JIDDATULRAHMAN 2
Ci gaba...
A firgice na ɗaga ido ina kallonta kamar yadda sauran mutanen da ke falon ke kallonta, sai dai yanayin kallon da suke yi mata ya bambamta da wanda Ni nake yi mata.
Shiru ya ratsa falon na wasu mintuna kafin Abiey ya katse shirun ta hanyar faɗin "Ke muke saurare".
Sai da tayi shessheƙa sosai kafin ta fara magana:
Bayan an ɗaura aurenmu Ni da Murtala kai tsaye garinsu da ke wata karamar hukuma a Bauchi muka nufa, da kudin da na tara mana wanda na karba a hannun dangina muka yi amfani da shi wajen kama hayar gida sannan muka siya kayayyakin amfani.
Da fari na so Murtala ya yi amfani da sauran kudin wajen fara kasuwanci sai dai ya nuna min ba haka ba, tsantsar soyayyar da nake yi masa yasa na kasa yi masa turjiya, tsawon shekaru biyu da wannan kudin muke amfani wajen ci da kanmu da kuma biyan bukatun rayuwa.
Da yake komai na duniya idan an samu zai kare ko da kuwa ana tattali bare kuma wanda ba tattalin ake ba, rana tsaka muka wayi gari babu kudin sun ƙare, a wannan lokacin ma ban gaza ba na sake shawartarsa da ta nemi sana'a koda kwadago ne ya fara sai dai a maimakon ya karbi shawarata sai ya rufe Ni da faɗa, dan haka ban sake yi mai maganar. A kwana a tashi sai abin da za mu ci ya fara gagararmu, daga nan kuma sai ya shiga ɗaukan wasu kayayyaki da na mallaka yana saidawa don mu samu abin saka wa a bakin salati.
Da haka muka wayi gari babu ma abin da za a siyar mu samu kudin da za mu siya abincin. Tun daga wannan lokacin kuma sai Murtala ya daina zama a gida, idan ya fita tun safe to sai dare zai waiwayo ni watarana ya zo min da garin kwaki watarana kuma idan ya dawo yace bai samu komai ba nayi hakuri, haka zan wuni na kwana da yunwa.
Da na ga hakan ba zai fisshe ni ba sai na yanke shawarar sai da itace kamar yadda na ga wasu matan da ke garin nayi, tun safe za su shiga jeji su saro itace a zo a shanya zuwa da yamma a saida, wasu ma tun da safen suke saidawa matafiya dake a bakin titi suke kasa itacen. Koda na shawarce shi bai ja ba yace na fara hakan, dan haka washegari na bi ayarin matan dake fita don ni ma na fara sana'ar.
Allah Ya sa wa sana'ar albarka, duk da wuyar da nake sha kafin na samu amma kullum idan na yi wo iccen na kasa zai kare. Daga wannan lokacin sai na fara raba kuɗin ina ajiye rabi, rabin kuma mu na amfani da shi. Har a wannan lokacin Murtala yaƙi kama sana'a guda ya yi.
Ana cikin wannan yanayi na samu shigar ciki mai lailayo sosai, har ta kai ba kowani lokaci ne nake samun damar fita ba, shi kuwa Murtala sai ya dawo da ɗabi'arsa na rashin zama a gida sai dare yake dawowa, a wannan lokacin ma baya dawo min da komai ko da na tambaya zai rufe Ni da fadan cewa ai na san ba sana'a yake yi ba.
Dan haka idan ya fita da kudin da na ɗan tara nake amfani ne siyo wani abu na ci.
Watarana na tashi da matsanancin ciwon ciki sosai har ta kai na fita a hayyacina, bansan me ya faru ba na farka na ganni a asibiti, a nan Murtala ke shaida min cewar na samu yin ɓari ne. Na yi takaicin zubewar cikin sosai dan har ga Allah ina son cikin.
Daƙyar Murtala ya nemo kudin da ya biya masu asibitin muka dawo gida sai dai kullum ƙorafi yake min tare da faɗin da naji sauki na fita na nemo kuɗin nan don aronsu ya yi sannan wa'adin da aka ba shi babu yawa.
Nayi kuka sosai, a wannan lokacin na fara da na sanin biye wa son zuciyata na rabu da dangina, da ace Muhammad na aura na san da yanzu bana kasar ma gabaɗaya.
Watarana mun wuni ba mu ci komai ba har yunwa ta fara galabaitar da Ni, da na ga Murtala ba shi da alamar yin wani yunƙuri sai na yanke shawarar shiga jeji na dari icce na zo na siyar tunda yamma ba ta yi sosai ba. Da ya ga na shirya sai ya miƙe ya ce mu tafi tare, ban ja ba muka tafi tare muna tafe muna hira jefi-jefi.
Koda muka isa shi yake sarar iccen Ni kuma ina tarawa waje guda, ba mu jima da farawa ba muka ji kukan jarirai ya yawaita a inda muke, lamarin da ya tsorata mu matuƙa har muka yanke shawarar guduwa. Sai dai har mun yi gaba sai naji na kasa ci gaba da tafiyar, kukan jariran na ci gaba da amsa kuwa a cikin kunnena, cak na tsaya a inda nake wanda hakan yasa shima Murtala ya tsaya daga saurin da yake ya waigo yana harararta.
"Bai kamata mu tafi ba tare da mun duba meke faruwa ba, tsawon lokaci ina zuwa nan ban taɓa cin karo da wani abu makamancin haka ba. Ka zo mu duba daga ina kukan jariran ke zuwa dan Allah." Na faɗa ina maida numfashi saboda gudun da na fara da farko.
Wani kallo ya watso min yace, "Saboda ke baki da hankali ko ba son rayuwarki kike yi ba, koda yake dama iyayenki sun jima da yafe ki shiyasa ba zaki ji shakkar yin komai ba. Ni dai kam iyayena ba su ce min 'jeka ka gani ba' kin ga tafiyata".
Maganar da yayi ta harzuƙa Ni sosai, lallai namiji ba ɗan goyo bane kamar yadda ake faɗa, wai Murtala da na sadaukar da komai nawa saboda shi amma yake jifana da wadannan kalaman. Ban ce uffan ba na juya saboda yadda naji kukan Jariran na sake yawaita, tsayawa ya yi a inda yake bansan nazarin me yayi ba na ga dai ya biyo NI a baya.
Sautin na ci gaba da bi har na iso jikin wata ƙatuwar bishiyar kuka, shi ma dai Murtala yana biye da Ni sai dai na fahimci alamar tsoro tattare da shi.
Wata mata muka tara a shimfide a ƙasa da jaririya a gefenta sai wani ƙaton akwati mai kyau a gefe, shiru muka yi muna kallon juna, jaririyar kuma ta cigaba da kuka sosai. Daga ƙarshe dai nayi shahadar sunkuyawa na ɗauki jaririyar bakina ɗauke da duk wata addu'a da ta zo min a lokacin.
Har zuwa sanda na ɗauki yarinyar ban daina jero addu'o'i ba, na shiga jijjigata a hankali har ta fara yin shiru, Murtala ya matso kusa da ni sosai yace, "Ba Aljanu bane ko?".
Na kalle shi nace, "Aljanun ne za su wulakantar da ƴan'uwansu mutane haka?".
Shiru ya yi ya matsa kusa da matar don duba yanayin da take ciki, a hannunta yaga wata farar takarda don haka ya zaro da sauri ya sake dawowa inda nake tsaye.
"Kin ga Fathiya ke ce ƴar boko, karanta mana mu ji". Ya faɗa yana miƙo min ƙaramar takardar.
Da kai nayi mai alamar ya warware na gani. Koda ya warware ga abin da takardar ta ƙunsa.
_Zuwa ga duk wanda takardar nan ta riska. Wannan yarinyar sunanta Hauwa Jiddatulrahman, mutum ce ba aljana ba kamar yadda wasu za su yi tunani. Dan Allah duk wanda ya tsinceta ya na ba shi amanarta duniya da lahira, ƴa ta ce da na haifa. Ina roƙon duk wanda zai tsince ta da ya nesanta daga inda ya sameta, ko da ace tare aka riske mu, kar ku damu da Ni ku tafi da ita kawai. Ga kayanta nan da dukiyar da za ta riƙeta na tsawon wani lokaci._ *Oum Jiddatulrahman*
A fili na karanta takardar don haka ina kai aya Murtala ya isa zuwa jikin akwatin, Ni kuwa tsantsar tausayinsu ne ya kama Ni sosai. Da ace ba ta fadi cewa mu barta mu tafi da ɗiyar ba, babu abin da zai hana mu tafi da ita. Ko wacce ƙaddara ce ta rabota da na ta ahalin har ta tsinci kanta a wannan yanayin, babu mamaki wani abu ne mai girma don kuwa babu wanda zai so ya rabu da ahalinsa, gefe guda kuma nima nawa dangi suka fado raina a karo na ba adadi.
