Rayuwar Faheemah

41-42

by @nooriman

🍇🍇RAYUWAR FAHEEMAH🍓🍓





_by NoorEemaan_📚✍️





kyautane( free novel)




***


Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




"Death is coming without notification 🔔 😭 may almighty Allah make our last word to be kalimatus-shahada ameen"🙏.





41-42


(Not edited)








Washegari karfe 8:00am daidai, kowannensu ya shirya cikin shiga mai kyau, Faheemah sanye take da turkish abaya ruwan kwaiduwar kwai ta yana kanta da dankwalin abayan, sosai tayi kyau duk bata yi wata kwalliya ba daga powder sai kajol yayinda cute lips dinta suke kara yin ja, duk da bata shafa komai ba, uban gayya fu'ad kuwa sanye yake da wata dak'ak'iyyar gezne baki wanda yasa farar fatarsa dake glowing ta sake bayyana.



"Kin gama shiryawa?"

Ya tambayeta


"Eh"

ta amsa masa, batareda yace komai ba ya riko hannunta suka fice domin zuwa part din ummu.




"Assalama alaikum"


duka su biyun suka yi sallama atare, ilairin yan falon suka amsa fuskarsu dauke da fara'a.


Faheemah kunya kamar ta nitse duk yanda taso kafin su karaso part din ya saketa yaki... gaban ummu suka tsugunna suka gaisheta, cikin farinciki daya kasa boyuwa a saman kamilaliyar fuskarta ta amsa.

Yan'uwan ummu dana abbuh suka shiga gaisarwa cikin ladabi, kowannensu ya amsa cikin farinciki.


"har kun shirya da wuri haka?" Fu'ad ya tambaya.



"Eh gwara mu tafi tun yanzu, mu isa abin mu da wuri".


Aransa kuwa cewa yake hajiya innah kenan sai ka ce ba flight zasu bi ba.


Saukar muryanta ne ya katse mata tunani

"sai kuma mun zo suna ko yarinyar kirki?" tafada tana kallon faheemah.


Cikin kunya ta tashi ba tare da ta iya bata amsa ba ta zauna kusa da small mom kana cikin muryan kasa kasa hadi da shagwaba tace "shine small mom kikamin wayo jiya ko? Har da aunty fareesa ma"




fareesa dake gefen su ta saki dariya kamar yadda yake dabi'ar ta, ba tare da tace komai ba ta cigaba ta chat da anwar dinta.


"Sorry my dear abubuwa ne suka min yawa, har na sha'afa" cewar small mom cikin son wanke kanta.



"Kin hakura dai ko?"



"Eh bazan iya fushi da small mom dina ba".


"Good girl"


Small mom ta fada cikin kaunarta duk da basu jima da sanin juna ba amma sosai take jin kaunarta, domin lokacin da fu'ad yake jinya, babu yanda ummu bata yi ba akan a bawa fu'ad daya daga cikin yanmmata yan'uwansa ya aura suka ki a fakaice, domin basu fito baro baro cewa basu son hadin ba, daga dagin ummu har na abbah sosai sukayi nadama abunda su kayi, musamman da suka ga baiwar kyau, nutsuwa, hankali, irin na faheemah, tabbas bare zai iya maka abunda dan'uwanka na jini bai maka ba, domin jiya suna makwancinsu sai da innah ta kawo maganar ta kuma ce su nemi yafiyar ummu, small mom tace a'a acewar ta tunda komai ya wuce, abarshi a hakan, domin tasan ummu bata da riko saboda haka a bar maganar, sun amincewa maganar small mom din yayinda jikinsu yayi sanyi sun kuma yi nadama domin abunda suka Kasa yiwa dan su, bare yayi masu.




"Small mom"



faheemah ta katse mata tunani.



"Na'am dear"



"idan za'ayi bikin anty

fareesa kada mu zauna a wajenta da mun kaita zamu juyo ko?"



"Eh sosai ma tunda har ta iya bar min ke ke kadai jiya."



