9-10
by @nooriman
🍇🍇RAYUWAR FAHEEMAH🍓🍓
_by NoorEemaan_✍️📚
free novel
***
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din.
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
Ya rabb, forgive us before death! Have mercy on us at the tym of death, And don't punish us after death. 🙏
9-10
(Not edited)
"BACK TO STORY" ( dawowan labari)
"Dole in shiga damuwa hindu, abu kusan shekaru shida yaki sauki" wata kyakyawar mata dake zaune a wani had'add'iyar falo ta fada.
" Kiyi hakuri ummunsu zai warke in sha Allahu".
"Allah yasa hindu cewar matar tana share kwalla. Hindu ina neman alfarma agareku, naso yiwa baban umaimah magana amma na lura kwatakwata ya zare hannunsa akan mu, amatsayin sa na kanin mijina, ya dace yana duba lafiyar ƴaƴan wansa, ko da a wayane"
"kiyi hakuri ummun su abubuwan ne suka masa yawa" cewar hindu tana kokarin kare mijinta.
Murmushi mai ciwo ummu tayi kana ta riko hannun umaimah dake xaune gefensu, tace 'alfarma nake nema agareki umaimah yata, zaki iya auren yayanki? Duk da nasan yana halin lalura, amma yakamata ace matarsa kadai yadace taga sirrinsa a yanzu domin akwai abubuwan da a yanzu matar sunnah shi kadai ya dace ta sani, ki taimaka yata, ki taimaki dan'uwanki umaimah"
ummu ta fada tana hawaye.
"uh..uhmm... wacce umaimah din?" cewar hindu a duburbuce....
Murmushi mai ciwo ummun tayi, saboda tasan sarai hindu ta fahimci wacce take nufi, kallon hindu tayi tace "hindu kenan umaimah nake nufi" umaimah dake zaune ta bata fuska kana babu kunya tace "ni gaskiya ummu banasonsa yanzu saboda lalurar sa, mutum kullum kwance kamar gaw....."
saurin rufewa umaimah baki hindu tayi, ko ba komai akwai kunya, ummu da iyalanta sun gama musu komai sun bawa rayuwarsu gudunmawa sosai.
"kiyi hakuri ummunsu yarinta ke damunta"
" kai mama nice ma yarinya shekarata 24 fah, inji umaimah cikin bata fuska, kana ta dora da cewa besides ma ina da wanda nakeso mun daidaita" tafada free free abunta, babu ko ƙara.
Sosai hakan yayi wa ummu ciwo, bawai dan kin aurensa kowai ba, a'a yanda suka nuna kyama karara ga danta. Allah ya sanya alkhairi kawai ummun tace, tana mamakin Wasu mutanan.
Sallama hindu tayiwa ummu saboda jitayi ta takura agabanta umaimah tabata kunya suna ficewa, wata kyakyawar budurwa tana danna hancin motar ta kirar Ferrari cikin gidan sallama tayi kana ta karaso da sauri ganin halin da mahaifiyarta take ciki.
"Ummunah meya faru?
Jikin brother ne ya tashi?"
Ta fada tana sharewa ummu hawayen
"Fareesah mutane nabani mamaki ace a rasa wanda zai auri dan'uwanki duk tarin masoyansa, duk wanda nafadawa sai suki yarda, yanzu hindu da umaimah suka bar gidanan nace a hada danwanki da umaimah auran tace wai sun daidaita da wani, naga kamar umaimah na sonshi ne yasa nayi tunani hadasu amma abun mamaki tunda wanna jarabawar ta sameshi ta dauke kafarta agidan, me hakan ke nufi, dana bazai taba aure ba kenan?" Tafada tana kallon fareesa
"ummunah bashi take so ba, she's after something else,,, idan da tana son brother na wanna lokacin yadace ta nuna masa amma bakomai Allah ya bawa brother lafiya zatasan dayi damu ne" tafada tana jan kwafa, domin fareesa bata barin ta kwana domin wuta wuta ce ( like meenash yar rigima ta lolz)
Numfashi Ummu ta sauke tace"Bari inje na nagyara shi sai inbashi abinci"
" toh ummuna nima zan shigo yanzu..
"Mama wallahi yanzu banasonsa" cewar umaimah.
