BAƘIN ƘULLI: 001
by @ouummey
BƘ FREE PAGE 1
_________________________
SASA CENTRAL PRISON, SASA STATE, 11:40 am.
Ihu da ta saki ne ya karaɗe ilahirin wajen, kuka take cike da raɗaɗi da azabar da take ji a jikin ta sanadin dukan da ƴan uwan ta masu laifi suka rufe ta dashi.
Abu ne da ya zama kamar wajibi in har za'a fito dasu aiki to fa se ta sha kashi kafin ta bar wajen, hakan ke faruwa tun daga ranar da aka kawo ta gidan kason amma har zuwa yanzu da ta tasamma shekara a cikin sa ta kasa sabawa, a kullum abun sabo yake zame mata takawa sabo dashi.
Bata san me ta tsare musu ba da suka yi mata irin wannan tsanar, kullum cikin ganin tayi ƙoƙarin kiyayewa duk wani abu da ze haɗa ta dasu take amma basa rasa samo abun da zasu ce tayi dan kawai su sami dalilin dukan ta.
Duka ne suke mata cike da mugunta su kusan biyar akan ta, jibga jibgan mata ne manya da akalla wasu sun haife ta wasu kuma sun kusa haifar Tata suka zage karfin su suna nuna bajintar ƙwanjin su akan jikin ta, dunƙulewa tayi gefe ɗaya tana kuka tare da ƙoƙarin kare dukan sedai ina samun ta yake ko ta ina dan ba dukan hankali suke mata ba.
Jinin dake zuba a bakin ta besa sun tausaya sun daina dukan ta ba dan ko a jikin su ma hakan be dame su ba da alamu so suke su fitar mata da wanda ya fishi dan sake dunƙule hannaye suke yi.
Duk yadda yaso ya samu bacci ya gagara sanadin ihun dake shiga kunnen sa yana amsa amo a ciki, cillar da pillown da ya toshe kunnen sa yayi tare da durowa daga kan lafiyayyen gadon da yake kwance.
Three quarter ne a jikin sa baƙi se Black singlet da suka karɓi tattausar fatar sa tare da sake bayyana hasken sa na farin mutum a fili, bedroom slippers ɗin sa ya zura tare da nufar ƙofa ya fita.
Se yanzu na sami damar ƙare masa kallo, ƙaƙƙarfan namiji ne da kallo ɗaya za'a yi masa a shaida hakan saboda body building ɗin sa da ya bayyana ta cikin shimin jikin sa, taku yake irin na cikakkun maza masu isasshiyar lafiya da wadataccen ƙarfi har ya zagaya bayan ɗakin sa cikin son ganin wane mai tsautsayin ne ke masa ihu a ka bayan lokacin hutwar sa ne yanzu.
"Shegiyar yarinya mara imani, makashiyar banza makashiyar wofi se ɗan banzan kyau kamar aljana amma imani kam ko na ɗigon cokali babu a ranta, ba ke har kinsan ki kashe mutum ba, to muma se mun kashe ki da azaba a gidan nan, ku ƙara mata mana".
Wata ma'aikaciyar gidan yarin ta faɗa aikuwa kattin matan suka kuma zage karfin su suka cigaba da jibgar ta kamar sun samu kayan wanki.
Tsaye yayi yana kallon su da ɓacin ran da ya gaza boyuwa, wane irin iskanci ne wannan da za'a kawo masu laifi aiki baya dakin sa bayan ansan dole ne buƙaci hutawa, lallai dole ya nuna wa shugaban gidan nan ɓacin ran sa dan da alama kasancewar sa sabon fara aiki a nan yasa be San principles din sa ba.
Mahaukaciyar tsawar da ya dakawa matan tare da ma'aikaciyar yasa sauka yi mutuwar tsaye a wajen da suke hannu a sama da suka daga da nufin dukan ta.
Cikin takun nan nasa ya ƙarasa gaban su kafin cikin husky yet low voice din sa ya nuna su duk su ukun
"Wane irin iskanci ne wannan, kashe ta zakuyi ko me?".