"Yawwa small mom"

tafada tanawa fareesa dariyar tsokana



"Tab Allah small mom bazan yarda ba"



Fareesa ta fada fuska amarairace.



" Yeehhh nima na rama" faheema tafada tana mata gwalo.



Hakan sai ya bawa small mom da fareesa dariya...




Wanda ya janyo hankalinsu ummu garesa, fu'ad kuwa ita yake kallon tun dazu, shi kam yana son childish ness dinta duk da baya jin me take cewa amma, yana karantar zallan sakalci da shagwaba a acting dinta, hakan kuma na burgeshi.



"Wai ke rabi'a ( small mom) me kike tattaunawa ne keda yarki taki kasa kasa ba'a so muji?"

Cewar wata tsahowa daga dangin abbuh mai suna innah suwaiba.


"Inna Sirrinmune ko my dear?"



Shigar da kanta jikin small mom tayi a kunyace kana ta jinjina kai alamun "eh "



"ke yarinya menene abun kunya? dazu nayi mgn keda mijinki ku mun shiru maganar haihuwar ce bakuso?" Dariya kawai su kayi domin daman sun san inna akwai Mita.


"Kinga yarinya an fa zama daya mu ma iyayenki ne kinjiko?"

Cewar innah suwaiba.


Kara shigar da kanta Tayi a jikin small mom din kana tace "toh "


"ja'ira sarkin kunya"


innah'n ta sake fada, dariya aka Sanya gaba daya ganin sai kara shigar da kanta take jikin small mom.




Mikewa sukayi domin tafiya, daman sun shirya jakankunansu gasunan tsakiyar falon.

Faheemah ce ta dauki akwati daya, ganin Hakan yasa fareesa daukan daya, meenal ma ta dau daya. Dayan daya rage fu'ad ya dauka, Hakan ya sake burge iyayen nasu duk da akwai masu aiki a Gidan amma bai hanasu dauka ba,

kuma sun san cewa ganin Faheemah ta dauka shiyasa su fareesa dauka suma, aransu suna yaba tarbiyyanta haka suna farinciki da samunta azuriyyan su, Ummu kuwa a ranta tana fadin zata aikata fiye da hakan, a lokuta da dama tana mamakin yanda faheema keda nutsuwa hadi da tarbiyya, domin bata da mai kwabarta tun bayan da uwarta ta rasu, domin matar ubanta bata kula da ita bare ta kula da tarbiyyanta, haka ma abbuhnta da bai san da zamanta ba, hakika tarbiyan faheemah daga Allah ne haka ma nutsuwarta....



Maganar fu'ad ce ta katse mata tunani, kasa kasa yace "ummu gashi ki basu dan Allah" yafada yana miko mata mata bandir uku na 1k Yakuma yi hakan ne domin bayason su masa godiya.




Murmushi Ummu tayi domin ta fahimce shi kwarai, Duk da itama ta basu kudi masu yawa amma, taji dadin yanda yayi.




"Kaltume tunda muna da yawa ku koma hakanan ba sai kun mana rakiya airport ba" cewar innah suwaiba.



Da "toh" Ummu ta amsa kana suka shishiga motocin biyun da zai kaisu, addua sosai su ummu suka musu na sauka lfy, sai da direba ya tashi motar Ummu ta Dora bandir daya na kudin a cinyar innah, sai kuma ta dora bandir daya a cinyar small mom dake dayan motan, sai kuma ta dora bandir daya cinyar meenal kana tace musu su raba inji Fu'ad.


Ai kafin innah da sauran su suyi magana drivers sun cilla hajin motocin waje...



Haka suka juyo gida cike da kewarsu, domin Faheemah har da kwallar ta domin ta saba da su babu laifi, musamman ma small mom.

Sai da ya bari su ummu sukayi gaba, kana ya matse hannunta daya, wanda ya kara gudun hawayenta.



