CHAPTER 6
by @deejasmah
WANI RABON..................🦋🦋🦋
Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)
Elegant Online Writers ( E.O.W)
In dedication to all single ladies out there...............❤
Are you a writer or an aspiring writer but without an association ? Are you that one that writes but doesn't have much shares and less audience ? Have you been dreaming to be that great writer but you don't have anyone to review your write-ups and rate it ?
Then your time to rise and shine is here as Elegant Online Writers have given out that opportunity to young and talented writers to join its great platform to work towards achieving one's goals at the best rate you can ever get
Pay 1k per form and the next thing is you are already in the platform !!
They offer training and lectures for writers to make sure your write ups are error free and to prepare you for becoming that your dream writer
Contact
@ gimbiya : ***
@ Nimcyluv: ***
Don't miss this opportunity!!!!!!
CHAPTER 6 ( I wish I could )
Tun last week Tuesday rabon da in ga mai kama dashi hakan bai wani dameni ba don ba ya gabana harkokina na cigaba dayi don banda damuwa ko kad'an yau ina shigowa da sauri don nai lattin zuwa office d'in a daidai parking space naci karo da k'amshin turarenshi mai mugun dad'i lumshe idona nai sai na jiyo sallamar shi a bayana
Waigawa nai na ganshi yana fitowa daga motarshi yana murmushi d'an tsayawa nai ina amsawa k'arasowa yai yana cewa " yau dai munyi latti " a gajarce nace " aikuwa dai " murmushi mai sauti ya kuma sakewa kafin yace " can i see you today after work " shiru na d'anyi kafin nace "anya kuwa ?"
"Don Allah kiy hak'uri i won't take much of your time " ya fad'a a daidai sanda muka hau stairs " OK " kawai nace masa " thanks much " he said grinning from ears to ears kamar na bashi wata gagarumar kyauta girgiza kai kawai nayi ina wucewa cikin office d'in kasancewar mun iso daidai floor d'in
Ina sauri zan fice daga wurin ni na manta cewa zamu had'u dashi kasancewar yau mun shiga local markets tareda manyan maaikatan the work is really interesting yet tiring yau naga many local markets da muke dasu a kaduna sannan kuma nasan location d'insu saidai kuma aikin ba na raggo bane don yawo ake sha ba kad'an ba don haka a mugun gajiye nake jan k'afa kawai nakeyi
Ina isowa daidai bakin complex d'inne na jiyo mutum a bayana da sauri na tsaya ina mai waigawa shi d'inne d'an dafe kai nayi ina kallonshi murmushi yayi tareda cewa "if u won't mind can i offer a ride?" girgiza kai nayi tareda cewa " thanks for the offer but I'm afraid that ........." Katseni yayi da cewa "issokay ......... Ya alk'awarinmu?"
"Why not talk tomorrow......... it's already late " na fad'a ina narke ido wani ajiyar zuciya ya sauke kafin yace " ya na iya wannan kallon ai dole ya hanani miki musu " baki na tura inajin kamar in zaneshi nisawa ya sake sannan ya cigaba " ok tomorrow by what time and where " d'an shiru nai ina tunani zuwa can nace " at the secretariat after asr " gyad'a kai yayi yana cewa " thanks dear Allah ya kaimu goben " wuce shi nai ba tare da na tanka ba ina rolling idanu cikeda jin dad'in rabuwa da shi kallonshi da tambayoyin shi
Zaune muke bayan ishai muna fira da Areepha k'asa k'asa yayinda fav yake kan dining yana kallon anime mu kad'ai ne a gidan dan Mamie tana clinic kasancewar yau night takeyi labarin Salem nake bata kallona tai tareda cewa " Addah don't tell me you are turning down this man ? " kallonta nai tareda cewa " in banyi turning d'inshi ba u want me to disappoint my self ?, Baby that's the only solution for my heart "
" Addah baa cire hope fa a rayuwa who knows ko Allah ya kawo k'arshen wahalarki ne? " girgiza kai nayi cikeda sarewa nace " baby mun dad'e muna wannan tunanin but were proved wrong,kar ki manta da irin abinda ya faru a baya shin hakan bai ishemu karatu ba ?"
