Papi ne!

61-62

by @nooriman

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓





*WATTPAD*

@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌



page 61-62



......"Nu'aymu me zan gani haka, ko dai tarihi ne zai maimaita kansa? Ina ka samo jariri kuma?" ƙaƙa ta fada Idanunta ƙuri a kansa



Wani kallon da Nu'aiymah ya jefa mata ya sanya ta fahimtar suɓutar baƙi ɗa tayi. Tamkar yar yarinya ta sanya hannu ta toshe bakin ta, kana tace "toh gayamin ina ka samu wanna yaron?"



Bai kulata ba, ya samu daya daga cikin fararen kujeran roba ya zauna. Ledar maganin da baby food din ya ajiye kasa.



"Papi nah kayi Shiru, dan waye wanna? Ka fadamana kaji" Nu'aiymah ta tambaya gabanta na fadu'wa, wanɗa bata san ɗalili ɓa.



"Ohhhh! Baby yaushe kika zama lawyer ne? Relax zan sanar daku, kin san me nake so kiyi min?"



A sanyaye ta girgiza kai.



"Nasan bakya raɓo da ruwan zafi a flask dinki, ga feeder'n nan ki wanke da ruwan zafi, sai hada masa madaran nan, kinga yunwa yake ji, gabadaya yayi laushi" (kasancewar Nu'aiymah na da jin sanyi, haka kuma ta jima a ruwan sama a sanda aka yar da ita, hakan ƴasa Papi ya sabar mata amfani da ruwan zafi, hatta fitsari sai da ruwan zafi take yinsa, hakan yasa kullum babban flask dinta ke cike da ruwan zafi).




Gama maganar Nu'aym ke da wuya, yaron ya saki wani marayan kuka cikin muryan da ƴa galabaita, take tausayin yaron ya mamaye illa'irin jikinsu, bare ma Nu'aiymah har wani tashi tsigar jikinta ke yi...



Cikin Sauri ta wanke feeder'n da ruwan zafi, ta dauraƴe.

Ƙana ta zuba madaran da ɗan spoon din cikin madaran cokali takwas, sai ta zuba ruwan zafi, rufewa tayi kana ta jijiga da k'yau, jin akwai zafi ya sanya ta debo ruwan sanyi a wani bowl ta saka feeder'n ciƙi domin ya huce.




Cikin mintuna hudu madaran ya rage zafi, mikewa Nu'ayimah tayi, ta zubar da ruwan cikin bowl din, ta dauraye ta mayar kitchen.



Wani ƙujera ta ja ta zauna kusa da Papi, tayi tagumi tana kallon su.


Hajiya kaka kuwa jiki ya mutu hakan yasa ta kasa magana...



Nu'aym na sanyawa baby'n feeder a ɓaƙi, ya cafke gwanin tausayi ya fara tsotsa, kafin ma ya gama shanƴewa ya hada uban gumi musamman a goshin sa.



Cikin kankanin lokaci jaririn nan ya tashi da feeder'n nan, kana ya saki wata doguwar gƴatsa yana sauƙe numfashi.




Da mamaki Nu'aiymah tace " kai! Papi wanna yaron akwai ci sosai, ya shanye duka madaran "



Dariya ta bawa Nu'aiym hakan ya sashi murmusawa yace "ba dole ba, yunwa yake ji sosai fa, shiyasa kika ga ya galabaita".



Jinjina kai Nu'aiymah tayi kana tace " toh Papi ka gayamana dan waye ka ji?"



"Rabu da shi, kasan bana son wulakanci ko? Sai faman jan aji kake mana, sai kace budurwar ka ce ni, toh kalle ni da k'yau fararen gashin ne a kaina, wanna gantalewa har ina, tun dazu nayi haku'ri, bana son magana, amma sai da ka kure ni" tofah kaka rikici ya motsa.



"Kai kaka dan Allah, ni ki daina yiwa Papi nah fada bana so, ai yace zai gayamana, ƙo papi?"


"Ke rufe min baki, da gulman ki"


Murmushi Nu'aiym yayi, kaka ba dai masifa da rikici ba, ya aiyana a ransa... a fili kuwa yace "Relax! Kaka relax yanzu zan gaya miki, kun san lokacin zuwa na hutun karshen mako bai yi ba ko? Toh wani takarɗa aka ce na kawo daga wajen aiki, toh na barsu a nan, hakan yasa ana tashi daga aiki na dau hanyar SOKOTO, daidai ta layin bayan mu na ga...."