Cikin dan hasala kana kasa kasa yace


"wata rana sai hawayen nan ya kare, da alama dadi kukan yake miki right?"



"A'a"

ta fada tana turo baki.


"Ok! maza share hawayen kinji banason su" Hannu tasa ta goge hawayen kana suka rufawa su ummu baya.



"Son kuyi breakfast dinku, munyi tareda su innah kafin ku fito"


da "toh" ya amsa, yayinda faheemah ta zuzzuba masa waffles, tea, da peppersoup, tayi, tana kokarin zuba nata ya dakatar da ita.

"ki kara ankan wanda kika zuba min muci a plate daya"



Dan xaro ido tayi ta juya domin ganin ko su ummu na nan, wayam ta gani ba Kowa. Girgixa kai kawai Yayi yana boye dariyar sa.



"ko me abun kunya a cin abinci a kwano daya?" Ta tambayi kansa kasa kasa, tabe baki yayi batare da ya kara ce mata komai ba...





Abincin ta kara ta dauki spoon ta fara ci a hankali, shi kuwa ko ajikinsa ci yake a sake, bayan sun kammala yace "tashi muje ki tayani shiryawa zan wuce aiki". Kasancewar Daman ya sanar bazai samu zuwa da wuri ba yau.




"Ni wurin ummu zan..."


Kallon daya jefa mata ne yasa ta mike babu shiri, Fu'ad kuwa kwata kwata bayason takurawa mutum a rayuwarsa amma idan bai yi mata haka ba, Baya tunanin zata sake dashi har suyi irin rayuwar daya tanadar musu.

Yana gaba tana binsa a baya ta doguwar corridor dake gefen benen suka bi sai gasu sun fito awani hadaden wurin mai yalwar furannin tamkar garden dai. Dan tafiya suka sake yi sai gasu a part dinsu, Faheemah ta danyi mamaki domin batasan da wanna bangaren cikin gidan ba.


kayansa ya cire ya daura sky blue towel kana ya shiga Wanka, bai wani jima ba ya fito, kayan sa dake ajiye gefen gado ya sanya bayan ya shafa lotion dinsa.


"yar kauye haka ake taya mutum shiryawa? zo ki samun neck tie"


asanyaye ta mike ta daura masa da murmushi saman fuskarta, ita kam idan ya kira ta da yar kauye dariya yake bata.


Lallausan gashin sa tayi oiling kana tayi brushing dinsa, agogo ya mika mata, sai kuma ya mika mata hannun yana dan bata rai shi ala dole ita zata daura masa. Murmushi kawai tayi ta daura masa kana ta fesa masa turarensa mai matukar kamshi...



Jakarsa ya dauka kana ya matso dab ita lips dinta na kasa ya yiwa sucking na minti 2 Wanda bandan ya jure ba da babu abunda zai hanasa cigaba saboda d'ad'add'an kamshin bakinta da saliva dinta...


Cikin rada yace 'take care heemah bye!" Yafada yana daga mata yatsun sa biyu, Kana ya fice cikin tafiyar kasaitarsa ...



" ooh ya rabb help me! zai kasheni da salonsa"

tafada tana sauke ajiyar zuciya.


Dakin ta shiga gyarawa duk da babu datti, kasa ta sauka ta shiga gyara wa shima, wanka ta shiga bayan ta fito ta shirya kana ta fice wurin ummunta...





*5days later*


Sosai yanzu faheemah tadan saki jiki da fu'ad wanda hakan ya sa shi jin dadi duk da bai furta ba.




"Hmmm faheemah ana can ana bauta aure, ana fama da nakashashen miji" cewar mami .


Dariya jin dadi jameela da Mami suka sanya kana suka tafa kamar sa'anin juna.

"mami xanso ganin Faheemah yanda ta koma, na san ta dawo lawashi daya sha rana tsabar laushi"

ta Karasa tana dariyar mugunta, mami na kokarin bata amsa wayarta ya shiga ringing.....




