63-64
by @nooriman
🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
*WATTPAD*
@NoorEemaan
EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌
Page 63-64
.............. A daidaita sahu suka tafi, jaririn na kwance a kafadar Nu'aymah yana baccin sa, domin taki bawa kaka ta rike tace ita zata rike shi.
Bayan sun isa police station DPO ya bukaci ganin Nu'aym, sun jima Sosai suna magana duk akan maganar matar ne, sannan ya sanar dashi cewa har yanzu matar taki magana, sosai Nu'aiym yayi mamakin taurin kai irin na matar, ko dayake ba abin mamaki bane idan aka yi duba da rashin imani irin tata.
Godiya yayi ya bar office din, nan ya tarar da kaka tana tijara ita lallai sai an barta taje taga muguwar mai fuskar alala, me yan station din zasu yi banda dariya, Nu'aiymah kuwa na tsaye tana sakin murmushi, wato kaka dai duk inda taje sai ta nuna halin ta.
Nan Nu'aym yace "menene kaka?"
"Yawwa dan nan! Ina ka je ne? Kace wa yan sandan nan su kaini wajen matar nan mai fuskar gudawa, Allah sai na wanke ta tas da soso da sabulu.
Girgiza kai Nu'aiym yayi ya kalli daya daga cikin yan sandan yace "zamu iya ganin matar?"
"Kwarai kuwa yallabai" daya daga cikin ƴan sandab ya fada, kana ya nufi guide room da aka garkameta.
Nan aka fito da ita tana nuna taurin kai da tirjiya, nan fa kaka ta shiga zagin ta, da ci mata mutunci iri _iri, ganin abun yayi yawa ya kalli kaka yace "it's a enough kaka! Ya isa haka please"
"Kai Nu'aymu ka barni, wallahi sai nayi magana, data samu banyi fata_fata da fuskar ta ba, kaga munafuka ta tsunkuyar da kanta taki magana, 'yar buhun uba mai fuskar alala" nan fa yan station din suka saki ihun dariya har da wadanda suka zo station din yin case.
Kara cewa tayi, "wallahi sai na cire wanna abun na fusk'ar ta domin Inga fuskar ta" ai kuwa babu zato babu tsamani aka ga kaka tayi tsalle tayi gaban abinda ya raba tsakanin su ta fisge nikab din fusk'ar ta...
Take fusk'ar ta daya yi wujiga_wujiga ya bayyana sai zaro idanuwa take..
Ai fa kaka tace "dole ki yi degree ki degirgire a mugunta, ga fusk'ar nan mai kama data mugaye marasa imani, billahi da abin nan bai raba tsakanin mu bako, ta fada tana buga abun katako daya raba tsakanin su, ta cigaba, da wallahi na Karya miki kafafu da bazai kara moruwa ba, ya....."
"Haba my Kakus ki yi haku'ri haka kinji yi Shiru" baby papi'n ta katse ta.
"Rabu da ni Nu'aiymahtou! Wanna matar sai na yi raga_raga da ita yau"
A firgice matar nan ta dago jin murya tamkar ta Raliya, take idanun su duka sarke dana Nu'aiymah.
Wata mahauk'aciyar bugawa k'irjin matar nan yayi, ganin photocopy Raliya sak tsaye rige da ita jaririn data so yarwa. Wanna kama ya yi matuk'ar bacewa, shekaru kawai Raliya zata nunawa Nu'aiymah.
Saboda rudewa ba tare da ta sani ba, tace "Raliya"
Kallon ta duk suka yi da mamaki, kana kaka tace "mayya! Kuruwar jika ta tafi k'arfin ki, daci gareta, fiye da madaci da shu'waka, ehe kuma karki sake kiran ta Raliya ba sunan ta bane"
Amma ina matar nan bata san kaka nayi ba, kawai kallon Nu'aiymah take, Nu'aiymah ma sosai k'irjin ta ke bugawa a duk sa'ilin data hada ido da matar...
Sosai kuma take kara jin tsanar matar a ranta, wasu abubuwa take hangowa a fusk'ar matar da baki bazai kwanta ta ba, sai dai a zuciya...
Nan dai aka mayar da ita garkama, idanun ta kuri kan Nu'aiymah sai data daina hango ta kana ta daina juyawa.
Nu'aiymah kuwa dasu kaka sosai kallon ya basu tsaro, domin kallon da take jefawa Nu'aymah ko nace take bin Nu'aiymah dashi na tattare da abubuwa masu yawan gaske...
Nan fa Nu'aym ya ajiye musu kudi yace su mata hora mai tsanani har ta fada dalilin 'yar da jaririn data yi, da haka suka bar police station din suka nufi gida...
*******
Da yamma duk suna zaune a falo, Nu'aiymah na hadawa jariri milk, sai da ta zuba madaran a cikin feeder kana ta cika cokalin ta zuba a bakin ta.
Nan fa kaka ta saki sallati tace "Nu'aiymu kaga abinda nake ce maka ko? Nace maka tana shan madaran yaron nan amma baka yarda ba, ka dai gani da idanun ka, shiyasa naga har wata kumatu da sulbi fatar ta ta kara ashe satar wa dan jaririn nan bawan Allah madara take"
Dariya Nu'aiym yasaki, "ohh kaka rigima, yanzu menene dan ta sha, ai kudin uban ta ne, ki barta, idan ma tana so zan iya ɓata nata daban" Papi ya gwale ta.
