kyautar koda

13-14

by @nooriman

πŸ‡πŸ‡Ζ˜Ζ³AUTAR ƘOƊAπŸ“πŸ“

(Its all about love, scracife, hatred and destiny)



*First edition*



_by NoorEemaan_πŸ“šβœοΈ



Wattpad

@NoorEemaan






Juma'at Mubarak to all Muslims ummah,

Allah ya sa damu da Alkhairi cikinta, yasa muyi kyakyyawar karshe, mu kuma cika da kyau da imani. NoorEemaan na kaunar ku my fans❀




_I must say this....πŸ˜ƒ What a coincidence! a ranar da nayi typing wanna page din Friday ne, which is last year, ikon rabbi kuma Gashi nayi reposting again still that Friday_😻



***

Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.



Page 13-14



............A sanyaye ta karaso gaban su, daidai lokacin Daddy ya dagawa bodyguards dinta hannu alamun su tafi, ba musu suka fice kasan su a kasa alamun girmamawa, yayinda suka ji relief na ganin Fadeelah, akasin hakan kuma da sunan su gawa a hannun Alhaji Imran.




Bin bayan Daddy Fadeelah tayi har main parlour, hannun sa goye a bayan sa ya juyo gareta kana ya jefa mata tambaya kamar haka " a iya sanina 'yata mai bin umarni na ce, sannan bata da wurin zuwa daga company sai gida, sannan yaushe kika fara fita ke kadai ba tare da bodyguard ba princess? Did you know thousands of enemy we have out there? (Kin san dubanin makiyan da muke dashi a gari?)" Ya karasa a dame, yana nuni da yatsa, duk yanda yaso yi mata fada abin ya gagara, matsanancin soyaayyar 'yarsa ta hana shi yi mata fada domin sam baya son ganin bacin ranta koda na sakan daya ne.



Ajiyar zuciya ta sauke, domin abinda tayi tunani daban, tabbas ta san cewa kaunar da yake mata yasa yake bata tsaro domin kula da lafiyar ta. Cikin zallan son mahaifin ta kana murya a sanyaye tace "am so sorry Daddy, bazan sake fita ba tare da bodyguard ba, na fita shakatawa ne, ganin ba nisa nayi sosai da gida ba yasa nace su taho gida" ta karasa cikin shagwaba da marairaita ta yadda zai fi tausaya mata.




Murmushi mai taushi ya sakar mata, wanna maganar da ta yi ya wanke masa dukkanin damuwar daya dauki awanni cikin sa, "its ok my princess, sannan ki dinga barin wayar ki a bude saboda irin haka, domin dana samu wayar ki da hankalina bai tashi haka ba"




Murmushi tayi, domin soyaayya ta dauke mata hankali har ta manta da wata aba wai waya "in sha Allah Daddy zan kiyaye, ina Mommah nah?"




"Tana part d'inta tun rana kanta ke ciwo, ita ma hankalin ta gaba daya ya tashi da rashin dawowarki... ni nace taje ta kwanta ta samu huta, yanzu zanje part dinta domin sanar da ita kin dawo saboda hankalinta ya kwanta, ke ma je ki huta good night" ya fad'a yana bata sumbata a goshinta....





Handbag dinta kadai ta ajiye kana ta dauki gum(gam) data siya takanas domin manna hotunan da yakan zana na fuskarta a duk haduwar su.



Tsaye tayi tana bin zanen da kallo wanda yanzu sun dawo shida reras, har yau ta kasa gane wanne yafi kyau cikin zanen domin dukkansu ba baya wurin kyau, murmushi take saki akai- akai hirar da suka tayi dazu ke dawo k'wak'walwarta, daga karshe ta cire kayanta ta fada wanka bayan ta kunna wayoyinta, ta jima sosai a toilet duk cikin sunan wanka kana ta fito daure da towel, lotion mai k'amshin gaske ta shafa kana ta sanya pajamas masu kyau pitch color na company *NIKE* dan karamin hijab fari half sunnah ta sanya, wata yalwataccen jallabiya kirar saudiya ta dora kan pajamas din kana ta tayar da sallah...


Bayan ta iddar ta cire jallabiyan ta haye gado, take wayarta ta dauki kara, lumshe ido tayi kana ta bud'e a nutse murmushi dauke kan fuskarta domin tasan Fadeel ne, domin shi kadai ta sanyawa wanna ringing tone din, latsa Kore tayi ta kara wayar a kunnenta hadi da furta "Assalama alaykum" cikin zazzakar muryarta.


