69-70
by @nooriman
🍇🍇RAYUWAR FAHEEMAH🍓🍓
Wanna littafina kyauta ne (free novel)
#Ending
69-70
(Not edited)
A cikin daren rana ta ukun ne ta haifi yan biyu mace da Namiji, zuwa lokacin ta galabaita domin ko motsi bata iya wa, sai da safe bayan anyi wa babies wanka da mummyn su aka Shigar dasu dakin hutun.
Sai a lokacin aka bawa su Ummu damar Shiga, ai fu'ad na Shiga wurin matarsa ya nufa. "faheee ta are you okay? Mike miki ciwo yanzu sannu wiffy! Yanzu me zaki ci"
Ya tambayeta Cikin alamun damuwa, riko hannu sa dake kan fuskar ta tayi kana ta ce "my maaan wacce tambaya kakeso na amsa maka yanzu?"
"Dukkan su Wiffy, I just want to be sure if you are ok"
"Am fine zauj, am very fine"
Murmushi jin dadi yayi Kana ya bata light kiss a lips dinta da suka yi jaa saboda walahan nakuda. Lolz.
Dan zaro ido tayi ganin yayi kissing dinta a a gaban ummu, kallo ummu tayi taga sam hankalinta na ga twins ajiyar zuciya ta sauke, dariya ta bashi yana tunanin ko yaushe zata daina kunyar nan mai yawa, duk da yana son kunyar ta
Ummu ce ta miko masa baby girl din, kura mata ido yayi yana jin matsananci soyaayar ta na ratsa shi, Namijin Ummu ta sake Dora masa a cinya, ai dariyan farinciki yayi, dukkan su Kama suke dashi kamar yayi kaki.
Haka kuma soyaayar yaran sai ratsa zuciyar sa take, godiya yayi ga Allah daya bashi kyautan yara har biyu at once.
"Fahee na miki wayo babu wanda ya yo ki a babies dina" Yafada yana mata gwalo.
Dariya Ummu da fareesa sukayi har da anwar da ya kawo fareesan Yanzu.
Kwabe fuska tayi kana a hankali yadda su biyu kadai zasu ji tace "zan rama nima next" kashe mata ido daya yayi yana dariyar tsokana.
Kasancewar lafiyar su lau yasa aka basu sallama, direct gidan suka nufa domin abbuh yace ta zauna a gidan ta zai fi tunda ba addini bane yace lallai sai mace tazo gida wanka, baya ga haka yasan cewar Ummu zata kula da ita kamar yar da ta haifa, sosai hakan yayi wa fu'ad dadi, domin daman yasa a ransa idan ma aka ce zata je gidan su murje ido zai yi yace bai amince ba.
Hakan yasa Mami tace zata je gidan ta taya Ummu kula da faheemah'n.
Duk da bakomai zata iya yi ba saboda hannunta daya, amma abbuh yaji dadi kwarai, ya kuma yarda lallai mami ta tuban gaske.
Ranar suna yaran suka ci sunan baban fu'ad ( Omar) da kuma sunan Ummin faheemah ( Haleematusa'adiyya ) amma za'a dinga ce musu Ayman da Aymana.
Sosai faheemah taji dadi haka ma abbuh domin fu'ad yayi musu Kara.
Sai da suka yi arba'in, kana mami ta koma gida.
Jameela ta hadu da sani a lokacin da mami ta aiki ta kasuwa. yi yayi kamar bai ganta ba, saurin shan gaban sa tayi ta roki shi gafara, kasancewar shi mai sanyin hali yasa shi yafe mata domin yana da labarin duk abunda ya sameta. cikin wata daya suka sake saba wa kasancewar har yanzu akwai tsohuwar soyaaya yasa suka daidai ta Kansu domin daman kwadayi ya sa ta bar shi, bai boye mata yana da aure da yarinya daya ba, ta amince masa, ta fara kokarin gaya masa haduwarsu da salman ya dakatar da ita kana yace mata ya san komai, hakan ya bata mamaki kwarai, bayan wata daya aka daura musu aure ta tare a gidansa Wanda kuma alhamdulillah suna zaune lafiya da kishiyar ta.
★★★
Zuwa yanzu FAHEEMAH ta Fara zuwa northwest university dake kano (YUMSUK)
domin tace tafi sha'awar yin karatu a kasar ta, Kuma jihar ta.
a ranar da zata fara zuwa fu'ad ya bata kyautar had'add'iyar mota mai kalan ja, a cewar shi duk ranar da yake busy sai ta kai kanta school domin baya son ta hau mota driver ya tuka ta, yayin da lUmmu ke kula da yan jikokin ta tareda taimakon masu aiki.
Karatunta take cikin kwanciyar hankali haka kuma tana samun support din gwarzon mijinta....
Fu'ad ya ginawa faheemah katon supermarket mai dauke da sunanta. ranar ya shirya mata surprise domin bata da labari, yana tsayar da motar ya fito hadi da zagayawa ya bude mata kofa, bayan ta fito yace "look up faheeeta" daga manyan idanunta tayi taga an rubuta *FAHEEMAH SUPERSTORE* ai wata runguma ta masa ta shiga zuba masa godiya, sauri sa hannunsa yayi a lips dinta alamun bayaso, Sosai tayi murna mara misaltawa, domin bayan sun shiga har staffs din wani girmamawa na musamman suke bata, har office dinta ya nuna mata gwanin kyau... A ranar ta faranta masa sosai domin nuna godiyar ta agareshi.