"Eh dama kullum sai ka gwale ni, Saboda 'yar kace, baka son a fadi laifin ta, toh wallahi wanna yaron zai girma kamar yau ne, zakaga yanda zamu muku ni da shi, sai mun zama a hade, shima yana goyon bayana, wanna wariya launin fatar ya ishe ni, Allah ya bamu tsahon rai dai"
Nu'aiymah dake jijjiga Madaran tana Dariya ta dawo gefen kaka ta zauna, kana ta karbi jaririn ta shiga bashi madaran...
Shiru wajen ya dauka na yan mintuna kana tace "wallahi ni bakina baya Shiru, bana iya shiru da baki na Saboda wari zai yi" ai fa nan su Papi da baby'n sa suka sanya dariya, Nu'aiymah har da 'yar guntuwar kwallar ta...
Itama kaka sai data fada taji dariya ya taho, mata, nan fa suka yi mai isar su kana tace "Allah gaskiya na fada, kun san me? Yaron nan bai yi sati muguwar taso 'yar dashi ba, ba tamtama ba a rada masa suna ba, toh yanzu wani suna mai ma'ana za a rada masa" ta karasa tana kallon su...
Jinina kai suka yi cikin nutsuwa kana Papi yace "gaskiya ne kaka kin kawo shawara mai k'yau, amma wanna karon baby'n Papi'n tace zata zaba masa suna"
Kallon Nu'aiymah dake murmushi Idanunta kuri kan jaririn yace "baby gareki ki zaba masa suna, in sha Allah ni kuma gobe zan nemo rago koda karami ne a yanka masa"
Kallon Papi'n take cikin so da kaunar sa, a fili tace "hakika ubana yafi na kowa, saboda ƙyawawan dabi'unsa, na kuma gode da wanna damar Papi nah, na zaba masa suna ADEEL".
"Masha Allah baby ƙin zaɓi suna mai dadi da ma'ana, Allah yayi miki albarka, Allah ya kuma raya mana Adeel"
"Ameen my sweet Dad"
"Kaka kinji sunan da baby ta rada ko?"Nu'aym ya tambaya.
"Eh ƙwarai na ji fa, ɓan dai san ma'anar sunan ba, domin a zamanin mu ban taba jin sunan nan na yan gayu ɓa, amma wallahi sunan yayi dadi sosai, dama ana Sanja suna dana dawo da sunana Adeelah, ko ba a saka sunan haka?"
Me su papi zasu yi in banda dariya, ooh! kaka rikici, ko Ina ta taba ji an bawa mace suna Adeelah oho?
Itama kakar sai data dara, nan Papi ƴa rada masa suna ADEEL, haka dai suka cigaba da Hirar su cikin nishadi, suyi hira, suyi wasa, suyi fada, dama wanna kamar dole ne, amma basa ko mintuna biyar sun shirya...
**********
JIGAWA
Ta ɓangaren su Raliya kuwa, sosai aka dage da yi mata add'uo'i ana sauke mata kur'ani ƴayinda damuwa ta sanya Al'ameen kwanciya a asibiti, nan fa abin ya hade musu, da ƴan gidan su Al'ameen har na su Raliya basu da nutsuwa, hakan yasa babu wanda ya lura mariya bata nan, sai siraru daga dangin Al'ameen amma babu wanda ya fada.
Saboda damuwar dake gabansu, Al'ameen Yayi mamakin jin ta Shiru domin tun a daran da aka sace masa jariri bai ganta ba, basu hadu ba, kila bata sani ba, ya bar wa zuciyar sa hakan, domin damuwar dake gabansa ta ishe shi.
Raliya kuwa har yanzu tana nan yadda take sai saukin da ba a rasa ba, kuma har add'uo'i da wasu ayoyi ake karanta a tofah a ruwa tasha, wanda sam bata yarda ta sha, sai an yi da gaske su yaya Auwal suke danne ta ake iya bata ruwan.
********
SOKOTO
Ta bangaren wanna matar kuwa taki magana, sai da aka saka wata macen yan sanda tayi mata duka mai Suna duka. Ganin ta fara jin k'amshin lahira ya sanya ta bude baki tace, ita babu wanda ya aiketa, ita ta saka kanta, bisa raddin kanta tayi, domin bata son ganin 'ya'ya a tare ɗa uwar yaron, shiyasa ta rabo su, kuma ita rashin imanin ta bai kai ba, da kashe yaron zata yi, sai ta ɗora ta cewa yan sandan su sake ta, ta tafi tunda bata yiwa yaron komai ba.
Nan fa 'yar sanda nan ta gwabje mata baki tda kataƙon hannunta, domin ta lura maganganun matar babu ɗa'a a ciki.
Nan fa 'yar sanda nan tace "ke mahauk'aciya ce ko? you thought abinda kika yi k'aramin abu ne? Da har kika son a barki"
Nan ta cigaba ta dukan matar nan sosai har ta galabaita, domin har bata iya ihun..., take ƴar sandan nan ta fidda wayar ta a aljihun wandon ta, tace "saka min number'n mijin ki ko wani naki, ina jin sai a gaban su zaki fadi gaskiya"
Jiki na rawa matar ta karbi wayar domin ta daku iya dakuwa saboda gabadaya ta fita daga kamaninta, ta kumbura, nan ta saka number'n mijin ta domin shi kadai take ganin zata samu sauki a wajen sa saboda saukin kansa, take kuwa 'yar sandan nan ta buga kira wa mijin nata....
muje zuwa
Share fisabilillah habibtie's
Comment dinku is needed
NoorEemaan ce
***