Duk irin takadiramcin matan nan kasa magana suka yi dan tuni suka gane wane a gaban su, batun yau ba suka san shi haka sun san duk iskancin su a gaban su yake, mutumin da be tafawa mahaifin sa ba to su waye su.
"Ehm, dama...dama..bat...Bata..yin..aikin da ...aaka..sa...tane".
"Saboda bata yin aikin da aka sata shine kika Basu chance da order din dukanta yadad suka so?".
Wannan karon kam ma'aikaciyar kasa magana tayi se aikin girgiza kai kawai da take yi, jinjina kansa yayi tare da duban jikin rigar ta da sunan ta ke rubuce kasancewar ta Christian Ademola Rose.
Agogon hannun sa ya shashhafa sannan ya soma magana cikin bada umarni
"Ademola Rose is fired, Kar a Kuma sa kowane prisoner aiki a bayan room dina ko mace ko namiji, this is my strict order, hope you get me".
Muryan shugaban gidan ne ya ratso ta cikin wristwatch ɗin while answering him
"Sure, za'a kiyaye insha Allah, and about Rose she'll leave immediately".
"Better".
Ya faɗa tare da swiping watch din ya juya ze koma se kuma ya dakata tare da juyowa, wani firgitaccen kallo ya shiga bin matan nan dashi da yasa lokaci ɗaya suka kai on their knees jikin su na bari kamar wanda aka sa a ruwan ƙanƙara suka buɗe bakin su da ke kakkarwa
"Ba zamu kuma ba boss"
Kallo ɗaya yayi musu ya juya ya tafi dan ya tabbatar ba zasu kuma ba din, ajiyar zuciya suka saki tare kafin su kalli juna suka saki dariya silently na samun sauki
"Kai amma dai wallahi boss takadiri ne, ki kalli yadda rose ta rasa aikin ta cikin kankanin lokaci".
"Hmmm, gwara ita fa, ba dan mun yi saurin apologizing ba kuma yasan samu akayi da se fa yasa an gana mana muguwar azaba muma, Allah dai ya cece mu wai ina ma arniyar nan tayi ne?".
Ɗayar ta faɗa tana waigen neman inda rose ta shiga, can suka gano ta tana tafe hannuwan biyu aka da alama kuka take, da sauri ɗaya ta tashi while looking at the other
"Kinga Kiki maza tashi mu bar wajen nan kafin mutumin nan ya canja mind ɗin sa ɗan tsaf ze iya".
"Aikuwa wallahi, amma kaka ya zamuyi da yarinyar nan, ko mu bar ta a nan ne?".
Zaro ido kaka tayi tana kallon kiki
"Ashe har yanzu ma baki san shi ba, wallahi ko da wasa ya gan yarinyar anan kashin mu ya bushe, salin alin ki kama ta nima na kama mu maida ta room area mu jefar, ta San yadda zata yi ta ƙarasa dakin su".
Haka suka yi kama kama suka kama matashiyar dake kwance magashiyyan tana jin su sedai bata da karfin jikin yin koda ƙwaƙƙwaran motsi me balle ta mike.
Kamar yadda suka ce ɗin kuwa a room area suka dangwarar da ita suka yi hanyan dakin su ta bisu da kallo kawai.
Kaff gidan prison ɗin babu takadiran mata kamar kiki da kaka, manya ne ba wai na tsufa ba sedai dukkan su zasu haife ta haɗu kuma ɓukaka ga kuma tashen jin karfi da suke yi, hakan yasa duk wata prisoner ke tsoron su sukuma suke abun da suka so batare da tsoro ba dan hatta gandirobobin ma wasu tsoron su suke.
A hankali ta lumshe idon ta tare da fara ƙoƙarin tashi sedai ina ta kasa, da rarrafe ta ƙarasa dan tsukukun dakin ta idanun ta na zubar da hawayen tausayin kanta, jingina tayi jikin bangon ɗakin tare da rushewa da kuka tunawa da bata da ranar fita daga wannan gidan da take wa kallon makabarta.
