53-54
by @nooriman
🍇🍇KYAUTAR KODA🍓🍓
(Its all about love, scracife, hatred and destiny)
*WATTPAD*
@NoorEemaan
EDITING IS NOT ALLOWED❌
***
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.
Page 53-54
Sosai Alhajin yake ja na a jikinsa, hatta idan zasu ci abinci sai ya kira ni mun ci tare, tunda nazo gidan ban ga wani d'a ko 'ya tasa ba, daga shi sai matar sa, su kadai ke rayuwa a cikin gidan...
Sati daya a gidan, da yamma alhajin ya kira cewa, na shirya gobe ne zamu yi gasar zane. Da toh na amsa kana na koma part din da suka bani, ƙarƙi manta kullum tunanin ki, hadi da matsanancin kaunar ki na nan daram a raina, bana iya bacci, Saboda tunanin ki da fargaban rasa ki, sosai nayi add'ua kan Allah ya bani sa'an wanna gasar.
*WASHEGARI*
Muka fita da alhajin zuwa inda za'a yi zanen, Hada'dd'en waje ne, mai dauke da duk wani abun bukata na zane, abokan gasan nawa babu wani talaka a cikinsu, domin hudu daga ciki ma turawa ne, amma still ban karaya ba, awanin shida aka bamu domin mu gama.....
Bayan awanin hudu na gama na saka suna na daga dan kasa in a fashionable way, sai dai ban rubuta full ba, *FFM* haka na saka sunana kana na miƙe.
Taƙe na ga abokan gasar tawa suna min dariya, ganin nine mutum na farkon gamawa, a tunanin su ban iya komai ba, Domin babu wanda ya sanni a duniya a matsayin architecture...
Bayan awanin biyu naga sauran masu zanen suka fito, Wani wajen mai kyau aka ƙai mu haɗi ɗa bamu hada'ɗɗen abinci da abin sha, suƙa ce mu jira har a kira result din wanda ya zo na daya.
Sam na kasa ko da shan ruwa ne, burina ƙawai a kira result na ji ko na ci, sabanin sauran dake cin abincin su cikin raha da farinciki, ni kuma ina gefe, ban shiga cikin su ba, domin irin kallon kaskancin da suke min, abinda na tsana ƙenan raini da wulakanci, duk da kasancewa na talaka bana daukar raini, komai arzikin mutum kuwa, domin sam bana son zuciyata ta mutu kan abun duniya.
*Da Misalin Karfe Shida Ɗa Rabi Na Ƴamma*
Muna zaune a wanna wajen ɗai da aka bamu, muna jiran jin sak'amak'o, bayan sallar bana ko motsi....
babu zato ɓaɓu tsammani muka ji muryar wata mace ta wani loudspeaker domin maganar ta karade ila'irin wajen kamar haka "The winner is FFM, congratulations to you"
Take na zube kasa nayi sujjadul-shukur, Yayin da hawaye masu dauke da abubuwa da dama suka zubo min, Sosai nayi farincikin hakan, finally ni na ci.
Abokan gasar zanen nawa kuwa, mutuwar zaune suka yi, domin basu taba tunanin cewa zan zo ana karshe ba ma, domin a dakin da muka yi zanen babban ne, sannan akwai tazara mai dan yawa tsakanin mu, babu mai ganin zanen wani...
Mutum daya ne daya kasance baƙin fata dan garin Ibadan ya min murna, kana ya fada min cewa "na maka murna sosai bro, congratulations! tabbas a rayuwa kada ka taba raina ko wulakantawa mutum komai kaskanci shi kuwa, hakika na koyi wani darasi daga gareka.." Yana fadamin haka yana ficewa daga wajen...
Nan sauran suma suka tafi cike da jin haushina ko nace tsana ta, domin naga hakan ta idanun su.
Bayan awa d'aya Alhajin ya fito yace mu koma gida, fusk'ar sa dauke da murmushi kana da sauran mamakina kan kwarewa ta, domin zanen yayi kƴau mai ban mamaƙi
Bayan munyi sallah, mun ci abinci a part di'n alhajin, ya mike ya shige bedroom d'in shi, babu jimawa ya d'awo dauke da wata madaidaicin jaka ya mika min....
Fuska ta da alamun tambaya nace "menene wanna alhaji"
Murmushi yayi yace "hakika kai gifted ne, kana da talent na zane sosai, kayi matuk'ar iya zane, wanna jakar mai dauke da million hamsin naka ne, ma'ana shine hakkin ka na zanen"
Sosai na shiga rudu, domin ban taba tunanin samun koda million ɗaya ba, cikin rudewa nace "Alhaji nawa ne million hamsin? dan Allah ka fadamin, zai Kai na iya mallakan Fadeelah ta? kudin zai isa da har Daddy zai bani auren Fadeelah?" Na fada hawaye na ciko idanuna, domin a lokacin burina na mallake ki.....
Sosai alhajin yayi mamakin ganin ban yi murna samun makudan kudaden nan ba, sai ma sunan ki daya ji na kira, hakama matar sa.
Hannuna ya riko yace "hakika akwai abubuwa da dama cikin tarihin rayuwar ka, wacece wanna fadeelah'n sannan waye zai ki baka auren ta?, ka fadamana labarin ka nayi alkawarin taimaka maka da dukiyata da ma duk wani abu da zaka bukata"...