"Hello hajja Hajara wai meya Samu wayarki sai kira nake bata shiga?"



"Wallahi kila sharrin network ne, amma lafiya wayata take

"

"mtssssssd" ta ja dogon tsaki kana tace


"ya akayi haka? Munafur ta ta kika yi daman?"


"Ban gane ba hajja hindu?" Baki ta faɗa baki a sake.


"Kada ki raina min hankali hajara, kinaso ki ce min baki san gidan da wanna kod'add'iyar 'yar kishiyarki taki take aure ba?"



"Wai kina nufin Faheemah? hhhhhhh ai tana can tana bauta wa nakashashen miji"



jin an ambaci Faheemah yasa jameela mikewa tsaye, itama burinta mami ta gama waya taji abunda ake cewa.



"toh kina raina wa kanki hankali domin Faheemah na auren dan gidan maragayi alhaji omar ishaq ne!"



"Buro.........."ta lailayo wata lukutar ashar kana cikin rudewa da kidimewa ta mike har zaninta na kuncewa, cikin daga murya ta sake lailayo ashar kana tace


"bai dai Omar ishaq daya shahara a duniya ba?"




"Eh kwarai shi nake nufi"


" Innalillahi! ya aka yi haka toh hajja hindu?"

Cewar Mami amatukar rude.


A ranta sai fadi take Anya kuwa? Kai ba dai faheemah bace...






"Ai ke zan tambayi wanna hajara." Hajja hindu ta faɗa cikin jin haushin Mami, kamar ta shako ta ta cikin wayar haka take ji.



"Ai wanna ba maganar waya bace gani nan zuwa yanzu yanzu hajja hindu..."




"Mami menene wai?"


"Hmmm jameela muje gidan kwata hajja hindu mayi maganar acan, muje muje kafin alhaji ya dawo..."



★★★


"Mama wallahi inasonsa, bata isa ta kwace ji a hannuna ba, dani wanna daular ya dace! dana sani dana jure na kula dashi, da duk ni zai nunawa wanna gatan, dani zai nunawa soyaayar daya nuna mata a bainar jama'a" tafada cikin kuka har shidewa take



Ran hindu a matukar bace ganin tilon yarta na Kuka.



"Yi shiru umaimah Fu'ad naki ne, rabuda yar matsiyata, dake ya dace gaki yar'uwarsa ai kwarya ta bi kwarya. Kawai so nake hajara tazo gidanan inji tayaya tabari har Faheemah taje gidan ummun taku har ta samu matsayi da arxikin auren fu'ad"


"Mama daman kin san ta ne?"


" Kwarai kuwa umaimah" nan ta shiga bata labarin faheemah data sani.........




Gama maganarta keda wuya suka ji sallamar Mami, hawayen umaimah Hindu ta yi saurin share mata kana ta basu izinin shigowa.




"Hajja Hindu k'wak'walwata ta toshe na rasa nagane kan maganarki" cewar mami a kidime tana kokarin zama.



Wata harara hajja Hindu ta watsa mata domin a ganinta tasan komai...




"Hajja hajara kenan kina so kice min baki san dan gidan alhaji Omar ishaq faheemah ke aure ba?

Ko wasa kike min da hankali ne? ba ke kika bawa hajja kaltume auren ta ba,

Ko bada amincewarki ta bar gidan ba?"




"Hajiya kaltume kuma? ban san wacece haka ba? Kuma kinsan ni, kin san tsanar dana ke wa wanna yarinyar ta ya ya kike tunanin ina ji ina gani zan bari haka ta kasance?" Nan ta dora da bawa Hindu labari zuwan Ummu gidan .........




A karshe tace "Wallahi ki yarda da ni kawata, ban gane abinda kike nufi ba"




Wani yawu mai daci hindu ta hadiya kana cikin muryan fushi tace" kin yi kurkure babba domin gidan arziki hadi da duk Wani jindadi rayuwa kika kai faheemah,

amma ban san dalilin daya sa kika ki gane arziki atattare da matar a xuwanta gidanki ba"



" Innalilahi wai da gaske faheemah na gidan jindadi ba gidan talauci da bauta ba kamar yadda nake tunani ba?"




