IDAN BA KE

Page 4

by @nimcyluv

A kusan tare macizan guda biyu suka ƙara fasa kai tare da kaiwa juna sara, ko wanne maciji ƙoƙarin jiwa ɗan uwansa ciwo yake da ganin ya kashesa har lahira. Gaba ɗaya macizan suka sarƙafe juna tare da nan na ɗewa waje guda ko wane huci yake yana fitar da hayaƙi ta baki nisan yadda Prince wanda ya a rikiɗe zuwa maciji ya matse macijin da Za'ai wasa dashi, gaba ɗaya ya ji masa rauni a hankali kuma Prince ya buɗe bakinsa ya fara haɗiye Macijin zuwa cikinsa sai daya haɗiyesa tsaf kafin ya sulale gefe guda ya kwanta yana mai da numfashi Wahala, sai fasa kai yake kamar zaici babu zuciyarsa tayo sama baki ɗaya zai iya sarar ko waye a wannan lokacin.


Sarkin ruga ya kalli tarin jama'ar da suke wajan hadda Shatu da Hamma Yabi, da sauran mutanan rugar kafin ya numfasa ya ce "Lokaci ya yi ake a kawo mana Halisa Dajeno Rome cikin fili, domin su fafata da maziji yau ranar tace" Wani mai suna Giɗaɗo ya rusuna tare da faɗin "Yanzu za'a kawota" yana faɗin hakan ya kalli Hamma Yabi tare da faɗin "Maza jeka kawo ɗiyar taku, tana ɓata mana lokaci" Hamma Yabi ya ce "Yanzu za'a kawota" yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi bukkarsu tun daga nesa ya hangeta kwance a bakin bukkar inda Prince ya kwantar da ita tana barci. 

Cikin sassarfa ya ƙara yana faɗin "Assha Subuhanallahi barci a ƙasa Danejo" ya faɗa yana ɗagota tare da jijjigata sosai, da sauri ya buɗe idanunta tana zabura "Hamma Yabi yaushe na dawo nan?" Kallonta yai ya ce "Kina nufin baki san lokacin da kika kwanta a nan ba?" Girgiza kai tai ta ce "Aradun Allah ban shina ba, kawai naji iska mai daɗi ta lulluɓeni wani barci yazo mini daga nan ban san komai ba" Girgiza kai yai yana kama Hannunta ya ce "Danejo ƙurushiya, maza muje sarkin ruga na jiranmu" dafe ƙirji tai cike da tsoro ta ce "Na shiga uku na lalashe, Kur'ani na manta yanzu hamma yabi shikenan mutuwa zan, zan mutu na bar Dada? Zan mutu banyi karatu na zama babbar mace ba? Don Allah kada na mutu yanzu bana son wasan nan" rirriƙeta Hamma Yabi yai sosai ya ce "Ma zaki mutu ba Danejo, sai na kai ki burni Kinyi karatu kin zama babbar mace abar ƙwatance, sai kin zama mace ta farko wacce zata kawo sauyi cikin Rugar Rome, ki daina kuka kinji" kai ta ɗaga masa kafin da sauri ta ce "Kuma zan zama wannan mutumin na jikin bango?" Zare idanu Yabi yai kafin ya ce "Wannan gwamna ne fa" murɗa baki tai cikin shagwaɓa ta ce "Ni dai irinsa nake son zama" Yabi ya dungure mata kai ya ce "Aradu ƙarya kike, ina zaki iya yin siyasa tayaya zaki zama gwamna daman mata na zama gwamna ne?" Banza tai masa bai ƙara ce mata komai ba ya jata zuwa filin da za'a gabatar da wasan.


Giɗaɗo dake tsaye shi da Sarkin ruga suna jiran zuwan Hamma Yabi da Danejo ya ce "Me ya sa ka zaɓi Danejo kasan ba zata iya wasan ba" murmushi Sarkin ruga yai kafin ya ce "Ina son ganin bayanta ne, kuma a hankali zan ƙarar da zuri'ar Manga a cikin Rugar nan, wannan macijin na tsafi ne hatta mutuwar Manga ni na shiryarta"... "Amma me Manga yai maka haka?" Cewar Giɗaɗo. Sarkin ruga ya ce "Sirri ne.." kaifin su ƙara magana Hamma Yabi ya ƙaraso hannunsa riƙe da Danejo wacce ta ƙanƙamesa sosai jikinta na rawa da ɓari. 