Ina daga tsaye nake kallon yadda Murtala ke kici-kicin bude akwatin har ya kai ga budewa. Kayan jarirai ne a saman, dan haka ya fara cire kayan daya bayan daya yana ajiyewa a gefe har ya gama kwashe kayan, sai ga kudi nan maƙil a ƙasan akwatin daga kan Naira har zuwa Dala, sai sarƙoƙin gwal na yara da na manya da yawa. Sai kuma hotonan yara kusan guda goma, a jikin kowane hoto akwai yara biyu da wacce ke hannuna sai kuma wani namiji, da alama ma yaran ƴan biyu ne.
Da farin ciki Murtala ya ɗago yana kallona yace, "Fathiya mun yi arziki".
Na kalleshi kawai ban furta komai ba saboda takaici, na ƙarasa na ɗauki wani ƙaramin littafi da ya ciro daga cikin jakar na bude, cikin Sa'a kuwa na samu abin da nake nema wato biro. Cikin sauri na yagi takardar nayi gajeren rubutu kamar haka:
_Da yarda Allah zan cika miki burinki kamar yadda kika buƙata, sai dai ban ji dadi da ya kasance zan bar ki a cikin yanayin mara tabbas ba. Idan har kin ci karo da wannan sakon nawa, ina mai tabbatar miki cewa ɗiyarki ta shiga hannu na gari kuma na ɗauki alƙawari har ga Ubangijina cewar zan kula da ita gwargwadon iyawa ta. Ina fatan Allah ya sake hada fuskokinmu". *Mahaifiyar Jiddatulrahman ta biyu*
Na miƙa wa Murtala takardar na ce ya saka mata a hannun da ya ciro waccan takardar, ba musu ya karba ya saka. Naji mamaki ƙwarai da Murtala ya tabbatar min da cewa matar tana raye kuma ba suna tayi ba, Allah kaɗai ya san karatun kurma, nan na umarci da ya tattara kayan mu tafi gudun wani abu ya faru kamar yadda nake hasashe.
"Fathiya ba gida za mu nufa ba fa". Murtala ya faɗa lokacin da muka fara tafiya.
"Ban gane ba gida za mu nufa ba, ina za mu je to?". Na tambaya ina kallonshi.
"Ba ki ji abin da ta rubuta a jikin takardar ba cewar mu yi nisa da inda muke, ko so kike a binciko inda muke a raba mu da wannan tarin dukiyar ne".
Nayi shiru ina tunanin, sai dai Ni a nawa ɓangaren ba dukiyar bace a gabana rayuwar yarinyar ne nake tunanin halin da za ta shiga idan mun zauna a nan ɗin, don ƙila sani mugun ƙuduri ne a ke jifansu da shi, gefe guda kuma ga kaunar yarinyar da ta mamaye rai da zuciyata lokaci guda.
"Yanzu ina muka nufa?".
"Na yanke shawarar mu tafi gaya kawai wajen wani kawuna da ke can".
"Kana ganin zuwanmu can din babu wata matsala?".
"Wane irin matsala kuma Fathiya, babu abin da zai faru. Hankalina yafi kwanciya da can ɗin".
"Shikenan, Allah ya mana zabin Alkhairi".
A wannan ranar muka yi sallama da garin Bauchi zuwa Kano, sai dare sosai muka iso garin Gaya.
A nan muka buɗe sabon babin rayuwa, gida Murtala ya fara siya duk da na ja hankalinshi a kan cewa wannan ba dukiyar da zai yi facaka da ita bane amma sam bai ji Ni ba, gudun kada a kuma yasa na kwashe duk wasu gwala-gwalai dake cikin jakar da kuma wasu abubuwa masu muhimmanci na bar shi da kuɗaɗen.
Watanni kaɗan da dawowar Gaya Murtala ya tasamma ƙarin aure, da fari na tada rigima a kan maganar amma sai ta fara yi min barazana da Jiddatulrahman, cewar idan na kuskura zai karbi yarinyar sannan ya kora Ni na tafi gurin dangina, sannan girman alƙawarin da na daukar wa mahaifiyar alƙawarin da ba ni tabbacin cewar ta gani yasa ba zan iya tafiya na bar ta a hannun Murtala ba, gefe guda kuma ga sharaɗin da dangina suka gindaya min a kan waiwayarsu.
Tun daga wannan lokacin sai Murtala ya samu kafar musguna min, a duk lokacin da na so yin magana kuwa sai yace na ajiye Jiddah na koma wajen dangina.
Matar da ya auro mai yawan shige da fice ne a tsakanin gidan Malamai, dan haka ba ta wani sha wuya ba wajen mallake shi gabaɗaya ya koma mijin ta ce. Tun da ta shigo cikin gidan na yi sallama da rayuwar farin ciki, tsakani na da wanda ya ajiye Ni sai dai kallo daga nesa, dan haka ne na fara ƙananun sana'o'i na cikin gidan dan na samu abin dogaro da kai da wanda zan ciyar da kai na da kuma ɗiyata.
Nan Umma ta shiga labarta musu irin wuyar da muka sha a gidan Baba har zuwa lokacin da aka kawoni aikatau Birni da kuma haɗuwarsu da Hajiya Kaka.
Nan falon ya rikice da koke-koken mutane, Ni kuwa dama tunda Umma ta fara magana nake kukan har wannan lokacin kuma ban daina ba, numfashina har ɗaukewa yake yi saboda kuka da nake yi.
Hajiya Kaka ce ta rungumo Ni jikinta tana shafa bayana a hankali alamar rarrashi.
Sai da aka nutsu kafin Abiey ya yi nasiha mai ratsa jiki a kan muhimmancin bin maganar iyaye da kuma karban ƙaddara a duk yadda ta zo wa mutum.
Daga ƙarshe suka yanke shawarar za su tafi har Kano su karɓuwa Umma takardar sakinta a gurin Baba sannan su tattaro mana sauran kayayyakin mu masu muhimmanci da Umma ta ce akwai, musamman akwatin da aka tsinci Ni dare da shi.
Ko a fuska babu wanda ke nuna cewa ba ni da dangantaka mai ƙarfi da wannan ahalin ba, hasalima gata da tarairaya nake sha daga gurin kowa har na kan rasa a wajen wanda zan zauna saboda yadda kowa ke nuna son zama da ni. Koda wasu daga cikin matan gidan suka fara maganar a bar Ni a Katsina nan Hajiya Kake tayi kicin-kicin ta ce bata yarda ba kuma kar a sake wannan zancen idan ba so ake ta bata ran mutum ba.
Satin mu ɗaya a Katsina muka shirya dawowa Kano har da su Abiey da za su je wajen Babana, Allah Sarki sai yanzu na fahimci dalilin da yasa wasu lokutan Baba ke yi min wasu abubuwan, ashe ni ba gudan jininsa ba ce.
Kwanaki biyu tsakani aka karbo wa Umma takardar sakinta daga wajen Baba, su Hajiya Kaka kuma suka kwaso mana kayayyakin da za su mana amfani sauran kuma suka rabawa jama'a dama kayayyakin ba wani yawa gare su ba.
Sun koma Katsina Ni kuwa na cigaba da zama a wajen Hajiya Kaka cikin kwanciyar hankali, duk da cewa ba ni da wata matsala ta rayuwa amma a yanzu addu'ata ba ta wuce na bayyanar Mahaifana musamman mahaifiyata da babu tabbacin tana raye ko ta mutu.
*Falmata*
Yau ta kammala rubuta jarrabawarta na karshe a jami'a, don haka farin cikin da take ciki ya kasa ɓoyuwa a fuskarta musamman da zaman garin Kano ya isheta sosai. Gobe take son tafiya gida sai bayan sati biyu kuma ta dawo bikin kammala makarantar da aka shirya musu.
Tana zaune gefen gado tana shirya kayan da ba a jima da kawo mata su daga wajen wanki da guga ba, Najwa na zaune a tsakiyar gadon da wayar Falmata a hannunta tana kallon hotonan da suka yi ɗazu bayan kammala jarabawarsu, jefi-jefi tana tambayarta game da wasu da take ganin kamar ta sani, har ta kammala kallon hotonan ta shiga gefen hotonan kan wayar Falmatan tana kallo. Daidai kan hoton da Falmata ta dauki Jiddah farkon haɗuwarsu ta tsaya tana ƙara kura wa hoton ido, ta daga kai ta kalli Falmata dake cigaba da jera kayanta cikin akwati tace, "Anty Falmata a ina kika san Jiddahn Hajiya Kaka har kika ajiyeta a wayarki?".
Jin abin da ta fada yasa Falmata saurin matsawa kusa da ita don kallon cikin wayar, ganin hoton Jiddah ya sa ta kalli Najwa da ɗoki tace, "Kin san ta ne?"
Najwa ta tabe baki, "Ni fa ba wani son zuwa gidan Hajiya Kaka nake yi ba saboda masifarta".
"Haka zaki yi hakuri mu je, don gobe nake son tafiya gida".
Bayan sallar Magriba kuwa suka shirya tafiya duk da Hajiya Zara'u ita ma bata wani yi ɗoki da zuwan na su ba amma ba ta da ikon hanawa, direba ya ja su sai gidan Hajiya Kaka.