Har yanzu ta kasa sabawa da rayuwar wannan gida bakomai cikin ta se bakar azaba, a kullum gari ya waye sabon rauni zuciyar ta take mata in ta tuna ba komai ya jawo mata zaman wajen nan ba face ..HARSHEN TA!.
A kullum dana sani sake lulluɓe ta yake tare da yin Allah wadai da zuciyar ta dake cike da tsananin kishin da yayi jagorancin kawo ta wannan gida, tayi danasani fiye da tunanin me tunani na biyewa zuciya tare da sakar mata linzamin ta da har yayi mata sanadin kasancewa a wannan baƙin bigiren.
Kuka da neman yafiya da gafarar Ubangiji ita ta saka a gaba ko da yaushe, fatan ta daya kar Allah ya maimata mata yin irin wannan rayuwar a gobe kiyama tun da ta tabbatar a nan duniya kam bata da rabo sanadin BAƘIN KISHIn ta na fitar hankali.
★★★
Tsaki ya saki tare da zame singlet ɗin jikin sa ya faɗa kan royal Italian bed ɗin sa, hannu ya kai a hankali ya lalubo remote din air condition din ɗakin ya ƙure masa gudu sannan ya ajiye.
Lumshe idon sa yayi dan sosia yake so yayi bacci, wata shegen murmushi ne ya wanzu kan laɓɓan sa tunowa da mahaifin sa da yayi, a hankali murmushin ya rikide zuwa siririyar dariya lokaci ɗaya kuma ya mike ya zauna sosai akan gadon.
Girgiza ƙafafun sa ya shiga yi da ya daura dayan kan ɗaya bayan ya miƙar dasu kan gadon, mahaifin sa yake aunowa da yanayin daze iya kasancewa a yau din, hakan ba ƙaramin sashi cikin farin ciki yayi ba.
A duniya in akwai rai daya da ya tsana yake kuma jin haushi tare da burin kuntatawa to ya biyo bayan wancan mutumin dake amsa sunan mahaifi a gare shi.
Farin ciki, jin dadi hadi da walwalar mahaifin nasa sune babban abokan gabar sa.
Izuwa yanzu yasan yana can yana fama da bakin ciki da ɓacin rai ba dan komai ba se dan buga sunan sa da yasan tuni yan jarida sun dade da yi a matsayin wanda aka kai gidan yari.
Ya sani dole siyasar baban nasa da yasa a gaba ta sami tsarki saboda tsabar yadda yake bata masa suna da yin duk wani abu da yasan ze dakushe nasarar siyasar tasa.
Babban burin sa be wuce ganin baban nasa yayi faɗuwar baƙar tasa a babban zaɓen da za'a gabatar wata me kama wa ba, in haka ya faru yasan lallai se yafi kowa farin ciki da jin daɗi.
Hannun sa ya cusa cikin tarin sumar dake kan sa ya shiga cakudawa yana sakin murmushi kaɗan kaɗan wanda ke nuna akwai abinda yake shiryawa cikin ransa, lallai dole ya aiwatar da plan ɗin sa.
A da ya tsara zeyi spending two weeks a prison din man sedai Kuma yanzu ya fasa, sati ɗaya zeyi ya fita dan aiwatar da aikin sa.
Seda ya gama duk tsarin da yake ganin ze yi sannan ya kwanta tare da kore komai daga zuriyar sa, nan da nan kuwa bacci yayi gaba dashi.
★★★★
Ba ƙaramin tsami jikin ta yayi mata ba da har yasa rarrafen ma ta kasa yi ga tsananin fitsari da take ji kamar marar ta zata yi bombing, izuwa yanzu kam Muryar ta ma ta daina fita kwata kwata saboda tsabar kukan da ta kwana tana yi, zazzaɓi ke a jikin ta me zafi amma nesa ko kusa ba wani mataimaki se Allah.
Jin kamar ana taɓa kyauren dakin yasa ta ɗan ɗago ido ta kalli wajen, abinda ta gani yasa ta manta da ciwo da wani zazzaɓi dake jikin ta ta miƙe kan ƙafafun ta jikin ta na kwasar rawa, ganduroba sani ne daga shi se gajeran wando a dakin ta cikin talatinin daren da kowane mahaluƙi ke kwance dan hutawa da samun gamsasshen bacci.
