Papi ne!

65-66

by @nooriman

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓





*WATTPAD*

@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌





*A gaskiya ina godiya a gare ku habibtie's da kaunar da kuke nunawa Papi ne! har da kyautar koda, ina godiya sosai ga readers din wanna tagwayen littafan nawa ɗa wanda na sani da wanda ban sani ba, ina muku son so fisabilillah, Nooreemaan taku ce, Nu'aiymah da Nu'aym ma naku ne*😁







65-66



..........kwance Al'ameen yake a gadon asibiti, idanunsa a lumshe yana jin dukkanin hirar dake tashi a dakin, wanda na yan'uwan sa ne da na Raliya.




Suna cikin hirar su yaji wayar sa ta fara ringing, amma bai da alamar dauka, har wayar ta sinke, wani kiran ya sake shigowa.... Hakan ya janyo hankalin yan dakin suka yi shiru, cikin sauri kanin sa mai Suna Abba ya daga kiran hadi da sakawa a hands free ya ajiye kan gadon da yake kwance, wajan kunnensa domin yasan ba bacci yake ba.




Take muryar 'yar sandan nan ya karade ila'irin dakin... "Hello ƴallabai sunana larai Usman jami'ar yan sanda, ina kira ne daga sokoto, ga wata mata ta bani lambar ka, wacce aka kama ta 'yar da jariri sabon haihuwa...."




A zabure Al'ameen ya miki, jin abinda 'yar sandan nan ta fada, fisge Karin ruwan da ake masa yayi, hannun, jiki, da bakinsa na rawa yace "wa....wa...ce...ce?"



Ɗaga dayan bangaren yar sanda nan wani mugun kallo ta watsawa wa matar tace "ya sunan ki?"



Shiru matar tayi tana zaro ido, ran yar sandan nan ya baci, wani mugun mahangurɓa ta bata a fuska, Saboda tsananin azaba, ga jikin ta yayi tsami dama, hakan yasa ta saki wata rikitaciyyar kara....




"Nace ya sunan ki? Ko bakya jini ne?" ɗomin sosai larai taji ta tsani matar.


A zabure Al'ameen dama sauran yan dakin suka mike, domin muryar wacce tayi ihun yayi musu kama dana wacce suka sani, cikin rawar baki Al'ameen yace "ki...ki... barta har mu zu, yanzu zamu taho, ki turomin address din wajen" kit Al'ameen ya koma ya zauna, gabadaya k'wak'walwar sa ta toshe, yama rasa tunanin yi, a hankali ya koma dabas ya zauna kan gadon



Kallon Al'ameen mahaifiyar sa tayi tace "Aminu! Ya da zama kuma? Ka mike mu tafi, karfafa jikin ka, kaji dan nan"



Gabadaya suka Mike, yaya Auwal, ya usman, su malam baba da mama, da dai sauran yan'uwan, da manager'n Al'ameen na company'n sa, daya zo duba jikin shi, har da Raliya malam baba yace a biya gida a taho da ita Saboda ba mamaki yan sandan su bukaci ganin ta, hakan kuwa aka yi, gabadaya kan su ya daure, so suke suje su ga mamallakiyar muryar da ta yi ihu, domin muryar yayi musu kama da na wacce suka sani, motocin ɓiƴar suka shiga, duka kirar sienna.




Karfe Shida na yamma suka isa wajen, ganin yamma tayi, yasa mahaifiyar Al'ameen ta kawo shawaran a kama hotel su kwana, idan ya so gobe sai su je police station din, hakan kuwa akayi, amma Al'ameen bai so ba, domin a k'age yake...


*********************



WASHEGARI da misalin karfe tara na safe, direct address di'n da larai ta tura musu suka dinga bi, hadi da tambaya har suka iso police station din, babu bata lokaci duk suka fito daga cikin motacin suka nufi cikin station din.




Suna shiga suka yi kicibis da Larai ta fito daga office din DPO fuskar nan a murtuke da alama aiki ya dau zafi, kai yayi chaji.


Hada idanu tayi dasu Al'ameen da shigowar su kenan, haka kawai jikinta ya bata Al'ameen shine mutumin da suka yi waya dashi jiya.




Domin ta kara tabbatar wa sai tayi dialling number'n sa, take kuwa wayar ta ta dauki kara, cikin sauri Al'ameen ya nufe ta yace "ni...ni...ne wanda muka yi waya, ina matar take? Wacece ita? Ina jaririn?" Ya jero tambayar ɗuƙ a rikice.




"Calmdown ranka ya dade, zaka ganta, ku zauna ina zuwa, zan fito da ita yanzu" daga kansa Al'ameen ƴayi tamkar jariri ya koma da baya da baya ya zauna dabas kan benchi, haka sauran duk suka zauna, kasancewar akwai abun zama wadatacce....



Sun kusan mintuna goma a zaune, larai ta tasa keyar matar nan ta nufi wajen su Al'ameen, babu abinda take sai faman jan kafa, kasancewar kafar tata tayi tsami sosai, domin ba k'aramin buga ta ke sha wajen larai ba...