Lokacin da suka iso muna zaune a falo Hajiya na gyara min gashi na da ya kwana biyu a tsafe, duk da mitar da take yi amma nayi shiru burina kawai ta gyara min yadda zanji daɗin bacci.
Najwa ce ta fara shigowa kai tsaye babu ko sallama, aikuwa kamar yadda ta za ta Hajiya Kaka ta fara masifa.
"Sannu mai ido a tsakar ka, ko haka na fada miki ina fita coci duk ranar sati da za ki shigo min kanki tsaye haka? Yo ko cocin nake zuwa ai suna fadin Inkus idan za su shiga waje. To ki fita min a nan idan ba za ki yi sallama ba ki koma inda kika fito".
Baki ta turo ta tsaya a jikin ƙofar har zuwa lokacin da Falmata ta shigo da sallama, da hanzari na mike ina nuna ta ita ma Ni take kallo tana murmushi. Sai da ta fara durƙusawa ta gaida Hajiya Kaka kafin ta riƙo hannuna tana faɗin ,"Zauna mana Jiddah ko duk mamakin ganin nawa ne haka?".
Hajiya Kaka da mamaki take kallonmu, na san tunaninta ba zai wuce yadda aka yi muka san juna Ni da Falmata ba.
Kicin na je na fara kawo musu ruwa da abincin kafin na dawo na zauna, ita dai Najwa tana jikin ƙofar falon tana kallonmu.
Falmata da kanta ta ba wa Hajiya Kaka labarin haɗuwarmu da yadda ta je nema kwanakin baya ba ta same ni ba, Hajiyar tayi murna sosai sannan ta shaida mata cewa Ni da Ummata mun ɓata ne shekaru da dama da suka shuɗe amma yanzu alhamdulillah an gano mu, ita ma ta taya Ni murna sosai.
Mun jima muna hira wanda yawanci abin da ya shafi karatunta ne, har na alƙawaranta mata cewar zanje bikin yaye sun da za a yi nan da sati biyu. Daga ƙarshe dai da Najwa ta ga hirar ta mu ba mai ƙare ba ce sai ta ƙaraso cikin falon ta zauna duk da mitar da Hajiya Kaka ta yi mata lokacin da ta zo zaman.
Sai da dare ya fara yi sosai kafin Falmata ta mike don su tafi, ta karɓi Numbar Hajiya Kaka ta kira nayi saving din Numbarta don mu dinga magana tunda Allah ya sake hada mu.
Mun yi sallama cike da kewa kamar farkon haduwarmu.
Washegari da safe ta wuce garin Bauchi don fara shirye-shiryen dawowa bikin kammala makarantarta. Kamar kowane lokaci ta samu kyakkyawan tarba daga mutanen gidan kama daga kan iyaye dama hadimai.
Wuni tayi tana zuwa sashe-sashe na cikin gidan tana gaida su, sai dai ba ta samu damar ganin mahaifinta ba a wannan rana don haka ta bari sai washegari kafin ya fita fada ta je su gana.
Sun yi hira sosai da mahaifiyarta, sai dai ta lura kamar akwai wani abu da take ɓoye mata duba da yadda take nuna tsantsar kulawarta a kanta, motsi kaɗan za ta ce me za a kawo miki, ba kulawar mahaifiyarta bane ba ta saba da shi ba amma wannan karon kamar gaisuwa da neman iri ne take yi, ita dai bata furta a fili ba amma a ranta tana fatan koma mene ne ya zama alheri.
Washegari da safe hayaniya ce ta tashe ta a baccin da ta koma yi tun bayan da tayi sallar Asubahi, ranta bai so ba amma ba ta da wani zabi da ya wuce ta tashin saboda yadda gabaɗaya gidan busar algaita ce ke tashi tamkar za ayi wani babban taro. A saninta dai babu wani gagarumin taro da za'ayi nan kusa amma ba ta sani ba ko Sarki zai yi baƙi ne ƴan'uwansa Sarakuna shiyasa ake busar. Wannan tunanin yasa ta miƙe tayi saurin shiga banɗaki don ta shirya ta ga mahaifinta kafin ya fita zuwa Fada ko bakin su iso.
Ba ta jima ba ta gama shirin ta fita a sashen ba tare da tayi kalaci ba, ganin yadda aka ƙawata farfajiyar gidan ne yasa ta fara gaskata hasashenta na cewar wani Sarkin daga wani gari ne zai kawo ziyara masarautar ta su.
A ƙofar shiga falon mahaifin na su ta tarar da Mamanta ta fito, kallonta Hajja Fulani (kamar yadda suke kiranta tayi) cike da kulawa tace, "Har kin tashi Gimbiya?".
"E Hajja, Ina son ganin Baba ne kafin ya fita Fada". Ta faɗa cike da girmamawa.
"Ai da kin yi baccinki kin huta sosai ma, don yau ba zai fita Fadar ba. Ki shiga ku gana idan kin gama ki same ni a sashena". Ta faɗa tana yin gaba, sauran Hadiman da suke jiranta a bakin ƙofar suka rufa mata baya.
Bayan sun gaisa da mahaifinta ya mata fatan alkhairi game da karatunta tare da alƙawarin shi ma zai halarci taron yaye su da za ayi.
"Ɗazu Fulani ke sanar da Ni dawowarki, nayi tunanin aikawa a kira ki ashe kina tafe ma".
"Haka ne Abba. Tun jiya na so shigowa nan din dare ya yi".
"Kin ji labarin dawowar mahaifinku ko?".
Ta ɗago tana kallonsa fuskarta cike da alamar tambaya tace, "Mahaifinmu kuma Abba? Ai babu wanda ya fadamin za ayi baƙi".
Kai ya kada kafin yace, "Sam wani lokacin Fulani sai ta dinga abu kamar ba babba ba. Kinsan na taɓa ba ku labarin ɗan'uwana dake ƙasar Chicago ko?"
Kai kawai ta gyada tana ƙoƙarin tunawa don ita har ga Allah ta manta Mahaifinsu na da wani ɗan'uwa a wata ƙasa, to ba su san komai ga me da shi ba bare ahalinsa duk da kuwa a lokacin da aka ba su labarin ance yana da ƴaƴa.
Murmushi ya yi da alama yana cike da farin cikin dawowar ɗan'uwan na shi yace, "In Sha Allah yau zai dawo gida gabaɗaya shi da iyalansa bayan shafe tsawon shekaru a wata ƙasar. Bansan ya zan misalta miki farin cikin da nake ciki ba yau Mamana, shiyasa na ba da umarnin duk wani ɗa na da baya gida ya dawo don mu tarbi ɗan'uwana".
Ita ma da fara'a tace, "Allah Ya dawo da su lafiya. Shikenan ba za su sake komawa ba?".
"In Sha Allah a nan za mu cigaba da zama tare da su, kila ma shi zai karbi wannan kujerar ta wa dama asali shi ne wanda zai gaje ta".
"Abba meyasa za ka sauka kuma? Kila baya son sha'anin mulki ne yasa tun farko ya bar ƙasar".
Yanayin fuskarsa ce ta sauya ya girgiza kai yace, "Ko ɗaya, wata gagarumar matsala ce ta raba shi da gida na tsawon shekaru. Labari ne me tsayi In Sha Allah za mu tattauna idan sun iso".
"To Abba. Bari na shiga ciki, a huta lafiya". Ta faɗa tana miƙewa, albarka ya cigaba da saka mata har ta fice a falon.
Falon Hajja Fulani ta nufa, ta sameta tana cin tufa cike da yalwar farin ciki a fuskarta, ganin zuwan Falmata yasa ta fadada fara'ar Fuskarta ta mike zaune daga kiahingiɗen da yaki ta umarci bayin da ke wajen su ba su waje.
"Gimbiya Falmata matar Yarimah Ajmal". Ta faɗa da fara'a
Cike da daurewar kai Falmata ta zauna tace, "Haka Yarimah Ajmal din ya faɗa?"
"Ai ko bai fada da fari ba, yana daf da faɗa. Don kuwa babu wanda zai so hada zuri'a da mugun iri, kin ga kuwa kin fita daban da sauran ƴan'uwanki don kuwa mahaifiyarki shaidar ƙwarai gareta. Sai yau nake ƙara yi wa Allah godiya da iya son abin duniya ya saka min a raina amma bana taɓa lafiya ko ran wani ɗan'adam".
Yanzun ma kallon rashin fahimta take yi mata kafin tace, "Hajja wai me kike nufi ne? Ni fa kin sani a duhu.".
Hajja Fulani ta kalleta ta ce" Labari ne fa me tsayi, ki bari idan suka iso na san yau duk sai anyi tone-tone, dadina ɗaya babu wani abu da na shuka bare na ji fargaba ta kama ni. Amma na san su Hajja Inno ana can ta kasa zaune bare tsaye".
Baki Falmata ta taɓe kafin tace, "Allah Ya kyauta, koma mene ne Allah yasa mu ji alkhairi".
"Ai alkhairin ma za mu ji mu kam". Hajja Fulani ta faɗa.