Ban musa ba, na basu tarin rayuwata, dama labarin soyaayyar mu, kin san menene? Ya tambayi Fadeelah, girgiza kai tayi Yayinda taƙe k'irjin shi har yanzu.
Gani nayi alhaji yana zub da kwalla, matar sa kuwa rushewa tayi da kuka, wanda na zallan tausayi ne...
ɓaƴan wasu mintuna yayi gyaran murya yace "idan kace zaka yi aure da duk kudinan daka samu, Tayaya zaka yi arziki? Tabbas mallakan Fadeelah a matsayin mata shine cikar farinciki ka, amma ba yanzu zaka je gareta ba, business zaka yi da kudin nan, sannan zan maka hanya ta yanda duniƴa zata san cewa kai babban architecture ne! hakan zai sa cikin lokaci kankani sunan ka ya daukaka, har ka dinga samun kudaɗe masu yawan gaske, idan arzikin ka ya sake bunkasa sai ka fara gina gida, Bayan nan ka zuba motoci, Bayan ka gama hada dukkanin abinda kasan cewa mahaifin ta zai baka auren ta, sai muje kwatsam"...
*******************************
Sosai suna na ya ɗauƙaƙa a duniya, a matsayin *Architecture FFM* duk yanda yan jaridah da yan gidan TV suka so hira dani ban bari ba, kana ban bari sun dauki hoto na ba, ina mamakin wai nine yau yan jaridah ke rububi akai, hakika idan baka da shi a duniya ka zama dan kalllo.....
Sosai na yarda da shawaran alhajin, cikin lokaci kankani na fara bushiness, ga manyan zane na masu kudi da nake ta samu abin har yawa yake min...
In tak'aice miki, cikin watanin kalilan nayi arzikin da ni kaina ban san yawan su ba, abu na farko dana fara yi shine gini na, wanda na zane ne da hannuna, na kuma yi shi a garin lagos domin nan nake sha'awan zama, sannan na zubo motoci da duk wani abun more rayuwa, na zuba ma'aikata, hadi da bodyguard's masu bani tsaro kamar yadda alhaji yace lallai sai na samu bodyguards domin tsaro......
a lok'acin dana shiga katafaran gidana sai dana yi kuka tuno Mahmah nah.
A dalilin rashin babu(kudi) cuta ya cita har ta koma ga Allah, sai bayan ranta nayi arziki da ban taba mafarki ba, sai kuma ma tuna haka Allah ya kaddara mana....
Daga wanna lokacin alhajin ya dauke ni tamkar Ɗan sa, daga baya yake fadamin duk tarin dukiyar sa, Allah bai basu haihuwa ba, amma mutum bazai gane hakan ba, domin suna zaune cikin farinciki, sun ƙuma fawwalawa Allah lamarin su.
A lok'acin dana ji cewa anyi baikon ki da Jameel na kusan zaucewa, domin ina sa ayi min bincike akan abinda ya shafeki..... Babu bata lokaci na samu Alhajina nace dan Allah ya taimaka su je tambayan min auren ki domin bazan jure rasaki ba a karo na biyu...
Sosai alhajina ya kwantar min da hank'ali, yace akwai shiri na musamman da yake yi, yana so komai yazo a bazata, yace na yarda dashi, na bar komai a hannun sa, ban sake cewa komai ba, amma kullum tunanin ki nake, ina fargaban rasaki, ga kuma tarin sonki dake nukurkusata, sau da dama ina son zuwa gareki alhajina ya hana yace na bari komai ya tafi kamar yadda ya tsara....
Makudan kudade da ban san hadadin su ba na bawa matar Alhajina domin ta hada min lefe, cikin kankani lok'aci ta fita kasar waje ita da wata kawarta da kanwarta suka hado....
A ranar da loƙacin dasu Jameel za su kawo lefe duk muna sane, hakan yasa alhajina yace a kawo nawa kafin su jameel su kawo nasu, hakan zai kawo rikitarwa.....
Nan matar Alhajina dama yan'uwan ta da wasu kawayenta suka k'awo lefen, Bayan kwana biyu muka zo estate dinku Alhajina yayiwa Daddy bayanin cewa yayi haku'ri, mun yi nema cikin nema amma ba laifin sa bane, Dan sa ya na matuk'ar son fadeelah da dai sauran su....
Abu biyu ne ya bani mamaki, Daddy bai ki amincewa ba, ban saniba ko dan alhajina yafi mahaifin Jameel dukiya ne, Allah masani.
Sannan abu na biyu Daddy bai gane ni ba, bai gane cewa nine wanna bakin talaka fakirin bane...
Naso zuwa gareki a ranar da muka zo wajen Daddy, still alhajina ya hana yace na bari sai ranar daurin aure domin inyi miki bazata....
Ajiyar zuciya Fadeel ya sauke kana ya cigaba...
har yau da aka d'aura mana aure, daddy bai san cewa nine Fadeel ba, ina matsayin dan Alhaji Sufyan Rufa'i ne a wajensa.....
BACK TO STORY
Kara rungumeta da kyau yayi, yana jin farincikin mallakar ta a matsayin mata, yace
"wanna shine tarihin Bayan rabuwar mu a tak'aice...."
Muje zuwa da sauran chakwakiyya😎😎😎
A tayani share dan Allah👏🏻
Share fisabilillah
Comment
Vote
NoorEemaan
***
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *****