shi a tashe yake, domin kusan 2hours yanzu doctor's da suka shigar da ita basu fito ba....





Bare ma Al'ameen sosai fuskar sa ke fitar da damuwa, ga gaban sa da har yanzu yake faduwa...





Bayan awa daya, daya daga cikin doctor's din ya fito yana sharce gumi.





Gaba daya suka yo kan likita bare ma Al'ameen har da rike masa riga, murmushi doctor'n yayi yana jinjina kaunar wanna ahalin ga Raliya...




"Congratulations ta haifi baby boy, Alhamdulillah da Cs zamu mata Allah ya takaita" doctor'n ya fada yana mikawa Al'ameen hannu.






Ai ba kunya Al'ameen ya rungumi doctor ya kasa boye murnan sa...





Haka ma sauran Ahalin, sosai suka yi farinciki da wanna kyautar da Allah ya Basu...





Ganin yadda Raliya ta jigata ta kuma zubar da jini, ya sa Doctor yi mata karin ruwa da jini domin ta zubar da jini sosai....





Bayan kwana uku aka sallamesu, Raliya tare da kyakyawan baby'n suna cikin koshin lafiya.





Kullum Al'ameen yana gidan, baya gajiya da kallon baby dake goge masa damuwar baby'n sa ta farko daya rasa, da har yanzu basu San a mace take ko a raye ba....





Haka ma mariya tun da aka yi haihuwar a gidan take wuni, sai yamma take tafiya gida, kuma sosai take nuna kauna ga baby'n.....






Saura kwana biyu suna... da misalin karfe bakwai da hamsin na dare a lokacin masallatai na ta yin sallah, yayinda wasu ke yin tasu sallar a gidan, a hankali wata mata mai sanye da hijab blue color hadi da likab baki ta shigo gidan..., Sam ba a hango fuskar ta balle a gane kamanin ta, cikin sauri ta nufi dakin Raliya.....





Kwance Raliyar take tana bacci, yayinda baby ke gefen ta sanye da tsad'add'un kaya masu kyau, sai wutsil² da kafafu yake, idanun sa tar....






A hankali wanna matar mai sanye da hijab blue color hadi da nikab ta lallaba ta dauki baby kana cikin sauri ta bar gidan.......





Tana fita, dai dai lokacin aka iddar da sallar, a kuma dai dai lokacin ne mama ta iddar da sallar ta, ta nufi dakin Raliya......







*(Kuyi hkr, phone dina Yana da matsala ne, shiyasa kuka ji ni shiru kwana biyu. Yanzu ma da wata wayar nayi muku update, in shaa Allah zamu gama littafin a sannu da yardar Allah duk mu huta ngd)*





Share



Comment



Vote





Noor

***