"nima bazan taba bari ki aure shi ba saboda inason kije gidan da zaki huta, tayaya zan bari kiyi auren bauta amma badadi ki nuna cewa bakya son jininta a gaban ta, kin manta lokacin da matsalar idon nan ya dame ki? Ita ummun ce ta tsaya aka shirya komai da taimakon shi fu'ad din , suka biya mana aka fitar dake kasar waje, ba gashi yanzu kin warke garau ba? kwarai da naso ki aure shi kodan arzikinsu but not anymore, Cos bazan bari kiyi auran bauta ba"...
"Wallahi kuwa mama har fa bahaya yake ajikinsa ina zan iya da kasantarsa, ranar dana fara gani wallahi nakasa cin abinci" ta fada tana yamutsa fuska,
" kwantar da hankalinki umaimah bazakiyi auran bautar nan ba, mu kai wanna abun kunyan har ina" tafada tana kama haba.
*FAHEEMAH*
bayan tayi sallar asuba bata koma bacci ba saboda tarin ayyuka dake jiranta, karin kumallo ta fara hadawa, sannan tayi wanke~wanke, tayi mopping tsakar gida hadi da gyara dakinsu da falo hadi da toilet. Haka take wanna aikin duk kwanan duniya. wanka tafada agurguje saboda ta makara makaranta, uniform dinta ta sanya masu kalan ja da fari wando ja, riga fara, sai dan maidaidaicin hijab dinta ja. Duk da kayan sun kode kuma ba guga amma atsaftace suke.
kyakyawace mai golden skin saidai halin rayuwar da take ciiki yasa kyawun fatarta dakushewa, tanada dogon hanci, idanunta manya ne farare kal, bakinta karamine masu kalan ja tana da wasu kwantaccen gashi a gefen da gefen fuskarta har saman goshinta daya karawa fuskarta kyau. Kirarta irin wanda akewa lakabi da figure 8 ne cikinta ashafe yake tamkar bata cin abinci hakan ya karawa shape dinta kyau! Dogon gashinta dake acike take kokarin tajewa, sai bata fuska take saboda zafi kasancewa baya samun gyara, hakan yasa 1side dimple dinta bayyana tajewa tayi sama~sama tadaure da tsohon ribbon dinta da duk ya saki, orange dankwallin mikaminta tadaura kana ta dauki jakarta daya fara yagewa sbd dadewa ta rataya duk da tana jin kunyar jakar, amma ya zatayi? Iliminta shine gatanta duk da halin datake fuskanta a gidan nasu amma bata bari ya shafi karatunta ba!
Shiga kitchen din tayi domin daukar nata abincin, ta ganshi abakar leda, hawaye ne suka ciko idonta amma bata bari sun zubo ba, daukan ledan tayi kana ta nufi kofar da'zai fitar da ita daga gidan...
Tazo fita ta hadu da wata budurwa da bata cika kyau bah. "Aunty jameela Ina kwana" cewar faheemah, kakauran labbanta ta tsuko kana da ja tsaki hadi da zabga mata harara da madaidaitan idanunta masu kalan milk color, sai kuma ta bangaje ta ta wuce , asanyaye faheemah ta bar gidan tana tuno nasihar umminta, "kada ki raina jameela ita din gaba take dake"......
Bangaren jameela kuwa, dakin mamin tashige, tace "mami zan wuce" tafada bako gaisuwa
" toh yar albarka kije dakin alhaji ki karbo kudi sai ki wuce".
Faheemah kuwa, tana shiga makaranta aka fara tarar makara, ajiyar xuciya ta sauke ganin ta kubuta, domin bata manta dukan da ta sha ba a jiya data makara, Kasancewar tana da perfect yasa nata dukan fin na sauran, assembly ta nufa hadi da shige layin ajinsu ss3a. Sanarwan dataji anyi ne yasa gabanta faduwa.....
Karfe 2:50 na rana daidai ta isa gida kasancewa da kafa da zuwa take dawowa.
Mami ta samu zaune a kujerar yar tsukunno tana waya, alwala tayi kasancewar bata yi sallar azahar ba, bayan ta idar ne ta fito hakan yayi daidai da gama wayar mami, "ina wuni mami, gidan uwar wa kika tsaya? Ta fada batare da ta amsa gaisiwarta ba. Ko yawon gantallin kika tafi? A kafa na dawo mami" tafada hawaye ya ciko kyakyawar idanunta amma bata bari ya zubo ba.