Da kallo duk suka bita, kasancewa kanta na kasa hakan yasa basu ga fuskar ta ba, wani dundu larai ta maka mata a baya tace " dago kanki" a kausashe


A hankali ta dago kumburarran fusk'ar ta ta sauke su fess kan na Alameen, a kidimie Al'ameen ya nufe ta yace "mariyaaaaaaaaaaa! Kice? miya kawo ki SOKOTO yaushe kika zo?"





kallon larai yayi cikin fushi yace "me tayi muku? Me matata ta muku? Miyasa kuka mata wanna dukan kawo mutuwar?"



Wani murmushi takaice Larai tayi tace "matar ka fa kace? dama wanna ita ce matarka? Amma tir baka yi sa'ar mata ba, wanna munafukar mai fuska biyun da kake gani ita ce aka kama ta yar da jariri sabon haihuwa"....




Gabadaya dakin ya dauki Salati, kowa ya shiga tofah albarka cin bakinsa, ga Mariya tayi kasa ta kanta, cikin rashin gaskiya ta ma kasa yarda ta hada ido da kowa, Al'ameen kuwa Sam baya son tunaninsa ya tabbata, amma yanzu da larai tayi maganar nan ya kara hargitsa tunanin sa, tamkar gunki haka ya tsaya, can wani jiri ya debe shi, luuuuuuuu ya tafi zai fadi, Abba kaninsa yayi saurin taro shi ya zaunar dashi yana bashi baki, Yayinda gabadaya sauran yan wajen kansu ya kulle, domin abinda basu taba zata ko tunani suka gani yanzu a zahiri, dama labari aka basu, tabbas da sun Karyata...





Cikin fitar hayyaci Al'ameen ya kalle ta yace " ma...ri...ri...ya wani jaririn ki ka yar? nawa jaririn d'aya bata ne?, innalillahi wa innah ilaihi raju'un" ya karasa cikin rawar baki, gabadaya yama rasa abin cewa, domin bai taba tunanin hakan ba, koda a mafarki ne.





Cikin wani fushi maman Al'ameen tace "ke Mariya! ba tambayar ki ake ba, bazaki yi magana ba?"




Sosai gaban Mariya ya sake bugawa domin wanna shine karon farko da surukar ta yi mata magana cikin fada da fushi, gabadaya kamar ta nitse a awajen, domin ji tayi ta muzan ta, da kallo da shiga bin kowa, yayinda su ma suke binta da kallon zallan mamaki, wasu har tsana take hangowa a idanun su, Raliya kuwa bata ma san abinda ake yi ba, sai faman abubuwan ta take irin na masu ciwon hauka, amma babu wanda ya kalleta, domin sun san lalurar ta....




Wani duka larai ta nada mata a baya, sak'amak'on shirun data yi, ihu ta tsala tace "e....eh...shi...ne .....jaririn ka ne, nina Sato shi" ta fada a rikice ɗomin ba k'aramin tsoron larai take ba, har bata son ta taba jikinta da suna duka...




" mahammadur rasulilillah! Mariya kece?" gabadayan su suka fada cikin madaukakiƴar mamaki, sosai hayaniya ke tashi a wajen, kowa fadin albarkacin bakinsa yake, hadi da aibata Mariya.





Ai fa nan jikin Al'ameen ya shiga rawa, ya shiga kokawa da numfashin sa, sosai Al'ameen yake kallon Mariya cikin zallan mamaki, dama makashin sa na kusa dashi bai sani ba? Matar sa, uwar gidan sa, abin son so itace dama ta sace masa jariri? Kenan cikin Raliya na farko tana da masaniya kan batan cikin da haukacewar ta? ya ilahi! K'wak'walwar sa ta gagara daukar wanna abin mai matuk'ar ban mamaki da al'ajabi.







Sai da larai tace "silent please, hayaniyar tayi yawa, dan Allah kuyi Shiru"


Kallon Al'ameen tayi tace "yallabai ina mahaifiyar jaririn, akwai tambayoyin da nake son mata".




Maman Al'ameen ce tayi saurin cewa " Yallabiya kin ganta nan, ai bata da lafiya"




Kallon Raliya, larai tayi, a kallo daya ta hango alamun cutar hauka a tare da ita.



Sai a lokacin bakin Al'ameen ya bud'e yace wa larai "ina dana yake? Dan Allah ku bani shi ko zan samu saukin abinda yake damuna"


gabadaya yan wajen sun tausaya masa, ace babban mutum na kuka, cikin girmamawa larai tace "yallabai, wani saurayi ne mai suna Nu'aym ne ya tsinci jaririn a lokacin da Mariyar take k'ok'arin yar da jaririn, yanzu haka yaron yana tare da su, ya kuma yi alkawarin zai cigaba da kula da yaron har iyayen sa sun bayyana, har....."



Cikin sauri Al'ameen ya katse ta da cewa "please ki kaini wajen su, kai gidan su yaron, domin in ga gudan jinin na dan Allah" sosai tausayin sa ya kama kowa.