Bikin umaimah saura sati biyu, har gida ta kawo wa fu'ad katin aurenta, ta kuma sake neman yafiyar su, sun kuma yafe mata domin sosai faheemah ta lallabashi kafin ma ya yarda ya fito.
Da za ta tafi fu'ad ya bata 1million a matsayin wedding gift dinta, wanda faheemah taji dadin yanda ya manta komai, Shiyasa take alfahari da gwarzon mijinta a kodayaushe...
Washegari faheemah da fu'ad suka je gidan malam haroon dake kurna, domin sun bar yan biyu wa kakar su( ummuh) Sosai malam haroon yayi murna bayan fu'ad ya gaya masa cewa abbuh ya dawo tunaninsa, daza su tafi fu'ad ya bashi bandir daya na 1k ya dinga shi musu albarka.
*4month later*
Cikin kuzari suke excerise a dakin motsa jiki dake part ɗin su, gaba daya sun hada gumi a sakamakon excerise din, tana bangaren kayan training din mata, yayin da shi ma yake bangaren kayan training din maza, cikin kwarewa yake daga karfe yayin da duka faffadan kafadunsa sun fito, ga babies kwance cikin Walker dinsu suna ta wutsil wutsil da kafa, after 30minutes faheemah ta sauko yayin da shima ya ajiye karfen, ruwan gora mai sanyi ya balle murfin ya sha rabi hadi da Sanya mata rabin a baki ta shanye tana sauke numfashi, murmushi yayi kana cikin tsokana yace
" raguwa"
bubbuga kafafu ta Shiga yi cikin shagwaba, saurin hade bakinsu yayi kana ya dauke ta cak kamar baby doll domin duk da ta haihu jikin ta na nan da kyaunsa kamar ba ita ta haifi cute babies din nan ba.
Aymana ce ta fara kuka a hankali ya xare bakinsa, ya jawo hannu ta kana ya zaunar da ita a sofa dake gyming room din, dauko aymana yayi ya Dora mata a cinyar ta kana ya daga half- vest dinta da Kansa ya sanya wa yarinyar, ta kama mama ta fara sha, ayman ya dauko shima ya Sanya masa a baki ya fara tsotsa.
Kwabe fuska tayi kana kalli fu'ad ta ce "Allah my man Aymana ta fiye ci, abbana ya fita hakuri"
murmushi yayi kana yace "bar min ummina ta ci please, baya ga haka inason ganin kina basu mama ,you look more beautiful than ever goofy angel"
Murmushi tayi kana tace
"I so much love you my man, the father of my children".
shima yace "I love you too Mrs fu'ad you are my everything"
Murmushi ta sake yi kana tace "Allah yabar mu tare har a aljanna domin kai din tamkar GARKUWA ne a *RAYUWAR FAHEEMAH*"
ta fada tana sakar masa kyakyawar murmushin ta, shi ma cutest smile dinsa ya sakar mata idanunsa cike da mayen soyaayar ta ya sake cewa
" I love you" hadi da bata Peck a goshinta dake cike da gashi kwatance kamar na jirarai.
Zagayo wa yayi ta bayan su kana ya dauke su Selfie da wayar sa fuskarsu cike da annushuwa.
*Nasan zaku ce ban kuma sako labarin salman ba. Kwarai hakan na faruwa a rayuwa kaga mutum ya shigo rayuwar ka da sharri ko alkhari , amma kuma ba lallai bane ka sake ganin shi, wani hisabin sai a lahira kawai. Allah yasa mudace*
ALHAMDULILLAH
THE END.
Special thanks to Abdul_rasheed mustapha (budu mie) for the support.
Special thanks to:
Sawun Giwa novels
S square novels
Noor Novelist world
Sarautau's library
Fitar rana group
Surrayhms novels
Nana haleema palace
Fadar Ummu Affan
Daular dalingo
Matan buri fans
wallahi groups din da yawa, time ba zai bani damar lissafo ku ba, amma ina godiya agare ku gaba-daya, Allah ya bar kauna.
*Kuyi hakuri banyi editing wasu wurare a book din ba saboda wasu uzurori nawa, so idan kunga typing error ku min afuwa, sannan wanna shine littafina na farko, shi na fara rubutawa kafin na yi mijin Ammi na ne sila, papi ne, kyautar koda, Abraham, Hoorain mai kusumbi. Na kuma ngd da yanda kuka karbi Novel ɗin, duk da kara reposting din shi nayi*🥰
Anan na kawo karshen book dina mai suna RAYUWAR FAHEEMAH kurakuran Dana yi a ciki Allah ya yafe min da ma Wanda ya karanta, Wanda nayi daidai Allah ya hadu mu a ladan (ameen).
Ban yarda a juyamin labari nan ta kowacce siga ba, idan kunne ya ji......
⚠️RAYUWAR FAHEEMAH
Hakkin mallakan NoorEemaan ne⚠️
All characters in this story are all drawn from my imagination any resemblance of story or life style should be considered as a coincidence.
Allah ya karbi ibadun mu a wanna watan radaman din da muka shigo Allah ya sa muyi ibada karbabiyya ameen.
Gaisuwa dubu ga masoyana a duk inda kuke, Noor na muku sahihiyar kauna💞
I love my fans
***
***
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851