"Ga kayan miya kiyi jajjage, sanna ki dafawa yata dambu acca alhaji kuma kidafa masa tuwon alkama miyar ganye komai yana kitchen" mami ta fada tana kokarin shiga dakinta.
"Ma... ma...mi yau zan bada hadda a islamiyya"
Dawowa mamin tayi hadi da cewa "toh sannu Sudais, nace sannu Sudais, Wallahi sai kinyi aikin nan duka! kima hakura da islamiyyan" ta fada tana harararta..
" mami zanyi idan na daw..." Saukar Marin datajine ya hanata karasa maganar ta, "yaushe kika ga wurin kwana na? Ina fada kina fadi"
" ki yi hakuri mami" faheemah tafada cikin sheshekan kuka, tsaki mami taja tawuce daki tana banbamin fada.
kallon uban kayan miya tayi hawayen tausayin kanta ya zuba mata wai kuma jajjage zata yi, kan miyan ta fara gyarashi, tana yi tana hawaye... Sai shida da rabi ta gama aikin, tana kokarin shiga dakinsu jameela ta dawo...
"sannu da zuwa aunty jameela"
"ke banason gulma, kawomin abincina"
"toh" ta amsa asanyaye kana ta juya zuwa kitchen...
"Kin dawo yar albarka?"
" Nadawo ya gida mami?"
"Lafiya lou, wai mami ya naga yarinyar nan har wani kyau take karawa, Anya bata shafa mai?"
Cewar jameela cikin hassada da bakinciki.
"ai yar albarka bawani kyau, ita da take bauta, kawai dai shegiyar fatarta ke rudarki, kin fita iya gayu ke harda haduwa ma, ke kintaba ganin wani yayi sallama da ita?"
"A'a, ina fa mami" jameela tafada cikin farinciki ...
" Kingani ai, ki kwantar da hankalinki haka zata kare a bauta babu mashinshini".
"Assalama alaikum"
cewar Faheemah cikin zazakan muryanta (hakan ya kara bata ran jameela gani take kamar da gayya Faheemah tayi wanna muryan...
A lokuta da dama ta kan gwada yin abinda faheemah keyi, aganinta hakan ke sata fin ta kyau, bata san Cewar kowa da nature din shi, wasu mutanen na kokarin kwaikwayon abubuwan burgewa da wasu ke yi, aganinsu hakan ke sa wannan mutumin finsu kyau, ko haduwa, but not knowing that kowa da yanda Allah ya hallaci ki/ka, kuma yanda Allah yayi ka shi yafi kyau da dacewa da kai, just be yourself, Allah yasa mugane).
ko sallaman babu wanda ya amsa mata, abincin ta ajiye kana ta fice cikin sanyinta domin ta dauro alwala, suka bita da harara...
Abincin jameela tafara ci hadi da janyo ledar kazar dake kusa da ita menene wanna cewar mami? wani saurayi nayi da zan dawo gida, shi ya kawo nima ta fada tana kai cinyar kaza bakinta "mami inaji nasamu irin mijin da nake fatan samu"
miyau kwadayi mami ta hadiya kana tace "amma yar albarka yazaki yi da sani?"
"Mtsww me wanna yataba min banda wanna wayar" tafada tana daga infinixhot8 dinta, kinga motar sa kuwa? Mami kinga kudin daya ban"
tafada tana sa hannu cikin jakarta hannu mami na rawa ta ansa tace "nawane haka?"
" Dubu hamsin ne wai nasa kati bai fito da kudi ba".
"Alhamdulillah" mami tafada cikin madaukakiyar farinciki, kana ta kara da cewa "daman ni bana sonki da wanna sani, dan banzan yaro sai rowar tsiya, ai ki rige wanna da kyau jameela karki yi wasa, nace ya sunan sa"?
"SALMAN"
"madallah salmanu dan albarka mai kyautar manya"
" bafa salmanu ake cewa ba, salman zakice"
cewar jameela kan tsaye kai kace da kawarta take hira kana ta tura mata ledar Kazan, washe baki mami tayi kana tace yi hakuri yar albarka ai sunan ne naku na yan gayu , bata ko damu da yanda jameelan ta mata magana ba.
(Allah yabawa dukkanin iyayen ikon tarbiyyantar da 'yay'ensu bisa tafarkin addinin islama)