Daidai lokacin kuma wayar Falmata ta shiga ƙara, ganin Jiddah ne yasa ta yin murmushi kafin ta ɗauka, ba da dadewa ba tayi mata sallama ta maida kallonta ga Hajja Fulani da ke tambayar ko Najwa ce. Nan Falmata ta faɗa mata cewa ba Najwa ba ce amma ƴar'uwarsu ce.
"Yauwa Hajja Bara na nuna miki hoton Jiddah yau kam, tun da dadewa nake son tambayarki Ina mantawa". Ta faɗa tana dubo hoton Jiddah da ke wayarta, tare da labarta wa Hajja Fulani yadda suka hadu da Jiddahn.
"Kalle ta da kyau Hajiya za ki ga kamar tana miki kama da wani wanda kika sani".
Wayar Hajja Fulani ta karɓa aikuwa ta mike tsaye babu shiri tana daɗa waro ido.
Ta kalli Falmata tace, "Kin tabbatar wannan hoton yarinyar da kike ba Ni labari ne?".
Kai kawai Falmata ta gyada cikin rashin fahimtar ɗimautar Hajja Fulani lokaci guda.
"Lallai muna da kyauta mai tsoka idan hasashena ya tabbata". Hajja Fulani ta faɗa da wani murmushi a fuskarta.
Ita dai Falmata kallonta kawai take yi har ta gama zantukan kafin tace, "Hajiya meya faru?".
"Kamar yadda na fada miki wannan zance mai girma ne, ki tabbatar idan za ayi zama a Fada kin zo da wayarki don za ta yi mana amfani".
Da to kawai Falmata ta amsa ta karɓi wayar ta fice a ɗakin don ita kam Hajja Fulani ta sa ta a wani tunanin daban.
Bayan ta gama karyawa ta ɗauki abubuwan da za ta bukata ta nufi sashen Bayi, a can ma aiki ta tarar suna yi sosai dan haka ta nemi gefe guda ta zauna tana kallon yadda suke gudanar da ayyukan.
Karfe 12 ta ji gidan ya sake runɗewa da tambura hakan ne ya tabbatar mata da cewa bakin sun iso, zamanta ta cigaba da yi a sashen Bayin don ta san ko ta koma cikin gida a yanzu Hayaniyar jama'a ba zai bari ta samu hutu sosai ba.
**** Tunda na tashi yau nake tsintar kaina da yawan faɗuwar gaba, bansan dalili ba sai dai na yawaita addu'a kawai, har Hajiya Kaka sai da ta fuskanci rashin walwala a tattare da ni amma na mata ƙaryar gajiya ce kawai ke ɗawainiya da ni.
Ga shi a ranar matar Daddy da ke ƙasar waje za ta zo Nijeriya kuma a gidan Hajiya Kaka tace za ta fara sauko, tare da yaranta da kuma Abdallah yaron Daddy na fari, shiyasa tun safe nake ta hada-hadar haɗa abincin da zan tarbesu da shi.
Da taimakon Hajiya Kaka na samu na kammala ayyukan da wuri na shirya komai a kan Dining na shiga ɗaki don yin wanka da sallah.
Ina tsaka da yin Sallah na jiyo shigowarsu, sai da na kammala komai a nutse kafin na fita don na musu maraba.
Gabaɗaya suka maida kallonsu gareni lokacin da nayi sallama a falon.
Ammi ta mike tsaye tana ƙara kallona sosai kafin tace, "Wallahi Hajiya Kaka da Jiddah ba mace bace babu abin da zai hana nace wannan ba Bilal ba ne saboda tsananin kamar da suke yi".
"Waye kuma Bilal?". Hajiya Kaka ta tambaya tana taɓe baki.
Sai da ta zauna kafin tace , "Yaron wata maƙociyar mu ne, su ma yau suka taho Nijeriya. Wallahi sun yi kama sosai da Jiddah har girmansu ma, Son ka kalli Jiddah fa sosai dan Allah ba Bilal kake gani a nan ba".
Sai a lokacin Abdallah ta hankalinsa ke kan waya ya ɗago yana kallona, nima shi nake kallo, kamar sauran shi ma yayi mamaki kamar yadda fuskarsa ta nuna.
"Kila kama ce kawai, kinsan haka na faruwa". Ya faɗa yana cigaba da latse-latsen wayar shi.
Nan dai suka yi ta mamaki har ƴan biyu na faɗin za su ɗauki hotona idan sun koma su nunawa Bilal, daga ƙarshe dai muka mike duka don zuwa cin abincin. Cikin lokaci kaɗan muka saɓa da Ƴan Biyu Nabila da Jalila musamman da suke sa'anni na, na lura da wani da Abdallah ke yi min a duk sanda muka hada ido, kallo ne me kama da harara Ni dai ban tanka ba bare yace na yi wani laifin don na fuskanci kamar ƙiris yake jira dama ya fara yi da Ni.
Sai bayan da suka yi sallar La'asar kafin suka mike don tafiya gida, nan fa ƴan biyu suka ce sai dai mu tafi tare Hajiya Kaka kuwa ta runtse ido tace ba ta san zancen ba. Daga ƙarshe dai dole suka yanke shawarar zama a gidan Hajiya Kaka duk don saboda ni, Ammi da Abdallah kuma suka bi direba ya kai su gida.
***** Ba ta jima da idar da Sallar La'asar ba wayarta da ke kan gadonta ta fara ruri, a hankali ta mike ta isa ga wayar ta ɗauka tare da karawa a kunne tana sallama. Daga dayan bangaren Hajja Fulani ba ta amsa sallamar ba ta fara magana da faɗa, "Sakon zuwa Fada bai riskeki ba ne?".
Fuska ta yamutsa tace, "Yanzu na shigo ne Hajja,na tsaya yin Sallah ne".
"To kiyi maza ki zo Fada don kowa ya hallara kuma kinsan ba tsayawa jiranki za mu yi ba".
"To Hajja ga Ni nan tafe yanzu". Ta faɗa cike da Ladabi, kashe wayar tayi tana sauke ajiyar zuciya.
Yunwa take ji amma a yanzu ba ta da damar da za ta tsaya cin abinci saboda jiranta da ake yi dama kuma ba ta je ta gaida baƙin ba tun isowarsu kar laifin na ta ya ƙaru.
Lafaya kawai ta ɗauka ta naɗa a kan kayan da ke jikinta ta dauki wayarta ta fita, kai tsaye babban Falon Mahaifinsu ta nufa dama duk sanda za ayi zama na family a can suke yi.
Da sallama ta shiga Falon, ƙalilan da hankalinsu ke kan ƙofar shigowa ne suka amsa, gabaɗaya ahalin gidan sun hallara kama daga kan ƴaƴa da jikoki har wadanda basa ƙasar ma duk sun dawo, lallai za a yi babban taro, ta faɗa a ranta. A hankali ta dinga bin mutane ɗai-dai tana gaishesu, wasu su amsa da fara'a wasu kuma ba yabo ba fallasa suke amsawa, da haka har ta ƙarasa kusa da mahaifinta da ke zaune shi da wani kyakkyawan mutum a kujera daya ta gaishe su sannan ta koma wajen Kakarsu ta gaisheta tare da zama a ƙasa gefen ƙafarta.
Wani daga cikin manyan ƴaƴan mai martaba ne ya fara bude taro da addu'a, bayan an shafa ne Sarki ya yi gyaran murya ya fara magana.
"Naji dadi da ku ka martaba ni a matsayina na mahaifi kuka amsa kiran da nayi muku duk da na san cewa da yawa daga cikinku suna fama da ayyuka amma kuka bari don ku zo nan".
"Abu na gaba da nake son sanar da ku shi ne dawowar ɗan'uwa na gida wanda wata gagarumar matsala ce ta zama silar tafiyarsa wata ƙasa ya cigaba da zama na tsawon lokaci a can, wasu daga cikinku za su iya tuna abubuwan da suka faru a waccan lokacin yayin da wasu ba za su iya tunawa. Ɗan'uwana ne shi na jini, ga mahaifiyarmu nan ita ta haife mu kuma ta raine mu. A tare da shi akwai iyalansa wanda nake so ku ci-gaba da zumunci a tsakaninku tamkar dama can tare kuke, kanne suke a wajenku don kuwa babu wanda bai girmesu ba a cikin ƴaƴana sai dai a cikin jikokine za a iya samun sa'aninsu. Ku matso kusa don ahalinku su kalleku da kyau". Sarkin ya ƙarashe maganar yana yafito yaran da ke rakuɓe a jikin mahaifiyarsu.
"Wannan shi ne Bilal". Ya faɗa yana shafa kan wani matashin yaro da ya zo kusa da shi. Ido Falmata ta ware sosai tana kallon wanda aka kira da Bilal ɗin cike da mamaki, ba ta gama mamaki ba ya sake kamo wata yarinyar da shekarunta ba za su wuce goma sha ba yace, "Wannan sunanta Anisa, sannan ga masu binta ƴan biyu ne Aryaan da Ayrah". Ya karasa yana janyo yaran da ba su wuce shekara Bakwai ba kusa da su. Sosai Falmata ta kara kidimewa saboda tsananin kamar da yaran suke yi da Jiddah.