"Na fiki shiga tashin hankali hadi da rudani hajara, naga alamar kina kokwanto, wacece wanna?"



Ta hasko mata fuskar faskekiyar wayarta mai dauke da hoton faheemah da fu'ad dake Murmushi.



Ai tsuman Zaune mami da jameela sukayi, luuuuuu mami ta tafi ji kake gwarab ta zube a kasan tiles...



Salati suka sa, duk suka yo kanta jijiga ta suka yi shiru bata motsi, ruwa mai sanyi a fridge umaimah ta dauko ta yayyafa mata, doguwar zuciya tayi kana cikin fitar hayyaci tace




"karya ne!

Wallahi baki isa, wanna arziki banaki bane, wahala, kunci , bauta ya kamaci rayuwarki faheemah, Hindu Kara nuna min hoton in gani" hajja Hindu kuwa ta sake hasko mata fuskar wayarta, ai Kara tafiya tayi luuu zata fadi suka taro ta.., "algugunman yarinya, daman tana gidan hutu da jindadi amma bata zo garemu ba, Wallahi baki isa ba, wanna gidan sai kin barshi, da diyata ya dace"...




Jin abinda take fada yasa hajja Hindu daga mata hannu



" kin ga hajara in ma mafarki kike Wallahi ki daina domin yata umaimah shi take so kuma dan uwanta ne, kinga waya dace ya aura?"



Sai ta hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya kana ta ɗora da cewa

" Wanna auran sai na warwareshi ko ta halin kaka" Shiru mami tayi bata kuma cewa komai ba, domin tana dan shakkar hindu, haka kuma Wani tunani datayi da ita kadai ta bar wa kanta sani yasa tayi shiru...




Umaimah kuwa sai antayawa jameela harara take ganin yadda ta kurawa hotonsu fu'ad ido tana sakin Murmushi ko maganar dasu mami keyi duk ba ji take ba.



Dogon tsaki umaimah taja daya dawo da jameela hankalinta, basarwa tayi ta ajiye wayan kan centre table dake gabansu , kana itama ta zabgawa umaimah harara



Ganin hajja Hindu tana yaba mata kananun maganganu yasa suka tafi babu sallamar arziki kai kace ba tight kawayen nan bane.


domin sosai hindu ke jin haushi mami, itama mami haushi ta take ji, jin cewar yarta umaimah zata auri mijjn faheemahn, ko waccensu da kudurin dake ranta.



"Mami wallahi lokaci daya naji ya kwanta min araina, inason shi sosai

ta fada tana lumshe kananun idanunta.



"Karki damu yar albarka ko duk abinda muka mallaka zai kare sai kin mallakeshi, ada ina tunanin salmanu shine mijin daya dace dake, ashe akwai wanda ya fishi kudi, kyau, wayewa. Gaskiya wanna yaron shine Mijin nunawa sa'a"...



Zallan farinciki ne ya bayyana a fuskar jameela, ada idan Mami ta Kira salman dinta da salmanu tana jin haushi amma yau ko kodan bata ji bacin rai ba.



"Nace diyar albarka wai har yanxu wayar yaronan bata shiga?"


Tabe baki tayi domin ita yanzu kam bata son wani zancen salman, "baya shiga" ta amsa atakaice,





"tabdi.... Amma yaron nan ya ci uwar rainin Hankali"


" ke ma Mami ki rabu dashi wallahi daga yanzu har duniya ta nade idan salman bai dawo na daina damuwa matukar zan samu mijin yar wahalar nan ( Faheemah)".


"Hmmm kuma haka ne yar albarka" cewar Mami.