"Wa'alaikumu salam" ya amsa yana kara curewa kan 'yar yololuwar katifarsa da alama muryar tace ta haddasa masa shiga wanna yanayin


"My darling yakike, ya gajiya, Fatan kin je gida lafiya?"duka ya jero mata tambayar a lokacin daya.

A shagwa6e tace "Alhamdulillah, wallahi my one na gaji sosai, amma yanzu na fara warwarewa sak'amak'on jin muryar muradina, muradin raina, Yes my heart desire".

Murmushi ya saki cikin wani sabon shauki yasake k'amk'ame jikinsa kana yace "I hope ina tare dake, I hope yanzu mu ma'aurata ne dana yi miki tausa" ya karasa cikin rada.


Murmushi mai sauti ta saki, tana ji ina ma Ina ma su din ma'aurata ne, da hakika sun gina rayuwar aure mai cike da so hadi da birgewa.


"Darling kaunar ki zata haukata ni, kinsan har mafarkin nake akan ki kullum, jiya da asuba Mahmah tazo tashina Saboda na makara taji ina ta kiran Fadeelah cikin bacci, dan Allah ki rike mun amanar kanki bazan iya juran rasa ki ba a rayuwa, ji nake tamkar dan soyaayyar ki kadai aka halicce ni" ya karasa cikin iyakar gaskiyar sa.


Pillow ta k'amk'ame a kirjinta, maganganun sa na shiga jini da tsokar jikinta har wani tashi sigar jikinta ke yi alamun maganganun na shigar ta sosai.




Cikin wani salon so tace "my one, kasani cewa babu kowa a birnin zuciyar Fadeelah fiye da Fadeel dinta, sannan Abadan da'iman muna tare, mutuwa ce zata raba mu in sha Allah"



Ajiyar zuciya mai karfi ya sauk'e daya sanya taji wani sabon so da tausayin sa, cikin muryar rada yace "Darling mutuwar ma nafison ta d'auke mu a lokaci daya, ko kuma ni na fara mutuwa domin bazan juri rasa ki a rayuwa ta ba..."


Katse shi tayi da cewa"gwara ta dauke mu a lokaci daya, mu tafi tare, nima bazan juri rasa ka ba my one, we are made for each other I love you"



"I love you so much too my Darling, ki kwanta kiyi bacci, ki yi mafarkina bye muaaahh" ya karasa da sakar mata sumbata ta wayar



Wani sanyi dadi ke ratsa ta hakika babu abinda ya kai kasamu masoyi mai son ka tsakani da Allah. "love is sweet when it's new, sweeter when its you fadeel, and sweetest when it's pure" ta fada a bayyane fuskarta d'auke da murmushi, addu'ar kwanciya bacci tayi kana ta rufe jikinta da duvet babu jimawa bacci mai dadin gaske masu cike da mafarkin Fadeel ya d'auke ta...



*WASHEGARI*

suna zaune a dinning table suna breakfast, Fadeelah sai murmushi take ita kadai har Daddy ya farga yayi gyaran murya hadi da cewa "My beautiful princess, wanna murmushi fa ke kadai? kwanan nan na kasa gane miki fa, You seems over happy" ya fada shi ma da murmushi kan fuskarsa alamun farincikin daya tsinci 'yarsa a ciki yayi masa dadi...




"Atoh professor nah, taya ni tambayar ta, domin yanzu hardly kaga fuskar sweetheart ba murmushi, ya dai kamata ki gaya mana what's the secret behind" Mommah tace tana kai Irish omelette bakinta.




Dariya tayi cikin jin kunya, kana tace "babu komai Daddy, Mommah"


"Haka dai kika ce, amma bari idan tayi tsami zamuji koma menene, ko professor nah?" Ta fada tana kallon Daddy.


"Haka yake my first Lady" Daddy yace cikin salon su na manya.




Fadeelah kanta a kasa tana cin chips dinta daya bayan daya, yayinda take tunanin shin ta gayawa Daddy'n ta cewa ta samu mahadin rayuwar ta, a life partner ko a'a?....✍️





_In sha Allah gobe ma zan sake baku sabon update da sannu zamu shiga cikin labarin..._

_Amma two pages as promise tunda reposting muke_



*Thanks my people da kulawar ku gareni a sakamakon jina shiru da kuka yi jiya, i was damn busy ko data ban kunna ba jiya, wadanda suka yi min mgn private dama groups, ina godiya sosai*




Share


Comment


Vote


Editing is not allowed❌



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I'm

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call *****