59-60
by @nooriman
🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
*WATTPAD*
@NoorEemaan
EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌
Page 59-60
...... hasƙen fitilar babur daya dalle ta, a daidai lokacin da taƙe ajiye jaririn a kasa ya sanya cikin zafin nama ta juya domin guduwa.
Cikin wani hanzari na kan babur din ya ɗiro domin ƴa cimma ma matar, amma ina babur d'insa ya fado ya danne masa kafa daya, sosai k'irjin sa ke bugawa wanda ya rasa na menene, take kuma abinda ya faru shekaru goma sha shida da suka wuce suka shiga dawo masa, a kuma daidai wanna lokacin, ɗa ƙuma daidai wurin, bambamcin kawai a wancan lokacin ruwan sama ne, aɓin ɗa mamaƙi.
ganin matar ta fara nisa sosai, dan ma tana da kiba bata iya gudun sosai.
Cikin wani zafin zuciya ya watsar da babur din, duk da uban zafin dayake ji, haka ya bi bayan matar da dukkanin speed din sa, abin ka da namiji, namijin ma dogo sosai, ya cimmata...
hijab dinta yayi nasarar damƙewa, cikin sauri ta fisge, ta cigaba da gudu, burinta kawai tsira daga hannun wanna yaron dake neman kowa mata cikas.
A karo na biyu ya sake damko hijab dinta, wanna karon ba riko na wasa yayi mata ba, tayi_tayi ta fisge ta kasa, sai ta tsaya cak! Kana ta a hank'ali ta juyo suka yi ido hudu da Nu'aym da idanu sa suka yi jajur babu abinda fusk'ar sa ke fitarwa sai zallan bacin rai...
Haka kawai matar taji gabanta ya yanke bana wasa ba, ganin wanna saurayin, cikin shammata ta dunkule hannu domin kaiwa marar sa naushi, Saboda nan ne kadai ta san zai iya zubewa kasa ƙila ma ƴa tsuma, domin wanna ingarman namijin bata iya kokawa dashi.
Sarai Nu'aym ya lura da ita, tana daf da kawo hannu kusa da marar sa, ta rike hannun ya lankwasa shi, ji kake kasss... Ihun azaba matar ta saki, da har ƴanzu Idanunta ke sanye cikin likab.
Hannunta ya damko, tamkar rakuma haka ya shiga janta, tana tirjewa har zuwa inda ta yar da jaririn, ikon Allah jaririn na kwance cikin galabaita, dama ba lallai a lura da shi ba, domin wajen ak'wai duhu.
Nu'aym ya rasa abinda ya dace yayi, burinsa kawai yanzu ya kai matar nan hukuma, domin shakka babu ta cika mara imani, ga wata muguwar tsanar ta da yake ji...
A zafaffe ya ji murya ta tace "ka sake ni in tafi, ina ruwanka dani? ka sake ni ko na maka ihun barawo ko kwarto" tace domin bashi tsoro.
Murmushi mai ciwo ya saki yace "idan kin haifu kiyi ihun, haka nake so, jama'ar nake son su zo, domin su ga taki kalar rashin imanin, kuma kika min sharri ina mai tabbatar miki har duniya ta nade ba za ki taba mantawa da mai suna Nu'aym ba!" Ya fada cikin dakiya.
Take tsoro ya lullube matar domin yau taga wanda yafi ta, a zafin kai, Nu'aym na cikin tunanin abin yi, ƙawai yaji jiniyar yan sanda, wani sanyi ² yaji a ransa...
Suna karasowa matar ta fincike hannunta cikin shammata zata gudu, Nu'aym yayi saurin saka mata kafa, take yan sandan suka saƙe tabbatar ɗa cewa mai laifi ce ita, nan take wata macen yan sanda ta fito ta dagata, hadi da maka mata handcuff a hannu.
Ajiyar zuciya Nu'aym ya saki, daya daga cikin yansandan yace "samari mai ya faru ne?"
Cikin muryar bacin rai Nu'aym yace "yallabai jariri na ga ta yar, tana ganina ta gudu da kyar na kamo ta, kaga jaririn ma" Nu'aym ya nuna wajen da jaririn ke kwance har yanzu...
Nan aƙa saka sallati, har da jama'ar da suka taru a wajen yanzu suna kallo.
A hankali Nu'aym ya karasa, ya tsugunna ya dauki jaririn ya rungume shi, take wani son yaron ya mamaye jik'in sa...
Nan dan sandan yace "samari wanna maganar babba ce! !dole zamu je da kai station"
ba tsoro ɓalle fargaɓa Nu'aym yace "Toh ba matsala"
kana ya fara kallon mutanen wajen, take ya hango wani yaro da gidan su ke gaban nasu ƙaɗan yace "Musa dan Allah kai min mashin dinnan gidan, ka cewa su kaka ina zuwa, karka ce station zani domin hankalin su zai tashi"
"Toh, babu abinda zan ce musu ma yaya Nu'aym" yaron ya fada yana hawa babur din. Yayinda su Nu'aiym suka nufi station.
Matar nan kuwa ta sha zagi da tsinuwa a bakin jama'ar wajen,gaba daya ta hada zufa, ga hijab din ta duk Lemar gumin rashin gaskiƴa.
*POLICE STATION*
Kimanin awa d'aya kenan ana tambayar matar waya aike ta? Miyesa ta yar da jaririn? Daga wani gari take? Da dai sauran tambayoyi... amma shiru kake ji ta kasa magana, sai zaro ido kawai take ta likab d'inta.
Nan aka sa ta a *guide room* aka kulleta, sannan suƙa ce mata idan zuwa gobe bata bud'e baki tayi magana ba, tofah za a fara yi mata hora mai tsanani...
Nan dan sandan ya rubuta report, Nu'aym yayi signing cewa zai rike yaron har iyayen sa na asali su bayyana.
Sai karfe goma na dare da yan mintuna ya bar station din, yana fitowa daga wani babban pharmacy a tsallaken titi, nan ya tsallaka, magungunan irin na yara aka bashi masu k'yau, kana ya samu baby milk *NAN 1* ya siyi gwangwani uku, sai set din feeder.
Komai yana yi yana tuna baby'n sa ne, musamman a lokacin daya tsince ta, duk da yana 15yrs a lok'acin amma har yanzu yana tuno komai...
Kara tsallaka titi yayi ya samu abin hawa ya nufi gida...
Bayan mintuna arba'in mai napep ya sauke shi kofar gidan.
Bayan ya sallame mai keke napep ya nufi cikin gidan.
Ya ƙuwa tarar da lifan d'insa fake a tsaƙiƴar giɗan, ga baby'nsa(Nu'aiymah) tsaye Idanunta kuri a kofa, ga kuma kaka zaune itama jigum da alama jiran dawowar sa suƙe.
Ganinsa, yasanya kaka furta _Alhamdulillah_ yayinda Nu'aiymah ta sauke ajiyar zuciya kana ta nufi shi da gudu domin hugging dinshi... Ta na karasowa ta tsaya cak! Sak'amak'on ganin kyakyyawan jariri kwance a k'irjin Papi'nta.
Cikin zaro ido ɗa mamaƙi tace "p...papi nah! jaririn waye wanna?"
Jin an ambaci jariri ya sanya ƙaƙa mikewa a zabure, domin sam bata lura da jaririn ba, sai yanzu data ji Nu'aymah ta fada, cikin sauri ta nufi wajen Nu'aym ɗin, bakin ta har rawa yace tace...
Manage please bacci nake ji😴
* please do vote and follow me on wattpad @NoorEemaan*
Share
Comment
my readers📚🖊
Noor loves you all💋