Gyara zama Jameela tayi kana tace "Mami tunda gidan ba boyayye bane muje mu zuga surukarta ta yanda zata sa danta ya saki Faheemah".


murmushi Mami tayi kana tace "yaro man kaza kenan, bazan so muje gidan yanzu ba, duk da zuciyata na mun zafi jin wai asarariyar yarinyar nan na gidan daula. Zamu je gidan amma da shirinmu ta yanda duk maganar damuka gaya musu zasu amince nan take!"


" Yawwa mamina shiyasa nake sonki kin iya plan".





Dariyar farinciki Mami tayi, jameela tace "Wallahi Mami idan har muka fitar da Faheemah agidanan, Sai ta dawo abun kwatance, abun tausayi, ta yanda ba zata Kara ganuwa ba balle har tayi tunanin mallakar abin da yace ace nina sameshi, kullum tun muna yara faheemah Ita ke kwashe duk abunda ya dace da ni, har ila yau" ta fada cikin tsanar faheemah.



"Kedai bari yar albarka, ai munafuka ce yarinyar nan, zata san ta yi damu ne cewar mami, nan kuma tashiga zakin Faheemah ta uwa da uba kana ta dora da, basan ta yadda yarinyar nan har ta samu Kafan zuwa gidan attajirai nan ba, Sai tayi dariyar mugunta sannan tace faheemah ki shirya shiga rayuwar kunci, bauta, walaha fiyeda Wanda kika shiga abaya, na tsan........."




Ai maganar makalewa tayi ganin abbuh ya kura mata idanuwansa, saidai ko kadan ba zaka Karanci wani abu a tare dashi ba.




"Uhmm...am... alh...alh... aji sannu da xuwa yanzu ko dawo ?" tafada aduburbuce.


"yawwa sannu" kawai ya amsa mata. Kana ya kalli jameela dake gaishe shi. Amsa mata Yayi kana yace "ina Maganar mu ta rannan?"




"Umm abbuh wallahi har yanxu bai dawo ba. Wayarsa ma yanzu bana samu".



"Yayi miki kyau, toh daga yanzu banason Kara ganinsa akofar gidanan. Ki kuma tabattar da kin fito da mijin aure, domin wannan yaron banga alamun tarbiyya atare dashi ba kin jiko?"



"Toh abbuh in sha Allah zanyi yadda kace"


" Allah ya miki albarka" yafada yana shafa kanta.


Da "ameen" ta amsa cikin jin dadi domin tagama da babin salman koda ya dawo, haka kuma tana sawa a ranta cewa zata mallaki Fu'ad.



Ganin ya shiga dakinsa yasa Mami sauke boyayyen ajiyar zuciya, domin boka ya fada mata cewa ta daina ambatan sunan Faheemah a gabansa, idan ba haka ba kuwa , zai tuno wacece Faheemah agareshi...



Zaune yake a hadadiyyar office dinsa yana shigar dawasu bayyanai...


kofar office din yaji ana knocking...


Runtse idanunsa yayi kana ya bude ahankali, Domin Sam baya son idan yana aiki ana katse shi, musamman da wanna ya kasance na office. Kamar ba zai yi magana ba Sai kuma yace " come in" turo kofar akayi, cikin tafiyar jan hankali ta shiga takawa zuwa garesa.


Black hill din kafarta ya fara bi da bi kallo kana ya sauke idanunsa a fuskarta daya sha heavy make up.



" Good morning sir" tafada cikin kissa.


"Morning, how may I help you?" Inji fu'ad




"Haba my Fu'ad sai shareni kake, haka ma gurin bikin ka baka bani fuska na gabatar maka da friends dina dana gayyota domin kawai su ganka haka ka kunya tani, Am so sorry idan fushi kake saboda abunda na maka abaya, kayi hakuri please"

tafada tana hada hannayen ta



"kin gama, I said kin gama? If yes! Leave my office"


kwallan karya ta fara matsowa kana ta tsugunna gabansa.



"please my Fu'ad ka amince min muyi soyaaya wallahi zan mallaka maka kaina matukar zaka saurareni. Kalleni da kyau da me wanna Karamar so called wife dinka ta fini?"