"Kwarai kuwa ɗanan, abinda ya kara tsorata mu kenan, har tunani nayi ko aure kayi a can, matar ta haihu" kaka ta katse shi, ciƙin iyaƙar gaskiƴar ta.



runtse ido Nu'aym ƴayi yace "aure kuma kaka? Yanzu zan yi aure baku sani ba"


"Yo Allah na tuba, dan yau ka haifa amma baka haifi halin sa ba, duk da na yarda da kai dari bisa dari, amma rayuwar ta zama abin tsoro" kaka ta ƙara fada cikin iyakar gaskiyar ta.




Murmushi mai sauti Nu'aym yayi, domin kaƙa ta bashi dariya sosai, cikin nutsuwa ya shiga fayyaice musu komai...




"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un! Ke duniya! Ke duniya!! Ke duniya!!! Ina zaki da mu ne? yaushe wanna lukutar masifar zai kaura a al'ummar mu, Allah sarki jariri bawan Allah bai ji ba, bai gani ba, shiƴasa ya shanƴe duƙa madaran, ashe horon ƴunwa tayi masa, oh! Allah na goɗe maka da Nu'aiymu ne ya tsince wanna jaririn, shegiyar mata mai fusk'ar alala, billahi gobe zan bi ka police station ɗin, domin in fada wa yan sanda su karya kafafun muguwar matar nan, mai kafar doya" kaka tace cikin kuka sosai har da majina.



A hanƙali Nu'aym ya maida duban sa ga Nu'aiymah data dora kanta tsakanin cinyoyin ta tana kuka sosai, wanda kukan bana iya labarin da papi ya basu bane, haka kawai take jin wani yanayi a jikinta, ga kuma wani sabon son jaririn da matsanancin tausayin sa dake bin jini da tsokan jikinta.




"Baby! Baby!!" Papi ya fada hankali tashe yana mikawa kaka jaririn dake baccin sa a nutse.



A hankali ya dago ta, ya dora ta kan cinyar sa, hawayen fuskar ta yake sharewa kana cikin damuwa yace "baby stop this ok! gayamin what's the matter?" Nu'aym ya fada a dame.



Jikinsa tafada tace "Papi ina jin tausayin wanna yaron, matar bata da imani, Papi ƙa sa a zane ta kajiiiiiiii" ta fada cikin ƙuka.



Nu'aym zai yi magana kaka ta riga shi... "A zane ta fa kika ce, kaji min shirmen yarinya, ashe tsoranta ake ji, ai karya kafafun ya kamata ayi, ko a sa addah a ɗaɗɗatsa kafafun muguwar mai ƙalar fuskar guɗawa, amma kya ce a zane ta, ashe tausayinta ake ji" ƙaƙa ta fada ciƙin masifa, ƙamar Nu'ayimah'n ce matar.



Shi dai Nu'aym rarrashin baby'n sa yake har tayi shiru, ganin tayi shiru ya sanya shi kallon fusk'ar ta yace "Baby zaki raka ni in siyo wa baby rigar sawa kinji?"



Nu'aiymah uwar son yawo da sauri ta mike ta dauko hijab di'n ta...



"Toh uwar son yawo, oooh ni Zainabu abu, son yawo a jikin ki kamar kin ci kafar kare"


Dariya kawai Nu'aiym yayi, Ƴayinda Nu'aiymah ta turo baki, hannunta Papi ya kama suka fice....


ɓaƙin titi suƙa je, sukayi sa'a kuwa mai shagon bai rufe ba, kayan maza jarirai kala TAKWAS Nu'aym ya siya, sai Pampers babban Leda, hadi da set din kayan shafa na company *Johnson_Johnson* sai turaren yara ya siya guda uku, ATM din shi ya bayar aka ciri kudin, shagon kusa dashi suka shiga, nan nu'aym ya siyawa baby'n sa Chocolate dangin su Nutella, Snickers, Bounty, M&M's Roxy, Dune, ɗa Mars.

Ai tun a wajen Nu'aiymah ta bare daya ta sanya a baki kana suka nufi gida, amma ɓata ɓari papi ƴa gani ba, domin faɗa zai mata, tana cin abu a hanƴa.