Ba shiri ta mike ta isa kusa da Bilal tana taɓa shi kafin kuma ta waiga ga Mai Martaba ta fara magana, "Wallahi hasashena ya tabbata, dama sai da na raya a raina akwai wata alaƙa mai ƙarfi a tsakanina da *Jiddatulrahman*, babu ko shakka ita ƴar gidan nan ce. Abba ka kalli wannan hoton dan Allah ka tabbatar min da cewa Jiddah ƴar wannan Masarautar ce". Ta ƙarashe maganar jikinta na kyarma tana ƙoƙarin fito da hoton Jiddah a cikin wayarta, da sauri ta mika wa Mai martaba tana jiran abin da zai faɗa. Tare da Ɗan'uwan na sa dake zaune kusa da shi suka mike tsaye tare da hada baki wajen fadin, "Jiddatulrahman!"
Jin abin da suka fada ne yasa mahaifiyar su Bilal da ke zaune gefe ta nufo gurin da sauri tana karɓar wayar don ganin hoton.
"Wallahi ita ce, ba ta mutu ba tana raye. Ki kaini inda take Jiddah ta tana raye ba ta mutu ba dama na fada muku da ranta". Ta faɗa tana girgiza Falmata da ta kara kidimewa da ganin Mahaifiyar su Bilal ɗin, da alama yaran kamanninta suka ɗebo don kuwa da ace a wani guri ta hadu da wannan babu shakka za ta kirata da Jiddah.
Sai bayan shudewar wasu mintuna kafin falon ya ɗan nutsu, mai martaba ya kalli Falmata ya ce, "Mamana a ina kika haɗu da wannan yarinyar?".
Nan ta ba su labarin tun farkon haduwar da suka yi har zuwa yau.
Shiru ya sake ratsa gurin kafin Sarkin yace, "Kira mana ita a waya".
Ba shiri ta dauko wayar ta fara ƙoƙarin kira.
Muna zaune da ƴan biyu muna hira a ɗakina wayar Hajiya Kaka da ke hannuna ta shiga ruri, ganin wacce ke kira ne yasa cike da zumuɗi na ɗauka da sallama.
Daga can ɓangaren ta amsa min, muka sake gaisawa kafin tace ta kira ne taji yadda nake tare da faɗin na gaishe da Hajiya Kaka.
Murmushi mai Martaba ya yi kafin yace, "Duk da ban ganta ba amma babu shakka wannan jinin mu ce, yanayin maganarta sak na mahaifinta. Lallai tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai da ya dawo mana da farin ciki a lokacin da muka ɗebe tsammanin samu. Dole mu tafi Kano da yammacin nan".
Shi dai Ɗan'uwan Sarki bai ce komai ba sai idanuwansa da suka yi ja sosai, ita kuwa mahaifiyar su Bilal shessheƙa kawai take yi.
Nan take Sarki ya umarci cewa a fito da Private Jet din masarautar don kuwa yana son tabbatar da kasancewar Jiddah jinin masarautar, bayan haka kuma a wannan karon tilas Mahaifiyarsu Jiddahn ta faɗi abin da ta ɗauki tsawon shekaru tana ɓoyewa, ya sha alwashin ko wane ne ke da alhakin ɓatan Jiddah zai fuskanci hukunci me tsanani. Dan haka ne ya ba da umarnin kar wanda ya fita daga gidan sarautar har sai sun dawo daga Kano.
Falmata, Hajja Fulani, Sarki, Iyayen Jiddah da ƴan'uwanta, Kakarsu, Waziri da kuma sauran wasu mutanen ne suka sauka a garin Kano a na tsaka da kiran Sallar Magriba. Daga masarautar Kano aka zo tarbarsu don haka kai tsaye Fadar suka wuce don yin Sallah kafin su wuce inda suka zo.
Muna tsaka da cin tuwon da yau Hajiya Kaka da kanta ta yi mana miyar kuka ta asali, ga yajin daddawa da man shanu da muka wadata tuwon da shi, a gaskiya na jima ban ci tuwo mai daɗin wannan ba, hatta ƴan biyu santin tuwon suke yi. Ita kuwa Hajiya Kaka tana gefe tana mana dariya hadi da tsokanar idan ba mu dage mun koyi girki ba da mun yi aure mazajenmu za su ƙaro mana abokan zama.
Dirin motoci muka ji don haka duk muka yi shiru muna sauraren har zuwa lokacin da muka ji an bude gate din motoci na shigowa.
Hajiya Kaka ce ta taɓe baki tace, "Yanzu haka Daddynku ne, shi a rayuwarsa ba zai dinga yawo da mota daya ba sai ya tara motoci mutane na bin bayansa, idan ma ya zama dole ai sai a ware mota guda bayan wacce zai shiga din". Ta ƙarashe maganar tana kwafa.
Nayi dariya nace, "Ke dai Hajiya har yanzu ba zaki waye ba sam, manyan mutane ai ba sa yawo haka nan ba tare da masu tsaron lafiyarsu ba musamman da ƙasar nan ta zama wani iri babu cikakken tsaro. Kin ga a yanzu koda Daddy zai fita shi kadai ba lallai mutane su gane ba tunda an saba ganin yana yawo da masu tsaronsa, Allah ma dai ya kiyaye faruwa wani abu da zai sa sai ya ɓadda kama kafin ya fita".
Harara ta watso min kafin tace, "Ga iya tsara zance kamar Ubanta, da ke da Abdallah halin Daddynku kuka biyo idan ku ka yi magana da mutum duk sai ya ji ya gamsu".
Dariya muka yi dukanmu musamman da yanayin yadda tayi maganar dole mutum ya dara. Ba ta kai ga yin magana ba mai gadi ya yi sallama a ƙofar falon aka ba shi umarnin shigowa.
Bayan ya gaida Hajiya Kaka mu kuma mun gaida shi ya ce, "Hajiya baƙi ne aka yi, sun ce a shaida miki daga Masarautar Boddo ta jihar Gombe suke".
Ƙirji Hajiya Kaka ta dafe kafin tace, "Allah Yasa dai lafiya!".
Ni kuwa gabana ne ya yi mummunar faduwa musamman da na tuna cewa daga Masarautar su Falmata ne, Allah yasa ba wani abin bane ya same Falmata.
Ban gama tunanin da nake yi ba naji Hajiya na ba da umarnin yace su shigo, ta mike da hanzari tana umartar mu tattara falon duk da ba wani datti ne a ciki ba.
Da sallama duk suka shigo Falon, su kaɗai ne babu rakiyar Fadawa kamar yadda Mai martaba ya bukata duk da kuwa Sarkin Kano ya so Fadawa su yi musu rakiya amma hakan bai samu ba, sai shi da kansa da kuma wazirinsa da suka biyo su musamman da suka ji abin da ke tafe da su.
Ido na fara rabawa don ganin ko zan ga Falmata duk da kuwa sake-saken da nake a raina na cewar wani abu ne ya faru da ita, aikuwa ita na fara gani don haka nayi ajiyar zuciya na koma gefe ina taya Hajiya Kaka da ƴan biyu yi musu sannu da zuwa, sam ban kula da fuskokinsu ba sai da naji Jalila tace, "Lahh Bilal kai ne, Mummyn Bilal tare kuke ashe. Sannunku da zuwa".
Su ma cikin mamaki suke kallon su Jalila, sai a lokacin na kalli wanda aka kira da Bilal da kuma sauran wadanda suke tare, sosai na yi mamakin matuƙar kamar da muke yi.
Ita ma Hajiya Kaka haɓa ta riƙe cike da mamaki.
Sai bayan da suka zauna kafin ita ma Hajiyar tayi ƙarfin halin zama tana ƙara mamakin kamannin, a takaice dai aka gaisa kafin Mai Martaba da kansa ya fadi abin da ke tafe da su.
Naji zancen tamkar a mafarkin da na saba yi na cewar na haɗu da Mahaifana, gani nake yi tamkar gizo abin ke yi min, na ƙurawa wacce aka ambata a matsayin mahaifiyata kallo ina mamakin tsananin kamar da muke yi. Zancen Hajiya Kaka ne ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi.
"Alhamdu Lillah. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da Ya halicci bayinsa sannan ya sanya ƙaddara abar jarabtar bayinsa da ita. Haƙiƙa ko ba a fada ba duk wanda ya kalli waɗannan ahali dole ya ambace su a matsayin jini ɗaya, Ma Sha Allah.". Abin da Hajiyar ta furta kenan tana matsar kwallar farin ciki. Take naji wata nutsuwa na ratsa lungu da saƙo na jiki na, ban manta da Ubangijina da ya sanya al'amura suka zo da sauki haka a gareni ba, don haka na zabe a ƙasa ina sujjadar godiya a gare shi. Bayan na ɗago wani kuka ya kwace min, daidai lokacin da Mahaifiyata ta ƙaraso inda nake ta rungume Ni tsam a jikinta tana sake kuka mai tsuma zuciya.