Check me out ta fada tana balle botiran gaban suit dinta


"Heyy stop this nonsense" are you insane? Bar min office" ya faɗa cikin Daga murya.



"Haba dan Allah kayi hakuri please don't be mad at me karka yi fushi banason bacin ranka"

tafada tana shafa cinyarsa har ta gangaro zuwa maransa...




wani Mari ya kife ta da shi, kana ya hankadata, cikin matsananci fushi yace

" baki da Hankali ne, na

miki kama da mutumin banza? Da kike ce wa matata Karamar yarinya ce ta fiki sau million agareni, itace farincikina, itace mahadin rayuwata".

Cikin daga murya dabai san yana da ita ba ya kara cewa "Leave my office before I squeeze your bone like an orange"




"Ok fine, I will leave".



Ta fada tana murmushi sai ta shafi fuskarta tace



"wayyo dadi! yau wanna soft hand din naka ya shafi fuskata, you no what? Wallahi banji zafin Marin ba, Saboda laushi hannunnka please gobe ma ka sake marina , I love you so much byeee"



Tafada tana huro masa kiss kana ta fice cikin tafiyan jan Hankali.





Cikin mamaki yabi ta da kallo, yasan dai salma bata da kamun kai amma be san yakai haka ba.


Kwafa yaja kana ya zauna, iska mai zafi ya furzar daga bakinsa, cikin husky voice dinsa dake cakude da bacin rai yace



" I will teach you a lesson of your life idan har kika sake shiga rayuwata...."





Karfe 4:00pm daidai ya tashi, a chicken republic yatsaya ya siya musu manyan manyan kaza guda hudu da yoghurt kana ya nufi gida, Horn ya danna aka wangala masa hadadiyyar gate din gidansu, hancin motarsa ya danna cikin yalwattacen haraban gidan cikin mutunta juna suka gaisa da malam iro kana ya bashi Leda kaza daya, bai saurari godiyarsa ba ya nufi parking lot domin faka motar.


Part din ummu ya nufa da sallama dauke a bakinsa....



Ummu Kadai ya tarar a falon.


Cikin farinciki ganin mahaifiyarsa ya saki murmushi itama ta mayar masa da martani. tsunnawa yayi agabanta ya Dora kansa a cinyarta cikin kasalaliyyar murya yace


" ummunah sannu da gida"


cikin kaunar yaronta ta shafa kansa kana tace


"welcome home son! Ya aiki?"



"alhamdulillah ummunah"


ya amsa yana zama kan hadadiyyar royal chair dake falon.



"Ummu ina sister ne?"


"Uhmm wanna sarkin wayan tana dakinta"


" Okay" ya amsa kawai kana ya ajiye mata leda biyu na kazar.

Lumshe idanu yayi kyaakyawar fuskarta na masa gizo, burinsa yanzu Yayi tozali da ita.


" Son!?"


" Na'am ummu"


"na ce ya kamata kaje ka huta naga da alama yau ka gaji ko?"



" wallahi ummu na gaji" yafada yana kwabe fuska



"maza je ka huta, an barmin yarinya ita kadai, ni yau tun safe rabona da ita kace mata ina gaidata".



Murmushi yayi yana jin dadi yanda ummu da Faheemah ke tsananin son juna Hakan na masa dadi sosai...


" zata ji ummunah"


mikewa ya yi ya sumbaceta a hannu kana ya bi ta baya ya shiga part dinsu....


Tun daga parlour yake jin kamar sautin Kuka na tashi daga dakinta cikin sauri ya nufi dakin hadi da turawa...






_ina godiya makarantar rayuwar faheemah, ina jin daɗin yanda kuke karban ko wani book nawa, much love habibte's_





I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or

*460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.


*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 0806626851





Share

Comment

Vote



Thanks for reading

my novel

# rayuwar faheemah





#NoorEemaan🥀🌸

***