"Ai yallabai bamu da address din yaron, sai dai a kira shi yazo" ta fada tana latsa tsadaddiyar wayar ta, dama ta karbi number'n Nu'aym wajen wani dan sandan.




*****


Zaune suke gabadaya a falo, Hajiya kaka na basu nishadi kamar kullum, yayinda Nu'aiymah ke bawa ADEEL abincin sa, sai faman tsotsan feeder yake, an shirya shi cikin kaya masu k'yau, yaron yayi bul_bul gwanin burgewa da sha'awa saboda sosai yake da shan madara, ga kuma kulawa yana samu, kullum kamanin sa da Nu'aiymah Kara bayyana yake, tun abin na basu mamaki har suka basar, ga wani mugu_mugun son yaron dake ratsa jijiya da bargon jikin Nu'aiymah a kullum.




Tsagaitawa Nu'aiymah tayi da dariyar sak'amak'on kiran wayar Papi da aka yi, mika masa tayi domin wayar na kusa da ita, amsa papi yayi ya latsa Kore hadi da karawa a kunnen sa, take yaji muryar larai na sanar dashi cewa " barkan ka dai malam nu'aym an samu iyayen jaririn wajen ka fa, domin ita Mariya ce ta bani number'n mijin ta, bayan taji wuya, ashe dan mijin ta ne, ba lokacin bayani, kazo station please yanzu, duk suna jira" kit ta kashe wayar...





Sosai gaban Papi ya fadi, haka kawai yake ji tamk'ar wani al'amari mai girma zai faru a yau.



"Dan nan lafiya?" Kaka ta fada tana kallon sa.



"Kaka an samu iyayen jaririn nan..." Nan dai yayi musu bayani kamar yadda larai tayi.




"Yo ai wanna abin farincikin ne, maza ku shirya muje, domin wallahi sai na kara zagin mai fuskar tubani can(in ji darma😂)"


a sanyaye ya mike, ya nufi dakin sa, dama kayan shan iska ne a jikinsu duka, amma duk sunyi wanka.


hakan yasa ko wannen su ya nufi daki domin ya Sanja kayan.



Nu'aym ya sanja kayan zuwa dagon wandon jeans da yellow'n riga, sai takalmi sau ciki baki, sosai yayi wani lafiyayyen k'yau.


Nu'aiymah kuwa abaya mai yalwar stone blue color ta saka, wanda ya sa hasken ta kara fitowa tayi das da ita, itama sau ciki mai k'yau black irin na mata ta saka, tayi rolling da mayafi.




Hajiya kaka kuwa atamfar ta mai k'yau ta saka super holland da hijab pitch color ya dan dara guiwar ta kadan, ADEEL Nu'aiymah ta rungume a kafadar ta, sai ta rufe shi da towel din babies saboda iska da hasken rana...




Kaka ce ta kalli Nu'aiymah tace " ke 'yar nan maza dauko yar jakar nan ki saka madaran Adeel da karamin flask da feeder'n sa, domin kada ya ji yunwa, kin san yaron nan acici ne, atoh kada ya cinye mu da kukan sa"



Dariya Nu'aiymah tayi, ta shiga daki ta dauko komai kamar yadda kaka tace, karban jakar kaka tayi ta rataya, Nu'aym na jin su amma babu halin dariya domin sosai yake jin faduwar gaba...





Rufe gidan Nu'aym yayi suka fito, a yanda suka jero sai kayi tunanin mata da miji ne, nu'aym da nu'aiymah da dansu, kaka kuma mahaifiyar papi, haka da yawa mutanen da suke kallon su, musamman wadanda basu san su ba suka dauka.




Keke napep suka tara suka shiga, bayan Nu'aym ya fadi inda zai sauke su, gabadaya wata muguwar faduwar gaba ke riskan shi, amma bai bari su kaka sun sani ba....




Bayan sun isa bakin gate din station din, Nu'aym ya biya mai keke kudinsa, kana suka nufi cikin asibitin...



Nu'aym ne ya fara shiga cikin wajen, followed ba kaka, sai Nu'aiymah da ta kasance ta karshe...


Da Kallo su Al'ameen suka bi su kaka, kowa da lugudin da zuciyar sa ke yi, yayinda babu inda idanun Nu'aiymah ya sauka sai kan Raliya...




Kura mata ido Raliya tayi, Yayinda ta mike a zabure ta nufi Nu'aiymah...mutuwar tsaye Nu'aiymah tayi sakamakon hango photocopy ta sak ta nufo ta, haka zalika su kaka da su Al'ameen haka suka yi, kowa ya kasa motsi, Raliya na daf da isowa wajen Nu'aiymah dake kallon ta bata ko kiftawa, ta zube kasa kana ta saki wata gigitaciyar kara ta suma....



A kuma daidai lokacin ne, cikin tsananin rudewa da ganin komai zai lalace mata Mariya tayi subutar wata kalma daya Kara hargitsa kwanyar su kamar haka.....






Muje zuwa habibtie's😍🔥

Sai lahadi, idan mai kowa da komai ya ara mana rai.





Noor😍