Kuka muke yi sosai, sauran yaran suka ƙaraso inda muke suna taya mu, tausayinmu yasa ita ma Hajiya Kaka ta sake fashewa da kukan. Sai falon ya zama kamar gidan mutuwa koke-koke ne kaɗai ke tashi harda su Nabila da Falmata, da dai mazan suka ga abin ba na ƙare bane nan suka tsawatar tare da yin nasihar cewa godiya ya kamata mu yi ga Allah ba wannan kukan ba. Bayan an nutsu Hajiya Kaka ta warware musu duk abubuwan da suka faru kama daga kan barin Umma gida har zuwa lokacin da muka haɗu har gaskiya ta bayyana. Nan a ka sake bude wani babin alhinin ana sake mayar da magana, Mai Martaba yace lallai ya kamata mu tafi Katsina gabaɗaya don a ga Ummana sannan kuma su yi godiyar irin rikon da aka yi min. An tsaida magana cewa gobe za mu sammakon isa Katsina, a nan aka bar su Bilal da Mummy kamar yadda naji yaran suna kiranta da shi sai Falmata don a nan za su kwana. Mazan suka yi mana sallama suka wuce Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, kafin su tafi sai da na keɓe da mahaifina yana ta saka min albarka.
Daren ya koma mana kamar rana, a daren aka kira Ammyn su Jalila aka fada mata ita ma murna tayi sosai tare da faɗin da ita za a tafi Katsina dama wani sati suke son zuwa ganin dangi.
Babin Hira muka buɗe sosai, nan Falmata take faɗa min yadda abubuwa suka faru a Masarautar a yammacin ranar tare da faɗin ita dama tun ranar da ta fara gani na ta ji kamar akwai wata dangantaka a tsakaninmu.
Washegari tare da Falmata da su Nabila muka shiga Kicin don hada abin karyawa, abinci mai rai da lafiya muka shirya wanda Falmata da kanta ta kawo shawarar yin wasu girke-girken, mun yi mamaki kwarai yadda ta iya tsara girki haka duk da kasancewarta ƴar gidan sarauta. Dariya kawai tayi mana.
Cike da farin ciki muka ci abincin, bayan mun gama kuma duk muka shiga ciki don shiryawa.
Ƙarfe sha biyu da rabi muka isa garin Katsina ta Dikko ɗakin kara kunya gare su ba dai tsoro ba. Mun samu tarba ta musamman daga ahalin Lamiɗo dama kuma an san da zuwanmu.
Lokacin da Ummana tayi arba da Mummy ai sai ta rude ta ƙanƙameta tana fadin wallahi ita ce, dakyar aka raba su saboda yadda murnar ta rikiɗe ta koma kuka sosai.
Sai da aka samu nutsuwa sosai kafin aka haɗu a babban falon marigayi lamiɗo, falon da na laƙabawa sunan falon tarihi saboda a wannan falon na fara sanin ko Ni wacece ga shi yau ma a cikin falon zan sake sanin abin da ya raba Ni da mahaifiyata tun ina ƙarama. Bayan an gama koke-koke da alhini aka ba wa mahaifiyata damar yin magana da faɗin musabbabin wadannan abubuwa.
A sanyaye ta fara magana kamar haka:
Masarautar Boddo masarauta ce dake da ɗumbin tarihi, an kafa wannan masarauta shekaru da dama da suka shuɗe kuma an sansu da mulkar jama'a bisa adalci da jin ƙai musamman ga marasa ƙarfi. Kamar kowacce Sarauta tun Kaka da kakanni ake gadonta haka abin zai yi ta za ga wa har zuwa kan ƴaƴan da jikoki, a wannan masarauta su ma abin bai bambamta ba. Sai dai tsarin gadon wannan masarauta an kafa shi ne bisa wata al'ada ko kuma nace wani canfi da ake yi.
A lokacin da girma ya fara kama Sarkin da ke kan karaga, to sai a duba a cikin matan ƴaƴansa maza wacece ta haihu a ranar da ake bikin zagayowar Ranar kafuwar Masarauta, an canfi hakan a matsayin wata hanya da za a gane wanda zai zama adali idan ya hau karagar mulki.
A kan wannan tsari ake tafiya har zuwa zamanin Sarki Abdallah wanda Ɗan uwa ne ga mahaifiyata da Allah ya yi mata rasuwa da jimawa. Sarki Abdallah Ƴaƴa uku kacal ya mallaka a duniya, biyun fari maza ne sai autarsu mace wacce a yanzu haka take Masarautar Sokoto inda anan ta kafa ta ta zuri'ar. Akwai tazarar haihuwa tsakanin Junaid da kuma Sameer wato ƴaƴa mazan da Sarki Abdallah ya mallaka, don haka Junaid shi ne Wanda ya fara yin aure.
Ya auri ƴar wazirin mahaifinsa a wannan lokacin Nafisa wacce ake kira da Hajja Inno a yanzu, sai dai har tayi haihuwa uku ba ta haifi wanda zai yi silar zaman Junaid a matsayin magajin Sarki ba, a zahirin gaskiya Hajja Inno tana bakin ciki da rashin haihuwar garkuwar Magaji kamar yadda ake faɗa. A lokacin girma ya fara kama Sarki sosai don haka ya umarci Junaid da ƙara aure, ba a jima ba ya auro ɗiyar wani hamshaƙin mai kuɗi a garin Bauchi Hauwa'u wacce ita ma yanzu girma yasa ake kiranta da Hajja Fulani, ita ma dai abin ya zo iri ɗaya da na Hajja Inno don har ta haifi ƴaƴa biyu itama ba a yi nasarar samun Magaji a cikinsu ba. A wannan karon ma Junaid aure ya sake yi ya auro Sajida da Ita ma a yanzu ake kira da Hajja Momi, wanda aka haɗa da auren Sameer wanda ya auro ɗiyar ƙanwar mahaifinsu da ta rasu Hamida wato Ni kenan da ake kira da Mummy.
Cikin buwayar Allah Hajja Momi ta samu ciki har ta haifi yara uku amma Ni ko ɓatan wata ban taɓa yi ba, matan Junaid har a wannan lokacin suna cigaba da haihuwa ko za a dace wata daga cikinsu ta haifo garkuwar Magaji musamman da har zuwa wani lokaci ban samu ciki ba. Sameer bai wani damu ba dama shi wannan canfi da al'adar gidan Sarautar ba wani birgeshi suke yi ba.
Kwatsam! Na wayi gari da shigar ciki, mun yi murna sosai duk da cewa ba mu saka a ranmu cewar zan haifo garkuwar magajin ba. A wannan lokacin sai na fara fuskantar kishi daga matan Junaid da duk sanda za mu zauna inuwa ɗaya sai sun nuna min, Ni dai ban damu ba musamman da bansan abin da suke kishi a kai ba don haka na shiga kebe kaina a sashena ba tare da na fito na kasance a cikinsu ba.
A ranar da aka yi bikin zagayowar ranar kafuwar Masarautar ne kuma Allah ya nufe Ni da haihuwar yara ƴan biyu masu matukar kyau da kama da Ni, mun yi mamaki ƙwarai saboda a lokacin cikina bai cika wata tara ba kuma haihuwar ba ta zo da wani matsala ba. A ranar aka ambaci Sameer a matsayin magajin Sarki, akwai kyakkyawan zumunci da soyayyar a tsakanin Ƴaƴan Sarkin don haka ne Junaid ya taya kaninshi murna sosai da kyakkyawar zuciya.
Sai dai a ɓangaren matan Junaid abin ba haka yake ba kishi sosai suke da kasancewar Sameer magajin Sarki don haka suka yanke shawarar kulla wani tuggun da zai sa sarautar ta koma hannun Junaid.
Sun so hada kai dukkansu sai dai Hajja Fulani ta nuna ita ba zata iya hada kai da kishiyoyinta a abinda ya shafi mulki ba, don haka Hajja Inno da Hajja Momi kadai ke shirya tuggunsu.
Yaran da na haifa sun sha gata sosai daga ahalin wannan Masarauta, rana suna aka rada wa yara suna Hauwa'u da Bilal wanda Sarki da kanshi ya zabar musu wannan sunan, a cewarsa masu wannan suna suna da muhimmanci sosai a tarihin Masarautar Boddo. Soyayyar da yake nuna musu kuwa ya dare wanda yake nuna wa sauran jikokinsa musamman Hauwa'u da shi da kansa ya rada mata inkiyar *Jiddatulrahman*, tun ba su wuce sati biyu a duniya ba yake aikowa a zo a dauke su ya kai su fada duk da cewa wannan wani sabon abu ne amma bai damu da cecekucen da ake yi ba. Wannan soyayya da Sarki ke yi wa ƴan biyu ya sake hura wutar tsana sosai a zuƙatan Matan Junaid don haka suka shirya ɗaukan mataki mai muni a kan yaran.