Alƙalin wasan ya ce "Yawwa yanzu zamu fara, Danejo ta shigo cikin fili jama'a ku buɗe idanunku da kyau yau za kuga wasa wanda baku taɓa ganin irinsa ba" Halisa Dajeno Rome na tsakiyar fili ko kuka ta kasa a wannan lokacin ta tsaya ne kawai tana jiran taga ta inda mutuwa zata zo mata, domin abune mai wahalar gaske ace yau ta rayu ko ta tsira da ranta. Sarkin ruga ya bada umarnin a fito da Macijin, da sauri Alƙalin wasan ya nufi bukkar da macijin yake. Yana kwance sharkaf yau lamo a ƙasa tare da yin gammo da jikinsa, wani irin zabura yai tare da fasa kansa a lokacin da alƙalin wasa ya shigo cikin bukkar, ƙuri yai masa da idanu yana ƙare masa kallo. Ko me ya tuna Ohhu a hankali ya fara sauka daga dokin zuciyar ya koma ya kwanta, shi kansa Alƙalin wasan ya tsorata jikinsa na rawa yasa hannu ya ɗauki Macijin da ƙyar sbd nauyin da yake da shi.


Tun da Halisa Danejo Rome ta saka idanunta akan macijin taji gabanta ya faɗi, jikinta ya ɗauki rawa hawaye suka fara sintiri a saman Fuskarta, bata taɓa ganin maciji mai girman wannan ba, tama rasa wacce kalar addu'a zatai duk da ba wani abu ta iya sosai ba. Alƙalin wasan ya ajjiye macijin nesa da Halisa, aka fara kallon kallo tsakanin Danejo da Macijin, an shafe tsayin wasu daƙiƙo aka rasa waye zai fara kaiwa wani hari tsakanin Danejo da Maciji Prince?. Zaro idanu tai waje ganin ya fara warware tare da yin tsayi sululuuuu kuma ya nufo inda take, tana ja baya yana biyota har ya ƙaraso dab da ƙafarta tare da tsorawa zoben hannunta idanu. Juya tai tana neman inda zata gudu can idanunta ya sauka akan wani ƙaton dutse. Da sauri ta ɗauka tare da riƙewa a hannunta, ganin haka yasa Macijin bin ƙafafuwanta suuu haka ya dinga sufa a jikinta, har ya naɗeta ciff kansa daidai Fuskarta yana tsora mata idanu tare da kallon cikin idanunta. 


Jirkinta na ɓari ta ɗaga dutsen tare da kwaɗa masa a tsakiyar kansa, wani kalar ihun azaba macijin yai yana fasa kai kamar zai sarata, sai kuma ya saki kansa tare da ɗorasa saman ƙirjinsa gaba ɗaya naman Macijin rawar azaba yake, kansa tuni ya fashe ya fara zubar da jini. Ganin nasarar da Halisa Danejo Rome ta fara samu yasa Hamma Yabi da Shatu tare da sauran jama'ar Rugar Rome suka fasa ihun murna, Sarkin ruga da Alƙalin wasan hankali tashe suka kalli juna tare da faɗin "Me ya samu macijin nan? Ki dai asiri akaiwa Yarinyar nan?".


Halisa a tsorace Macijin a tsorace amma a haka cikin dakiyar zuciya ta ƙara ɗaga dutsen a karo na biyu ta ƙara bugawa Maciji, Innalillahi a wannan lokaci kururuwar da Macijin yai sai da kowa na wajan yaji, jini ya sake ɓalle masa a hankali ya sulale ƙasa baya ko motsi alamar ya mutu... ajjiyar zuciya ta sauke haka kurum taji kuka ya ƙwace mata, durƙushewa tai a wajan ta shiga rera kuka tausayin macijin ya kamata musamman yadda taga jini na zuba a jikinsa, Hamma Yabi ya ƙaraso wajan Halisa Dajeno Rome tare da ɗagata yana dariya ya ce "Danejon Dada kin kashe macijin, kin kashe sa bana faɗa miki cewa ba zaki mutu ba? Zamu samu ƙwayar nono da Nagge masu yawa" ƙanƙame Hamma Yabi tai cikin kuka ta ce "Bana so Hamma Yabi, mu bar nan wajan kaina juyawa yake, bana son ganin jinin nan kaji" hannunta ya kama sukai gefe guda. Cike da taƙaici Sarkin ruga yake bin Macijin da kallo bai taɓa tunanin haka ce zata kasance ba, cike da baƙin ciki ya amshi wani sanda ya shiga kwarɗawa macijin aka tun macijin na motsi har ya daina jikinsa yai face face da jini tare da raunuka. "Ka ɗauke sa ku cillar a gefen gaɓar ruwa wani abin yai kalace dashi" Giɗaɗo da Alƙalin wasan suka ɗauki Macijin tare da nufar cikin jeji da shi. Suna zuwa suka cillar gefe guda da sauri suka juya cikin Rugar Rome.


Sanyin gaɓar ruwan daya ratsa cikinsa ya sanya ya fara Girgiza yana juyi tare da murmurɗe jinsa gefe guda, wani kalar ihu yake mai nuni da azabar da yake ciki, ya daɗe cikin wannan halin kafin yai Girgiza tare da rikiɗewa ya dawo siffarsa yadda yake fitowa a mutum ba Aljani ba, yana kwance sambal gefen ruwan Farar Alkyabbar jikinsa duk ta ɓaci da jini. A hankali ya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa inda yake zubar da jini, runste idanun yai sosai cikin ƙasa da murya ya ce "Ya Allah" yana nan ƙwance yaji iska ta mamayesa baki ɗaya kafin kace wani abu iskar ta ɗaukesa zuwa sama.