Wani munafukin murmushi sani ya sake tare da fiddo harshen sa ya shiga lasar lips ɗin sa yana binta da lustful look, a hankali ya shiga takawa dan isa gare ta sedai dole ya tsaya ganin yadda ta shiga ja da baya tana matsawa.
Wata shegiyar dariya ya saki tare da kai hannu yana shafa ƙirjin sa kana ya shiga mata magana da wata yar iskar murya dake sake shaida mata tabbas fa wannan mutumin shaidancin sa ne ya kawo kanta yau dan ta daɗe tana jin labarin irin halin sa sedai bar taɓa gwada mata ba se cikin kwanakin nan da yake Binta da wani mayataccen kallo se kuma yau da ya shigo mata.
"Yana ga kina ja da baya kamar baki san abinda ya kawo ni dakin nan ba, kinga in ma tsoro kike kar a gane to ki saki jikin ki dan hakan ba wani abu bane, mun dade muna wannan harkalla da matan gidan nan ta taimakon juna dasu musamman irin ki da ake yankewa hukuncin ɗaurin rai da rai, kinga kuwa in ba wajen irin mu ɗin ba ina zaku sami masu taimakon ku irin haka".
Tun da ya fara magana gabanta ke faɗuwa ta shiga zame wa kasa a hankali dan kafufuwan ta da suka gaza riƙe ta, hasbunallah wani'imal wakeel kawai take ambato dan izuwa yanzu bata da wani sauran dabara da ta rage mata, a karo na ba adadi ta kuma Allah wadai da ZAFIN KISHI iri nata da ya kai ta ya baro, shekara guda iwar wannan lokacin tana kwance ne kan gadon auren ta, cikin gidan mijin ta amma yau gashi an wayi gari wani ƙato na neman haike mata duk sanadin HARSHEN TA.
Hannun ganduroba sani da ya ɗora kan kafaɗar ta ne ya dawo da ita hayyacin ta, a firgici ta ture hannun tare da tashi ta matsa da gudu tayi daya side din ɗakin, ganin ya kuma yiwa kanta yasa ata fice da gudu duk da ko da bata da agogo yasan in biyun dare bata yi ba ta mintinan da suka rage ƙalilan ne.
Shima cikin zafin nama ya rufa mata baya cikin son cimma ta dan kar ta tona masa asiri duk da yasan yana da babban da ya tsaya masa amma sanin boss na gidan baze so ta kwaye masa riga ba.
★★★★
Wutar ɗakin sa da ta ɗauke ya tilasta masa farkawa daga barcin sa me daɗi, sam sam baya shiri da zafi shiyasa in har ze kwanta se ya kai a/c din sa karshe, yanzu kuwa zafin da yaji ne ya tashe shi.
Wayar sa ya kunna ya haska tare da lalubar takalman sa ya saka ya fita dan zuwa duba meye matsalar da yasa hakan dan yana hango wasu dakunan har yanzu akwai wuta.
Jin yadda yayi karo da mutum yasa ya ɗan yi tsai cikin mamaki sedai ihun da yaji ya shaida masa macece hakan yasa yayi gaggawar cire ta daga jikin sa tare da haska fuskar ta da fitila.
Razani da firgici kawai ya hango a yanayin ta da kuma yadda take juyawa tana kallon bayan ta hankali a tashe
"Hey, what's your problem?".
"Shine, ya..yaa..biyo ni..., Kamani zeyi..he'll molest me...shine..help me pls".
Dubanta yake kafin kuma ya kalli bayan sa daidai lokacin da yaga juyawar wani mutum da gudu ya shige wani kwana, mamaki ne ya kama shi ya shiga zare kyawawan idanun sa, so that's what's happening a nan, a prison din ma, lallai mutane are so unbelievable.
Seda yaga ɓacewar mutumin kafin ya juyo ya haske fuskar ta fitilar wayar sa ya shiga bin ta da ido yana yamutsa fuska.......................✍🏻.
Ouummey 📚✍🏻.
Vote, comment, share and patronize fisabilillah.