Gurin wani boka suka nufa don ya yi musu asiri, kamar yadda suka bukata bokan ya sha alwashin yin asirin da zai sa naji na tsani Masarautar baki ɗaya sannan na ɗauki yaran na tafi da su guri mai nisa da ba za mu sake waiwayar Masarautar Boddo ba, shi kuma Sameer za a saka mi shi ciwon da za a rasa maganinshi har ciwon ya zama ajalinsa. Na samu labarin hakan ne a wajen wata amintacciyar jakadiyarsu da taji tausayina ta faɗa min. Sai dai a lokacin na rasa mafita kuma na rasa a'a zan fara tunkara da wannan zance don kuwa a lokacin wata tafiya ta kama Sameer zuwa ƙasar waje baya nan, don haka na yanke shawarar jiran dawowarsa don mu san ta inda za mu ɓullowa lamarin. Sai dai lamarin ƙaddara ya riga fata don tafiyar ta shi ta ɗauke shi tsawon lokaci, Ni kuma har ga Allah a lokacin na fara mantawa da zancen musamman da na ga an kwana biyu babu abin da ya faru dama asali na fawwalawa Ubangiji al'amura ne.
Wata safiya Jiddatulrahman ta tashi da matsanancin zazzaɓi don haka ne da aka zo ɗaukarsu don kai su wajen Sarki da Bilal kawai aka tafi, inda Ni kuma na cigaba da kulawa da Ƴar'uwarsa.
Ina tsaka da shirya Jiddatulrahman bayan tayi amai ta ɓata kayan jikinta naji wani abu mai kama da yana ya rufe idanuna, lokaci guda kuma naji ƙirjina ya yi min nauyi, na ɗauki wasu mintuna a haka kafin naji sassauci. Sai kuma me! Naji gabaɗaya tamkar ina cikin wuta ne naji tsanar masarautar ya mamaye ƙirjina, zuciyata sai tafasa take yi burina kawai na fice a masarautar. Don haka ba shiri na tattara wasu daga cikin kayan Jiddah da na Bilal da kuma gwala-gwalai da suka samu kyautarsu a lokacin da aka haifesu na zuba a cikin wani akwati sannan da buɗe wata durowa da Sameer ke ajiyar kudin da yake kasuwanci da su na ɗebi kuɗin da yawa da Ni kaina bansan adadinsu ba, na manta da Bilal da ke Faɗa, na goya Jiddah a bayana na bi wata ƙofa dake baya na fice a masarautar.
Wani ikon Allah kuma ina fita naji na dawo hayyacina har na gane abin da ya faru da Ni, amma da nayi ƙoƙarin komawa kuma sai na sake rudewa. Don haka nayi tunanin zuwa ga wani da na sani sai dai kuma lokaci guda na manta da kowa, zuciyata ke azalzalamin da kawai na shiga duniya, don haka na rufe fuska gudun kada na haɗu da wani da ya sanni ma na fara tafiyar da bansan inda na nufa ba.
Nayi tafiya mai tsawo har na fara barin cikin gari amma babu ko alamar gajiya a tattare da ni, ba Ni da niyyar zama na huta ko kuma na ba wa Jiddah abinci duk da kukan da take yi a bayana. A haka har na iso wani ƙaramin gari, sai dai abin da ya ba Ni mamaki shi ne yadda naji gabaɗaya bana son zama da mutane don haka kawai na fara bin cikin gonaki har na yiwa wani jeji tsinkaye, jejin da shigarsa tayi sanadin da na rabu da gudan jinina na tsayin shekaru, sai dai ba zan fasa yi wa Allah godiya da yasa ta faɗa hannu na gari ba...
A daidai nan Mummy ta fashe da wani kuka mai sosa rai, gabaɗaya labarin ya kashe wa jama'ar da ke falon jiki don haka cikin lokaci ƙanƙani ta samu masu taya ta, ciki kuwa har da ni da na fara fahimtar silar rabuwa ta da Mahaifana na tsayin shekaru..
Sai da tayi kukan sosai kafin ta ci gaba da cewa:
Sai a wannan lokacin naji na samu nutsuwa sosai dan haka na nemi guri a ƙasan wata bishiya na zauna, sannan na kunto Jiddah daga baya na ina kallonta lokaci guda kuma tausayin yarinyar ya kama Ni sosai. Na yi shirin shayar da ita sai na ji maganganu na tashi ƙasa-ƙasa don haka na miƙe da sauri ina dube-dube har na fahimci daga inda maganar ke fitowa, ba wasu na gani ba face Umman Jiddah, na jima sosai ina nazari kafin daga ƙarshe zuciyata ta aminta da shawarar da na yanke lokaci guda. Don haka na koma inda na baro kayana na bincika na samu takarda da biro, cikin sauri nayi wani gajeren rubutun da suka gani wanda yasa suka aminta da daukarta, da fari na yi shirin kai ta har inda suke sai yarinyar ta fara kuka don haka nayi saurin kwanciya saboda na san babu shakka za su jiyo kukanta.
A idona komai ya faru tun daga lokacin da suka zo har zuwa lokacin da suka ɗauketa.
Bayan sun jima da tafiya nima na miƙe na ci gaba da tafiya har dare ya fara yi, na nemi guri na kwanta. Bansan me ya sake faruwa da ni ba tun daga wannan lokacin, har zuwa ranar da na farka na ganni cikin Masarautar Boddo sai dai a ranar ban ji tsana da rashin son zaman Masarautar ba.
Sai da na samu nutsuwa ake faɗa min na yi shekaru huɗu ba na gida, a lokacin da aka ganni kuma ba na cikin hayyacina ma'ana dai a haukace aka tsinto Ni. Babu abin da yafi ƙarfin addu'a, cikin lokaci ƙanƙani na samu waraka bayan addu'o'i da aka tsananta sosai da kuma saukar Alqur'ani da aka dinga yi.
Mun yi alhini rashin Jiddah, anyi jigiya sosai amma babu labari don haka muka fauwala wa Ubangiji.
Watarana wannan Jakadiyar da same mu a sashinmu ta bayyana mana duk wasu makirci da Matan Junaid suka shirya har da batun asirin da aka yi min. Sosai ran Sameer ya ɓaci sai dai ya kasance mai haƙuri, don haka ya yanke shawarar mu bar ƙasar dama a lokacin kasuwancin da yake yi ya haɓaka sosai sannan yafi ƙarfi a ƙasashen waje. Bayan kai ruwa rana sosai daga ƙarshe Mai Martaba ya amince ba don ranshi ya so ba, har sai da Sameer ya bayyana mai dalilinsa, ya yi mana fatan alheri tare da faɗin mu rike zumunci duk rintsi. Daga wannan ranar muka yi sallama da Ahalin Masarautar Boddo zuwa ƙasar Chicago, inda a nan muka ci gaba da zama.
Ko bayan rasuwar Mai Martaba ma ba mu dawo ba gudun cewa manyan da ke cikin Masarautar za su iya naɗa Sameer a matsayin Magaji, shiyasa ya yanke duk wata hanya da za ta sada shi da ƴan gida, har sai da ya tabbatar da an naɗa Junaid a matsayin Sarki kafin ya kai musu ziyara, shi ma bai jima ba kwanaki biyu ya yi ya koma Chicago tun daga wannan lokacin kuma ba mu sake waiwayar gida ba sai wannan lokacin. A can na haifi sauran yaranmu.
Falon ya dauki shiru na tsawon lokaci, har sai da Abiey ya katse shiru, shi kuwa Mai Martaba jin labarin abin da bai sani ba tsawon wannan shekarun yasa tun da ya sunkuyar da kai bai ɗago ba, da alama bayan alhini har da kunyar Abbana yake yi.
Daga ƙarshe dai abin da yafi alherin aka yi, wato yafiya ga juna. Sannan Abiey ya ja hankalin Mai Martaba a kan kada a dauki hukunci mai tsanani a kan Matanshi, tun da abu ya jima to a yafe, musamman da yanzu ya ke a matsayin Sarki wanda dama dalilin da yasa aka samu rashin jituwar kenan.
A wannan ranar da yamma muka yi shirin tafiya garin Bauchi, don Mai Martaba ya ƙi batun su ƙara kwana kuma Abiey ma ya goyi bayan hakan tunda dai shi mutum ne da ke da nauyin al'umma a kansa.
Gaba ɗaya Ahalin Marigayi Lamiɗo tun daga kan iyaye, yara da jikoki duk tare muka tafi a jirgin Masarautar Boddo saboda walimar dawowata da za a gabatar, wani abu idan aka yi na kan kasa aiwatar da komai sai dai hawayen farin ciki da ke ziyartar fuskata.
Na yi godiya ga Allah da Ya ya ye min matsalolina cikin ƙanƙanin lokaci a kuma sanda ban yi zato ba.
A garin Bauchi na ga abin da ake kira gata, kowa marmari da son na kasance da shi yake, Ni dai na kasa sakin jiki da kowa tunda dai Allah kaɗai ya san karatun kurma. Wani babban sashe aka warewa mutan Katsina sannan aka turo kuyangu da za su dinga kula da su. Ni dai ko da yaushe muna tare da Falmata daman a ɗakinta na sauka.