Duk farin cikin dasu Shatu suke ciki banda Danejo rasa abin da yake mata daɗi tai, gashi jinin Dada ya matsa ga tunanin dake wanzuwa a cikin zuciyarta. Dada ta kalli Shatu ta ce "Farin ciki za kiyi Halisa ba damuwa ba, da tuni an rabani dake Allah bai ba, akwai ƙaddarorin da suke biye dake, amma duk wahala duk tsanani waya rana zaki zama abar ƙwatance tabbas zaki samu miji wanda zai kula da maraicinki" Danejo ta ce "Dadana nifa ba marainiyya bace, ina dake ga Hamma Yabi ga kuma Shatu" jinjina kai Dada tai idanunta akan zoben hannunsa Halisa ta ce "Ina kika samu wannan Halisa?" Girgiza kai tai cikin damuwa ta ce "Ban sani ba Dada, kawai na gansa a hannuna"... "Bana son ƙarya fa" da sauri Halisa ta ce "Da gaske nake miki, kalli kiga" ta faɗa tana nuna mata tambarin zoben, Dada ji tayi kansa ya sara idanunta akan Zoben da sauri ta riƙe kanta tare da rufe idanunta, kamar mai son tuna wani abu babu abin da take gani a cikin idanunta sai tambarin masarauta dake manne cikin zoben. Ganin yadda Dada ta rirriƙeta kanta ya sa Hamma Yabi fita da gudu ta tatso mata kindirmo mai zafi, da taimakon Halisa Dajeno Rome suka bawa Dada kindirmon nan da nan zufa ga shiga saukar mata bacci ya ɗauke ta.


Juyawa Halisa tai ta kalli Shatu dake barci a nutse ta kalli Hamma Yabi ta ce "Hamma yaushe Dada zata samu lafiya ne? Kullum a ƙwance take ina tsoran na rasa ta aradu" Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya ce "Ba zaki rasa Dada ba, gobe zan koma asiti bamu da kuɗin kai ta asibitin burni" Da sauri Danejon ta ce "A siyar da Nagge to" zare ido Hamma Yabi yai ya ce "Aradu ƙarya ne, Uban waye zai taɓa Nagge ai mu dasu mutu karaba" ba tace masa komai ta miƙe tsaye tare da yin waje lokacin rana ta faɗi, can gefe ta nema ta zauna ita ɗaya sai tunani take a haka har akai magariba tana zaune, ganin duhu ya fara yasa ta miƙe tare da zagayawa bayan bukka ta kwaɓe kayan jikinta, halittar jikinta ta tsorawa idanu, musamman ƙirjinta tana mamakin abun mene amfaninsu a jikinta? Ita a gareta basu da wani abu kullum sai dai su ƙara girma. Ruwa ta sheƙa babu ko sabulu tana gamawa tai alwala, wasu kayan fulanin ta ɗauka farare ta saka tare da Ajjiye waɗan can, da sauri tai sallah tana gamawa taci tsiran da Hamma Yabi ya kawo musu, tana ci ta kwanta barci domin da wuri take son zuwa kiwo ta dawo ta tafi tallan kindirmo.


Ciki zafin nama Prince ya saka hannu tare da ɗauke Safwan da mari ya ce "Ka fita a sabgata, kaje ka faɗawa Sarki halin da nake ciki ya ɗaukeni, kuma kasan yana gab da rabani da matata wanda ba zan iya jure hakan ba sam" Safwan ya kalli Prince cike da mamaki ya ce "Ban taɓa ganin mai taurin kai a duniyar Aljanu irinka ba Prince, cutar da yarinyar nan kake fa, babu haɗi tsakanin mutum da Aljani na faɗa maka, abin kunyane ka rasa wacce zaka so sai Bil adam? Allah zai saka mata fa" banza Prince yai da Safwan a wannan lokacin rabinsa na mutum rabi kuma na siffar Aljani da sauri ya juya zai tashi sama Safwan ya ce "Ina zaka? Ba dai wajanta ba?" Prince ya ce "Ba zan iya yin wasu daƙiƙo ba, ba tare da naga matata ba, da matata nake son kwana a yau ɗin nan" yana faɗin haka ya ɓace ɓat kai tsaye Rugar Rome ya nufa. Halisa juya cikin barci taji wani sanyi na ratsa mata jiki, ga wani mafarki da ke ƙafafuwanta sai motsawa suke amma ta kasa koda motsi bada ji take kamar ana danneta. Can dai ta farka a firgice Innalillahi a ruɗe ta fara kallon inda take, tana kwance tsakiyar dokar daji ba gida gaba ba gida baya...




Waye ya kawo Halisa Dajeno Rome cikin dokar daji?...


#Sarautar marubuta

#true life story