Miyau ta had'e idanunta sun fara kawo ruwa niko na cigaba da cewa " I'm no more young babe irgen da ake mun ya isheni hakan shi kanshi nasan in yasan wacece ni rabuwa dani zaiyi balle 'yan uwanshi wainda sune suke da iko akanshi d'in "
Hawayen da ya zubo mata ta share tareda cewa " na sani Anty but u should try to hear from him first tell him everything about you,kiji mai zai ce don't conclude maybe ba za a samu matsala daga side d'inshi ba " girgiza kai nayi dan nasan ba zata tab'a fahimtar mai zan fad'i ba tunda she's not in my position
Wayata na d'auka Ina kunna data don ban san me zan ce kuma ba daga nan kuma muka cigaba da fira jefi-jefi har 10 tayi muka kashe kayan kallon muka nufi d'aki don yin bacci
Washegari ni ce last person da na bar gidan Fav da Areepha sun wuce school ita CBS take zuwa shikuma waec suke shirin yi yanzu hakan kammala gyaran gidan nayi tareda tabbatar kammaluwan lunch saboda Mamie dai sai ta huta kan ta fito
10 dai-dai na shiga secretariat d'in bamu kammala abinda mukeyi ba sai around 3 mosque muka nufa da bestie hutawa mukayi bayan munyi sallah sannan muka fara lissafin abinda zamuci a dai-dai lokacin ne wayata tai k'ara dubawa nayi unknown number ne yake kira wanda hakan yasa na jinkirta kafin nai picking
" Hello princess " aka fad'i daga d'ayan side d'in lumshe ido nayi don na gane mai magana Salem ne " hello there " na bashi amsa " how are you doing today " ya tambaya a gajarce na bashi amsa da fine don bansan damu " Ahmmmm......kina ina ne ?" He asked
Cikeda k'osawa nace " it isn't yet time ai, I said after 4 .....Abi?" ina jiyo murmushin shi ta side d'in turo baki nayi cikeda jin haushin shi I'm surely getting r*d of him this very day takuran tai yawa
"Yeah you said so.......I'm just asking sorry!" hararar wayar nayi kamar yana wurin "muna masjid" na sake bashi amsa muryan nan a cushe kana ji kasan dole nake maganar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "okk dear " yana fad'in hakan na kashe wayata don banda abin ce masa
Kallon bestie nayi da ta zura min ido ware mata nawa idanuwan nayi tareda cewa " what?" harara ta tayi tareda cewa " you asking me?! U know quite well that what you are doing ain't good night ?,meye laifin wanda ya nuna yana sonka "
Lumshe ido nayi a hankali ina cewa " you blaming me?, well I didn't see anything wrong with what I'm doing i don't want to get attached only for me to be rejected at the end! Wanda nayi a baya ma banji da dad'i ba"
"But babe not all men are the same,some will stood up with you through good and bad wasu suna jure komai for love why not give Salem a try may be he's the right man for you " ta fad'a tana mai dafamin kafad'a cike da son k'arfafa min gwuiwa
Dariya na kwashe dashi Ina cewa "Men from tales right? Ai na riga na farka daga wannan dogon baccin nawa........ Those kind of men don't exist no more....."
Sakin baki tai tana kallona kafin tace " don't lose hope jare......give love another chance" girgiza kai nayi a daidai sanda wani kiran ya sake shigowa wayata " I wish i could........" Na fad'i ina mai kara wayan a kunnena Salem ne wai yana waje
Ce mata nai bari in dawo fita nai na sameshi jingine da motarshi hannunshi d'auke da leda sallama nayi na tsaya ina kallon k'asa ledar hannunshi ya mik'o min yana cewa " I come to deliver this.....sak'o daga mijin k'awarki zan dawo after asr akan tamu maganar" amsar ledan nayi Ina cewa thanks
Juyawa nai na shige ina mai jin idanunshi a kaina...................
Deejasmah❤🥀🦋