Bayan sun isa gida Nu'aym ya rufe gidan. basu tarar da kaka a waje ba, leka dakin ta suka yi, suka ga kaka da jaririn kwance suna baccin su, kallon ta Nu'aym yayi yace "Baby muje ki kwanta, kinga sunyi bacci ko"


Shagwa'be fusk'a tayi tace "a'a ni Papi wajen jaririn nan zan kwanta" ta fada cikin iyakar gaskiyar ta, domin wani mugu_mugun son jaririn take ji.



Zaro ido Nu'aym yayi yace "rufa min asiri baby nah! ƙin manta Kin iya magagin bacci, salon ki d'aura wa jaririn kafa a fusk'a" ya ƙarasa yana saƙin siririyar dariya, ɗomin tuno ƴanayin magagin baccin ta, saɓoɗa tun tana karama suna bacci tare, sai ta dora masa kafa a fuska, ko ta mirgina ta hau kansa ba tare da ta sani ba...



Turo baki tayi ta shiga dukan sa a k'irji ganin yana mata dariyar, har da kukan sakalcin ta, dif ya gimtse dariyar sa yace "Am sorry na daina kinji" ya karasa yana kamo lallausan, farar, siraran hannunta cikin ƙarfaffan hannayensa masu dan nauyi...



Ɗakin ta ya ja ta, ya sa tayi alwalar ƙwanciya bacci, ta kuma sanja kayan zuwa na bacci a toilet, kana ta fito, ƙwanciƴa ta yi, ya lulluɓe ta ɗa bedsheet.



Hannun sa ta rike gam cikin nata ya dinga yi mata hira, kana ya ɗora da yi mata wakar da ta fi so a lokacin tana ƙarama, har yaji hannunta ya saki, alamun baccin ya dauke ta...



Add'ua ya tofa mata, ƴa ƙara lulluɓe ta ƙana ya sumbaceta a goshi da haka ya fita yana jin wani abu mai matuk'ar girman kan baby'n ta sa...



*Haƙa ko wani dare, matuk'ar Nu'aym yana nan haka yake lallaba ta har tayi bacci, haƙan yake fama duk ɗare, shiyasa idan ya koma JIGAWA take kewar sa sosai, wani zubin har kuka take kafin tayi bacci domin ya riga ya sabar Mata*




*WASHEGARI*

Ɗa misalin ƙarfe taƙwas na safe, kaka tasa Nu'aiymah tafasa ruwan zafi ɗomin yiwa jaririn wanka.




Bayan ruwan ya tafasa kaka ta sirka shi dana sanyi kadan!


Dauƙo yaron daga kan gado Kaka tayi, domin tun jiyan nan bai farka ba.

"yarasulillahi manzon Allah" kaka ta faɗa Idanunta kuri kan jaririn, domin jiya nepa ɓasu ƙowa wuta ba, hakan yasa bata ga ƙamanin yaron ba.



"Lafiya ɗai kaka?" Nu'aiymah ɗaƙe tsaye, ƴayin da papi dake zaune suka fada a tare.



Cikin mamaki tace "gane min abin al'ajaɓi danan! sak Nu'aiymah tamkar tayi kaki, kalli ƙaga kamar Nu'aiymahtou tun daga yarinta har girma, ƙai wanna kamanin ya baci"



Cikin sauri Nu'aiymah da papi suka iso gabanta, zuciyoyin su suka buga a tare, ganin tsantsar kamanin, domin dukkanin su jiya basu lura da kamanin yaron ba.



Daga karshe dai suka bar komai a zuwan kawai kamanin ne, kamar yadda aka samun wasu na matuk'ar kama ciƙin al'ummah, kuma basu hada jini ba, amma sosai abin ya zauna a ransu.




Nan kaka tayi masa wanka, ta gasa masa jikinsa sosai da ruwan zafi, kana ta shirya shi cikin daya daga cikin kayan da papi ta siyo.




Nan kaka tace "Amma wanna muguwar matar daƙiƙiya ce! yaran nan ku gane min, ta iya yar da yaro amma bata iya sauya masa kaya ba, ashe ita ba tantirya bace, domin kayan jikin yaron nan ya nuna ba jiyan aka saka masa shi ba, duk da tsaɗar kayan kuwa. Ni wallahi Allah_Allah nake mu je station din domin naga yanayin mara imanin, yo wanna dole na kirata da ƙanwar firauna"



Dariya su Nu'aiym suka sanya mata, kaka ba dai bawa mutum nishadi ba.



Nan dai su kaka suka shirya kana suka nufi police station...





Share


Comment


Vote





Vote and follow me on wattpad @NoorEemaan





Thanks for reading my novel

🔥PAPI NE!🔥