Kwanaki biyu da zuwanmu aka shirya babbar walimah na dawowata, an gayyace manyan mutane sosai har daga ƙasar waje inda Daddy da Abbana ke aiki duk abokan harƙallarsu sun amsa gayyata. Hajiya Zara'u da Najwa ma sun samu halarta, sai dai na fahimci rashin sakewa a tattare da su.Anyi ƙayatacciyar walima na samu manyan kyaututtuka da dama. Daga ƙarshe dai an watse kowa na fatan alheri.
Bayan kwana biyu su ma mutanen Katsina suka koma sai dai Hajiya Kaka tana nan, don tare za mu koma Kano idan hutuna ya ƙare saboda an yanke cewar ba za a karbe Ni daga wajenta ba.
Mai Martaba ya sa aka kira masa matansa cikin sirri ba tare da sanin kowa ba ya yi musu faɗa sosai da kuma gargaɗi, daga ƙarshe kuma ya musu nasiha. A zahiri dai sun nuna nadamarsu sosai tare da neman yafiya.
Tun daga wannan lokacin farin ciki ya yi sallama cikin rayuwata. Ba Ni da sauran damuwa don ta kowane fanni tattali da kulawa na ke samu.
Hajja Fulani kuwa tunda taji labarin yadda rayuwata ta kasance ta saduda, ta daina nuna ƙyama da hantarar Talakawa musamman Bayi da Kuyangu, sai dai fa wannan izzar da mulki na matar Sarki na tattare da ita.
Hutuna yana ƙarewa muka koma Kano Ni da Hajiya Kaka, sai dai fa a wannan karon an hada mu da masu yi mana hidima sosai maza da mata, duk da da fari Hajiyan ba ta so ba amma Mai Martaba ya nemi alfarmar hakan.
Sai na zama tamkar tsuntsuwa, idan bana Bauchi ina Kano, idan kuma ba na Kano to babu shakka za a iske ni a Katsina.
An daura auren Daddy da Ummata bayan da suka sabonta tsohuwar soyayyar da suke yi wa juna. Ita ma a Kano ya ajiyeta tare da Hajiya Zara'u da a yanzu ta zama shiru-shiru sam ta daina son hayaniya, ga kuma uwa uba biyayya da take yi wa Hajiya Kaka.
Burin Hajja Fulani na ganin auren Falmata da Yarima Ajmal ya cika, anyi kasaitaccen biki irin na sarauta a masarautun guda biyu. Inda daga ƙarshe amarya Falmata ta bar gidan sarauta kuma ta koma gidan Sarauta.
Rayuwa mai da farin ciki da kwanciyar hankali ne ta ci gaba da wanzuwa a tsakanin wadannan ahali, sai abin da ba za a rasa ba na jarabawa daga Ubangiji wanda hakan ya kasance wajibi a kan kowane Bawa kamar yadda Ubangiji ya alƙawaranta cewar, zai jarabci bayinsa muminai da abubuwa da dama.
**** Wata Safiyar Asabar muna zaune a babban falon Hajiya Kaka, wanda a yanzu aka ƙara fadada shi sannan aka wadata da kayan alatu na zamani. Abdallah ne ya yi sallama ya shigo Falon, cikin shigarsa ta ƙasaita da ta dace da yanayin zubin halittarsa, na rasa dalilin da yasa a duk lokacin da zan yi ido biyu da Abdallah sai na tsinci kai na da faduwar gaba da kuma kunyarsa sosai. Yanzu ma da ya shigo sunkuyar kai na yi sosai ina gaida shi cike da kunya, ga shi babu ko ɗankwali a kaina kitso ɗaɗɗaya da ke kaina ya bazu a kafada ta da kuma bayana.
Hajiya Kaka ce ta daure fuska cikin wasa ta ce, "Ni fa ba kasafai nake son gauraye suna ziyartar min gida ba, na fi so a duk lokacin da mutum zai kawo min ziyara ya sako matarsa da yaransu a gaba su zo tare ehee".
Murmushi ya yi kafin yace, "Ai ba ki gaji da gani na ba kuwa tunda kin riƙe min mata a gidanki kin ƙi bada damar da zan ɗauketa zuwa gidana".
Baki ta bude cike da mamaki tana kallonsa, lokaci guda kuma ta saki dariya haɗe da guda.
"Alhamdu Lillah! Amma dai jikar ta wa tana da tsada sosai gaskiya".
Wannan karon bai tanka mata ba sai tsareni da ido da ya yi, sai da ya kalleni sosai kafin yace, "Nana Hauwa ki faɗa mata ke ko babu lefe za ki zauna a gidan Abdallah kinji"
Kunya sosai ta kama Ni, nayi shirin miƙewa na gudu daki muka ji hayaniya na tasowa daga farfajiyar gidan, shiru muka yi muna saurara, jin abin ya ƙi ƙare ne yasa Abdallah miƙewa ya nufi fita don yaga meke faruwa, Hajiya Kaka ma ta rufa masa baya. Ni kuwa daki na shiga na fara dauko mayafi kafin na fita zuwa wajen dan ganin meke faruwa.
Mamaki ya kama ni sosai ganin Babana, wai dama tun ɗazu ya zo amma masu gadi suka hana shi shigowa shi ne yake hargagi da masifar dole sai ya shigo ya nemi gafararmu Ni da Umma.
Sosai yake kuka yana faɗin mu yafe masa, ya faɗa mana dama ashe da asiri Inna ta aureshi sai yanzu alkadarinta ya karye, garin zuwa neme-neman asiri da take yi ta karɓo wani magani wanda ke da sharaɗi idan za a yi amfani da shi shine fa ta kuskure, dama kuma sharaɗin duk wanda ya kuskure to hauka ne, da ta haukace ne tayi ta tonawa kanta asiri.
Cikin kuka yake fadin cewa alhakin Ummata ne ya kama shi, dama shima tunda fari asirin ya yi mata a lokacin da ya ganta yaji yana sonta har ta bijirewa Iyayenta saboda shi.
Hmm! Wane dare ne jemage bai gani ba, ai sai na mutuwarsa. Ba zan iya rikeshi a raina na kasa yafe masa ba, ko babu komai ya taimakawa Ummata wajen killaceni a waje guda na tsawon shekaru, don haka Ni dai nace na yafe masa. Ita ma Umma da aka kira a waya tace dama ba ta riƙe shi a zuciyarta ba ta yafe.
Hajiya Kaka ta so yin masifa na ja ta muka koma cikin gida. Maƙudan kudi na ɗebo na kawo masa tare da faɗin duk sanda ya shiga cikin wata damuwa ya neme mu za mu taimaka masa, don na fuskanci yana cikin wahala sosai duba da yadda ya zama kamar tsohu saboda jigata.
A takaice na ba shi labarin abin da ya faru tun bayan barinmu gidansa, aikuwa kamar na ce ya cigaba da kukan, haka ya dinga yi hade da surutan da na sani. Daƙyar dai aka samu ya tafi.
Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na tabbatar ya fita a gidan, lallai wannan rayuwa ba komai bace. Shiyasa zai fi kyau mutum ya shuka alkhairi don shi kadai zai dinga bibiyarsa ko bayan baya ban ƙasa haka sharri ma idan mutum ya shuka.
A tsaye na iske Abdallah a ƙofar shiga falon yana tsaye yana kallona cike da murmushi a fuskarsa, kaina na sunkuyar ina ƙoƙarin rabawa ta gefensa na wuce, hannu ya saka ya tare ƙofar yana kallona.
"Nana Hauwa! Ina sonki, za ki aure Ni?". Na tsinkayi maganarsa kamar daga sama.
Kai na sunkuyar kawai tare da rufe fuskata da hannayena, abin da ya faɗa ya sake maimaitawa. Don haka na gyaɗa kai kawai, hannu ya cire daga inda ya tare ƙofar, aikuwa na shige da gudu cike da farin cikin da na kasa tantance menene.
Cikin lokaci ƙanƙani soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninmu, wanda har ba ma iya ɓoye son juna ko a gaban waye. Iyayenmu sun yi murna sosai don haka aka yi mana baiko aka tsaida ranar aure.
Alhamdu Lillah! Shine abin da nake furtawa a koda yaushe saboda ni'imar da Allah ya wadata ni da ita bayan jarabawar rayuwa da na shiga a baya. Na sake gaskatawa cewa lallai komai na duniya mai farawa ne kuma watarana zai gushe.
Tsarki Ya tabbata ga Ubangijin Talikai, wanda ke jarabtar Bayinsa kuma ya samar musu da maslaha. Allah Ka ƙara dubban salati ga Masoyi Mai cetonmu Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama, Ahali da Sahabbansa da kuma sauran wadanda suke kan tafarkin koyarwarsa har zuwa ranar busa ƙaho.
Tammat Bi Hamdullahi! Da wannan na kawo ƙarshen Littafin Jiddatulrahman wanda ya kasance labari a gajerce. Abin da na rubuta daidai Allah Ya ba ni ladansa, inda na kuskure kuma Allah Ya yafe min.
Ba zan gushe da yi muku godiya ba makarantana, ina riskar saƙonnin addu'o'i da fatan alheri daga gareku, Allah Ya saka muku da mafificin Alkhairi, Allah Ya tabbatar da wannan zumuncin na mu har Aljannah Firdaus.